Showing 99001 words to 102000 words out of 182942 words
Chapter 34 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
a hankali insha Allah zaki samu sauk'i
Ibtisam tace sau'ki d'aya shine NAJEEB ya sakeni
Zarah dai rarrashinta tai tayi tare da bata baki, akan ta daina waya da kabir har sai NAJEEB din ya saketa
Ibtisam dai batace komai ba sai shurun da tayi tana sauke ajiyan zuciya
Yau watan ibtisam biyu da dawowa daka America, ibtisam gaba d'aya komai nata ya canza kirjinta sun ciko sai ta k'ara haske Sosai, ga yawan ciwon kai, dacin abinci kaman hauka, yau ta fito daka lecture kallo d'aya zaka mata kasan sauri take, ibtisam sauri take domin taje taci abinci dan wani irin yunwa takeji, tafiya take tana fad'in dole insha maganin macijin ciki, Nasan shine yake sani irin wannan cin abincin kaman hauka
Tana shiga daki ta iske Zarah nacin abinci zama tayi tare dasa hannu ta faraci
Zarah tace wai ibtisam wannan wani irin ci kike kwanan nan haka?
Ibtisam tace uhm macijin ciki ke damuna, zansha magani shike sani wannan mugun cin Wlh, ga ciwon kai, saifa naci abinci ciwon kan yake lafawa, anjima kad'an kuma sai ciwon kai din ya tashi inna k'ara cin abinci saiya lafa haka yake min...
Zarah tace toh anya kuwa?
Ibtisam tace anya kuwa me??
Zarah tace gaskiya kije asibiti a dubaki, ban taba jin irin wannan Abun ba
Ibtisam tace zani
Zarah tace Allah ya kyauta
Ibtisam tashi tayi tare da tube kayan jikinta tasa wata riga mara nauyi tasa sannan ta kwanta tare da lumshe ido, ba komai take tunani ba sai KABIR daya daina d'aukar wayarta tunda ta kira wata rana ya dauka yace tayi hakuri ta daina kiranshi tunda ita matar wani ce, yana fad'in haka ya kashe wayar tun daka ranan bai K'ara d'aukan wayarta ba, itama ganin haka saita daina kiranshi tare da burin suyi hutu ayi Mai yihuwa NAJEEB ya saketa,.
Tunda tazo NAJEEB bai kirata ba, balle yaji ya take ba, itama hakan bai dameta ba, dan tasan dama za'ayi hakan, Toh Mai ma zaice Mata inya kira din??
Ibtisam kasa bacci tayi sai juyi take tayi, ganin haka yasa ta tashi tare da d'aukan hijab tasa tace Zarah Bari inje waje insha iska Wlh wani iri nakeji gaba d'aya jikina babu dad'i, ni gashi ba ciwo ba, amma jikina wani iri
Tashi Zarah tayi tare da fad'in muje tare musha iska din
Fita sukayi inda suna nan zaune suna fira saiga Salees yazo ya zauna ta gefen ibtisam sunata fira ana dariya, Zarah tashi tayi tare da fad'in kai na manta inada lecture 5 wai assignment zamu bashi bari inje in dauko.
Bayan Zarah ta tashi Salees yace Wai nikam ibtisam kodai kin Fara shafa Mai ne??
Tace maika gani?...
Yace naga yanda kike wani walkiya, kinyi haske gashi kin k'ara kyau Sosai Kai ibtisam nifa gaskiya wannan guy din ya kwafsa min
Dariya ibtisam tayi tana fad'in bleaching Rufamin asiri ina ni Ina bleaching.....
Yace Wlh Kinga yanda kike walkiya kuwa......
Tun daka nesa ya hangosu a zaune, fuskanshi ne ya canza
Bayan driver ya faka wanda dai dai lokacin aka kira Salees a waya ya tashi tare da fad'in ina zuwa
NAJEEB cikin zafin rai ya fito ibtisam kawai ganin mutum tayi a gabanta ya tsaya, fuska d'aure
Gabanta taji ya fad'i Sosai gaba d'aya abunda ya mata ya fara dawo mata, hannunta ya kama tare dayin gaba da ita ya bud'e motar ya Jefata sannan shima ya shiga ciki yace driver ya tada motar suje
Ibtisam ganin haka ta Fara k'okarin bud'e motar.....
