Showing 39001 words to 42000 words out of 182942 words

Chapter 14 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

tare da fad'in kinci gidanku, y'ar banza.


Ibtisam dariya ta Fara, "KABIR yace kina tare da Granny ne?


Tace eh muna tare duk ta ishemu da surutu


Jin haka yasa Granny Jan tsaki tare da fad'in zanyi maganinki, kanki zan dawo yanzu, "tunda miskili dai baida farin jini anki bashi mata, "Dan bai iya fulatanci ba


Ibtisam sallama sukai da kabir suka zauna suna fira da Granny, inda Granny take basu shawara akan suyi aure, domin Sun tsufa a gida


Granny tace Wlh Idan kuka je jami'a kallon y'an iska za'a dinga muku, "kuma a jami'a a nan yara ke lalacewa, baki ga yanda miskili ya koma ba ya fetsare ya koma mara mutunci ba? Ana fad'a yana fad'a, dan banza mara kunya


Zarah tace Granny, shifa university ba haka yake ba, mutane ne suke mishi wani irin kallo, duk da akwai wanda suke lalacewa a can, amma mu Granny kiyi mana kyakyawan zato.


Uhmm Granny tace tare da fad'in nidai Ina baku shawara Wlh ku fito da maza kuyi aure tun Kafin lokaci ya k'ure muku ,"domin matan da sukai karatu basu cika samun mijin aure ba


Ibtisam tace injiwa? Mata nawa sukai aure Bayan sun kammala karatu? Kai Granny waike wake fad'a miki wannan labarin kanzon kurege dinnan ne?..


Granny tace uwaki ke fad'amin, "ke bakya ganin abunda ke faruwa ne a duniya? Ai nasan Kun San komai dake wakana, "yarinya zata tai karatu saita gama babu mijin aure, daka wannan yazo ya dauketa sai wancan yazo, in tayi Sa'a ta samu miji Toh sai kuga tsoho ne komai mata..


Dariya Zarah ta saki tana fad'in Kai granny wannan sharri haka? "Wanda ya fad'a miki wannan maganan ba gaskiya ya fad'a ba..


Ibtisam tace fad'a mata dai.


Tsaki Granny tayi tare da fad'in abunda yake a zahiri, maza yanzu basa son auren y'ar jami'a, domin suna ganin kaman idonta a Waye yake Sosai, kuma haka dinne "yara an turasu wani gari karatu babu Mai kwaba a can AI dole suyi ta tsula tsiya, iya son ransu


Ibtisam tace Granny ko ina akwai y'an banza akwai na Allah, "karki manta karatun y'a mace yana da matukar muhimmanci," Kema da kinyi karatu da yanzu tayu kina da ma'kami a gwamnati.


Dariya Zarah ta saki tace aikuwa, da yanzu hala kina office d'inki zaune, kina sanye da glass kina zuba turanci


Tsaki Granny taja tana fad'in AI gwara da Banyi ba, "Wlh nidai na fad'a muku ku fito da mazajan aure tun lokaci bai k'ure muku ba, "domin indai kuka tafi jami'a babu aure toh samun mazan aure sai kunji jiki, Inba so kuke ku auri tsoho ba sa'ana ko kuma mai mata biyu ko uku


Dariya ibtisam tayi tace ai gwara in zauna banyi aure ba, da in auri tsoho ko Mai mata ba, "Kut nifa ban son kishiya Wlh.


Granny tace in bakya so fito da miji tun kan ki tafi jami'a, inko kikai wannan kuskuren damai mata zaki k'are in kinyi Sa'a kenan, in kuma bakiyi ba ki k'are da tsoho Sa'a na, ko wanda ya girmeni mara hakori


Ibtisam da zarah dariya suke Sosai suna fad'in lallai kam wa yaga mara hakori, "zarah tace Tashin hankali


Granny tace kuna d'auka wasa nake koh? Shikenan ai


Karan wayar zarah yasa ta d'auka tana dariya domin taga Sunan Najeeb ne, tace Bros har ka tafi ne?


Mai yakon ya bata amsa sai yace Maiya kaiku yola?


