Showing 108001 words to 111000 words out of 182942 words
Chapter 37 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
ya amshi kaddara data fad'a mishi....
Yana zaune shi d'aya Bayan ya dawo daka office, direct d'akinshi ya shiga ya zauna
Hafsat ce ta shigo cikin d'akin ta sameshi idon shi, na kallon k'asa
Kiran sunanshi tayi da my barrister
D'agowa yayi tare da kallonta, lokaci d'aya kuma ya kuma yin k'asa da kanshi.
Dan murmushi tayi tare da fad'in kazo kaci abinci, naga tun d'azu baka fito ba
Kabir yace no am OK bana jin yunwa
Hafsat shuru tayi tana kallonshi Kafin ta kuma cewa, dan Allah ina son ka cire komai ka manta da komai duk da nasan is not easy but Ina son ka sani am your wife, inada hakki a kanka, koda bakai min komai ba ina bukatar fira dakai, ina bukatar dariyanka Ina bukatar yin abubuwa dakai alot, you are my husband plz kabir ka tausaya min kaji tausayi na, Nasan baka sona amma ina son ka amsheni a matsayin kaddara, bazance dole saika soni ba, but plz ka dinga nuna min caring plz am begging you..... Sai kuma tasa kuka mai ban tausayi
Kabir shuru yayi amma jikinshi yayi sanyi which yasan abunda hafsat ta fad'a gaskiya ne, tabbas Tana da hakki a kansa, in ba haka ba, yasan Allah bazai barshi ba, Allah zai kamashi, domin ya tauye mata hakki
Kabir d'ago dakai yayi tare da fad'in hafsat kibar wannan kukan, insha Allah daka yau I will change
Kamota yayi tare da d'agota tsaye yace let go and eat
Hafsat ba k'aramin dad'i taji ba, Sosai, tun daka wannan ranan KABIR ya canza ya fara sakar ma hafsat, yana biya mata duk wata bukata, kuma yaji dad'in daya sameta a budurwa domin saida jini ya fito ranan daya sadu da ita, duk da bako wace mace ce ke jini ba.
Kabir ya sakar ma hafsat Sosai yana bata kulawa, sai dai fah ya kasa sata cikin zuciyarshi domin ibtisam ce kad'ai a cikinta
Itama da kanta hafsat din tasan haka, and tana matukar kishin ibtisam Sosai, domin tace saboda ita ne yasa mijinta har yanzu baya nuna mata tsan tsar so, sai dai yayi mata fake love
Hafsat tana kishin ibtisam Sosai har take mata fatan dama tabar duniyar kowa ya huta, a cewarta inta bar duniya ai dole ya cireta cikin ranshi
*ZARIA*
ibtisam bacci take Sosai sai wajan 10 ta farka tare dayin mi'ka, ta bud'e idonta, lokaci d'aya kuma ta tashi da sauri tare da kallon d'akin taga najeeb baya nan, a hankali ta furta where is he??
Tashi tayi ta sauka akan gadon d'akin tare da nufa kofa ta jita a rufe, tsaki taja tare da kallon kofar toilet tace ko yana ciki ne??
Komawa tayi ta zauna, jin kanta na Mata ciwo yasa ta tashi danta had'a tea, tasha
Tana cikin zuba madara aka bud'e kofar, da sauri ta kalli kofar taga najeeb ne ya shigo cikin d'akin, cikin ranta tace A Shema baya nan, ajiye spoon din tayi ta nufi toilet da sauri ido ya bita dashi
Koda ta shiga toilet brush tayi tare da wanke fuskanta sannan ta fito ta ganshi yana tube kayan jikinsa, kallo d'aya tayi mai ta kauda ido, gaba d'aya tunda ya shigo kamshin turarenshi ya gauraye d'akin, ta rasa ina yake boye turaran, dan tsaki tayi mara sauti, tare da had'a tea d'inta zama tayi akan kujeran d'akin ta Fara sha Tana kashe ido alaman tana jin dad'in tea din
Kallonta najeeb yayi tare da tabe baki yace mai zaki ci??
