Showing 159001 words to 162000 words out of 182942 words
Chapter 54 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
ganta a kwance kanta a cinyar najeeb, wanda yasa ta tashi da sauri tare da kallonshi suka had'a ido, tayi saurin kawar da kanta gefe
Murmushi yayi domin ganin yanda take Abu kaman dole an matsa mata.
Tafiya suke har suka k'arasa garin Abuja babu wanda ya k'ara koda kallon Dan uwansa balle yayi mishi magana, koda suka k'arasa masu aikin Gidan suka kwashe musu kaya, inda ibtisam kai tsaye tayi d'akin Zarah domin har yanzu kanta na Mata ciwo tana bukatar ta kwanta ta huta, tana shiga toilet tayi ta dauro alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta hau gado sai bacci
Zarah ganin tana bacci yasa tayi dariya tare da fad'in ai dole gaba d'aya tunda akai rasuwa bata samun wani baccin kirki
Najeeb shima part d'inshi ya nufa, inda yayi toilet tare dayin wanka, da yake shi yayi sallah domin saida yasa driver ya tsaya yayi sallah, shima kwanciya yayi domin yana bukatar ya huta
Yau kwanan ibtisam Biyu a Abuja bata K'ara bari sun hadu da najeeb ba, domin kullum tana d'aki, yau Tana zaune tayi wanka tasa Wata ba'kar jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan yayi mata kyau duk da ita ba ma'abociya son kwalliya bace.....
Zarah ta fito daga toilet tace sai Ina haka??
Ibtisam tace ai tare zamu fita, domin zamu skul din su Ahmad ne Ina son ganinshi na tabbata bai San Granny ta rasu ba
Zarah tace hakane kam, bari insa kaya muje Toh, Suma naji ance sun kusa Fara exam, ya kusa dawowa gida
Zarah itama jallabiya ta saka amma ita nata brown, ya mata Kyau, tace ma ibtisam muje
Fita sukayi inda Zarah tace bari in fad'ama Mum samu fita, part din Mum tayi inda ibtisam ke tsaye a falon tana jiranta.....
Najeeb ne ya shigo falon kallonta yayi har zai wuce ya fasa tare da dawowa yazo gabanta ya tsaya.....
Ibtisam fat fat fat gabanta ke fad'i ga zuciyarta dake bugawa da karfi
Idon shi na kanta yana kallonta, da sauri tayi k'asa da kanta
Yace sai Ina??
Kasa magana tayi domin gaba d'aya yanzu ta rasa mai yasa take jin nauyinsa gashi yana mata wani kwarjini Sosai
Yace am asking
A hankali tace zamu skul din su Ahmad
Yace da izinin wa??
Da sauri ta d'ago ta kalleshi ganin ita yake kallo shima yasa tayi k'asa dakai da sauri
Najeeb yace ban yarda a fita ba, saida izini na, tunda zaki fita without my permission ban amince ba, and kin San hukuncin macen data fita ba tare da izinin mijinta ba??
Ibtisam shuru tayi tana jinshi, amma cikin ranta Abun haushi yake bata akan wani dalili zaice saita wani tambayeshi Bayan shi ba d'aukanta yake a matsayin mata ba....
Yace koh kina son tsinuwan mala'iku ne a kanki??
Da sauri ta girgiza kai alaman a'a
Ganin haka yasa yace so as from today duk inda zaki you have to ask me, inna yarda sai aje in ban yarda ba a zauna a gida
Ibtisam bata ce komai ba,..... Zarah ce tazo tana fad'in bros Mum ta fita ne??
Yace eh ta fita d'azu what happen??
Tace no dama zan fad'a mata zamu fita ne
Najeeb yace zaki fita da matata ba tare data tambayeni ba?? Wato ke kike son janta yawo right???
Zarah ta zaro ido tare da fad'in Wlh bros nifa Banyi niyan fita ba, ita tace in shirya in rakata, ni Wlh fitan nan dan dole zanyi ni dama zaka kaita.....