NAJEEB janyota yayi da karfi tare da ri'ke mata hannu
Shidai driver tuk'i yake
Koda suka fita daka cikin school din driver ya tambayi NAJEEB Ina zasu?
NAJEEB yace ya kaisu best hotel dake ZARIA
Driver ya amsa da OK
Koda suka k'arasa NAJEEB yaba driver ATM d'inshi tare da fad'a mishi pin din yace yaje ya Kama musu d'aki Biyu a cire kud'in a ciki
Ibtisam ganin driver din ya fita yasa ta kalli NAJEEB daya ri'ke mata hannu tace ka sakemin hannu
Wani irin kallo ya watsa mata Kai Kama da ni sa'anki ne
Ganin haka yasa ta Kame bakinta tayi shuru tare da k'okarin taja hannunta daka nashi, amma ta kasa
Har driver din ya dawo, yace an Kama d'akin sir
Najeeb bud'e kofar yayi tare da janyota suka fita, hannunta na ri'ke da nashi suka shiga ciki har d'akin inda ma'aikatan hotel din suka kaisu
Suna shiga ya jefar da ita tare da rufe kofar
Kallonta yayi idonshi wanda ya canza launi alaman bacin rai, yace keda uban wa kike magana a skul?? Kenan abunda kikeyi kenan koh? Shuru yayi yana kallonta alaman yana tunanin maima ya kamata yayi mata ne lokaci d'aya ya d'aura hannunshi akanshi tare da lumshe ido
Ibtisam kam ganin haka yasa ta tashi a k'asa daya jefar da ita, tare da tsayawa a tsaye
Najeeb bud'e idonshi yayi wanda ya sauka akan na ibtisam din yace am asking you keda uban Waye kike zaune???
Shuru tayi amma gabanta faduwa yake saboda tsoro
Ganin yana nufota yasa tayi saurin fad'in class mate d'ina ne....
Najeeb karasawa ya farayi inda take harya ganin haka yasa ta Fara matsawa baya, harta had'e da jikin bango inda ya k'araso inda take tare da janyo mata hijab lokaci d'aya ya cire mata hijab din, rigan jikinta irin Mai budaddan kirjin nanne nononta ana ganin Sun fito waje amma ba duka ba
Idon NAJEEB ne ya sauka akan nononta wanda suke a tsaye kuma a ciki, domin Sun k'ara wani girma, ganin ya kura mata ido yasa ta kalli inda yake kallo da sauri tasa hannu ta janyo rigan tare da rufewa amma still ana ganin nonon
Da yake NAJEEB Dan duniya ne saiya basar tare da fad'in your class mate? Kin manta da aurena a kanki??..
Ko kin d'auka ni Wawan namiji ne wanda ban San abunda nake ba? Am talking you tare da daka mata tsawa
Ta tsorata da Tsawan daya daka mata, wanda harta furta Kalman kayi hakuri ba tare data sani ba
Jin haka yasa ya k'ara mata ido yana kallon fuskanta da idonta ke rufe, gaba d'aya yaga yanda ta tsorata, domin yanda tayi da jikinta
K'are ma fuskanta ido yayi inda idonshi ya sauka akan bakinta mai laushi domin yaune rana ta farko daya k'are ma ibtisam kallo
Najeeb gaba d'aya ya kasa mata abunda yayi niya lokaci d'aya yaji ranshi ya fara sanyi, domin yayi niyan Idan yazo ya mata abunda sai tayi dana sanin kula wani namiji amma duk da hakan zai d'auki mataki
Ibtisam a hankali ta bud'e idonta ta ganshi akan gadon d'akin daka shi sai boxer da singlet
Da sauri ta kawar da idonta gefe, gabanta ya buga da karfi tare da tunanin mai zai Mata? Gaba d'aya abunda ya mata ya dawo mata lokaci d'aya kuma ta fara hawaye, domin tana tunanin abunda yayi mata rannan shine zai K'ara mata yau
Ibtisam cikin kuka tace dan Allah ka barni in koma skul, kayi hakuri ka barni in wuce dan Allah.....