Kaman jira take yayi mata magana tace waina da miya Asa Man shanu a ciki
Najeeb kallonta yayi lokaci d'aya kuma yaja tsaki tare da fad'in a Ina za'a samo miki? Kin San a hotel basa yin waina, so just change it
Ibtisam tace ana sai dawa a wani waje, idan aka duba za'a samu
Najeeb yace I said no, baza kici ba, just tell me mai zaki ci??..
Ibtisam tayi rau rau da ido tare da fad'in na koshi bana cin komai
Najeeb kafad'a ya d'aga alaman I don't carry, cikin kine ba nawa ba
Ibtisam ji tayi kaman ta buga mishi cup din dake hannunta tayi saboda takaici da haushi
Bayan ta gama shan tea din ta tashi ta shiga toilet ta dauraye cup din tare da fitowa ta ajiye, sannan ta koma tayi wanka
Koda ta fito da kayan jikinta ta fito domin ta manta bata d'auki Wanda zata canza ba
Najeeb ganin ta fito yasan wanda tayi domin yanda jikinta ya ji'ke da kayan da tasa, ganin ta dauki ledan kayan yasa yayi tsaki tare da fad'in idiot
Toilet ta koma tana duba wacce zata saka mai dan dama dama, gaba d'aya kayan sai a hankali, tsaki tai taja a toilet din tana fad'in nifa Wlh na gaji, miye na kawo ni nan ya ajiye ni ba tare da son raina ba, gashi inada lecture yau, tsaki ta kuma ja yanzu kowa yake son ya saka wannan kayan ya fita ohon mishi
Wata riga tasa wanda ta Kalli kanta a madubi, gaba d'aya rigan ana ganin komai nata, da sauri ta cire tare da fad'in Allah ya kyauta insa wannan in fita dashi
Wata ta d'auka itama dai duk sam makai,amma ita wannan Tana da Dan kauri sai dai samanta wajan nonon da tasa ana ganin tsakiyar nononta domin rigan akwai tsaga a wajan sai kuma ya kamata daka wajan cikinta zuwa duwawunta, rigan ta tsaya Mata dai dai giwa
Ta dad'e a toilet din kafun ta fito daka ciki Tana tafiya a hankali
Shikam NAJEEB kallo d'aya yayi mata ya kauda kai, domin baya son ya dinga bada kanshi ta raina shi, danshi bazai d'auki rainin taba
Ibtisam ganin baya kallonta yasa ta saki tare dajin dad'in hakan
Kiran waya yayi tare da fad'in shigo da kayan da muka siyo, yana fad'in haka ya kashe wayar, idonshi yakai kan ibtisam dake zaune ta juya mishi baya, gaba d'aya shape din duwawunta ya bayyana cikin rigan, wani irin miyau ya hadiye lokaci d'aya kuma yaji yana bukatar ya taba
Nocking akayi wanda yasa ibtisam ta waigo ta kalleshi, ido suka had'a Wanda ita yake kallo dama, da sauri ta tashi ta waigo domin taga mai yake kallo irin haka..
Wai gawan da tayi yasa nononta dake bud'e suka sauka akan idonshi, da yake dan duniya ne saiya basar tare da fad'in mai zaki ci?
Ibtisam tace na koshi nace
Yace OK tare da tashi danya bud'e kofar yana fad'in karki cemin kina jin yunwa anjima
Ibtisam Hararanshi tayi ta baya, cikin ranta tace kaji dashi nidai kawai Malam ka Mai dani skul
Najeeb bud'e kofar yayi ya amshi ledoji yazo ya ajiye sannan ya rufe kofar
Kallon ibtisam yayi tare da fad'in ga kaya nan, wanda zaki iya fita dasu
Ibtisam kallon ledan daya nuna mata tayi tare da tashi ta nufi ledan ta bud'e
Jallabiya ne guda biyar different colour and design gaba d'aya size d'inta ne, domin tana saka size 60 tayi mamaki daya kawo mata dai dai size d'inta
Kallonshi tayi wanda taga wayarshi yake dannawa, tace inada lecture 4 I have to go now
Najeeb kallonta yayi tare da k'ura mata ido, lokaci d'aya yace bazaki ba, skul din na hanaki zuwa daka yau
Ibtisam tace akan wani dalili? Nika bud'emin kofa in tafi
Najeeb yace saboda am your husband
Ibtisam tace husband indeed, sai Kuma ta saki dariya tare da fad'in am not your wife an d'aura maka ni by mistake, so just divorce me p....