Ibtisam wani harara ta sakar ma Zarah ta gefen ido
Najeeb kallon ibtisam yayi tare da fad'in Kinji abunda tace nima inada abunyi saiku koma ciki, domin ban yarda da wannan fitan ba
Yana fad'in haka yayi part d'inshi
Ibtisam wani haushi ne ya cika ta, ji tayi kaman ta fasa ihu dan takaici, yanzu kenan duk inda zata saiya bata izini
Zarah dariya tayi tare da fad'in Kinji abunda mijinki yace saiki koma
Tsaki taja tare da hararan Zarah tayi ciki da sauri
Zarah dariya tayi tana fad'in, wannan Abun naku yana ban dariya
Najeeb koda ya shiga part d'inshi kwanciya yayi tare da lumshe ido bacci yake son yi amma ya kasa gaba d'aya sai juyi yakeyi, maganan Granny ne yake tamai yawo a kunne, ina son ku kasance a haka har abada, da sauri ya k'ara lumshe ido yana mata addu'a
Tashi yayi lokaci d'aya ya fita inda ya shiga mota tare da tada ta ya fita yabar gidan
Ibtisam na kwance gaba d'aya ranta babu dad'i domin tana son ganin k'anin Nata amma ya hanata fita
Tana nan zaune saiga Ahmad ya shigo yana fad'in sis sis
Ibtisam da sauri ta tashi Tana fad'in Ahmad, dama yau zaka dawo? Rungume juna sukayi ita dashi suna murna
Yace a'a bros NAJEEB ya daukoni yace Kece kike son ganina
Ibtisam bata san lokacin data saki murmushi ba
Zama sukayi inda zarah ta shigo d'akin Tana fad'in Toh yanzu saiki bar fushi tunda mijinki ya kawo miki abunda kike son kije ki gani
Murmushi ibtisam tayi
Ahamd yace ina Abba da ummi, da y'ar tsohuwa mai jaraba
Ibtisam kuka ta saki tare da fad'in Ahmad Granny ta rasu......
Ahmad gaba d'aya shuru yayi yana jin wani abu yana mishi yawo a Kai..... Yayi wajan 5 mnt a haka sannan ya saki dariya yana fad'in granny din kike ma fatan mutuwa?? Wlh Bari ta jiki zaki sani shine harda wani kuka koh?? Toh ai ba first April bane balle ace April Fool .....
Ibtisam tace Ahmad dagaske Granny ta rasu jibi ne zata cika kwana 7
Tashi yayi da sauri ya fita ganin haka Zarah da ibtisam suka bishi
Direct part din najeeb ya shiga inda ya Tarar dashi daga shi sai boxer da singlet
Najeeb yace Ahmad lafiya kuwa??
Dai dai lokacin ibtisam ta shigo ita da Zarah
Najeeb idonshi ya sauka akan na ibtisam dake kuka
Nufan Ahmad tayi ta rungumeshi tana fad'in Ahmad dagaske nake maka....
Ahmad yace Ban yarda ba, kallon najeeb yayi tare da fad'in bros dagaske abunda take fad'a gaskiya ne Granny ta rasu....
Najeeb yace eh dagaske ne ta rasu....
Ahmad wani irin kuka yasa Mai ban tausayi, tare da fad'in shine babu wanda ya fad'amin sai yanzu, wayyo Granny, kuka yake Sosai
Najeeb gaba d'aya sun Fara juyar Mai dakai ga ibtisam na kuka wanda yake jin kukan nata har cikin ranshi, ga Ahmad shima yana kukan
Karfin hali yayi inda ya kalli Ahmad yace haba Ahmad karka manta addu'a take bukata ba kuka ba, kaifa namiji ne, taya zaka dinga kuka irin haka?? Namiji an sanshi da dauriya
Nan Ahmad ya share hawayen idonshi tare da fad'in hakane, addu'a take bukata ba kuka ba, rayuwa kenan, Allah yaji k'anki Granny yasa kin huta.
Zarah da najeeb suka amsa da Ameen
Ganin Ahmad yayi shuru yasa najeeb nufan ibtisam tare da ru'ko hannunta....
