Showing 54001 words to 57000 words out of 182942 words

Chapter 19 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt




Salis dake bayansu yace ibtisam, idan Kinje ki rokeshi ya baki text din da bakiyi ba, domin 20mrk ba wasa bane


Ibtisam tace kana ganin zai yarda inna rok'eshi?


Salis yace Am not sure zai yarda, but try May be ya yarda, tunda mutum ne kuma yasan Allah


Zarah tashi tayi tana fad'in bari inje inyi sallah, in tafi lecture


Koda ibtisam ta fita itama taga Aisha ita da wasu mata a zaune suna ta surutu, kuma duka firan akan in sunje club ne ga yanda zata kaya,"ibtisam tace suko kunya basaji, "club din da babu abunda ake sai iskanci da shaye shayen giya


Aisha ce ta katse mata tunani da fad'in ibtisam har kun fito?


Ibtisam ta saki murmushi tare da fad'in eh yanzu muka fito, "naga kinzo kin koma.


Aisha tace Aiko na shigo korana zaiyi wlh, baida mutunci ko kad'an


Sauran matan da Aisha take fira dasu suka zuba ma ibtisam ido, "wata Mai suna kubra tasha attachment brown da wando an matse tace wannan fah? Ban taba ganinta ba sai yau


Aisha tace d'akinmu d'aya sannan course d'aya muke karanta


Kubra tace OK, amma shine bakwa zuwa club tare


Aisha ta kalli ibtisam tace Kinji abunda take cewa, wai bama zuwa club tare


Ibtisam murmushi kawai tayi, "amma cikin ranta tace Allah ya rabani da zuwa club, kuma ina muku fatan shiriya, ku tuba ku daina...


Kubra ce ta katse ma ibtisam tunani da fad'in ibtisam koh?


Ibtisam tace eh


Kubra tace Sunan yamin dad'i, Sunan larabawa


Ibtisam murmushi tayi tare da fad'in ngd


Kallon AISHA ibtisam tayi tace plz zaki rakani wajan Dr jibril.


Aisha tace ni? Rufamin asiri Mai zakiyi a wajansa?


Ibtisam tace yace yana son ganina


Aisha tace toh fah, Allah yasa dai lafiya, kodai shima d'an hannu ne, ya gani ya kyasa?


Kubra ta saki dariya tare da fad'in uhm kibar lecturers dinnan, suna da iskanci, "amma Dr jibril ban tunanin zaiyi haka fah.


Aisha tace ke ba'a shaidan mutum wlh, "yanzu mutum zai nuna Shina Allah ne anjima kiga ba haka bane, rayuwa kawai Ayi sha'ani kawai


Kubra tace nikam ibtisam muje in rakaki, inje inji gulma komai zaice miki


Ibtisam kam kunyar jerawa da kubra take, domin irin shigar dake jikinta, Wanda mutumin kirki dan musulmi bazaiyi ba, "amma babu yanda ta iya dole ta bita suje tare tunda tana neman dan rakiya, musamman da taji ana fad'in kodai dan hannu ne shima, "sai taji ta tsorata dan dama tasan ana cewa lecturer suna iskanci da student d'insu in ta'ki yarda sai su fadar da ita a course d'insu


Har office din Dr jibril suka isa, da yake kubra tasan office din, nocking sukayi yace yes coming


Bud'e kofar kubra tayi ta Fara shiga, ibtisam na bayanta kallo d'aya zaka mata ka gane jikinta yana d'ari d'ari


Karatun al'qur'ani yake saurara


Ganin Sun shigo yasa ya kashe karatun tare da kallon kubra yace lafiya?


Tace sir cikin d'ari d'ari na rakota ne.


Yace OK you can leave


Fita kubra tayi da sauri


Ibtisam kanta na k'asa idon Dr jibril na kanta ganin yanda ta tsorata ba tare da ance wani abuba, inda zaiyi ihu da karfi zata iya zabura


A hankali yace you can sit


Zama tayi akan kujeran daya nuna mata


Yace ya sunanki?


Tace Amina, but ana cemin ibtisam


Yace OK


Tare da fad'in mai yasa kika fita a lecture Rannan da zan bada text, ko mark dinne bakya so?


