Showing 18001 words to 21000 words out of 182942 words

Chapter 7 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

yayi lokaci d'aya kuma ya saki tsaki tare da fad'in Wlh ta raina ni that old woman, ci gaba yayi dashan alcohol d'inshi har saida ya shanye duka kwalban sannan yayi jiba dashi gaba d'aya wani bacin ran da yakeji saiya nemeshi ya rasa, baya iya tuna komai, toh taya Zaima tuna tunda a buge yake, k'okarin tashi yayi lokaci d'aya ya fad'i akan gadon bacci ya D'aukeshi


Zarah kallon Granny tayi wacce take ta cema ibtisam sannu, tace Granny Wai yanzu wa Innan matan Najeeb zai aura? Ibtisam dake zaune hannu na Mata azaba domin alluran da aka mata na cire zafi ya gama aiki, ta d'anja tsaki mara sauti domin jin an kira sunan Najeeb din.


Granny tace kwarai kuwa, duka zansa a aura Mai su, tunda shi Dan banza ne, inko kikaga bai auresu duka ba toh a ciki ya zaba d'aya ne, ni Wlh mai Yaron nake so ya aura, yaron tausayi yake ban, duk ya fige, Kinga ya murmure Idan miskili ya auri uwarsa, zasu tafi inane ma yake aiki k'asar masu jajayen fatan nan?


Zarah ta kwashe da dariya tare da fad'in America.


Granny tace yauwa Ameka.


Ba zarah ba harda ibtisam da hannu ke Mata zugi sai da tayi dariya


Zarah tace Kai granny America ba Ameka ba, kawai kice Turai in baki iya fad'a ba


Tsaki Granny taja tare da fad'in kince Ameka, maina fad'a ba dai dai ba Ameka


Zarah dariya harda sauka k'asa tace Wlh Granny bazaki kasheni da dariya ba, kallon ibtisam tayi tare da fad'in za kiyi wanka ne In taimaka miki?


Kaita d'aga alaman eh, toilet zarah ta nufa ta Tara Mata Ruwan zafi a bath sannan ta fito ta tayata ta tashi, har toilet takai ibtisam sannan ta fito ta barta dan tayi wankan, tunda tace zata iya


Wayar ibtisam ce tayi k'ara, Zarah ta d'auka ta Fara tsokanan Kabir tare da fad'in sai kira kake tayi, toh yanzu ta tashi amma tana wani uzuri kad'an, dariya kabir yayi tare da fad'in ya hannun nata? Zarah tace da sauki, yace Alhmdlh ina kofar gida nazo in ganta.


Zarah tace ok bari inzo in shigo dakai, tare da kashe wayan, ta kalli Granny tace kabir ne yazo, Granny tace maza jeki shigo dashi.


Zarah fita tayi inda taba security umarni dasu bud'e gate, bayan an bud'e kabir ya shigo, nan suka gaisa harda Tahir, falon ba'ki takaisu Kabir ya bata ledojin kayan fruit din daya siyo da yawa, ansa tayi tare da fad'in bari in kirata, koda zarah ta shiga saida ta bada umarnin akai musu Abun tabawa sannan ta nufi d'akinta, inda taga ibtisam tana cire hijab alaman ta idar da sallah, tace Aida kin maida Kabir yana jira


Granny tace maza kije Kinji, zarah rakata, zarah ta amsa da toh, tare da taimaka ma ibtisam tasa hijab din, sannan suka fita falon ba'kin, inda an ajiyema su kabir abun taba baki, amma basu ci komai ba


Kabir yana ganin Sun shigo ya tashi tsaye cikin tausayin ibtisam d'inshi, ya fara fad'in sannu ibti, ya hannun?


Murmushi tayi tare da fad'in Alhmdlh, zarah cikin wasa tace tunda ka ganta sai a zauna


Dariya yayi tare da zama, yana fad'in baki da dama, wai yaushe abun ya faru? Zarah tace dazu Wlh, yace Kai Allah ya kyauta. Shiko Tahir tunda ibtisam ta shigo ita da zarah, idonshi ke kan ibtisam din, lallai Allah yayi halitta, dole Kabir ya nace, gata ita ba faran mace ba chocolate colour, kala Mai tsada kenan, amma kallo d'aya zaka mata kaga madaran kyau lallai inda b.... Kabir ya katse mishi tunani da fad'in Tahir ga Ibtisam fah


Murmushi Tahir yayi tare da fad'in, Malama ibtisam ya hannun? Allah ya k'ara lafiya yasa kaffara ne


A hankali tace Ameen nagode, cikin muryanta Wanda ya dashe dan tasha kuka


Kabir yace ibti wannan shine Tahir, aminina, ko ince dan uwana, danya wuce amini a wajena.