Ganin ya taso yasa tayi shuru domin tsoran Karya taba ta, matsowa yayi gab da ita tare da janyota ya rukota da hannunshi huda d'aya, "matseta yayi yana fad'in repeat what you are saying right now
Ibtisam ganin idonshi na kanta yasa tayi saurin rufe ido..
Najeeb fuskanta ya kura ma ido wanda yake jin wani iri a jikinsa, ya rasa mai yasa in yana kallon fuskanta yake shiga cikin wani yanayi, lokaci d'aya ya fara K'asa da kanshi tare da k'ara d'agota yasa bakinshi cikin Nata ya fara kissing d'inta
Ibtisam kokarin tureshi take amma ta kasa Saida yayi kissing d'inta wajan 3mnt kafin ya saketa tare da d'agota ya k'ara matseta a jikinsa yana fad'in, ki daina bata ma kanki lokaci, me and you will live together forever, babu saki, daraja d'aya kika ci niba namiji bane Mai son tara mata da yawa da saina k'ara aure but may be nan gaba in naga wacce nake so in k'ara aure.....
Ibtisam tureshi tayi amma ko gezau baiyi ba.
Yace kina bama kanki wahala
Ibtisam hawaye ke zuba a idonta tace NAJEEB bazan taba zama dakai ba har abada, domin bana Sonka ban.....
Sakinta yayi tare da sha'ko mata wuya yace same with me, keda kanki kin San bana sonki, nafi karfinki har abada, niba type d'inki bane but what should I do? An cuceni an bani ke, tunda na yarda zanyi hakuri dake kema you must dole ki zauna dani
Ibtisam da NAJEEB ya shaketa hawaye ke zuban Mata shar shar tace Najeeb zaka iya Yimin Komai Amma Ina son ka sani, bana bukatar zama dakai, ka tausaya min ka sakeni Dan Allah ni nasan bama son juna ku..... Sakinta yayi tare da marinta k'asa ta fad'i tana kuka
Shiko najeeb gaba d'aya idonshi ne ya kad'a yayi ja alamun ranshi a bace yake
Yace I don't care Either you love me or not, is none of my business infact to hell with your love, the only tin I want you to knw is dat dole ki zauna dani, either you like it or not...... Dan shuru yayi kafin yaci gaba da fad'in and this should be the last and first time in your life da zaki k'ara confronting d'ina kice bakya sona, if that tin happen again..... Shuru yayi tare da lumshe ido, lokaci d'aya kuma ya bud'e yace only God knows what Will happen
ita dai ibtisam bata komai sai kuka, lokaci d'aya ya daka mata tsawa tare da fad'in keep quiet, nonsense
Batai shuru ba taci gaba da kukan
Lokaci d'aya yaji zuciyarshi na karaya domin kwata kwata ji yayi baya son jin kukanta, gashi taki yin shuru dan haka fita yayi daka d'akin
Ibtisam ganin ya fita yasa ta k'ara fashewa da wani sabon kukan ga kanta na Mata ciwo, wanda tasan yunwa ne, ga cikinta dake son ya fara Mata ciwo
Tashi tayi dakyar taje ta had'a tea, sha ta farayi da gudu ta tashi tayi toilet ta Fara kwarara amai kaman hanjin cikinta zai fita, zama tayi a akan bath Tana sauke ajiyan zuciya ga idonta daya firfito saboda wahala
Gaba d'aya bakinta taji yana mata d'aci, abinci taji Tana son ci, kuma dambu taji Tana kwadayi da zobo
Lokaci d'aya tasa kuka, tunawa da tayi NAJEEB ya fita gashi ya kulleta, kuka take Sosai ganin kanta yana k'ara Mata ciwo yasa ta tashi ta dauraye fuskanta tare da fitowa ta kwanta akan gadon d'akin, lokaci d'aya zazzabi ya rufeta Tana ta rawan sanyi, duk da ta lulluba da blanket
Shikam Najeen koda ya fita, zama yayi a reception tare da d'aura hannunsa akansa gaba d'aya ya rasa maike damunshi, tunda ibtisam ta shigo rayuwarshi Tana k'okarin ta canza mishi lissafi da tunani..