Tashi tayi ta fita Tana fad'in Wlh munje akan maganan aurenka ne


Yace what?


Tace kwantar da hankalinka bros ba'a d'aura ba.


Yace what happen?


Labari ta Fara bashi yanda akayi


Yace better domin inda an d'aura nan take zan saketa saki uku


Zarah tace uhm


Kashe wayarshi yayi gaba d'aya danya samu ya kwanta ya huta koda ya kwanta kasa bacci yayi domin ya gaji gashi ya kora Gina data mishi massaging, tunani yai tayi Kala Kala


Lallai shida ya k'ara zuwa Nigeria saiya dad'e tunda Idan yazo har Dad na biyema wannan old woman din , wai shi za'a d'aura ma widow kuma Mai yaro yar kauye, "murmushi yayi tare da fad'in god forbid, "bazan iya shiga ramin da wani ya shiga ba, kai never, inda wacce zanyi wani abu da itane da sauk'i, amma aure kam never in auri bazawara, ido Ya lumshe lokaci d'aya yana Mai jin zafin abunda akaso mishi, "taya zai auri bazawara wacce ta tabayin aure?


Murmushi ya saki lokaci d'aya tare da fad'in, I think inna tashi aure bazan fad'a musu ba sai dai suga mata, koda zanyi aure secret marriage zanyi, Danni inna auri mace bazan saketa ba, domin inna rabu da people will say my ex wife, I won't let that happen, ina da kishin abunda nake so, gwara ace ta mutu akan ace na saketa har a kirata da ex wife d'ina, tsaki yaja tare da fad'in ni bama auren bane a gabana, Indai Mata ne gasu nan like Recharge card everywhere you go, murmushi yayi tare da fad'in na them they rush us, so why will I marry? In ajiye abunda zai daman no bazanyi wani aure ba, ban son takura.....
















Read and leave it, don't share to anyone


*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*










Washe gari tunda sukai sallah asuba suka Kama hanya, domin so suke su isa da wuri,"ibtisam taso a tabi Abbanta su koma tare, "amma Dad yace dole tare zasu koma dan zasu wuce Zaria maganan registration d'insu hakan yasa ta bisu Abuja din suka koma tare.


Sai wajan yamma suka k'arasa gaba d'aya a gajiye suka shiga gidan, koda suka isa su ibtisam d'akinsu suka shiga, "kai tsaye toilet ta nufa dan tayi wanka ko zataji dad'i,"Tana fitowa itama Zarah ta nufi toilet din dan tayi wanka.


Bayan sun kimtsa suka nufi falo dan suci abinci, kowa na gamawa ya wuce bedroom dan hutawa, "Granny kam fad'i take Ahmad ya huta dabai bimu ba, "ni ku bani man zafi inje in shafa a kafata wannan wahalan zama haka. "Niko wancan karan da naje yola bansha wuya irin haka ba, haka dai ta tafi tana mita waita gaji kafafunta na mata ciwo Sosai.


Washe gari da safe wajan 11 su ibtisam suka farka, kai tsaye falo suka nufa, "Mum suka gani tace sai yanzu? Ai tun dazu na shiga d'akinku naga baku farka ba,"gaskiya kunsha bacci ko duk gajiyan ne haka?


Zarah tace Kai mum wlh akwai gajiya, irin wannan tafiya haka.


Gaida mum ibtisam tayi, "Mum amsawa tayi cikin sakin fuska, tare da fad'in ansha hanya, "dariya ibtisam tayi tare da fad'in kai Aini mum ban taba yin tafiyan da nasha wuya irin wannan ba.


Zarah tace ina Granny ne wai?


Mum tace itama tana d'aki tana bacci, bata farka ba, har yanzu.


Kai tsaye d'akin da Granny take ibtisam ta nufa,"ganin Granny tayi tana bacci, yanda take baccin harda munshari wannan shine zai tabbatar ma mutum da cewa lallai Granny a gajiye take Sosai, dariya ibtisam tayi sannan ta fita falo dan tayi breakfast danta Fara jin yunwa.