Da sauri tace a'ah


Yace so tell me why kika fita?


Tace saboda ban San abunda zan rubuta ba, sai yasa na fita, ranan shine farkon shigana lecture


Yace amma ai an dad'e ana lecture why baki Fara attending ba sai ranan?


Tace akwai problem din da yasa ban fara attending da wuri ba, sai daka baya aka yarda inzo


Yace which problem?


Shuru tayi tana d'an nazari, can tace "sir is family issue


Murmushi yayi tare da fad'in oh ok sorry for asking you


So yanzu kinyi missing 20mrk kenan right?


Ibtisam tace plz kayi hakuri ka bani inyi, tunda ranan na fara attending kuma kona rubuta I will fail, that is the reason da yasa naga gwara kar in rubuta din


Idon Dr jibril na kanta yana kallon yanda take magana, ba kaman daba da take kaman a tsorace, "yanzu ta dan sake


Yace OK zan baki text, but not now kizo gobe by 5pm sai in baki.


Da sauri ta d'ago ta saki murmushin da yake k'ara Mata kyau, tare da fad'in "nagode sir


Yace karki damu you can go


Tashi tayi cikin murna ta fita..


Dr jibril da ido ya bita yana murmushi.


Koda ibtisam ta fita taga kubra tsaye tana jiranta.


Bayan ta fito kubra ta kura mata ido tun daka sama har k'asa


Ibtisam tace lafiya irin wannan kallon?


Kubra tace ina son insan koya miki wani abune, "Sai yasa nake kallonki inga Ina ya taba .


Ibtisam tace auzubillah "wlh kinyi mishi sharri domin ba haka yake ba, kuma ko maganan banza baiyi min ba, "infact ma magana yayi min akan Mai yasa da yace zai bada text na fita? "shine na fad'a mishi dalili, har yace zai ban text din inyi, "ni Bama yanda nake tunanin ana fad'a akanshi Nayi ba, mutum ne mai sauk'in Kai a yanda na Lura raini ne kawai baya so, "sannan yana kama kanshi ne da shaidanun student masu kaima lecturer tallan kansu.


Kubra tace uhm ibtisam kenan, daka had'uwa dashi yau yau har kin Fara bada shaida a kansa haka?


Ibtisam tace ba haka bane, kubra Ina son ki gane wani abu, koda yanzu kika had'u da mutum indai kuka zauna kukai maganan minti biyar Zaki dan iya fahimtar Waye mutum da kuma irin abunda mutane ke fad'a akanshi


Kubra tace toh ba girin girin badai, "Allah yasa Dai kar nan gaba inji kina tsine Mai, kina fad'in Ashe haka yake


Ibtisam tace insha Allah bazaiyi abunda za'ace tir ba, domin koda Yana aikata wani mummunan Abu, yanayi a boye Toh Allah zai iya shiryashi tunda a boye yakeyi "amma wanda yakeyi a fili shikam sai dai ace Allah ya kyauta, mutum ya dinga Abu baya tsoran kowa, baki'i uban kowa ya gani ba, Kinga wannan yayi nisa baya fatan shiriya,"kuma shaidan duniya itace ta k'iyama daka ranan da mutum ya mutu za'a turo mala'iku suzo suji abunda mutane ke fad'a akan ka


Idan mutane na fad'in oh an rage mugun iri, ka bani


Inko aka samu ana yabanka ana fad'in mutumin kirki, koda kana aikata sabo a boye babu wanda ya Sani, sai Allah to Allah zai yafe ma mutum tunda wannan tsakanin Allah da bawa ne, kuma sirrin da Allah ya rufe babu Mai tona shi


Kubra tace Allahu Akbar, "Ashe ibtisam din malama ce?


Ibtisam tayi murmushi tare da fad'in daliba dai, muna koya ne


Tafiya sukayi daka wajan inda suka nufi d'akin su ibtisam din, suka iske Aisha na zaune tana waya


Ita dai ibtisam zama tayi tana jiran gobe tayi taje Dr jibril ya bata text din, d'auko littafi tayi ta Fara karatu


Bayan Aisha ta gama wayar ta kalli kubra tace ya kuka kaya dashi?