Yace will you keep quiet and stop that crying
Ibtisam shuru tayi amma tana hawaye, ga kanta ya fara ciwo alaman tana jin yunwa, ganin tana jin ciwon kai din bazata iya zuciya ta daure ba yasa ta saki ihu tana kuka, lallai dole inje hspt wannan wani irin jaraba ne ya kamani....
Najeeb yace if I hear your voice again I will teach you a lesson nonsense
Ibtisam shuru tayi, lokaci d'aya taji har jiri jiri take ji, da sauri ta nufi fridge din d'akin ta bud'e taga harda Hollandia aiko d'auka tayi ta kafe Kai ta Fara sha kaman mayya
Idon najeeb na kanta yanda yaga Tana sha tsaki yaja tare da k'ara sanyin AC din d'akin ta remote, domin yana bukatar ya kwanta kafin yasan hukuncin da zai yanke mata
Ibtisam bayan ta gama sha taji dan dama dama, lokaci d'aya kuma taji yunwar har yanzu nufa wajan gadon tayi inda ta dauki wata takarda akan side drower din, inda y'ar wayar telephone ke wajan inda zaka kira masu hotel din in kana bukatar Abu
Duba takardan tayi taga irin abincin da suke dashi, sannan ta danna wayar ta Fara magana
Najeeb harya Fara bacci yaji muryanta kaman tana waya wanda hakan yasa ya farka ile kam wayar takeyi, da sauri ya amshi wayar tare da sawa a kunne dai dai lokacin ana tambayarta room number din
Najeeb fad'a mishi yayi tare da fad'in mai zaka mata??
Yace sir abinci za'a kawo mata
Yace OK tare da ajiye wayar ya janyota tare da rungumota ta kwanta ta gabanshi
Tana k'okarin tashi yace ki nutsu kona zaneki
Ibtisam jin haka yasa tace plz ka sakeni in tashi bana jin bacci
Najeeb yace an so what, I don't care kina ji ko bakya ji, I need silent, so don't disturb me
Ibtisam tace OK allow me to go
Bai bata amsa ba sai hannunshi daya saka tare da toshe mata baki da karfi
Ibtisam ta Fara shure shure Da k'afa alaman ya saketa, amma NAJEEB ya'ki gashi dakyar take nishi, NAJEEB har hawaye yaji yana taba mishi hannu amma ya'ki sakinta..... Bacci ne a idonshi Sosai,.... Jin nocking din da akeyi yasa ya saketa tare dayin tsaki ya tashi
Kofar ya bud'e tare da amsan abincin, Kun San hotel in aka kawo maka abinci zaka bada kudi ganin ya tsaya yasa NAJEEB fad'in am coming
Shiga yayi ya ajiye abincin tare da kallonta yanda take kuka yace kawo kud'in in bashi
Wani irin kallo ta watsa mishi tare da fad'in ai bani nace ka d'auko niba, kaida ka dauko ni saika biya
Najeeb kallonta yayi yanda take maganan cikin tsoro amma dole sai tayi rashin kunya.
Yace banda kud'i a wajena
Ibtisam Banza dashi tayi tare da tashi ta dauki abincin ta faraci kaman wata mayya
Yanda take cin abincin abun yaba NAJEEB mamaki cikin ranshi yace sai kace wacce bata taba cin abinci ba
Najeeb d'aukan wayarshi yayi ya kira driver da shima yake d'ayan dakin da aka Kama, yace yazo d'akinshi..
