Showing 153001 words to 156000 words out of 182942 words

Chapter 52 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

dole shi dinnan dai zan zauna mawa, ba wani ba, granny inda kin San zafin rabuwa da wanda kake so da ance Nayi hakuri, da yawa mutane basa gane wani abu, yau Indai Abu ba'a kansu yake ba, koya fad'a musu ba, toh basa gane irin zafin abun da kuma rad'adinsa


Nasan ni mace ce, kuma Aljanna ta tana k'asan kafar mijina, Nasan dole nayi masa biyayya, dole nayi masa abunda yayi umarni da inyi masa Indai bai saba ma sha'ria ba......


Duk Nasan wannan, toh amma shi najeeb din yana bin abunda ubangiji yace??


Baya bi, mutumin daya kauce ma mahaliccin shi taya wani zai bishi.....


Kuka ta saki mai cin rai sannan tace Granny, Koba alakan aure najeeb jinina ne, duk da tun Farko bama jituwa haka koda mukai aure babu wata magana Mai dad'i data taba shiga tsakanin mu, yau Koba najeeb dake jinina ba, ko wani naga yana shan giya Wlh zan tsaneshi, amma da yake najeeb akwai ala'kan jini sannan aure ya had'amu dole haka na hakura, kuma na tabbata inda najeeb ba jinina bane kuda kanku zaku ce saiya rabu dani, tun a lokacin da yayi min sharri yace wannan cikin ba nasa bane


Ya kamata inda kuna sona a lokacin da kun raba wannan auren, amma daga karshe sai kuka barni a wajansa, duk da ya nuna baya bukatar in zauna a tafi dani amma sai lokacin kika ce dole in zauna, haka kuka tafi kuka barni dashi


Granny Kun San irin abunda naji?? Kun san irin kuncin da naji?? Duk baku Sani ba, ku burinku in zauna dole a gidan miji, tunda ni mace ce banda wani zabi face inyi hakuri da duk irin abunda miji zaimin, ku matsalanku kar ace y'arku ta zama bazawara koh?? Koba shi bane matsalan??


Granny da yawa a k'asar Hausa Anfi samun irin wannan matsalan, kiga namiji shine dukan mace, cin zarafin ta, ya hanata haiyuwa, saboda baya bukata, ya tauye Mata hakkinta, etc


Kinga duk irin wannan matsalolin ba zasu gyaru ba, har sai iyaye sun daina jin tsoran kar y'ay'ansu su dawo gida su Zame musu nauyi ko kuma kar ace suna da bazawara


Granny shifa aure sunna ne, ba farillah bane, sannan shi aure daka ranan da mace tayi komai kikayi lada ake baki, bauta ne


Ni a nawa ganin Nasan duk abunda akace bauta ne sai an jure, amma da mace ta zauna miji ya dinga kuntata Mata, ita kuma tana masa abunda zaiji baya so, gwara a raba auren, domin anyi aure Dan samun lada sannan yakai mutum da Aljanna, amma babu farin ciki kuna kai kanku hanyar halaka, ku jefa kanku wuta, Indai irin wannan ne miye amfanin auren?? Kinga babu shi


Namiji zai bugi mace, ya mata mummunan duka, inta dawo gida sai a bata hakuri ace ta koma aure d'an hakuri ne shi dama bauta sai an jure, aita bata hakuri ana fad'in kiyi ta hakuri wata rana sai labari.....


Toh Kunga tun daga nan kun ba mijin daman ci gaba da dukanta kenan, domin yaga yayi na Farko ba'a d'auki mataki ba, an k'ara tura mishi ita, kinga zaiga baki da wani gata, wani namijin ma sai yaga kaman Turaki akeyi wajansa, kinga ba'a Fata a haka sai kiji ana fad'in ya kasheta wata rana, ko ita ta kashe shi, domin ita zuciya bata da k'ashi. Bawai Ina nufin Idan namiji ya bugi mace a raba auren bane a'a, but ya kamata a nemo shi aji dalili da zai bugeta, in Abun ta Kama a nemo har waliyansa ayi magana akan Karya k'ara dukanta, in Abun bazaiyi ba ko babu Mai fad'a mishi yaji zaku iya zuwa kotu, alkali ya bashi takarda yayi signing akan inya K'ara dukanki akwai hukunci akansa.