Kubra tace korana yayi da muka shiga


Aisha tace ita d'aya kika bari? Maiya mata?


Ibtisam dake karatu tace babu komai, tare da bata labarin abunda ya faru


Aisha tace kodai yana miki wayau ne nan gaba ya fito da mayyatarshi, dan naga nashi Abun kaman da salo yakeyi


Ibtisam tace Wai Mai yasa kuke mishi mummunan zato ne? Dan Allah ku daina Wlh babu kyau, tunda baice komai ba Kubar mishi mummunan zato, ku dinga kyautata zatonku akanshi plz


Aisha tace lallai ibtisam ke yarinya ce baki San mai duniya ke ciki ba, kin ganni nan, "babu irin iskancin da ban sani ba, "sannan babu wani salo dana miji zai kawo in kasa gane inda ya dosa, "kuma Wlh zaki ce ni Aisha na fad'a miki, wata rana saiya fito miki da manufarshi


Mutumin da baya wasa, baya sakar ma kowa, in bakayi text d'inshi ba, kokai Waye kayi missing kenan, 'amma ke har yace kije office d'inshi sannan ya yarda zai miki, uhm akwai wata a k'asa Dai


Ibtisam cikin ranta tace Wai Mai yasa mutanan da suke aikata sabo suke ganin kaman kowa ma haka yake.


Lallai maganan da malamin su ya taba fad'a musu gashi yau ta tabbatar, in mutum yana Abu sai yaga kaman kowa ma irinsa ne, sai yaga kaman kowa ma yana irin abunda yakeyi," mutumin kirki shine wanda yake ganin kowa kaman na kirki ne, na banza yana ganin kowa na banza ne. "Amma a fili sai tace nidai bayyi min Kama da mutumin banza ba


Kubra tace bazaki gane ba, gaba muke miki tunani kuma zakice mun fad'a


Tashi kubra tayi tana fad'in bari inje in dawo tare da kallon Aisha tana fad'in "anjima 8 akwai birthday din fatin d'akinmu ta fad'a miki kuwa?


Aisha tace eh ta fad'amin Zanzo


Kubra tace OK tare da kallon ibtisam tace Kema Ina inviting d'inki Tana fad'in haka ta fita


Aisha ta kalli ibtisam tace ina fatan zaki je koh?


Ibtisam tace Kai Anya kuwa


Aisha tace a cikin skul ne ba wani waje ba


Ibtisam tace OK tunda cikin skul ne Zanzo nida Zarah


Aisha tace OK saimu je tare gaba d'aya


Koda zarah ta dawo ibtisam tace su shirya zasu birthday din wata cikin skul din za'ayi


Zarah tace ok, amma fah ni bana son shiga iri irin wannan Abun.


Ibtisam tace nifa da Farko nace ba zani ba, saida akace a skul za'ayi


Zarah tace ok.


Ibtisam da zarah sun shirya duka cikin dogayen riga, ita Zarah doguwar rigan atamfa tasa, ita kam ibtisam jallabiya sunyi kyau Sosai duk da ba makeup sukayi ba, sai dai ita Zarah ta shafa powder


Bayan sun gama shiri, suka zauna jiran AISHA Dan tare zasu, dan ita ibtisam ba sanin d'akinsu kubra din tayi ba.


Aisha ce ta shigo cikin riga da wando, tare da fad'in ku muje, na tsaya amsan abune


Fita sukayi, har bakin gate Aisha ta tsaida mota suka shiga


Ibtisam tace kunce cikin makaranta?


Aisha tace eh amma a cikin gidan wanda suka Kama d'akin waje za'ayi...


Ibtisam bata k'ara cewa komai ba, har motar da suka shiga Aisha tace ta tsaya a nan.