Gaba d'aya tasa yana abunda bayayi, Tana k'okarin kawo mishi damuwa cikin rayuwarshi, shi bai San miye tunani ba ko damuwa amma gashi yanzu ibtisam tasa ya fara wanda kwata kwata bayayi, kanshi yaji yana mishi ciwo, ciwon kai din Sosai dole tashi yayi ya koma ciki domin ya bukatar ya kwanta harya kusa zuwa kofar d'akin ya tuna da ya barta tana kuka sanda zai fita, tsaki yayi ya juya tare da kiran driver akan yazo su fita Dan baya son jin kukan nata ko kad'an
Ibtisam kam, bacci ta samu ya d'auketa
Najeeb bai dawo ba sai wajan 3 shima tunawa da yayi ya rufeta yasa ya dawo cikin sauri Bayan yayi mata siyayan abunda zata iya ci
Koda ya dawo ya ganta a kwance alaman tana bacci, sai yaji ta bashi tausayi a karo na farko, tare da fad'in yasan baccin wahala ne
Nufan gadon yayi Bayan ya ajiye Mata ledojin, zama yayi a kusa da ita tare da kallon fuskanta ya kura mata ido sai yaga kaman tana kyarma..
Taba jikinta yayi da sauri yaji zafi Sosai, yace fever, a hankali ya kira sunanta da ibtisam
Tace uhm, sai a sannan ya gane ba bacci take ba,
Yace baki da lafiya ne??
Bata bashi amsa ba
Ganin haka yasa ya d'agota tare da kamota yana son sauketa akan gadon, yace muje hspt a dubaki
Ibtisam tace plz ka barni I need only paracetamol, and food
Jin haka sai yaji ya k'ara jin tausayinta Sosai, ya tabbata tana jin yunwa Sosai
Yace OK ga waina nan na samo miki, zauna kici Bari inje in d'auko miki paracetamol a cikin mota
Zaunar da ita yayi tare da kawo mata ledar da aka saka take away, din waina din a ciki ya bud'e mata ledan kamshin wainar da taji yasa ta k'osa ta faraci ga kuma kamshin turaren najeeb din wanda take mutuwar so
ibtisam tun kafun yace taci ta faraci kaman mayya ci take Sosai,
Najeeb daya k'ura mata ido sai yaji ta bashi tausayi Sosai, lokaci d'aya ya nufi fridge ya d'auko mata Ruwa tare da fita danya d'auko mata paracetamol din tasha
Koda ya dawo gani yayi harta cinye kuma wainar Nada yawa, Abun mamaki ya bashi, nufanta yayi tare da bud'e mata maganin gudu biyu ya bata tasha, zata kwanta ya hanata tare da fad'in no tsaya kiyi kaman 10mnt saiki kwanta ba'a shan magani a kwanta
Ibtisam zama tayi lokaci d'aya kuma ta tashi, da ido ya bita ganin ta shiga toilet yasa ya kauda idonshi daka kanta, kwashe kayan da taci abinci tayi tare da sakawa a wata Leda ya fitar dashi waje
Koda NAJEEB ya dawo d'akin yaga Tana sallah, da alama sallah azahar take, tana cikin yi aka kira la'asar shima ji yayi yana son yaje masallaci yayi sallah a jam'i
Toilet din ya fad'a yayi alwala tare da fita Bayan ya rufe kofar
Ibtisam Bayan ta idar kwanciya tayi a wajan, yanzu taji dan dama dama zazzabin Ya fara sauka, ba k'aramin dad'i taji ba da taci wainar daya kawo mata ba, taji dad'in wainar Sosai.
