Showing 69001 words to 72000 words out of 182942 words
Chapter 24 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
da ango sun hallari dinner din, inda Zarah ta bada kad'an daka tarihin Amarya, Tahir kuma ya bada na ango, ranan anyi B'ari da kud'i wajan lik'i, kabir sai kafu kafu yake da ibti d'inshi
Anci ansha sannan aka fara tafiya, ango da kanshi ya dawo da Amaryanshi gida, koda suka faka motar a kofar gidansu ibtisam, kallonta yayi tare da fad'in Amarya bakya laifi, koda kin kashe dan masu gida
Ibtisam tayi dariya tare da fad'in kai dako an d'aureni, in kashe d'an masu gida Kut
Shima dariyan yayi tare da fad'in babu Mai d'aureni karki manta kefa amaryan barrister Kabir ce, Kinga kuwa babu Mai d'aure min ke
Dariya tayi Sosai ba tare da tace komai ba
Yace Kinga yanda kikai kyau kuwa? Kai dama haka kike dakyau ban sani ba? Gaskiya am lucky
Ibtisam tace uhm.
Kabir ido ya k'ura Mata yana kallonta.
Ibtisam da kanta ke k'asa jin yayi shuru yasa jikinta ya bata kaman yana kallonta ne, A hankali ta d'ago kanta Aiko caraf idonta ya sauka a nashi, da sauri ta kauda kanta gefe tare da fad'in ina jin bacci Zan shiga gida
Kabir murmushi yayi tare da kamo hannunta ya ri'ke yace kin gaji da ganina ne??
Kaita girgiza alaman a'a tana kuma k'okarin kwace hannunta daka nashi
Ganin tana son ta janye hannunta daka nashi yasa ya k'ara ri'ke hannun Nata dakyau, tare da fad'in tunda dai bakya son ganina let me go
Tace a'a kawai na gaji ne Sosai
Kabir yace OK saida safe
Da sauri tace Allah ya kaimu, domin ita burinta ya sakar mata hannu daka ri'kon da yayi mata
Shiko kabir bai sakar mata hannun ba, sannan bai bud'e motar ba,dan yayi luck d'inshi
A hankali tace let go of my hand, I need to go and sleep plz
Sakar mata hannun yayi tare da fad'in take care
Tace I will sannan yayi unlock din motar ta fita
Cikin gida ta shiga wanda yake makil da mutane, kai tsaye d'akinsu ta nufa wanda babu wani ba'kon daya sauka a d'akinsu
Zarah tace ina kuka je keda angon naki?
Ibtisam tace muna waje tun d'azu
Zarah tace nasha ko AI kun biya wata duniyar ne
Uhm kawai ibtisam tace tare da kwanciya akan gadon d'akin Tana fad'in Kai na gaji Wlh, Bari in huta kad'an, in tashi inje in wanke wannan makeup din
Zarah tace aiki ja, wlh kinyi kyau Sosai, sun iya makeup
Ibtisam tace Sosai kuwa.
Zarah tace nifa ina son saki a status Amma saboda karsu Aisha su gani na kasa saki
Ibtisam tace in banda abunki kiyi Hiding nasu su daina kallon miki status mana
Zarah ta saki dariya tare da fad'in hakane fah, kai Bari inyi yanzu in saka
Washe gari Thursday kuma ranan za'ayi kamu, A ranan Ahmad brother d'in ibtisam yazo, shida Dad, ita dama Mum a hotel ta sauka, domin tace bata iya kwana cikin mutane
Ibtisam tayi murnan ganin Ahmad Sosai
Anyi ma ibtisam makeup inda aka tafi wajan kamu, shima kamun an k'ayata shi Sosai, inda ango da abokanan ango suka zo suka musu lik'i tare da d'aukan amarya da ango hoto, suka dan zauna na wani lokaci wanda bai wuce minti 30 ba, sannan suka wuce.
