Showing 63001 words to 66000 words out of 182942 words

Chapter 22 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

nemi number d'inshi Dan yayi min wlh


Ibtisam tace gwara ki kama kanki wlh, domin gudun raini


Aisha murmushi kawai tayi tare dayin gaba tana fad'in Indai dan uwan Zarah ne sai tasan yanda akayi ta had'asu


Ibtisam wajan su Mum ta koma, bayan sun kammala cin abinci suka fito Kai tsaye wajan mota suka nufa inda Mum ta shiga tana fad'in zamu kama hanya


Zarah tace Mum Abuja zaku tafi yanzu?


Mum tace a'a kaduna zamu shiga gobe zamu koma yanzu yamma tayi ban son tafiyan dare


Zarah tace Mum plz mu biku gobe sai mu dawo da kammu


Mum tace OK Toh kuzo muje, "amma baku da lecture ?


Zarah tace nidai banda shi, ban dai sani ba ko ibtisam Nada shi


Ibtisam tace banda lecture gobe sai 4


Mum tace toh kuzo muje


Zarah tace bari muje mu d'auko kaya, Jan hannun ibtisam tayi sukai ciki basu dad'e ba suka fito


Najeeb ganin Sun shiga motar da yake shi yana gaba yasa shi fadin Mum Ina zasu kuma?


Mum tace tare zamu gobe zasu dawo


Tsaki yaja


Driver dai tada motar yayi sukai gaba


Gudu driver din yake shararawa a titi, suna tafiya suna fira "Mum tace yanzu saura wata d'aya biki koh?
.zarah tayi caraf tace eh mum, kuma za'ayi bikin muna hutu wlh ba k'aramin dad'i naji ba


Mum tace Yadai kamata, naga ma ibtisam duk kin rame, ko karatu ne?


Ibtisam murmushi kawai tayi


Da yake da Hausa suke maganan najeeb na sauraransu sai dai wani ya gane wani kuma baya ganewa, Yadai San suna maganan ibtisam zatai aure, "cikin ranshi yace amma kam duk Wanda ya aureta zaiyi fama, yarinyar da kwata kwata nawa take? Shekararta nawa da za'ayi mata aure tun yanzu, "Wanda dai ya aureta zai auri rashin kunya sannan babu abunda zai samu dan banga alaman tana da abunda mata ke dasu ba


Kai tsaye basu tsaya koh inaba sai hotel 17, inda suka Kama d'aki, guda hud'u, Mum ita d'aya Zarah da ibtisam d'aya sai NAJEEB d'aya driver d'aya.


Kowa shiga d'akinshi yayi danya huta.


NAJEEB Bayan ya shiga abinci yayi order yace a Kawo Mai, "domin yunwa yake ji, and bazai iya cin abincin dasu mum sukaci ba a skul din su Zarah


Washe gari k'arfe 10 duka suka gama shiri domin Kama hanya bayan sunyi breakfast a restaurant din hotel din "shi kam NAJEEB baici komai ba dan bai fito ba, koda ya fito yace kawai su kama hanya basai yaci abinci ba


Zarah gaida Najeeb tayi ya amsa da fine kawai. " ganin mum a wajan yasa ibtisam itama gaidashi Mai yakon ya amsa saiya saki tsaki tare dayin gaba "ibtisam wani irin haushin kanta taji gashi Mum hankalinta baya wajansu dama ta sani bata ko kalleshi ba


Mum tace ma driver ya kaisu garage susa su zarah a mota Kafin su tafi


Haka koh akayi Kawo garage suka kaisu, inda akayi ciniki driver ya dawo ya fad'a ma Mum, ciro kud'i tayi taba masu Zarah sannan suka fita Bayan sunyi ma mum Allah kiyaye hanya..


Wani dan tasha ne ya shiga gaban ibtisam yana fad'in hjy Ina zaki, daka ta matsa saiya shiga gabanta "tace Malam ba tafiya bane


Yace y'an mata kina dakyau fah ko zan samu number


Tsaki taja tana k'okarin matsawa ya k'ara shiga gabanta


Zarah tace Malam lafiya kuwa?