Ba'a dad'e ba driver din ya k'araso, najeeb yace suje a cire kud'in abincin ta POS sannan yace ma driver din shima yaci abinci tare da fad'in inya gama ya ciro Mai kud'i domin yana bukatar kud'i a hannunsa kud'in Nigeria,
Driver ya amsa da OK sir tare dayin gaba shida wanda ya kawo abincin
Najeeb wani irin kallo ya watsa ma ibtisam sannan ya koma ya kwanta
Ita kam ibtisam ci take hankali kwance, abincin ya mata dad'i sai dai Naman ne data Fara ci taji kaman zatai amai dan haka ta barshi, zuciyarta taji Tana tashi Wanda yasa da gudu tayi toilet tana kwarara amai kaman hanjinta zai fita
Najeeb jin kaman nishinta yasa ya tashi jin Tana toilet Tana amai yasa ya tashi ya nufi toilet din duk da baya son ibtisam ta dan bashi tausayi harda yi mata sannu tare da rukota yana buga mata baya kad'an k'adan
Ita kam idonta duk ya firfito yayi ja Dan azaba
Kamota yayi Bayan ta dauraye bakinta ya fito da ita tare da ajiyeta akan gadon d'akin yana fad'in ba dole kiyi amai ba, kinsha Hollandia and now kalli yanda kike cin abinci kaman wata witch
Ibtisam kallonshi take tana mamaki yanzu ya nuna kaman ta bashi tausayi harda sannu, amma jiba kuma yanda yake mata fad'a kaman wata y'arshi
Najeeb tsaki yaja tare da fad'in komai mutum ya samu yaci, may be Kinje kinci food poison
Kwanciya yayi tare da fad'in I need to sleep so don't disturb me plz
Ibtisam Hararanshi tayi cikin ranta tace kaji dashi Wlh ka tashi kaban takarda na domin kabir na jirana mugu kawai........
Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Ibtisam kwanciya tayi akan kujeran d'akin amma a zaune tunda k'anana ne kujeran, bata dad'e ba bacci yayi gaba da ita a haka
Najeeb na bacci yaji ana nocking dole ya tashi yayi tsaki tare da fad'in bazasu Bari mutun ya kwanta ba, tashi yayi inda yaga ibtisam na bacci a zaune akan kujera, bud'e kofar yayi yaga driver, yace ya akayi??
Driver din yace na ciro kud'in ne
Yace ok tare da amsan kud'in daya ciro mai din, sannan yace Ina zuwa bari in baka plate d'insu ka basu, komawa yayi tare da bashi plate din da ibtisam taci abinci
Har zai koma ya kwanta domin har yanzu bacci yake ji, ya kalli ibtisam yanda take a takure, nufanta yayi tare da d'aukanta cak ya kwantar da ita akan gadon d'akin, cire mata hijab din jikinta yayi wanda ta kuma maidawa
Nononta rabi duk a waje
Ido NAJEEB ya kura ma nonon yana mamakin a jikinta suke koya? Danshi abun mamaki yake bashi, dama Tana da nono haka? Gasu fresh irin nonon da yake mutuwar so da k'auna, gasu a cike a tsaye kyam dasu, dama matan Nigeria akan samu mace Mai nono irin haka??....
Gaba d'aya najeeb kasa bacci yayi domin idonshi nakan nonon ibtisam dake a bud'e tana bacci, lokaci d'aya yasa hannunshi har zai taba ya fasa tare da lumshe ido yaja tsaki.....
Juyawa yayi yana ta tsaki k'asa k'asa, gaba d'aya ya kasa bacci dole tashi yayi ya fad'a toilet yayi wanka, koda ya fito tana ta baccinta hankali kwance
Najeeb fita yayi tare da rufeta cikin d'akin, inda suka fita shida driver domin ya kaishi boutique yasai kayan sawa, d'aukan kaya yayi a kalla wajan Kala biyar, har zai wuce ya tsaya tare da komawa gefen kayan mata duk da bai san size din ibtisam ba, Yadai d'aukar mata kuma duk Wanda ya d'aukar mata kusan duk masu nuna tsiraici ne haka dai ya biya kud'in suka tafi
Koda NAJEEB ya dawo bata tashi ba, baccinta take Sosai abunda, sai wajajan magrib ta farka tare dayin mi'ka
Ganinta akan gadon d'akin yasa ta tashi da sauri tare da kallon kanta Tana mamakin yanda akai tazo nan ba tare da saninta ba, ganin najeeb zaune yana danna wayarshi yasa tasan tabbas shine ya kawota kan gadon d'akin
Ibtisam da sauri ta tashi ta d'auko hijab d'inta data ganshi a k'asa tasa tare da shiga toilet tayi alwala ta fito, wayarta ta d'auka da yake silent danta duba lokaci taga misscall wajan 11 da sauri ta bud'e taga d'aya na Abba biyu na ummi, sai sauran na Zarah
Kiran Abba ne ya k'ara shigowa wayarta, d'auka tayi tare da fad'in hello Abba
Abba yace ibtisam ina kika shigane!? Zarah tace tun d'azu bata ganki ba, taita kira baki d'aga ba Kina ina
Cikin sauri tace Abba NAJEEB ne yazo shine muka.... Sai kuma tayi shuru alaman tana jin nauyin fad'an inda suke
Abba yace ah NAJEEB yazo kenan?