Granny ba ita ta tashi ba sai wajan karfe d'aya lokacin ana kiran sallah azahar,"Bayan ta farka ta Fara mi'ka tare da fad'in kai yau nasha Bacci, toilet ta shiga tayi wanka, tana jan y'an kafafunta.


Granny falo ta fito inda ta iske su mum dasu ibtisam da Zarah, "tace shine baku tasheni ba? Kuka barni inata sharar bacci haka.


Mum gaida Granny tayi, "Granny amsawa tayi tare da fad'in Sannunku Ya gajiyan hanya?


Mum tace Alhmdlh, hanya babu kyau babu dad'i.


Granny zama tayi tana fad'in ina yaga dad'i, gaba d'aya jikina tsami yakemin Sosai wlh, damma na shafa man zafi, kar kiji yanda kafana ke zugi kaman nayi tafiya a k'asa, lokaci d'aya kuma "taja tsaki tare da fad'in "duk wannan uban wahalan babu biyan bukata, "ni ko shi miskilin ne yaje kauye yace karsu yarda da wannan auren dai?


Zarah ta kwashe da dariya tare da fad'in "kai Granny taya zaije kauye, shida ko hanyar bai sani ba, inma yaje Mai zaice musu yazo yi? Shida baya jin Hausa, "balle fulatanci, taya ma zai san kauyen da kika dibo matan? mutumin da yake America yanzu.


Granny tsaki taja tare da fad'in kibar miskili ni gaba d'aya ban yarda dashi ba yanzu wlh, amma zan gamu dashi nan bada dad'ewa ba, "zan duba mishi wata matar kwanan nan wlh, zanyi maganin shi, dan banza, mara kunya.


Yau Monday kuma granny a yau zata koma Kano, "su kuma su ibtisam a yau zasu wuce kaduna domin registration d'insu.


Granny driver ya kaita har Kano, yayin da driver din daddy shi kuma yakai su ibtisam Zaria, a hotel suka sauka, inda suka fara kuciba kuciban registration, basu wani sha wuya ba, domin dad yama VC magana, VC ya had'asu da wani, cikin kankanin lokaci sukai komai har an fara shiga Aji an fara lecture.


Su Zarah Abuja suka koma,inda Zarah ta had'o kayanta domin Sun zamu d'aki a cikin skul din su hud'u ne a cikin d'akin, kwanan su d'aya,"suka nufi Kano inda itama ibtisam ta had'o Nata kayan Washe gari zasu koma


Ibtisam na zaune a tsakar gida da Granny da Zarah, suna fira, "Granny tace ku yanzu wannan makarantar kun dage sai kunje koh?


Ibtisam tace Kai Wlh Granny kina da mita, ke kullum magana d'aya kar muje karatu kar muje karatu, haba mana, ki barmu dan Allah


Granny tace kinci uwarki, ai dole in fad'a, tunda ke baki San ciwon kanki ba, dole kice haka, wlh Ina guje muku rasa mazajan aure, "Dan naga ke kabiru kaman bada gaske yake ba, domin kuwa inda dagaske yake aiya kamata ya turo, nifa yanzu haushi yake bani, sai shegen kira a waya, daka zuwanki jiya jiya kin hanani bacci da shegen waya, wlh gwara kibar kulashi in bazai turo ba.


Ibtisam tace au yau kabir dinne ke baki haushi? "Wai Mai yasa ke Granny baki da gwani ne? Daka kice mutum kaza sai kaza, waya had'ani da Kabir din Inba ke ba.


Granny tace eh muka had'u dai a hanya, kuma Aiko da nace ki kulashi AI danya fito ne Ayi aure, badan yazo ya kashe miki kasuwa ba, shi bai fito ba baiba wasu waje ba, ni wannan ai mugunta ne wlh


Zarah dariya ta kwashe dashi tana fad'in lallai granny.


Itbisam tace rabu da ita, "itama ta dage saina kula Kabir din, harda wani in amsan Mata number, shine yanzu take kushe shi.


Granny tace aikin banza da hofi Aini da nace ki kulashi a tunani na zai fito ayi biki, amma har yanzu naji shuru.