Ganin haka yasa Ahmad da zarah suka fita daga d'akin
Najeeb d'ayan hannunshi yasa yana share mata hawayen idonta tare da fad'in plz ki daina wannan kukan, kalla yanda gaba d'aya kika saka kanki cikin damuwa duk kin rame, karki manta duk wani mai mai mamaci ne, dole mai rai saiya mutu komin dad'ewa, sannan ita Granny addu'a take bukata ba kuka ba.....
Cikin kuka tace kasan zafin rabuwa da wanda kake so a rayuwa kuwa?? Sai yanzu nake yarda da abunda ake fada ba mutuwa akema kuka ba sabo ne, d'aki d'aya nake kwana da Granny, gado d'aya, koda tafiya zatayi yawanci tare mukeyi, sabo dani yasa ko tafiya bata son yi, sanda zan tafi skul babu yanda batayi ba akan in fasa tun Tana fad'in bata so harta dawo tana fad'in in zauna a Kano inyi kar inje wani gari, kasan mai yasa take fad'in haka??
Duka saboda Sabo ne, ta saba dani, bata son inyi nesa da ita, gashi yau na wayi gari gaba d'aya babu ita a cikin wannan duniyar, dole inyi kuka, kukan ne kad'ai zaisa in rage abunda nake ji, kaf duniya bana tunanin akwai wanda ya shaku da Granny sama dani, a gaban idona ta fad'i ta Fara jinyar kwana biyu, haka a gaban idona ta mutu, wannan abubuwan gaba d'aya sun kasa goguwa a idona
Najeeb matseta yayi a jikinsa tare da fad'in daga ranan da mutum ya rasu, a lokacin baya son komai sai addu'a, domin wannan addu'a ita yafi bukata, ita kad'ai ce mutum Zaima mutum ka nuna mishi gata
Nasan yanda sabo yake, lallai nasan dole ki shiga cikin wani hali, but Ina son kiyi hakuri a duk sanda kika tuna ta kiyi mata addu'a, kinji
Ta tsagaita da kukan amma bata bashi amsa ba, tana nan dai manne a jikinsa
Najeeb ganin haka yasa ya dan cireta a jikinsa, yaja hannunta yai gadon d'akin da ita tare da zaunar da ita akai
Shima zama yayi a kusa da ita, ya kura mata ido, abubuwa da yawa yake ji a game da ita, wanda bazai iya misalta yanda yake jiba, gaba d'aya baya Son ya ganta cikin damuwa
Ibtisam kam lokaci d'aya ta tashi tare da fara tafiya Tana son barin d'akin
Najeeb rukota yayi tare da rungumeta yana fad'in ibtisam, sanda Granny zata rasu ta ro'ki alfarma akan mu kasance tare har abada, wannan shine magananta na karshe......
Ibtisam a hankali tace ina sane ban manta ba, amma ina son ka sani zan zauna dakai domin haka Granny take Fata, amma badan ina so ba, najeeb gaba d'aya har yanzu na kasa manta abun da..... Sai kuma ta saki kuka tare da k'okarin jan jikinta daga nashi
Shi kam najeeb ido ya lumshe jin tana k'okarin kwatan jikinta daga nashi yasa ya saketa tun Kafin ta fad'a mishi Kalman da yafi tsana a duniya
Fita tayi da sauri Tana kuka
Najeeb idonshi ne ya canza launi, Lokaci d'aya ya lumshe ido, tare da zama a kujeran dake kusa dashi wanda yake cikin bedroom din nashi
Ibtisam kam daki ta shiga inda ta tadda babu kowa kwanciya tayi akan gadon d'akin tana kuka, ba komai take tunawa ba sai yanda taga najeeb da Najwa, duk yanda taso ta manta da abun amma saita kasa, Abun yana damunta sosai, tana jin Abun Sosai a cikin ranta, ko tayi niyan sakewa dashi saita kasa inta tuna abun , taci kuka Sosai har bacci yayi gaba da ita
Washe gari da safe suna zaune a dinning suna breakfast saiga najeeb yazo inda ya gaida iyayenshi cikin girmamawa
Dad amsawa yayi tare da fad'in an tashi lafiya??
