Showing 66001 words to 69000 words out of 182942 words

Chapter 23 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

rashin mutunci ya iya


Mum tace zan fad'a mishi yanzu sannan sukai sallama da Granny


Mum kallon Najeeb tayi dake zaune yana danna waya, tace Najeeb yanzu mukai waya da Mama


Kallon Mum alaman wace Mama kuma?


Mum kaman tasan abunda yake nufi tace da Granny mukai waya, tace in fad'a maka ka jira Ayi bikin ibtisam dakai


Tsaki Najeeb ya saki tare da fad'in that old woman sai kuma ya kuma sakin wani tsakin tare da fad'in bazan tsaya ba akan Mai zaisa in tsaya? Mum ki fad'a mata nace bazan tsaya ba, ina ruwana da wani biki? Miye nawa a ciki da zan tsaya? Plz Mum ni inada abunyi


Mum tace Najeeb bikin y'ar uwarka nefa za'ayi, kake fad'in haka


Yace Mum banda business da bikin, saboda biki sai inki tafiya wajan aiki?


Mum tace zaka iya d'aukan excuse ai Najeeb, inaga hakan zaiyi


NAJEEB yace no Mum gobe zan koma, bazan zauna ba, sannan aure kuma Allah ya bada zaman lafiya, I have nothing to do with d weeding infact yarinyar da bata da kunya why will I have to attend her wedding


Mum tace toh fah, kai kowa kace baida kunya?lallai kam amma k'aryar mutum yace ibtisam bata da kunya yarinya mai ladabi


Najeeb tabe baki yayi


Mum taci gaba da fad'in aure ne dai kace bazaka tsaya ba, amma kar ka k'ara fad'in cewa ibtisam bata da kunya domin kuwa tana dashi Sosai ga girmama na gaba


Najeeb yanda Mum take Yaban ibtisam sai Abun ya bashi mamaki da dariya kuma, cikin ranshi yace Mum bata san wacece wannan yarinyar bace, green snake kenan


Hhhhh kunji NAJEEB wai ibtisam ce green sneak


Granny Bayan ta gama wayar ta mi'ka ma ibtisam maganin dake hannunta, tace gashi Kinga nama manta na tsaya fira gashi ki dinga tsarki dashi


ibtisam tace Granny miye wannan kuma?


Granny tace maganin sanyi ne, kin San yanzu idan Mace Nada sanyi saiya rage mata ni'ima, kiga miji yana Abu da mata baya jin dad'i


Ibtisam kam kunyar maganan Granny taji


Granny ta lura da hakan tace yama kuke kiran abunda da turanci?


Zarah tace infection


Granny tace yauwa shi, ai mugun ciwo ne, kusan yawanci mata na d'auke dashi, wasu sun sani wasu basu sani ba, sai dai muce Allah ya kiyaye, "Dan haka ke ibtisam saiki Fara maganinshi


NOTE: yana dakyau in yarinya zatai aure tayi treating infection, kije hspt a dubaki aga ko kina dashi, ko baki dashi, inko kina dashi ki nemi magani Kafin aure, domin infection yana rage ma mace ni'ima Sosai, bawai aita dura ma yarinya maganin Mata ba, a'ah ku nema Mata maganin sanyi, domin duk maganin da zaku bata babu abunda zai Mata Indai tana da infection, domin yakan saka ni'imar mace ta daskare, gashi kunyi ta dura mata maganin Mata, wanda zai tursasa ni'imar fita, gashi tana da infection ya'ki fitowa sai yaita sama yarinya ciwon ciki da sauransu, "so plz maganin Mata bashi bane, Nop kuyi maganin infection shine babban matsalan, da yawa Mata na complain akan matsalan wata tace tayi na asibiti baiyi ba wata tace tayi na gida shima baiyi ba, y'ar uwa saifa kin dage, domin infection ba lokaci d'aya yake tafiya ba, shigarshi baida wuya amma fitanshi akwai wuya, musamman masu abokiyar zama, inke kina magani keda miji, ita abokiyar zamanki batayi Kinga infection bazai barki ba, sai dai ya ragu, so mata ku daina wani rubibin siyan kayan mata, just ki tsaya ki nemi lafiya daka wannan cutar ta infection


Najeeb kam kaman yanda Ya fad'a Washe gari yabar k'asar domin shidai bazai iya zama ba, gashi babu giya babu y'an mata, dole yasa ya koma inda yafi wayau


An fara hidiman bikin ibtisam da Kabir, ibtisam tayi wani mugun cikowa, tare da wani haske Tana shinning, lallai anyi mata gyara ko Ince ana kanyi, ibtisam gaba d'aya ta saki jikinta Sosai ana hidiman da ita, dan tasan Kabir bata da matsala dashi akan karatun ta.