Ibtisam tace koma dai miye nidai ba damuwa ta bace, kabir dai tunda kika had'ani dashi, dole ki barni dashi, aure kuma saina gama karatu za muyi sh.....


Innalillahi'wa inna ilaihirajiun Granny ta zabga salati tare da tafa hannu, tare da fad'in a ina zaki gama karatun? Wlh badai a gidan nan ba, keda kikai min alkawari za kiyi aure in miskili yayi aure.


Ibtisam tace ai cewa nayi in yayi, toh yanzu tunda baiyi ba, nima ban shirya ba, Kinga in yayi sai nima inyi.


Granny tace zanyi maganinku Wlh kuwa, zan baku mamaki, zan shuka muku tsiya wallahi in baku fito da mazaje ba.


Zarah tace Granny inaga sai Kinje masallaci kin bada sadakan su Gamai bukata


Granny tace yauwa shawara Mai kyau h....


Ibtisam takai ma Zarah dukan wasa tare da fad'in kin San wannan tsohuwar zata iya, wlh ki bari.


Granny tace ai zan baki mamaki wlh


Ibtisam tace kullum haka kike fad'a, dama kin daina fad'in haka wlh


Granny ta galla mata harara tare da fad'in zaki gani Ai, wannan karan bada wasa zan miki ba


Ummi ce ta fito hannunta d'auke da tray, tasa plate guda uku, ajiyewa tayi, faten tsaki ne wanda yaji alaiyahu da Naman rago, ta ajiye ma Granny a gabanta sannan tace ma Zarah "gashi ki d'auka zarah kisha da zafinshi Kafin ya huce


Granny tace inada yaji cikin jakata a d'aki, d'auko min.


Ummi tace bari in d'auko miki, "kai tsaye d'akin ummi ta shiga sai gashi ta kwala ma ibtisam kira.


Da sauri ibtisam ta tashi tare da amsawa.


Koda ibtisam ta shiga d'akin kwalin wayar da kabir ya bata ta gani a hannun ummi.


Ummi tace waya baki wannan wayar? Na tabbata inda babanki na abuja ya baki zaki fad'amin waya baki?


Ibtisam tace ummi Kabir ya bani.


Ummi tace Waye Kabir?


Ibtisam tace shine wanda ya taba zuwa, granny tace in fita, harya Kawo min su chocolate, kika ce bakya son Ina am....


Ummi ta daka mata tsawa tare da fad'in Yimin shuru mara tunani, ke yanzu har kinyi girman da zaki dinga amsan abu wajan samari, har a baki kyautar waya koh?


Mai Abbanki yace miki akan ri'ke babban waya? Yace baya sonki da babban waya, Shine har kin iya amsan na saurayi koh? Yayi miki kyau, "ummi fita tayi wayar na hannunta ta fita takai ma Granny yajin ta koma d'aki ta ajiye wayar, sannan ta fito


Ibtisam kam cikinta ya dura ruwa, domin tasan yau kashinta ya bushe Idan Abba yaji labari, gaba d'aya kasa fitowa tayi daka d'akin domin jinta tayi zazzabi ya kamata lokaci d'aya.


Granny tace Wai ina takwara tane? tabar abincinta a bud'e saiya huce, "kwala mata kira Granny tayi tare da fad'in ibtisam kina inane?


Fitowa tayi kamar wacce kwai ya fashe mawa a ciki, tace Granny gani.


Granny tace kizo kisha wannan fatan koh saiya huce baki shaba?


Ibtisam tace na koshi bana jin yunwa


Zarah tace Kai Kinji yanda yayi dad'i kuwa? Wlh kisha kiji


Ibtisam bata k'ara cewa komai ba, sannan bata d'auki faten ba, sai zama da tayi tana kallonsu Suna cin abincin suna fira .


Ummi kam ko kallon ibtisam batai ba, Illa faten ta da tayi tasha ,Tana fira da Zarah.


Bayan sun kammala, ana kiran sallah magrib duka suka tashi sukai ciki, domin yin sallah, ibtisam na ganin ummi ta shiga d'akinta ta bita tana mata magana akan tayi hakuri da....