Indai aka d'auki wannan matakin bazai k'ara ba, shine ake kira da kwatan y'anci


Idan ana haka za'a rage irin abubuwan dake faruwa a gidajan aure musamman......


Granny ta dakatar da ita da fad'in ya isa haka ibtisam, na fahimta, amma ina son ki sani, shi aure dace ne, kuma ko wace mace tana da nata jarabawan, Mai hakuri yana tare da Allah, eh abunda kika fad'a gaskiya ne, yana dakyau a kwatan ma mutum yancinshi , amma ina son ki san wani abu guda d'aya akan najeeb, sannan ina son ki sama ranki wani abu, ki d'auka duk abunda yayi miki yayi miki ne cikin rashin sani, ba tare da yasan yayi ba...... Ibtisam na k'okarin magana Granny ta Katseta da fad'in kiyi shuru in Gama magana sai kiyi


Granny taci gaba da fad'in yanzu kinga NAJEEB yana Abu ne ba tare da sanin ilimin addini ba, kinga baiyi karatun addini ba, duk wasu abu da zaki ga yanayi Ina son ki d'auka cewa bai sani bane, abunda muke k'okarin yanzu mu d'aura shi a hanya kenan, muna son yasan addini ta yanda zai bauta ma mahaliccin sa, duk wannan Abun laifin mahaifinshi ne daya fifita boko akan karatun addini, wanda shi yake d'auka yama d'ansa gata ne, bai san ba gata ya masa ba, domin inda yana sonsa yana son nuna mishi gata shine ya koya Mai ilimin addini, wanda shine zai kaishi ga tsira ranan lahira,.


Granny kamo hannun ibtisam tayi tana fad'in dan Allah takwara ta, Ina son ki zauna da najeeb, ki ceto Dan uwanki daga fad'awa halaka, ina son ki zauna dashi matsayin mata Mai biyayya, domin ke y'ar uwarsa ce, Kece zaki fi kowa sanin darajansa, Koba dangantakar aure akwai na jini, ina son ki duba girman Allah kiyi hakuri ki koma wajan mijinki..........


Ibtisam kuka ya kubce mata sosai gaba d'aya ta kasa magana, ta rasa mai yasa Granny take ganin kaman itace take gudun zama dashi, shine fah yace ya saketa, Bayan haka kuma ance Mai sakin baiyi ba, amma ya tafi ba tare da yace komai ba, sannan tunda ya tafi bai kuma waiwayo waba, amma granny tazo tana d'aura mata laifi........












Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*












Kaman granny tasan abunda ibtisam ke tunani, tace ibtisam zaki ga kaman bana goyan bayanki, ba haka bane, yanzu duniya ta canza, komai ya canza, idan mace batai hakuri gidan mijinta ba inta fita bata san wanda zata aura ba, kinga gwara tayi hakuri ta zauna da Wanda tasan halinsa, saita dinga kiyaye wa, amma yanzu in mace ta nemi saki , inhar mijinta ya saketa bata san wa zata fad'a mawa ba, sai yasa ake cewa hakuri shine gaba da komai, kuma Mai hakuri yana tare da Allah, wlh ibtisam ban taba ganin laifinki ba gaba d'aya na najeeb ne, domin ke aka cuta amma gashi ina rokanki akan kiyi hakuri wata rana insha Allah za kiyi dariya


Ibtisam nidai burina in ganku tare har abada, shine Fata na, indai kukai haka zan mutu cikin salama......