Shima driver da yake gaba ya waigo yana kallonsu tare da dawowa


Wanda a dai dai lokacin NAJEEB ya k'araso wajan wanda yana Mota yana kallon abunda ke faruwa bayan ya k'araso kallon mutumin yayi tare da tambaya lafiya kake shiga gabanta!?


Mutumin da bajin turanci yake ba yayi gaba


Najeeb kallon ibtisam yayi itama akaci Sa'a shi take kallo wani irin mugun kallo ya Mata tare da fad'in idiot, kallon Zarah yayi tare da fad'in kuzo muje mu saukeku sai mu wuce


Zarah da ibtisam bayanshi suka bi


Mum tace a'a ya kuka dawo?


Najeeb yace Mum zamu mu saukesu


Mum tace ai mun koma baya, sai kuma mun k'ara dawowa fah, suje su shiga mota kawai mana, muda ga hanyar mu nan


Yace Mum plz, muje ban son long magana plz


Mum shuru tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba


Najeeb kallon driver yayi tare da fad'in what are you waiting for?


Driver yace nothing, "tare da tada motar suka k'ara kama hanyar zaria


Cikin 45mnt suka k'arasa inda suka saukesu sannan suka Kama hanyar komawa kaduna dansu wuce Abuja


Zarah ta kalli ibtisam tace Anya Najeeb baya sonki kuwa?


Ibtisam tace kina da hankali kuwa zarah?


Zarah tace da hankali na mana, kalla saboda ke fah yasa yace a Kawo Mu har skul, duk saboda abunda wannan mutumin yayi miki


ibtisam yace badan ni yayi ba, karki k'ara fad'in haka, wlh a yanda dan uwanki ya tsaneni na tabbata ko fyad'e yaga wasu za suyi min bazai hanaba, kawai yayi hakan ne saboda ke


Zarah tace ni kuma? Naga bani mutumin yayi ma Abu ba, ke akama Abu


Ibtisam tace plz ya isa, ki daina min wannan maganan karki manta ni matar wani ce bikina saura wata d'aya so plz banso tare tajan tsaki tace ko maza sun k'are sai yayanki gwara in zauna banyi aure ba Tana fad'in haka tayi gaba cikin fushi.......




















Read and leave it, dnt share to anyone


*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*


Zarah tsayawa tayi tana kallonta cikin mamaki, "lokaci d'aya tace ikon Allah, kai Indai ana son ganin fushin ibtisam toh a had'ata da Najeeb, ace sun dace, dariya Zarah ta saki lokaci d'aya sannan tayi gaba itama


Koda ta k'arasa ganin ibtisam tayi dasu Aisha a cikin d'akin, "inda Aisha take tambayan ibtisam ina wannan handsome cousin din naki?


Ibtisam tace Idan Zarah tazo ki tambayeta yayanta ne....


Shigowan Zarah ne yasa Aisha fad'in yauwa Zarah naji dad'in ganinki, "wlh tun jiya na k'osa ku dawo sai naga baku dawo ba, yanzu ibtisam ke fad'amin kunje kaduna ne


Zarah tace eh bata wlh


Aisha tace Zarah naga brother d'inki Kai Wlh ya had'u Sosai, plz ki had'ani dashi mana


Zarah murmushi tayi cikin ranta tace aikam Indai Najeeb ne yafi karfinki domin keda kika watsar da kanki kizo kice kina sonshi, Allah ya kyauta, "amma a fili sai tace uhm karki bada mata mana


Aisha tace Wlh Indai akan dan uwanki ne wlh zan bada mata kam, "Dan Allah Zarah ki had'amu dashi, "wlh sonshi kawai naji Inayi


Zarah tace toh fah


Aisha tace ki taimaka min da number d'inshi


Zarah tace aishi baida number d'aya, domin baya zama waje d'aya


Aisha tace miye aikinsa?