Hall din da akai kamu din yayi matukar tsaruwa, da had'uwa, komai dai gwanin burgewa da sha'awa, abun ba'a cewa komai
Anci ansha Anata son Barka Kafin kowa ya watse daka wajan
Koda suka koma Gida, ibtisam wanka tayi tare dayin sallah sannan ta kwanta danta huta, domin gaba d'aya tunda aka fara wannan hidiman bikin bata samun hutu
Tana kwance tana tuna ranan da Kabir yayi kissing d'inta, ido ta lumshe tare da furta Anya zai barni kuwa har in kammala karatu na kuwa? Uhm naga yanda yake ta zakewa uhm..... K'aran wayarta ne ya Katse Mata tunani
D'auka tayi taga kabir dinne, sawa tayi a kunne tare da fad'in hello
Kabir yace my ibti kinyi bacci ne?
,
Tace a'a, nadai kwanta Ina shirin inyi
Yace OK, yau fah kinyi kyau Sosai gaskiya
Tace uhm nagode
Yace gobe zani Abuja, gaba d'aya na manta muna da zama a court wlh, gashi gobe Friday
Ibtisam tace toh fah, yanzu inka tafi goben sai yaushe kenan?
Kabir yace goben zan dawo, zan tafi da sassafe, coz 10 zamu zauna, shap na manta wlh gaba d'aya
Ibtisam tace Allah ya kaimu, Allah ya kaika lafiya ya dawo mun dakai lafiya
Ya amsa da Ameen my ibti
Sun taba fira Sosai inda yayi mata sallama
Washe gari tun 6 kabir ya kama hanyar zuwa Abuja
Masu iya magana dai sukace rana bata k'arya sai dai Uwar d'iya taji kunya, A yau juma'atu babban rana a garin Kano Bayan an idar da sallah juma'a aka fara maganan daurin auren ibtisam da Kabir Wanda Dad ne wakilin ibtisam
Ana faman son a d'aura aure sai ga wani ya shigo cikin masallacin da sauri yana fad'in ku dakata, inada magana
Nan kowa hankalinsa yayi kanshi..
Mutumin ya kalli Abba, tare da fad'in karka yarda ka aura ma kabir y'arka, domin yana da cutar nan Mai karya garkuwan d'an Adam, wato HIV aid
Gaba d'aya aka saki salati, d'aya daka cikin dangin kabir ya tashi cikin zafin rai, tare da fad'in amma kam bawan Allah wannan wani irin kazafi ne?
Mutumin idonshi nakan Abba yace, bawan Allah gaskiya na fad'a, amma idan zaku cuci yarinyar shikenan, ni Nayi gaba, in kuna tantama ku gwada
Abba kam shuru yayi yana nazari, gaba d'aya kanshi ya kulle
Dad ne yayi karfin halin yin magana tare da kallon iyayen Kabir, yace inaga Ayi gwajin HIV, Kafin Ayi bikin
Nan k'anin mahaifin Kabir yace wannan ai cin fuska ne, kenan Sun yarda da abunda wannan Makaryacin yace?
Dad yace ko d'aya, amma domin a kauda tantama ko zargi inaga Ayi gwajin
Nan k'anin mahaifin Kabir yace tunda suna zargin kabir su ri'ke y'arsu, basa son auren
Wani aminin mahaifin Kabir yace gaskiya ne, dama su Dad sun tarasu ne dan suci musu zarafi
Dad abun dariya ma ya bashi, shidai baiga Abun fad'a ba, kojin zafi, kenan dagaske yana da HIV, din tunda suka d'auka da zafi
Dad yace kuyi hakuri, dukanmu ba yara bane, ina son ku sani mu iyayen yarinya bazamu Jefa rayuwarta cikin hatsari ba S....
Nan abokin baban kabir yace babu damuwa mun gode, amma ina son ku sani yanda aka tara mutane a nan, toh sai anyi wannan aure, ni naba ma kabir auran y'ata, ku kuma saiku aurar da y'arku mu gani
Dad murmushi yayi tare da fad'in shikenan, itama yanzu za'a aura Nata auran a gabanku, tunda baku da adalci...
Nan Dad ya ciro kud'i ya mi'ka ma Abba d'aya sannan yaba iyayen Kabir masu, ya kalli Abba yace ina nema ma Najeeb auren ibtisam
Nan Abba ya girgiza kai tare da fad'in ni zan bada sadaki domin d'ana ne NAJEEB,
Nan take Abba ya ciro dubu d'ari aka d'aura auren Najeeb da ibtisam
Suma aka d'aura auren kabir da Hafsat
Toh kabir dai yana hanyar dawowa kaduna, koya zaiji wannan Abun inya dawo?