Da sauri ibtisam ta rungume Granny tana kuka tare da fad'in insha Allah bazaki mutu ba Granny


Granny tayi murmushi tare da fad'in ai mutuwa ta zama dole ibtisam, lokaci kawai ake jira, amma dole ce ko Ana so ko ba'a so


Ibtisam tace toh nidai Granny abar maganan mutuwar nan dan Wlh ba son jinta nake ba, gaba d'aya


Granny tace Indai kam baki Sonta saiki koma ma mijinki, yanda zaki sani farin ciki


Ibtisam tace Granny ni Kinga Wlh yunwa ma nake ji, Sosai mai kuka dafa ne Inci


Granny tace ja'ira wato canza firan zakiyi koh?? Yayi miki kyau ai


Ibtisam tashi tayi ta nufi kitchen inda ta dibo abinci domin taci, tana cikin ci sai ga Ummi ta shigo cikin d'akin tana fad'in ah Ashe y'an karanta an dawo


Ibtisam cikin fara'a da murna take fad'in eh Ummi tun dazu na dawo bakya nan


Ummi tace Mun fita da Maman fati ne, ya karatun an Gama jarabawan kenan?


Ibtisam tace eh mun gama zamu sha hutu Mai tsawo harna wata d'aya da sati Biyu


Ummi tace Kai Aiko zaku dad'e a gida Sosai Allah ya taimaka bari inje in watsa ruwa duk na kwaso rana, Ummi ciki tayi tabar ibtisam da Granny










*AMERICA*


najeeb ne zaune yana karanta al'qur'ani domin gaba d'aya yanzu ya iya had'a ba'ki, abun har mamaki yaba malamin yanda yayi saurin iyawa, gashi najeeb baya dad'ewa ya gane Abu, wanda yawanci tun a k'aramin shekaru mutum yake saurin haddace Abu haka, amma sai gashi Abun mamaki shi najeeb da girmansa yana haddace Abu da wuri


Malamin ne yazo inda najeeb yake yana fad'in gaskiya najeeb ka gode Allah, wlh komai naka Abun sha'awa babu wuya ka haddace Abu, nan da nan wlh kana da kwakwalwa sosai


Najeeb saida yakai karshen Aya sannan ya kalli malamin Bayan ya ajiye al'qur'ani yace malam ba komai bane yasa kaga Ina saurin haddacewa ba sai Dan Ina son in koya wanda Allah yaga zuciya ta, duk abunda nake da Wlh Ina aikatawa ne ba tare da sani na ba, sannan yanzu dana gane nake son in koya in iya dole in dage, aikina gaba d'aya na dau hutu dan in nemi ilimin addini, inta Kama ma Wlh ajiye aikin zanyi, duk da nayi yunkurin yin hakan amma suka d'age akan bazan ajiye ba, inje inyi hutu, shine nace na d'auki hutun 5mnt


Malamin yace hakan ma yayi tunda gashi yanzu ko wata biyu bamu yiba amma harka iya abubuwa da dama, ko a haka ka tsaya aika gode Allah, domin wani wanda ya taso tun yana yaro yayi karatun ban tunanin zaiyi aiki dashi akan Kai yanda kake aiki dashi, yanzu nima tafiya ta Kama ni dole zan tafi saudiya, domin mahaifina baida lafiya, Kaga bazan zauna ba har inyi wata ukun da Nayi alkawari ko a haka na Barka Alhmdlh Nasan ka koya abubuwa da yawa


Amma idan naje naga yanayin jikin nasa inda hali zan dawo.....


Najeeb yace a'a karka damu, nida kaina zan biyo ka saudiya, zanje Nigeria insha Allah daga nan Zanzo harda iyayena domin su ganka, ku gaisa


Malamin yace haka yayi, tare dayi MA NAJEEB addu'an samun nasara a rayuwa


Najeeb Bayan ya koma gidansa gaba d'aya baya son zama shi d'aya sai yaji gidan yayi masa girma, kwanciya yayi akan kujeran falon inda ya lumshe ido, lallai sai yanzu yasan yana rayuwa, a da yana rayuwa ne amma kaman matacce, domin bai San yanda zai bauta ma Allah ba, gaba d'aya wannan canjin daya samu ya sameshi ne ta sanadin rayuwarshi da ibtisam ta shigo