Yau za'a kawo kayan akwati dan haka ibtisam da Zarah suka bar gidan gaba d'aya, suka shiga kasuwa, Dan suyi siyayya


Zarah da ibtisam suna wani shagon siyan Gyale domin Zarah zata siya, saiga kiran Dr jibril ya shigo wayan ibtisam mamaki tayi domin tunda ta kirashi baije ba tun sanda sukai hutu bata K'ara kira ba, dan haka ta d'auka tare da sawa a kunnenta


Tace ina wuni sir?


Dr jibril ya amsa da lafiya Amina, ya gida hope ana karatu a gida?


Ibtisam tayi dariya tare da fad'in eh munayi sometimes


Yace sometimes kuma?


Tace eh sir kasan ba kaman a skul ba, nan mutum yana gida, koka Fara wani abun zai taso dole ka bari kaje kayi, ga kuma Aiki, Kaga duk a skul babu wannan


Yace you are right, I just call to say hi


Ibtisam tace nagode sir, tare dayi mishi sallama


Zarah ta kalli ibtisam Bayan ta kashe wayan, tace Dr jibril neko?


Ibtisam tace eh


Zarah tace yasan ko zaki aure kuwa


Ibtisam tace a'a nifa babu wanda ya Sani a skul


Zarah tace inaga yana dakyau ki fad'ama Dr jibril zaki aure


Ibtisam tace akan wani dalili zan fad'a masa?


Zarah tace saboda wlh mutumin nan koda bai fad'a ba, sonki yakeyi


Tsaki ibtisam taja tare da fad'in kema kin Fara biyema su Aisha koh?..


Zarah tace ba haka bane, na dad'e Ina nazari akai, amma ina Mai baki shawara ki fad'a Mai zaki aure domin.... Toh wai miye na boye boyen zaki aure ne ma


Ibtisam tace Kinga malama biyashi kud'inshi mu tafi inada abunyi


Zarah tace uhm Allah ya kyauta tare da biyan kud'in gyalen suka fita


Shop rite, suka je daka kasuwa, inda suka fara siyayyan kayan za'ki, duk dan su bata lokaci kar suje gida da wuri, tunda 4 akace za'a kawo akwatin.


Y'an Kawo lefe Sun kawo akwati goma sha biyu, aka kawo set biyu kenan, gaskiya kabir yayi k'okari domin ya zuba kaya na Kece raini, anba ma y'an Kawo akwati abunda aka tanada na ciye ciye tare da kud'i wanda ake badawa na tukwici


Au ibtisam sai wajan 6 suka dawo gida a gajiye, suna shiga toilet ibtisam ta fad'a domin tayi wanka, dan KABIR yace zaizo anjima


ita kam zarah kayan akwati ta tsaya gani tana fad'in ibtisam anyi goshi gaskiya kayan sunyi kyau, domin kaya ne masu tsadan gaske KABIR yasa ma ibti d'inshi


Koda ibtisam ta fito daka wanka, bata koje inda kayan lefen suke ba, domin kunya takeji, Toh akan wani dalili ma zata tunda Nata ne, kuma tare dasu za'a kaita


Wajan karfe 8 da wani abu saiga kabir yazo wajan ibtisam, kiranta yayi a waya tare da fad'in ina waje


Fita tayi Kai tsaye hijab ne a jikinta domin wando tasa da top saita d'aura hijab, "Kai tsaye cikin motarshi ta shiga inda ta ganshi shi d'aya tace yazo su shiga falon ba'kin dake gidansu.


Kabir yace a'ah nazo ne kawai na ganki, in wuce Nayi missing d'inki Sosai


Murmushi ibtisam tayi tare da fad'in yaushe ma ka shigo Kano baka fad'amin ba sai d'azu naji ka kira zaka zo.