Fita sukayi Aisha ta biya kud'in suka shiga wani Gida inda d'akuna ne Kala Kala a kalla yakai 30 daka ganin dai gidan d'akin dalibai ne, "baka jin k'aran komai saina kid'a da ihun Mata ana rawa, ko wacce ta tsuke cikin shiga mara kyau


Ibtisam da zarah kallon juna sukayi


Samun waje sukayi suka zauna inda suke kallon irin rawan da sukeyi, gaba d'aya babu maza sai mata, ibtisam tana cikin wannan tunanin saiga maza sun Fara shigowa kaman ana turosu kuma duk dalibai ne mazan student


Nan wajan ya k'ara kacamewa da ihu, inda maza da mata suka fara rawa cikin rashin kamun kai da fitsara


Suna rawan a manne da jikin junansu, basa kojin kunya.


Yayin da wasu ke zaune a gefe suna shan shisha wasu kuma suna shan codeine kuma duka student Abun dai babu kyan gani


Zarah ta Katse ma ibtisam tunani tare da fad'in jiba birthday din babu ko tsari, wannan Aiba birthday bane, ni ko cake ban gani ba


Ibtisam tace uhm, kawai dai sun had'a party suyi rawa, "ni tashi mu koma dan ban son kallon wannan iskancin wlh


Zarah tace a'ah mu tsaya Kinga dare yayi saimu fita muda yawa, mu zauna a nan iya kacin mu kallo


Ibtisam tace Allah ya kyauta


Zarah ta amsa da Ameen


Haka suka zauna suna ta kallo ashe anyi cake, an ajiye ne a ciki lokaci d'aya aka d'auko birthday girl ta yanka nan suka saki ihu ana tafi


Su ibtisam na nan zaune saiga kubra tazo, tace zan kuka zauna? "kuzo kuyi rawa mana.


Ibtisam tace a'a barmu kawai a nan


Kubra tace haba miye haka? Duka fa nan student ne babu bare, plz ku tashi mana, janyo hannun ibtisam tayi wanda dole yasa ta tashi sannan ta janyo zarah itama, tare da fad'in muje kuyi rawa


K'aran wayan ibtisam ne yasa ta janye hannunta daka na kubra tana kallon wayar cikin tsoro ganin sunan Ummi ne a cikin wayar tana kiranta, "gashi wajan k'ara yayi yawa, "janyo Zarah tayi suka fita daka wajan amma still k'aran kid'an har waje


Saida sukayi nisa da wajan sannan ibtisam ta tsaya "Zarah tace miye kike ta jana lafiya?


Ibtisam tace ummi ce ta kirani ban San mai zata cemin ba, gashi wajan k'aran kid'a yayi yawa, "bari in kirata inji mai zata ce


Kiran Ummi tayi, "ummi ta d'auka tare da fad'in ina aka shige aka ajiye wayar?


Ibtisam tace ummi wayar na silent ne tunda na fito daka lecture Ashe ban cireta a silent ba


Ummi tace ok, Nayi magana da abbanki, gobe zai bada wayar ta Mota a Kawo miki, zaiba driver din number d'inki saiki je ki amsa


Tace toh ummi tare da fad'in nagode ummi na.


Ummi tace akwai abunda kike bukata?


Tace a'a ummi bana bukatar komai, ina Granny?


Ummi tace bari inkai mata


Ummi taba granny waya, ibtisam tace Granny shine ko kirana bakyayi a wayarki koh?


Granny tace yaushe zan kiraki yanzu kin zama y'ar jami'a Kema zaki fara fitsara irin na miskili, in kira a fad'amin ba dad'i


Ibtisam tace Granny lallai kince wani abu, Sharrin da zakiyi min kenan koh?


Granny ta tsuke baki tare da fad'in ke yanzu kin fison zama a wani gari koh?"zaki sa aita miki kallon y'ar iska, ni wannan Abun kunyar har Ina, haba takwara ta ki dawo gida mana in anyi bikin naku keda kabirun sai kici gaba a dakin ki, Kinga babu wanda ya gani balle yace


Ibtisam tace Kai granny wai Mai yasa kike haka ne? Ni ginka sai anjma


Granny tace ai kyace sai anjima tunda ba'a son gaskiya, zan kira kabirun ai inji dalilin da zai yarda yace kije wani gari karatu tunda shi baida kishin kanshi


Ibtisam dariya ta saki tare da fad'in Kinga Granny sai anjima tare da kashe wayar


Zarah itama dariya tayi tana fad'in Granny ba dama hala mita take miki


Ibtisam tace Wlh kuwa, mitan na'ki aure kin San ita magananta kenan, ta matsa inyi aure ansa rana amma duk da haka bata kyaleni ba, ita wannan bokon ne dai bata so, na rasa dalili tsohuwa sai jaraba.