Zarah tace pilot ne


Aisha tace wow, Toh plz ki bani number d'inshi na Nigeria


Zarah fad'a mata tayi, domin tasan indai Najeeb ne gata gashi


Ibtisam kam sai taji tausayin Aisha ya kamata, ita ta rasa wanda take so sai wannan mara imanin, mara tausayi Wanda bai san darajan dan Adam ba, lalle Tana da aiki, inda tasan Waye shi dako kallo bai isheta ba, miye ma Abun so a tare dashi? Tsaki ta saki mara sauti


Karfe hudu dai dai ibtisam ta tafi lecture wanda Dr jibril ne ya shigo musu, bayan ya gama lecture ya bu'kaci ibtisam ta sameshi a office


Koda ibtisam taje office d'inshi tayi nocking, "bada izinin shigowa yayi


Kai tsaye ibtisam ta bud'e kofar sannan ta shiga, "gaida Dr jibril tayi


Idonshi na kanta ya amsa tare da nuna mata kujera ta zauna..


Ibtisam zama tayi


Dr jibril baice mata komai ba sai rubutu da yayi tayi, a kalla yayi minti Goma yana rubutu sannan ya d'ago ya kalleta tare da kiran sunanta da Amina..


Amsawa tayi da na'am sir


Yace Amina Mai yasa kike son bata rayuwarki? Koma ince kin bata, keda y'ar uwarki


Kallon mamaki take mishi alaman bata gane abunda yake nufi ba


Yaci gaba da fad'in, "koda kika ga ina biye miki, ina son hulda dake badan komai bane sai yanda naga irin nutsuwarki, da kunyarki, Ashe ba haka kike ba a cikin zuciyarki ....


Amina a yanda na fahimta, koma ince gidanku kaman dakyar aka barki kika zo skul, na tabbata gidanku gidan tarbiya ne, koda ka irin firan da naji kinayi kwanaki keda granny d'inki, "is lyk ba'a son kizo skul but an barki kinzo shine kike son cin amanar iyayenki kika Fara bin kawayen banza Kece har tafiya kaduna


Da sauri ibtisam tace sir bani d'aya naje ba, wlh nida Mum ne da Zarah


Kallonta yayi cikin mamaki yace a wajan garage din Kawo na ganku kuna fitowa zaku shiga mota


Ibtisam Labarin abunda Ya faru ta bashi, lokaci d'aya hawaye ya siraro mata, wanda bana komai bane sai na zarginta da yayi da Farko, Koba komai a zargi mutum abunda ciwo Sosai


Dr jibril ido ya kura mata, yana kallonta yanda take hawaye, "lokaci d'aya ya sauke ajiyan zuciya tare da fad'in miye na kuka ibtisam?? Yau ce rana ta farko daya kirata da ibtisam


Kasa magana tayi balle ta bashi amsa


Dr jibril yace ibtisam abunda yasa na kiraki har nake fad'a miki haka, because ina miki kallon sister na, so am so sorry Kinga inda bakiyi min bayani ba zanyi ta miki wani irin kallo


Ibtisam ta share hawayenta tare da fad'in hakane, ngd daka fad'amin


Nan Dr jibril yaita bata shawara akan ta k'ara kame kanta akan kawayen banza, "daka karshe ya bata umarnin ta tafi, "koda ta tashi da ido ya bita har saida ta bace ma ganinsa


Ibtisam da Dr jibril yanzu sun saba Sosai, har takanje office d'inshi tayi mishi tambaya wani zubin, "inda su Aisha suke fad'in soyayya suke ita da Dr jibril din


Duk yanda ibtisam tayi musu bayani akan ba soyayya suke ita da Dr jibril d'inba sunki yarda Dan haka kawai ta barsu a haka dinne,.


Su ibtisam Sun Fara exam gaba d'aya koda yaushe bata samun kanta saina karatu kullum suna cikin karatu ba dare ba rana


Kabir ya kawo mata Katin biki danta rabama friends d'inta, "amma ibtisam ta'ki bama kowa, inda Zarah tace abama su Aisha Katin


Ibtisam tace a'ah bata so ta gayyaci su Aisha, domin wlh Idan Abba ya gansu zaice da y'an duniya nake kawance


Zarah taci dariya tare da fad'in Allah ya kyauta, "in mun dawo skul zasu San kinyi aure ai, zaki sha ciwon baki, suce baki fad'a musu ba


Ibtisam tace karki damu Nasan yanda zanyi musu kawai Kedai kiyi shuru dan Allah karki fad'a musu


Zarah tace shikenan, Nina k'osa ma muyi hutu wlh muje mu fara shiri dashi yanzu saura sati uku


Ibtisam tace uhm nikam ko kad'an ban k'osa ba wlh


Zarah tace uhm wai irin gulman nan na amare


Ibtisam tace Wlh dagaske nake


Zarah tace "kabir fah zaki aura masoyinki, Wanda kike so, kuma kike k'auna, wanda kuke burin mallakan junanku "ko yanzu dai an rage sonshi ne?