Kabir yace Wlh Ina zaune kawai naji Ina son ganinki


Ibtisam murmushi tayi tare da satan kallonshi taga shima ita yake kallo


Da sauri ta juya tare dayin k'asa da kanta


Kabir kam dariya yayi danya ganta sanda take kallonshi domin idonshi na kanta, "a hankali yace ibtisam bazaki iya kallon mijinki ba na wani lokaci?


Uhm kawai tace tare dasa hannunta a fuska ta rufe tana murmushi


Jin hannun Kabir tayi akan hannunta ya ri'ke yana k'okarin cire mata hannunta akan fuskanta


Gabanta taji ya fara dukan uku uku, domin tunda take dashi Bai taba Taba mata jiki ba sai yau, harya cire mata hannun nata daka fuskanta kanta a k'asa ta kasa koda d'aga kanne domin ta rasa mai takeji a halin da take yanzu


Hannunshi yasa ya d'ago Mata da fuskanta tare da juyo da fuskan Nata tana kallon nashi, ido suka had'a, da sauri ta lumshe idonta domin bazata iya kallon idonshi ba dan ko yanzu data kalla saida taji wani irin mugun faduwan gaba


Shiko kabir idonshi na kanta, wani irin sonta ne ke fusganshi ji yake kaman yayi hugging d'inta, "lokaci d'aya ya saki murmushi tare da kiran sunanta da ibti plz open your eyes I need to see it


Ibtisam bata bud'e idon ba,haka bata motsa ba, domin gaba d'aya jikinta a mace yake tunda kabir ya tabata, mamaki take cikin ranta tare da fargaba, ko ince sabon al'amari daka Kabir din data gani yasa ta kasa wani kwakwaran motsi.


Kabir kam har yanzu idonshi nakan fuskan ibtisam yana kallonta, wanda idonta yake a lumshe, lokaci d'aya yasa bakinshi cikin nata ya fara kissing d'inta


Ibtisam da sauri ta bud'e idonta tare da k'okarin tureshi amma ta kasa, a kalla yayi wajan 2mnt yana tsotsan bakinta, tun tana tureshi harta Fara hawaye.....


Lokaci d'aya ya saketa.


Ibtisam ganin ya saketa yasa ta Fara k'okarin bud'e kofar amma ya danna luck, wanda kofar ta kasa buduwa


Kuka ta saki Sosai tare da fad'in ka bud'emin kofa in fita


Kabir janyota yayi jikinshi


K'okarin tureshi ta farayi amma ya ri'keta dakyau wanda yasa ta kasa kwatan kanta, dole yasa ta tsaya tare da k'ara kwantar da kanta akan jikinsa tana kuka


A hankali yace am so sorry my ibti, na kasa controlling kaina, plz forgive me, sonki yasa nayi hakan amma ba halina bane ibtisam


Bata ce mishi komai ba, sai dai kukan da takeyi yad'an lafa, ba kaman daba


Nan yaci gaba da rarrashinta, cikin ranshi kuwa k'ara godema Allah yayi domin ya tabbata ibtisam koda baya nan zata ri'ke mishi kanta, duk da yana fama da so da kuma burin kasancewa da ita, yayi hakan ne danya gwadata kuma Alhmdlh taci jarabawan


Domin inda ta yarda batai k'okarin hanashi ba, zaiji tsoran auranta domin zaiga bazata iya ri'ke mishi kanta ba, toh yanzu Alhmdlh gashi harda kuka takeyi danya Mata kiss Wanda shi d'aya yayi mata bata maida mishi martani ba, sai k'okarin cire bakinta daka nashi da tai tayi


A hankali ibtisam ta janye jikinta daka nashi tare da saka hannunta Tana share hawayenta


Mi'ka mata tissue yayi


K'in amsa tayi tare da fad'in plz ka bud'emin kofar Ina son shiga gida


Kabir yace ibtisam wai wannan fushin da kikeyi na miye? Karki manta nine Zan aureki nan da kwana biyar za'a d'aura auranmu, toh miye dan nayi kissing d'inki is nothing b....