Tace eh
Abba yace saiki fad'ama Zarah inda kike domin hankalinta ya kwanta
Tace toh Abba tare da kashe wayar, Tana kallon NAJEEB Wanda shima ita yake kallo
Jefar da wayar tayi tare da fara sallah, koda ta idar bayan ta sallame tashi tayi tare da kallon NAJEEB tace zan wuce skul
Wani irin kallo ya watsa mata sannan yaci gaba da danna wayarshi
Dan tsaki tayi mara sauti sannan ta nufi kofar d'akin gaba d'aya ta kasa bud'ewa domin ya cire card din da yake bud'e kofar
Kallonshi tayi tare da fad'in zan wuce ka bud'emin kofa
Banza da ita yayi baiko kalleta ba yaci gaba da danna wayarshi
Wani irin haushi taji har cikin ranta, nufanshi tayi tana fad'in ka bud'emin kofa nace, akan wani dalili zaka kawoni nan?
Najeeb still banza da ita yayi ibtisam ganin ya maidata mahaukaciya ga yunwa tanaji gashi yayi Banza da ita, wato ga mahaukaciya
Tsaki ta saki tare da galla mishi harara
Tashi yayi ya matse Mata baki da karfi tare da murd'a mata bakin, ta saki wata irin K'ara mai sauti domin taji wani irin azabban zafi Sosai
Najeeb yace don't you ever try it again in your lyf
Hawaye ne ya zubo daka idonta
Ganin haka ya watsa mata wani kallo tare da zama yana danna wayarshi, kallo d'aya zaka mishi ka gane ranshi a bace yake, wayarta dake huta alaman kira ta d'auka domin ganin Sunan Zarah
Bayan tasa a kunne tace Zarah
Zarah tace kina inane ibtisam?
Tace ina nan nida yayanki ya d'auko ni ya kawo ni nan, Wlh Zarah hakuri na ya k'are fah
Zarah tace au ashe kina tare da mijinki
Tsaki ibtisam taja tare da kashe wayar, duk cikin harshen Hausa take maganan
Najeeb baiko kalleta ba, balle yasan mai takeyi, ibtisam jin tana jin yunwa Sosai kuma bazata iya jura ba yasa ta nufi wajan wayar telephone din tare da kira tace su Kawo mata tuwon semovita miyan kuka
Tana fad'in haka ta kashe wayar tare da zama a gefen gadon ta d'aura hannunta akan fuskanta Tana tunanin mai yake nufi da itane haka??
Kanta ciwo yake Sosai domin yunwa takeji, so take a Kawo abincin taci, ga cikinta dake faman Mata kugi
Nocking akayi da sauri ta tashi ta nufi kofar zata bud'e, tsayawa tayi domin tunawa da tayi kofar a rufe yake, dole saiya bud'e
Najeeb tashi yayi tare da Hararanta ya nufi kofar ya bud'e tare da ganin an kawo mata abinci amsa yayi tare da fad'in nawa?
Fad'a mishi akayi ya koma ciki
Ibtisam nufanshi tayi ta amsa tare da fara ci
Najeeb tabe baki yayi tare da d'auko kud'in ya bashi
Kallonta yayi yaga yanda take