Sannan ga ibtisam da aka d'aura mata aure da babban enemy d'inta, itama koya zata ji wannan Abun?
Toh Uwar Gayya NAJEEB, Zaima yarda da wannan auren kuwa? Musamman yanda baya shakkan kowa, yaga an d'aura mai ibtisam yarinyar da yake fad'in bata da kunya, sannan bata da komai..... Yanzu aka fara muje zuwa......
Read and leave it, dnt share to anyone
*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Bayan an d'aura auren ibtisam da Najeeb, nan take aka d'aura na hafsat da kabir suma. Inda dubban mutane suka shaida wannan auren
Bayan mutane sun Fara fita, daka family din ibtisam saina KABIR cikin masallacin
Abokin mahaifin Kabir yace kayan da kuka saka a gidan nawa kuka kashe?
Abba shuru yayi ba tare da yace komai ba, domin ya Lura kaman y'an uwan kabir sun d'auki abunda zafi, wanda shi baiyi zaton haka daka garesu ba, ko kad'an, dan yasan y'an gidan mutunci ne
K'anin mahaifin Kabir yace ku Fada nawa kuka kashe, dan Inaga tunda Abun ya zama haka gwara a baku kud'in kayan tunda ankai an kuma jera
Dad yace hakane, sai dai ina son ku sani, mun bar ma kabir kayan da duk mukasa a cikin gidan, koba komai ya nuna mana k'auna domin na tabbata inda ya.....
Mahaifin hafsat ya dakatar da Dad tare da fad'in kayi hakuri amma maganan gaskiya bazamu amshi wannan kyautar ba, domin y'atace zata zauna a gidan, kuma a matsayina na mahaifinta inada burin yi mata komai in zatayi aure Dan haka ku fad'i abunda kuka kashe
Dad ya kalli Abba tare da fad'in ya fad'a abunda ya kashe tunda yace haka
Nan Abba ya fad'a, tare da fad'in wasu ya manta
Mahaifin hafsat check ya rubuta tare daba wani yace yaje banki yanzu da sauri inya Kawo kud'in saiya kaima mahaifin ibtisam gida
Abba da Dad tashi sukayi suka tafi, harda Allah Abba baiyi zaton haka daka family din KABIR ba, koda yake ya gode Allah da hakan ta faru Koba komai y'arshi ta tsira daka wannan mugun cutar Mai Karya garkuwan jikin d'an Adam, toh Ina ma mutumin da yazo ya fad'a? Koma wanene Allah ya biyashi, "lallai aure Kafin gwaji yanada matukar amfani Sosai ya kamata a dinga yin gwaji Kafin Ayi aure domin gudun dana sani nan gaba
Nan su Dad da Abba suka shiga mota Bayan sun gama gaisawa da mutane Wanda suka zo ko ince suka tsaya aka d'aura aure Bayan an idar da sallah
Kai tsaye gida suka nufa inda taron mata ne makil a ciki, amma haka Abba ya shiga bayan yakai Dad falon ba'ki ya zauna wanda babu kowa a ciki.
Gidan cike yake da mutane y'an biki, Zarah dake zaune a falo tana ganin Abba tasan an d'aura aure dan haka da sauri ta shiga inda ibtisam take tana waya da kabir kwace wayar Zarah tayi a hannun ibtisam tare da fad'in kai wannan angon ai sai kayi hakuri tunda an d'aura aure ka barta taji da mutane Wanda suka zo dan tayaku murna, waya tun d'azu
Kabir yayi dariya tare da fad'in ayi mana hakuri, Nima tun dazu aketa kirana amma na'ki kashe wayar inata ganin calls Nasan duk y'an tayamu murna ne
Zarah tace toh gaskiya ka d'auka kabar ibtisam taji da mutane, anjima fah za'a kawo maka ita
Kabir dariya yayi cikin jin dad'i tare da fad'in insha Allah, Nima na shigo Kano yanzu plz ki kulan min da my wife
Zarah tace an gama barrister Kabir tare da kashe wayan
Kallon ibtisam tayi dake zaune tana dariya, Zarah tace congratulations burinku ya cika yanzu Naga Abba ya shigo Nasan har an d'aura auren
Ibtisam tace uhm
Dukan wasa zarah takai Mata tare da fad'in ya kika ji?