Ibtisam ta Katseshi tare da fad'in may be Kai a wajanka ba wani abu bane, kabir ina son.... Murmushin da kabir yayi shine yasa tayi shuru ba tare data fad'i abunda tayi niya ba


Kabir murmushi yayi domin jin ta kira sunanshi Kai tsaye abunda bata tabayi ba kenan,


Kabir yace ina son ki sani ibtisam ni kabir nine mijinki insha Allah, Ina son ki fahimci wani abu, wlh ibtisam ina sonki dagaske ban taba tunanin koda da minti d'aya bane ni in cutar dake ba, so ina son ki sani sonki a jinina yake, nayi miki kiss just to know who you are, in zakiyi min adalci how many month na sanki, but ban taba attempting na in taba koda hannunki ba.


Ibtisam shuru tayi tana jinshi lallai abunda kabir ya fad'a hakane, bai taba tabah mata jiki ba sai yau, ido ta lumshe cikin jin kunya wannan ne rana ta farko dana miji yayi kissing d'inta, gaba d'aya jikinta wani iri yake mata, damma anyi bada son ranta ba hhhhh


Kabir yace my ibti plz forgive me


ibtisam cikin murya wacce tayi kuka, tace ina son hakan Karta kuma faruwa, plz karka manta Idan mace dana miji suka kebe na ukunsu shaidan ne, ina jin tsoran karmu aikata abunda zai haramta auranmu, ko kuma muyi abunda za muyi dana sani, ban taba fad'a maka wannan Abun ba but yau zan fad'a maka, "bazan iya juran in rasaka ba, ni nasan Sonka a jini na yake, ban San ya kakeji a tare dani ba, but ni Ina jinka duka ilahirin jiki na, nasan abunda nake fad'a mata bako wace mace zata iya fad'ama namiji gaba da gaba ba, ina fad'a maka hakan ne domin kasan irin sonda nake maka, sannan kuma karka k'ara aikata abunda kamin yau, domin bazan iya juran rasaka a rayuwa ta ba,"ban taba son wani namiji ba sai kai, ban San so ba sai a kanka, Dan Allah Ina son karmu aikata abunda za muyi dana sani, wlh Ina jin tsoran abunda zai rabamu sai kuma ta saki kuka mai sauti


Gaba d'aya KABIR rudewa yayi tare da rungumo ta jikinshi yana fad'in ibtisam ni nasan abunda nayi miki Allah shine shaida na bada wani mugun abu nayi miki ba, sannan ina son ki sani bazamu aikata abunda za muyi dana sani ba, "ibti Kece mace ta farko Nima dana Fara so, duk da y'an mata da dama sunce suna sona, amma Kece naji Ina So, kuma nake burin aure, ban taba tunanin inyi wani abun da zai zama Abun kunya gareni ni dake ba, yau Ina cikin farin ciki my ibti ta fad'amin irin sonda take min am so happy


Da sauri ta janye jikinta daka nashi, wani irin kunya taji ta kamata lokaci d'aya, tare da fad'in maina aikata, hannu tasa ta rufe fuskanta cikin jin kunya


Kabir kam dariya yayi tare da canza firar tasu dan yaga yanda taji kunya akan abunda yace, dan haka saiya canza firan da fad'in ibtisam kinga kayan lefenki kuwa?..


Kaita girgiza alaman a'a


Yace Mai yasa ko kayan ne basuyi miki ba?


Tace a'a haka kawai


Kallonta yayi tare da kura mata ido, yace ibti are you happy with this marriage kuwa?


Da sauri ta kalleshi ido cikin ido domin ita yake kallo, tace am happy with it mana, "maika gani??


Kabir yace naga kince baki ga kayan lefenki ba, naso in miki yafi haka, in miki guda 24, but banda enough kud'i gidanki ya cinye kud'in


Ibtisam tace ko d'aya wlh, abunda kayi yayi fatana shine Allah yasa ma auren albarka, sannan abunda yasa ban gani ba saboda ina jin kunya, bazan iya zuwa ince zan kalla ba, gasu ummi a gidan,"kaji wannan shine dalili na, nak'in kallon kayan


Kabir yayi murmushi tare da fad'in yayi kyau, hakan yayi my shy ibti


Dariya tayi


Yace Bari inzo in gudu yunwa nakeji Sosai


Ibtisam tace ko in kawo maka abinci


Kabir yace a'a, Bari inje kawai


Ibtisam tace plz muje kaci, kaga in....


Yace ya kikai shuru


Tace ba komai, muje kaci a nan.