Ya fara tunanin yasan mai yasa shan giya ya zama haramun da zina, lokacin da tace mishi duk manyan laifin da Allah ya hana kana aikatawa, tun daga ranan ya fara tunanin sanin Mai yasa ya zama laifi har yakai shi ga kiran malam, wanda gashi yanzu gaba d'aya rayuwarshi ta canza, sai dai abu d'aya da yake fatan shima ya canza


Lokaci d'aya ya tashi ya nufi bedroom d'inshi inda ya fad'a toilet yayi wanka ya fito daga shi sai boxer da singlet Kai tsaye kitchen ya nufa inda ya Tarar damai mishi aiki yace ta Kawo mai coffee, yana fad'in haka ya juya falon ya zauna yana danna wayarshi dake hannunsa


Bayan Mai aikin ta kawo mai coffee ta ajiye Mai akan center table har zata wuce najeeb yace ta tsaya tare da fad'in gobe zani Nigeria so zaki iya d'aukan hutu, but amma ki dinga zuwa kina duba gidan coz ban son in dawo inga datti ko k'ura


Ta amsa da OK sir


Najeeb d'aukan coffee din yayi inda ya fara sha.....


Washe gari kaman yanda yace hakan ko ta faru domin kuwa jirgin k'arfe 10 yabi inda ya tafi Nigeria Kai tsaye a abuja ya sauka inda aka turo mai driver yazo ya d'auko shi,.


Bayan sun k'arasa gida, Zarah da saurinta ta nufeshi tana fad'in Wlcm bros


Murmushi ya sakar mata tare da kallonta yace ya gida da skul? Yana ganki a gida??


Tace lafiya bros munyi hutu ne


Yace OK


Nan suka shiga ciki abunda najeeb bai taba yiba yau yayi gaida iyayenshi cikin girmamawa, gaba d'aya daga Dad har Mum sunyi mamaki tare da kallon juna


Najeeb ya lura da hakan sai yayi murmushi tare da fad'in kai am so tired I need to rest hope d'aki na a gyare yake??


Mum tayi murmushi tare da fad'in eh my only son, a gyare yake, AI ban barin dakinka da datti, domin Nasan yaron nawa baya son kazanta, amma before ka huta Aida kaci abinci koh


Yace Mum bari in huta na gaji Sosai wlh, nayi missing food d'inki amma tunda kika ga na kasa ci, toh na gaji ne


Tace OK a huta dakyau


Yayi murmushi tare da shiga d'akin nashi wanda yana shiga ya fad'a gado ya kwanta sai bacci


Mum da Dad sukam zama sukayi inda Dad yake fad'in kinga yanda yake gaidamu cikin girmamawa, gaba d'aya harta magananshi ya canza kaman bashi ba


Mum tace Wlh kuwa abun ya bani mamaki, bari dai ya tashi muji ya akayi










Ibtisam ce zaune tana ta wanke underwear d'inta, a wajan fanfo din dake waje, a tsakar gidan


Granny ta fito tana fad'in in banda kazanta mutum saiya tara su wando da skirt da yawa Kafin ya wanke, ai wannan kazanta ne


Ibtisam tace kazanta?? Lallai Granny Wlh kina shiga sabga ta da yawa, d'ago wani pant d'inta tayi tare da nuna mata da tace ina kika ga alaman kazanta a nan?? Kuma pant d'in ga sunan gudu biyar ne duka amma kina wani kiramun kazanta, salan wani yaji kisa a d'auka haka nake


Granny tace toh aji mana, AI gaskiya na fad'a Inba Kazami ba, taya mutum zai dinga tara pant da yawa haka babu wanki, ko ni da nake tsohuwa bana irin haka saike yarinya karama saboda lalaci.