Ibtisam tace Zarah gabana yana fad'i, wlh yanzu naji gabana ya fara fad'i,kodan an d'aura auren ne yasa nake jin haka??
Zarah tayi dariya tare da fad'in ina tunanin hakane amma ki dinga furta Kalman Innalillahi'wa inna ilaihirajiun.
Ibtisam tashi tayi daka k'asa tahau gadon d'akin ta kwanta tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, tana ta nanata wa, lokaci d'aya kuma ta lumshe ido
Tayi wajan 5mnt sannan ta bud'e idon tare da kallon Zarah wacce ita din ita take kallo
Ibtisam tace Zarah har yanzu gabana yana fad'i plz bani wayana in kira kabir
Zarah tace ki kira kabir kuma? Ba yanzu kuka Gama waya ba? Kai Wlh ban taba ganin amarya da ango masu zumudi ba irinku,saurin Mai kukeyi ne? Anjima fah kad'an za'a kaiki
Ibtisam tace uhm wlh ko d'aya kawai gabana ne ke fad'i, sai yasa nake son ji ko KABIR ya isa Gida, kin San yana hanya ne
Zarah tace kwantar da hankalinki dazu dana amshi wayar yace Min ya shigo Kano, may be yanzu yana gida ma
Ibtisam tace nidai plz bani waya ta, inyi magana dashi
Mi'ka mata zarah tayi ganin yanda ta damu, kiran Layin KABIR tayi taji call waiting alaman yana waya, dan haka ta kashe dan tasan inya gama zai kirata
Aiko ko 1 mnt ba'ayi ba sai gashi ya kirata, d'auka tayi da sauri tare da fad'in ka isa Gida?
Kabir yace ibtisam maike faruwa ne wai?
Tace Dame?..
Yace waya nakeyi yanzu haka Ina kan Layin gidanmu ne, ance an samu matsala wajan auren kuma sunki fad'amin wai saina k'araso
Ibtisam tace matsala kuma? Kai Anya kuwa
Yace zan kiraki Ltr Bari in shiga inji
Tace OK tare da kashe wayar ta tashi tsaye.... Dai dai lokacin Ummi ta shigo d'akin Tana fad'in ibtisam abbanki yana kira
Tace ummi yana ina
Ummi tace yana falonshi na ba'ki
Ibtisam gyalenta ta d'auka tare da yafawa tabi bayan Ummi suka shiga har falon ba'kin, inda taga su mum da Dad da Abba da Granny
Granny tace ku fad'amin maiya faru mana, tun dazu sai jira muke gata tazo AI
Ibtisam zama tayi a k'asa tare da gaida Dad wanda ya amsa
Lokaci d'aya Dad ya fara magana kaman haka, an samu matsala wajan daurin auren ibtisam da Kabir
Dam ibtisam taji gabanta ya yanke ya fad'i
Dad ya zayyano musu abunda ya faru har d'aura auren najeeb da ibtisam da akayi da kuma auren da akayi ma kabir din
Ibtisam tashi tayi tana hawaye tare da fad'in Wlh sharri akayi masa, wlh k'arya akayi masa, ni na yarda koda yana da HIV Wlh zan aureshi a haka, dan Allah Abba kar a fasa wannan auren na ro'keka Abba cikin kuka mai ban tausayi....
Abba yace rufemin baki mara hankali, baki ji abunda akace ba, an d'aura miki aure keda Najeeb b....
Wani irin ihu ta saki Wanda ita sai yanzu taji hakan, domin sanda Dad na bayani tunda taji ance an fasa aurenta da Kabir saboda yana da HIV gaba d'aya taji kunnenta ya toshe bata ji
Tace Wlh Abba bana son wannan auren, kabir..... Lokaci d'aya jiri ya d'auketa tayi k'asa luuuuuuu..