Yace no my ibti


Ibtisam tace Bari in kawo maka snack Toh, bud'e kofar tayi amma taji a rufe kallonshi tayi alaman ya d'aga mata


Murmushi yayi tare da d'aga mata sannan ta fita


Tayi wajan 5mnt sai gata da cooler guda uku a cikin basket dasu wasu Abu a plate guda biyu ansa full paper an rufe, bayan motar ta bud'e tare da ajiye Mai sannan ta rufe kofar


Bud'e gaban motar tayi wanda ta tsaya a tsaye ba tare data shiga ba, tace gashi saida safe koh


Kabir murmushi yayi tare da fad'in wannan ne snack din koh?


Dariya tayi tare da fad'in Toh naga kaki yarda in kawo ma, kuma Nasan in ba'ayi wasa ba, sai dai kasha tea


Dariya yayi yace tunda shine abincin gauraye koh


Ido ta lumshe tana murmushi


Sallama yayi mata tare da fad'in sai munyi waya yayi gaba


Cikin gida ibtisam ta shiga, kai tsaye d'akinsu ta shiga inda ta iske Granny da Zarah suna fira


Granny tace Sai yanzu kabirun ya tafi?


Ibtisam eh kawai tace tare da kwanciya tayi ruf da ciki Tana tunani, wanda ba tunanin komai take ba saina abunda ya faru tsakaninta da kabir, ido ta lumshe wani irin son kabir Mai tsafta takeji yana k'ara shigarta, lallai ina son kabir, sonshi ya kamani da yawa.


Allah na gode maka daka bani shi a matsayin miji, Allah ka bamu zaman lafiya, tare da hakuri da junanmu da kuma son juna.....


Zarah ce ta katse mata tunani da fad'in ibtisam Yadai naga kinyi shuru?..


Granny tace uhm ai tayi shuru tunda ansha kalaman soyayya


Dariya ibtisam tayi tare da tashi ta zauna tana kallon Granny tace Wlh Granny kina da abun dariya


Granny tace ahaf ai Nasan komai, domin wannan shurun bana banza ba


Ibtisam sai taji ta tsargu tana tunanin kodai Granny taga sanda kabir ya mata kiss ne?


Wanda hakan yasa ta kame bakinta tayi shuru ba tare data k'ara cewa komai ba


Granny tace uhm bari dai inje in watsa ruwa inyi bacci


Ibtisam kam gaba d'aya ranan sai juyi take tana tunanin abunda ya faru tsakaninta da kabir


Haka shima ta gefen KABIR din, wani irin sonta yakeji yana k'ara fusganshi, lallai yana son ibtisam da yawa, wanda ya tabbata sonta a jininshi yake.


Hidima ake Sosai na bikin ibtisam anje anyi mata danki a dangareren gidanta ginin gidan sama, sama akwai d'aki uku, k'asa kuma akwai d'aki biyu, ansa Mata gado a d'aki uku, sannan anyi mata jeran falo, gaskiya Abba yayi k'okari Sosai domin ya kashe dukiya Sosai akan wannan hidiman bikin, sannan ya fitar da y'arshi kunya, dan yayi mata kayan d'aki masu kyau masu tsada kuma, sai dai ayi musu fatan samun zaman lafiya da zuri'a dayyiba


Biki Wan shagali, yau za'ayi bridal shower inda aka kayata a hall, Mata ne zallah kawai a wajan inda Amarya tayi dressing cikin wata arniyar gown, Wanda yayi mata mugun kyau, ibtisam ba'a Mata wani makeup Sosai ba, Zarah ce tama shafa mata powder domin sunce kwalliya sai ranan dinner, Anci ansha anyi rawa kowa ya watse


Ranan da za'ayi dinner Mum tazo Kano Wanda ranan bikin saura kwana uku


Masu makeup aka kawo inda suka tsara ma Amarya kwalliya na Kece raini, gaba d'aya ban gane ibtisam ba, domin tayi wani irin mugun kyau, lallai ibtisam kyakyawa ce, shi kanshi kabir daya ganta ranan saida yayi mamaki, domin ita ba ma'abociyar yin kwalliya bace, lallai yayi Sa'a daya samu ibtisam a matsayin mata, wajan zaman amarya da ango su biyu inda sukai bala'in kyau, gaba d'aya iyayen amarya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login