Yace lafiya kalau..
Ahmad da Zarah gaida najeeb sukayi wanda yasa itama ibtisam ta gaidashi
Amsawa yayi ba tare daya kalleta ba..
Dad yace ma najeeb anjima kaida mamana ku shirya kuje kuga wani gida dana siya nasa an saka komai, saiku koma can, inda akwai abunda kuke bukata saiku k'ara da kanku
Mum tayi dariya tare da fad'in Aikam, yauwa ba yanzu zata koma ba, sai anyi Mata kayan akwati gaskiya, domin ba'ayi mata ba, naso inyi tafiya inje in had'a mata Toh ban samu naje ba, abubuwa nata taso wa
Najeeb yace Mum zamu saudiya cikin week dinnan, domin ina son muje mu duba mahaifin malami na, sannan kuyi mishi godiya daya koyar dani
Mum tace hakan yayi.
Wajan k'arfe biyar NAJEEB ya kira Zarah tare da fad'in ta turo Mai ibtisam tazo ta sameshi a mota
Fad'ama ibtisam abunda najeeb yace tayi har zata ce basai taje ba, ta tuna da abunda abba yace, tashi tayi tasa after dress akan kayan dake jikinta ta fesa turare sannan ta kalli Zarah tace kizo muje tare mana
Zarah tace wa?? Sai dai kun dawo, ban zuwa gayyan sodi muje in rakaki Mota dai
Fita sukayi najeeb tunda ta fito ya kura mata ido, har suka k'araso zarah ta bud'e Mata Bayan motar inda najeeb ke zaune ta shiga driver yaja
Har suka k'arasa gidan babu wanda yama dan uwansa magana
Bayan sun k'arasa fita yayi itama ganin haka yasa ta fita suka nufi cikin gidan, wanda NAJEEB ya bud'e wow Masha Allah, falon babba ne yayi mugun tsaruwa ga kyau, gidan d'aki d'aya a k'asa da falo sai kitchen sannan d'aki hud'u a sama da falo
Ko wani d'aki ansa kayan furniture Gidan yayi mugun tsaruwa, kallonta najeeb yayi tare da fad'in mai kike bukata a saka a ciki??
A hankali tace babu komai
Yace ok, fita sukayi inda ya amshi ke din motar yace driver ya koma Gida bayan ya bashi kud'i, kallon ibtisam yayi yace shiga gaba muje
Bata Musa mishi ba, domin a yanzu tayi aniyar bin umarninshi duk da bawai tana sonshi bane, zata bishi tunda shine a saman ta, uwa uba tana tuna abunda Granny tace sannan da abunda mahaifinta shima yace Mata
Tuk'i yake basu tsaya ko ina ba, sai wajan saida waya inda yace ta fito suje, Bayan sun shiga yace a bashi latest iPhone inda aka d'auko Mai iPhone 11 ya amsa tare da tambayar Kudin aka fada mishi, ATM d'inshi ya bada aka cira cikin POS sannan suka fita kai tsaye mtn office suka nufa yace a bashi sim card, shi yayi register da sunanshi da komai nashi
Bayan sun koma Mota ne yace ta bashi duka iPhone d'inta
Kallonshi tayi alaman akan wani dalili??
Ganin bata da niyan bashi yasa ya d'auki wayar duka a gabanta ya goge komai na ciki, tare da kallonta Wanda itama shi take kallo yace ba bincike zanyi miki a waya ba, gashi na goge komai, ciro sim d'inta yayi a gabanta ya karya sim din guda biyu, ya jefar tare da mi'ka mata wayar daya siya da sim din, yace bana bukatar kiyi amfani da abunda bani na siya ba...... Yana fad'in haka ya tada motar sukai gaba
Ita ibtisam mamaki abun yake bata, Toh miye na karya mata sim, tare da ri'ke Mata wayoyi, Indai haka yake ji basai ya siya mata sim kawai ba
Shi kam NAJEEB ganin wayoyin hannunta yasa yake zargin kabir ne ya bata, wanda ya tambayi Zarah tace kabir ne ya bata wannan shine dalilin da yasa baya son ganin wayoyin a hannunta, domin kwata kwata baya bukatar abunda ya shafi kabir a wajan ibtisam din....... Hmmm ikon Allah toh wannan idan yaji kabir din yabar mata kayan akwati ya zaiyi????
Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Bayan sun isa Gida ibtisam tana ganin ya faka motar ta fita tayi cikin Gida da ledan wayar daya siya mata, koda ta shiga ciki babu kowa a falon d'akinsu ta tafi Kai tsaye inda ta iske Zarah zauna tana danna waya, ajiye ledan wayar tayi akan gadon d'akin
Zarah d'auka tayi tana bud'ewa lokaci d'aya tace wow latest iPhone, waya baki??
Ibtisam tace wa kike tunani zai bani
Dariya zarah tayi tare da fad'in your darling hubby
Ibtisam Hararanta tayi tare da fad'in kyaji dashi dai
Zarah tashi tayi tare da saka wayar a caji tana fad'in, ni kam so nake inga camera din wayar nan, da suka saka har guda uku, bari yayi caji in gani
Ibtisam tace uhm aiki ja
Najeeb ganin ta fita yasa ya girgiza Kai tare da fitowa shima yayi cikin gidan inda yayi d'akinshi direct
Ibtisam bayan sun fito yin dinner inda Mum take tambayanta gidan yayi
Tace eh mum cikin jin kunya
Dad yace ina najeeb din yake ma??
Mum tace yana d'akinsa Nasan
Dad bayan ya gama cin abinci tashi yayi yana fad'in yau a gajiye yake, kai tsaye bedroom yayi domin yana bukatar ya kwanta ya huta
Mum tashi tayi itama tabi bayan mijinta inda ya rage daga Zarah sai ibtisam Ahmad ya koma skul
Zarah sai faman d'aukan hoto take da wayan ibtisam din, ita kam ibtisam abinci take ci abunta
Najeeb ne ya fito inda yazo ya zauna a kujeran dake kallon na ibtisam
Zarah tace bros shine ni baka siyo min wayar ba, nima in fito gari ba
Kallon ibtisam yayi wacce akai Sa'a itama shi take kallo gira ya d'aga Mata alaman Yadai
Da sauri ta juyar da kanta tare da ajiye spoon din abincin da takeci
Najeeb ganin haka yasa yayi murmushi, lokaci d'aya kuma ya kalli Zarah tare da fad'in, wace waya kike ri'kewa??
Tace Bros iPhone 7 cefa
Yace ok saiki bari in munje saudiya in siyan miki
Tace Bros plz kaban kud'in gobe muje mu siya mana..
Yace ke dawa zaki goben??..
Tace ni da ibtisam, ta k'arasa maganan cikin dariya
Najeeb yace ashe ba zaki ba, ni daga yanzu babu inda zata dinga zuwa
Kallon ibtisam yayi da take sauraransu yace plz yunwa nakeji bani abinci Inci
Ibtisam kallonshi tayi cikin ranta tace Wlh wannan ya iya abu, kalla yanda yake wani abu kaman irin mun saba dinnan, tashi tayi tare da d'aukan plate ta zuba Mai sannan ta kai mishi gabanshi ta ajiye
Gaba tayi zata wuce yace heey come back Ina zaki??
Ibtisam tsayawa tayi cak, ta kasa magana bata ma san mai zata ce mishi ba
Janyo mata hannu yayi tare da janyota ta fad'o ya ri'keta tayi jikinsa..... Ganin haka zarah yasa ta tashi tabar wajan tana murmushi cikin ranta tana fad'in sai aukin fad'in basa son juna.....
Ibtisam data tsorata domin sai taga kaman zata fad'i ta lumshe ido da sauri, jin bata fad'i ba yasa ta bud'e ido wanda suka sauka akan na najeeb, gaba d'aya kallon idon juna suke.....
Sunyi wajan minti biyu a haka ibtisam ta rufe ido domin bazata iya juran kallon