Ibtisam tayi murmushi tare da fad'in ko kad'an, wlh Zarah ina matukar son kabir, tsantsar so nake mishi, bazan iya kwatanta miki irin sonda nake ma kabir ba, but zan iya cewa sonshi yana tafiya tare da jinin jikina ne, domin daka ranan da sonshi ya fita ina tunanin nabar duniya kenan, domin jinin dake gudana a jikina ya tsaya cak....


Zarah tace ikon Allah, haka kike son kabir din? Ah lallai Kabir yayi Sa'a Sosai


Ibtisam murmushi tayi tare da fad'in, ko kuma kice Nayi Sa'a ba, domin na samu namiji kamili, bai tabamin maganan banza ba, wanda da yawa mazan yanzu in suka had'u da yarinya maganan banza ke kawo su


Zarah tace hakane kam, sai dai muyi fatan Allah ya had'amu da maza na gari


Ibtisam tace Allahumma Ameen.


Kullum Aisha bata da hira yanzu saina Najeeb tare da k'ara fad'a musu yanda take sonshi, da kuma irin haduwarshi, gashi kullum ta kira baya d'auka


Shi kam Najeeb a duniya ya tsani yaga aita kiranshi da yawa, sai yaji kawai baya bukatar d'aukan wayar, domin kuwa a cewarshi Indai aka kira mutum sau d'aya sau biyu bai d'auka ba, saika barshi yana uzuri, inya gani zai kira, "amma bawai kaita kira ba, yana ganin kira da wata number wanda bai sani ba, baya d'auka ne kawai saboda baya son yawan kira, sannan yasan koma Waye mistake din number yayi domin Najeeb waya Sani a Nigeria balle ya kirashi, duk Wanda ya sani yana da number d'insu, saina ibtisam dana Granny da baida shi.


Najeeb wannan karan shi d'aya yazo, ba tare da y'an matanshi ba, dan haka sai yaji kwata kwata baiji dad'in k'asar ba, dan haka ya yanke zai koma jibi kawai.


Ranan dasu ibtisam sukai hutu harna wata d'aya da sati d'aya, haka suka dinga sallama da kowa, yayinda wasu ke murna zasu gida, sukam irinsu Aisha haushi sukeji, domin Sun san idan suka koma Gida babu runs, dole a kame Kai sai an dawo skul


Ibtisam office din Dr jibril taje amma bata sameshi ba, dan haka ta tura mishi message da fad'in "sir I come to your office but you are not around, "nazo Nayi sallama, but mun wuce sai an dawo skul, Tana fad'in haka ta tura mai sa'kon sannan ta wuce tare da saka wayan cikin jaka


Ibtisam da Zarah motar Haya suka shiga, inda suka tafi Kano, domin dai Zarah tace Tana tare da ibtisam tunda biki ya matso.


Koda su ibtisam suka isa Gida, basu suka kaiba saida yamma, gaba d'aya a gajiye suka k'arasa gida, domin motar da suka shiga batai wani gudu Sosai ba


Granny ganin su ibtisam da zarah yasa ta saki gud'a tare da fad'in kunga Amarya wajan kabiru


Ibtisam da gudu ta nufi Granny din tayi hugging dinta tana fad'in wayyo Granny I miss you so much wlh


Granny tace karki karyani miye kuma nis ziyu


Dariya ibtisam da Zarah suka saki, sannan ibtisam tace Granny ina nufin Nayi kewarki da yawa


Granny tace au yanzu na gane


Nan sukai ciki inda suka zauna a falo sunata fira harda ummi.