Zarah tace nikam wlh abunda Granny take fad'i gaskiya ne, ai kinzo jami'ar Kinga irin abunda akeyi a cikinta


Ibtisam tace Aiba duka aka taru aka zama d'aya ba, akwai na Allah Sosai, amma y'an iskan ne sukai kaurin suna


Zarah tace Allah ya kyauta Kinga mu wuce skul kawai, dan bazan koma ba tunda mun fito, machine suka samu suka hau 2 in 1 domin Sun dad'e suna jiran Abun hawa basu damu ba, sai yanzu shine suka haye machine din guda d'aya su biyu


Har cikin skul ya kaisu inda suka sauka suka biyashi sukai d'akinsu, suna shiga kiran kabir na shigowa wayar Ibtisam tace Wai Allah ya soni


Washe gari kaman yanda Dr jibril yace ma ibtisam hakan ko akayi 5 dai dai ibtisam ta nufi office d'inshi tayi nocking ya bata izinin shiga


Bayan ta shiga ta gaidashi cikin girmamawa


Ya amsa tare da sakar mata murmushi yace you can sit


Tana zama wayarta dake hannunta ya fara K'ara, k'okarin kashe wayar ta Fara yace you can answer it


D'auka tayi tare da sawa a kunne


Sallama aka mata tare da fad'in nine akaba sa'ko IN baki gani garage kina ina?


Ibtisam tace ina ABU plz ka taimaka ka Kawo min ban San ko inaba a cikin zaria ba


Yace kai gaskiya kiyi hakuri kiyi tambaya sai kizo ki amsa, kuma kiyi sauri dan nan da awa d'aya zan juya Kano.


Ibtisam tace toh kaban nan da lokaci kad'an zan tambayi inda garage din yake inzo


Dr kabir idonshi nakan ibtisam Bayan ta kashe wayar yace Mai zakiyi a garage?


Tace sa'ko aka aiko min dashi, daka Kano, gashi yace bazai dad'e ba zai koma and....


Sai kuma tayi shuru


Yace and?


Tace nothing sir am ready for the text


Tashi yayi tare da daukan key din motarshi yace muje tare dayin gaba


Binshi tayi da ido tana kallonshi, tare da tunanin Ina zamu????


Ganin yakai bakin kofa bata ko motsa ba, yace I said let go


Tashi tayi da sauri ta fito ya rufe office din


Tafiya ya fara tana bayanshi har wajan daya faka motarshi k'iran Benz, yace shiga muje


Bata shiga ba sannan batai magana ba, domin ita dai bata san ina zasu ba inta shiga, sannan akan wani dalili zata shiga motarshi?


Dr jibril yace Amina Mai yasa idan akayi magana sau d'aya bakya d'auka sai an k'ara repeating din magana?


Tace sir kawai naga ban San inda zamu bane sai yasa


Yace zanje in sai dakine


Da sauri ta d'ago ta kalleshi cikin mamaki


Ganin irin kallon data mishi yasa yayi dariya tare da fad'in calm down am joking,"just enter d car


Ganin bata da niyan shiga yaga alaman tana jin tsoro yace shine matsayin text d'inki, and in baki shiga ba zanyi failing naki


Bud'e kofar tayi ta shiga Tana tunani iri iri a ranta


Shiko ganin ta shiga ya tada motar yabar skul din


Ibtisam kam bata sake ba domin a tsorace take dashi, tana tunanin Ina zai kaita daya d'age saita shiga cikin motarshi, kodai abunda su Aisha suke fad'i gaskiya ne. ....






*nayi na yau da gobe coz gobe inada uzuri bazan samu daman typing ba, sai jibi insha Allah zanci gaba*














Read and leave it, dnt share to anyone




*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login