Ummi ta dakatar da ita tare da fad'in fitar min a d'aki sallah zanyi banda lokacin magana yanzu, ummi na fad'in haka ta shige toilet dan tayi alwala.


Ibtisam ji tayi kaman tayi ihu dan takaici, tare dayin data sanin amsan wayar da kabir ya bata tayi, lallai inda tasan hakan zai faru data maida mishi tun Farko, yanzu Allah kad'ai yasan Mai Abba zai Mata in Ummi ta fad'a mishi, "na shiga uku yau, wani hawaye ne ya zubo mata a ido Mai zafi tare da tunanin wani irin hukunci zata fuskanta yau wajan Abba in yaji wannan batun


Sai wajan 9 Abba ya dawo Gida, "tunda ibtisam taji ya dawo ta kasa zama, gaba d'aya a tsorace take, dan tasan yau ta shiga uku wajan Abba, "wani abun mamaki har wajan 11 Abba bai kirata ba, hakan yasa tace Ummi bata fad'ama Abba ba, ko kuma ta fad'a Mai yace babu komai, wannan tunanin da tayi shine yasa lokaci d'aya taji ta Fara jin yunwa, wanda sai yanzu ta tuna bata ci komai ba, wanda da bata jin yunwa din gaba d'aya, "fita tayi inda taga Abba a falo Wanda batai zaton zata ganshi ba, "yace mamana d'auko mun ruwa.


Tace toh Abba, "ibtisam dad'i ne ya cikata ta tabbata babu abunda ummi ta fad'ama Abba domin tasan inda ta fad'a Mai dasai ya Mata magana, "amma yanda ya Mata yanzu ya nuna mata babu komai hakan ya mata dad'i Sosai


Koda ta kawo ma Abba Ruwa, baice mata komai ba, harta koma kitchen ta d'auko abincinta ta nufi d'aki Abba na nan zaune a falo yana kallo.


Hakan yasa ibtisam yin bacci cikin kwanciyan hankali ba tare da shiga damuwa ba, ko tsoro ba, "Dan tasan Abba bai San komai akan wayar da uummi ta amsa ba


Washe gari da safe , koda ibtisam ta tashi ita ta d'aura abincin safe dan kawai ta faranta ma ummi duk da wani lokacin dama takan d'anyi mata.


Ibtisam doya dakwai tayi da tea ta dafa Lipton dasu citta da Kanin fari, sannan ta juye cikin flask, takai falo ta ajiye akan center table


Koda ummi ta fito ganin ibtisam ta Gama komai, yasa ummi cema ibtisam sannu da aiki?


Ibtisam tace yauwa Ummi Ina kwana?


Ummi tace lafiya kalau


Nan ummi ta koma d'aki Jim kad'an saiga Abba ya fito ya zauna ya faracin abinci, bayan ya kammala yace Ummi ta kira Mai ibtisam.


Ummi tace toh tare da kwala ma ibtisam kira.


Ibtisam amsawa tayi tare da fad'in na'am ummi gani nan, "bayan ibtisam ta fito falon gabanta taji yana fad'i domin irin kallon da taga Abba yana yi mata,.


Gaida mahaifin nata tayi, ya amsa fuska d'aure babu annuri balle wasa a cikinta


Zama tayi a kujeran dake kusa da ummi tace gani Ummi.


Ummi tace babanki ke kira, bani ba.


Abba ya jefo mata tambaya Waye Kabir?


Dam gabanta ya fad'i, tare dayin k'asa dakai, "Abba ya daka mata tsawa tare da fad'in ba dake nake magana ba? Waye Kabir nace?


Cikin in Ina tace mun had'u dashi ne, nida Granny ranan zamu kasuwa.


Abba yace shine ya baki waya kika amsa koh?


Kanta na k'asa tana hawaye


Abba yace Ina son kice Ina son ganinsa, aure dai kike so za kiyi ki kirashi kice Ina son ganinshi, tunda har kin iya had'uwa dashi ba tare da ya nemi izinin iyayenki ba.


Granny ce ta fito tana fad'in fad'a mata dai, gwara yazo asan abunyi, danni nafi son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login