Najeeb ne ya shigo d'akin, ganinta a k'asa yasa shi fad'in lafiya?
D'ago dakai tayi ta kalleshi Wanda suka had'a ido su duka, itace ta Fara kawar da idonta gefe tare da sauke wani irin ajiyan zuciya
Najeeb ido ya lumshe tare da fad'in ya zaki kwanta a k'asa? Keda kanki kike janyo ma kanki ciwo, kina fever and you sleep on d floor
Ibtisam bata kulashi ba sannan bata tashi ba
Ganin haka yasa ya dauketa cak yayi gado da ita
Shima kwanciya yayi a bayanta, tare da janyota ya rungumota da hannunshi
Ido ya lumshe yana wani irin sauke ajiyan zuciya, gaba d'aya ya rasa maike damunshi....
Ita kam ibtisam batai kokarin matsawa ba, domin tana shakar kamshin turarenshi Wanda take cewa ya boye ne, tunda duk ta fesa turaren nashi amma bata ji kamshin ba, sai dai a jikinsa take ji, kuma daka ya shigo d'akin take ji ko inya matso kusa da ita
Gashi wani abun takaicin duk yanda taso ta mishi Abu, saita kasa indai taji kamshin turaren nashi ita da kanta tana mamakin irin sauyin ta, amma tabi bama kanta macijin ciki ke damunta shine yake sata take irin wannan mugun cin, wanda ya wuce misali
Lokaci d'aya ta kira sunan Najeeb
Yace plz allow me to slp
Tace magana zanyi and you must listen to me
Najeeb tashi yayi ya zauna tare da fad'in mai yasa bazaki banni in huta ba, and kinsha magani Kema plz slp Quickly and allow me to slp too
ibtisam tace uhm nifa inada lecture 4 gashi time harya wuce
Najeeb yace tunda Kema kin San time ya wuce so just keep quiet
Ibtisam tace toh yanzu mai kake nufi dani? Ko a nan zanyi ta zama?..
Najeeb murmushi yayi tare da fad'in exactly that is what am thinking
Ibtisam tace Hmmm, nidai Dan Allah ka barni in tafi
Najeeb yace ashe kin iya ro'kan mutum
Ibtisam tace uhm I can apologize Indai zaka barni, inma kana son I should go on my kneel and apologize I can do it, indai zaka barni in tafi I will do what ever you ask
Kallonta yayi tare da fad'in saboda kije ki dinga hulda da maza right????
Da sauri ta kalleshi tare da nanata Kalman hulda da maza as how??
Najeeb tashi yayi tare da fad'in I tell you I will never allow you to go to that skul har sai naga kinyi ciki.....
Ido ta zaro waje tare da fad'in ciki? Gabanta taji ya fad'i gaba d'aya hankalinta ya tashi ita sai yanzu tama tuna da sex din da yayi da ita zata iya samun ciki.... Innalillahi'wa inna ilaihirajiun kodai cikin ma gareni?? Ina yawan Kwadayi tare da cin abinci anyhow gashi 2month kenan banga period d'ina ba.....
Dira tayi akan gadon tare da fad'in dan Allah NAJEEB Ina son inje hospital ayi min test
Kallonta yake cikin mamaki, lokaci d'aya yace test??? Wani irin test??
Tace plz najeeb bani da lokacin bayani I need to see a doctor plz najeeb Ina son ganin dr dan Allah sai kuma tasa mishi kuka tare da nufanshi ta ri'ke mishi hannu Tana fad'in NAJEEB ka taimaka ka kaini hospital na shiga uku, Allah ba Ameen ba, wayyo Allah na..
Najeeb yace ibtisam maike damunki? Cikin damuwa yake mata maganan
Tace najeeb ina cikin wani hali bazan iyayi maka bayani ba, idan abunda yake tunani ya tabbata Wlh bazan yarda domin kabir.....
Wani irin tureta yayi daka jikinta tare da sha'ko mata wuya yace how dare you.....
Shuru yayi na wani lokaci kafin yace how many times did I warn you not to call his name in front of me???. Tell me how many times did I warn you..... Lokaci d'aya kuma