Koda ibtisam suka shiga d'aki ta ciro wayarta cikin jakarta Wanda tunda ta saka wayoyinta cikin jaka bata K'arabi ta kansu ba, sai yanzu, ganin misscall d'in Dr jibril tayi har guda biyu, sannan message d'in da shima yayi mata kaman haka...


Plz just give me 5minnute muna meeting, I need to see you before you leave.


Koda ta gama karantawa ido ta lumshe alaman kash mai yasa nasa wayar cikin jaka? Gashi banji kiranshi ba and banda message d'inshi ba, kiranshi tayi amma taji baya shiga har sau biyu tana kira amma not reachable dole ta hakura ta barshi


Tun daka ranan da ibtisam ta dawo aka fara Mata gyaran jiki, su dilka


Gefen maganin Mata kuma Granny tace baza'a bata wani abu Sosai ba, tunda budurwa ce, kar a wahalar Mata da jika, gwara inta tare da sati biyu sai ta Fara shan maganin Mata, granny Tana gyara ibtisam Sosai, kaman yau ibtisam da Zarah na zaune saiga Granny da wani magani tazo tana fad'in firan Mai akeyi ne haka?


Zarah tace firan duniya mukeyi da kuma yanda biki zai kasance


Granny tace ai ranan saina taka rawa, "lokaci d'aya kuma ta saki gud'a


Ibtisam dariya ma Granny ta bata, tare da fad'in ai dole ki taka rawa tunda burinki ya cika za'ayi min aure, kinyi nasara


Granny tace Wlh kuwa, kaman kin sani, yarinya ai bazaki gane ba, sai an d'aura kin shiga daka ciki, zaki gane banbancin aure da kuma rashin aure, "wlh ibtisam babu abunda yakai dad'i yau a duniya kaman ace mutum na d'akin mijinshi, cikar mutum saida iyali, "yau ki duba koda namiji ne In baida iyali duk dukiyarshi sai kiga ana mishi wani kallo, in ba'ayi wasa ba sai kiga ana zargin mutum, wanda ba komai yaja mishi ba sai rashin iyali da bai dashi


Zarah tace Wlh hakane Granny ai cikar mutunci shine gidan miji, sannan in mutum Nada aure ana mutunta shi Sosai, fiye da wanda bai dashi


Granny tace yauwa y'ar albarka, "Kema Bari a Gama na takwarata sannan in dawo kanki keda wancan dan banzan miskilin, ni naji ance yazo yana nan koya koma?


Zarah tace kaman yana nan fah, dan munyi waya dashi d'azu amma yace cikin week dinnan zai koma


Granny tace saboda tsiya bazai tsaya Ayi auran ibtisam ba, Kafin ya koma?


Zarah tace Granny ai saiki kirashi kice karya koma ya jira


Granny d'auko yar karamar wayarta tayi tana fad'in kiramun mamanki tare da mi'ka ma Zarah wayar


Zarah saka number d'in Mum tayi tare da dialing number din sannan ta mi'ka ma Granny


Ringing uku Mum ta d'auki wayar tare da sallama, tana gaida Granny


Granny amsawa tayi, tare da fad'in "Ina miskili?


Mum tace yana d'akinsa... Yauwa gashi ya fito ma in bashi wayar ne?


Granny tace a'a koya amsa wayar Mai zaice? Koni Mai zance Mai tunda ba yaran juna muke jiba


Mum dariya tayi tare da fad'in hakane Mama, Yadai kamata ki koya wannan yaran na Najeeb


Granny tace wa? Allah ya kyauta barni da nawa Yaran, kina jina?


Mum tace eh inaji Mama


Granny tace ki fad'ama miskili ya tsaya Ayi bikin ibtisam Kafin ya tafi, "naji Zarah tace Zai koma.... Kallon Zarah tayi tace yaushe ma kika ce zai koma? Fassara min d'azu naji turanci kikayi


Zarah dariya ta saki sannan tace cikin satin nan, "Granny tace yauwa kina jina


Mum da itama Dariyar takeyi tace eh inaji


Granny tace cikin satin nan zai koma, kice ya tsaya Ayi bikin dashi, dan naga shi baya son zumunci sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login