Da sauri mum ta ri'keta tare da kiran sunanta ibtisam ibtisam, amma ina ko gezau batayi ba
Granny ce ta kawo ruwa aka yayyafa Mata ta Farfado aiko tana farfadowa tare da fad'in Wlh kabir nake so Dan Allah karku rabamu sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi Tana fad'in na shiga uku
Abba ranshi ya baci da abunda ibtisam din take fad'i dan haka cikin bacin rai yace in batayi shuru ba saiya karyata
Dad yace a'a akan wani dalili, taya zaice mata haka, Aiko dan abunda ya sameta dole tayi shock, in baka lallabata ba ai baka Mata fad'a ba, abun saiya mata yawa
Abba kallon Ummi yayi tare da fad'in ku tashi ku shiga ciki da ita.
Tashi sukayi harda Granny akai ciki, ibtisam na ri'ke jikin Mum Kai tsaye d'akin su ibtisam din suka shiga, inda suka iske Zarah
Zarah ganin ibtisam na kuka yasa ta d'auka ko anyi mata irin nasihan da akema amare ne yasa take kuka
Mum tace ibtisam kiyi hakuri, ki d'auki hakan a matsayin kaddara, Allah yasa kabir bashi bane mijinki K....
Cikin kuka tace mum Dan Allah ki taimaka kisa a bama kabir ni, na yarda zan zauna dashi koda yana da cutar, wlh Mum zan zauna dashi hakan, kuma Wlh nasan kabir baida Shi,sharri ne wlh sharri ne....
Ummi takai Mata duka tare da fad'in yi mana shuru mara hankali kawai, tunda ke baki San inda yake miki ciwo bako? Wlh.....
Mum tace haba ya zaki bigeta? Miye haka kuma? Damai zataji?..
Ummi tace baki ji abunda take fad'a ba? In banda iskanci tanaji ance yanada cuta amma tana fad'in ita zata zauna dashi haka, tunda bata da hankali bata san maike mata ciwo ba.
Zarah kam gaba d'aya ta shiga rud'ani, kenan ibtisam da Kabir ba'a d'aura aurensu ba? Gaba d'aya sai tausayin Itbtisam din ya kamata
Mum tace ai ba'a haka, bakya ganin irin halin data shigane? Komai a hankali za'a bishi
Ummi tace ai zancan Abu a bishi a hankali wlh bai taso ba, dan bazamu bita a hankali ba dan ubanta, tunda an d'aura aure, yanzu ita matar aurece kar in k'ara ji ta kira sunan wani kabir a gidan nan sha sha sha kawai mara tunani
Granny ce ta shigo tazo ta zauna kusa da ibtisam wacce ke kuka kaman ranta zai fita, wai itace matar Najeeb? Wlh da sake, gwara susa ya saketa domin kabir Zan aura
Granny tace ibtisam kiyi hakuri Kinji? Ki d'auki hakan shine dai dai, kuma haka Allah ya tsara, inaso ki sani komai da yake faruwa a rayuwar Dan Adam rubutacce ne, Allah ya riga ya tsara sai hakan ya faru, mu kawai muna bine, "Allah yasa kabir bashi bane mijinki NAJEEB shine mijinki Ina son ki dauki hakan a matsayin kaddara.....
Cikin kuka tace Wlh Granny bazan d'auka ba, ni Kabir nake so, shi kuma zan aura bana son wannan auren, dan Allah ku taimaka ku rabani da wannan ba'kin auren, wlh da nasan zanga wannan ranan dana ro'ki mutuwa Kafin tazo min, wayyo Allah kabir.... Lokaci d'aya tayi shuru tare da Fara dube dube kaman zararra, d'auko wayarta tayi ta Fara dannawa tare da dialing number d'in kabir.....
Amma Abun mamaki sai taji switch off.
K'ara kira tayi shima switch off, kuka ta k'ara saki mai sauti tare da fad'in shikenan, shikenan yaji wannan mummunan labarin, k'asa tayi jiri ya d'ibeta.
Da sauri Mum ta rukota Tana kiran sunanta ibtisam, ruwa aka saka mata amma