Ibtisam tashi tayi tana d'iban kayan domin ta gama zata toilet ta shanya tace Kedai kika sani, nidai banda lokacin wannan surutun dake inada abunyi da yawa


Granny tace ai kyace haka mana t..... Wani irin K'ara ta saki tare da yin k'asa, da sauri ibtisam ta saki roban dake hannunta ta nufi Granny tana fad'in Granny lafiya kuwa? Maiya sameki tana tambayar Granny tana kuka


Ganin granny bata ko motsi yasa ta nufi d'akin ummi dake bacci da gudu tana fad'in ummi Ummi kizo mukai Granny asibti na shiga uku Granny ta fad'i k'asa


Ummi dake bacci sai taji kaman tana mafarki da sauri ta tashi amma sai taji ba mafarki bane domin dai dai lokacin ibtisam ta shigo d'akin Tana fad'in ummi Granny ta fad'i muna cikin magana Dan Allah mu kaita asibti ki kira abba


Da sauri Ummi ta tashi tare dasa hijab tana fad'in maiya faru da ita?? Kai tsaye waje suka nufa inda suka tarar har yanzu tana nan kwance a k'asa tana nishi sama sama


Nan Ummi tace maza su kamata su kaita asibiti, hakan ko sukayi ibtisam ta fita ta kira Mai adai daita sahu inda suka Kama Granny ita da Ummi sukai motar da ita, direct asibiti suka nufa da ita inda aka amsheta akai emergency da ita domin a duba lafiyarta


Ibtisam kuka take Sosai, domin a duniya Tana son Granny, ko kad'an bata son taga wani abu ya sameta


Ummi sai a sannan ta kira abba Inda ta fad'a mishi halin da ake ciki, ko minti 30 baiyi ba ya garzayo asibitin Kai tsaye inda ya Tarar dasu suna zaune ibtisam nata faman kuka


Abba yace maiya sameta?? Nan ibtisam ta Fara fad'a mishi Abba muna fira na tashi inje inyi shanya tasa ihu tare da faduwa


Abba yace Toh ya isa mana kibar wannan kukan Mai Dr yace ??


Ummi tace baice komai ba, har yanzu Dr bai fito ba


Nan Abba ya zauna suna jiran fitowan Dr din


Wayar abba ce tayi K'ara d'auka yayi yaga Dad ne Bayan sun gaisa Dad yake cema Abba d'anka ya dawo yau


Abba yace a Barka da fatan ya dawo lafiya


Dad yace lafiya


Abba yace gamu a asibiti Mama bata da lafiya


Nan Dad yace Subhanallah maiya sameta??


Abba yace gamu nan dai har yanzu Dr bai fito ba


Nan Dad yace bari yanzu mu kamo hanya


Abba yace kai yamma yayi fah


Dad yace ya zamuyi dole mu tawo


Nan Bayan sun kashe wayan Dad ya kalli Mum yace mama bata da lafiya yanzu zan kama hanyar Kano


Mum tace maike damunta?


Dad yace wlh ban sani ba, Tadai fad'i ne kuma ance Dr bai fito ba


Mum tace amma daka bari gobe saimu tafi gaba d'aya koh??


Yace a'a yau zani ku saiku tawo gobe


Nan Zarah tace zata bishi


Yace Toh kiyi sauri muje kin San ban son jira


Zarah tashi tayi da gudu taje ta zuba kayanta a akwati tare da abun bukata sannan ta fito suka Kama hanya ita da Dad, mum dai tace ita da najeeb gobe zasu tawo


Bayan fitan su Dad saiga najeeb nan ya fito ya tashi Daga bacci.


Mum tace harka tashi


Yace eh mum Ina Dad ya fita ne??


Tace ya tafi Kano yanzu


Yace yanzu da yamma haka? Lafiya kuwa??


Mum tace granny ce aka kwantar a asibiti, shine ya tafi shida Zarah Nima gobe zamu tafi


Yace Subhanallah maike damunta?? Kai ni bamma taba ji ance tana ciwo ba sai yau


Mum tace Wlh bata ciki ciwo ba, gashi wanda bai ciwo inya tashi yi bai iyaba


Najeeb yace Allah ya Sawake, nima da Ina nan Aida nabi Dad munje tare


Mum tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login