Ibtisam murmushi tayi tare da kallon Tahir Wanda idonshi na kanta tace sannu da zuwa.


Nan dai sukayi fira harda zarah, inda ibtisam duk ta gaji da irin kallon da Tahir yake mata, bini bini daka ta d'aga idonta sai su had'a ido, sai ta kauda kai, gashi tana ta setin shi, kaman Kabir yasan ta gaji da zaman ya tashi tare da fad'in za muyi magana Allah ya k'ara sauk'i, ya kalli zarah yace plz ki dinga kulan min da ita Sosai Kinji?


Zarah tace insha Allah, amma fah sai an Biyani, gaskiya


Dariya kabir yayi yace ki fad'i farashi Mai tsada in biyaki, domin my ibti komai nata Mai tsada ne, duka dariya suka sa, sannan sukai musu sallama suka wuce ba tare da sunci abunda aka kawo musu ba.


Zarah da ibtisam cikin gida suka shiga inda suka ga Dad da mum da Granny zaune akan dinning, Granny na fad'in na kawo mishi Mata har guda hud'u amma dan banzan yaron nan baka ga Rashin mutuncin da yayi min ba, toh yanzu na yanke koya auresu duka koya zabi d'aya, inko ya'ki zaba toh Wlh cikin satin nan za'a aura mishi dukansu, tunda su auransu ba irin na y'an bariki bane, babu tsada


Dad yace kiyi hakuri mama, zai zaba, ina Najeeb dinma?


Granny tace tunda yamin rashin mutunci ya fita, bai dawo ba har yanzu


Su zarah da ibtisam sannu da dawowa sukai ma Dad, inda ya kalli ibtisam yace ya hannun naki?


Tace da sauk'i Alhmdlh


Dad yace sannu mamana Allah ya k'ara sauki. Ta amsa da Ameen , mum tace kuzo kuci abinci, zama sukai akan dinning din inda zarah ta Fara zuba ma ibtisam.


Dad yana ta kiran wayan Najeeb bai d'aga ba, yace Wai ina ya shiga haka ne, sai kira nake ya'ki d'agawa


Granny tace taya zai d'aga, bayan ya gama zuba min rashin mutunci, wlh inaga aljanace ta aureshi, yaro kwata kwata baya son aure, inaga Wlh a d'aura Mai duka hud'un zaifi


Dad yace Indai sun Mai AI babu matsala saiya auresu duka.


Granny tace Aiko basuyi Mai ba, saiya auresu tunda shi ya kasa kawo wacce yake so, yanzu ni na zabo mishi, a ciki harda wani Wanda mijinta ya rasu ya barta da d'a d'aya, ni Wlh tausayi take bani, Niko bai zabeta ba inaso inna isa kasa ya aureta saboda Yaron Nata, ta k'arasa maganan cikin tausayi


Dad yace Mai yaro kuma? Toh fah sai kuma yayi shuru yana nanata maganan cikin ranshi, lokaci d'aya ya cire tunanin tare da fad'in Bari Najeeb din yazo saiya zaba, inya d'auketa Mai yaron Kinga shikenan, in kuma bai had'a da itaba sai mu bashi ita mu


Ibtisam kam cikin ranta dad'i takeji, dan d'azu taga matan da Granny ta Kawo, kuma tasan sune, wani irin murmushi takeyi na mugunta, taso sanda aka nuna ma Najeeb matan ace tana nan taga yanda zaiyi, amma ba komai zanyi ta zuga Granny Wlh, a aura Mai y'an kauye mugu kawai, saiya kashe kanshi karshen miskilanci da mugunta...








*gskya zan daina typing kullum saboda rashin sharhi, nifa bana bukatar godiya a'a sharhi nakeso inga kuna min, ta yanda zan gane kuna fahimtan sa'ko na ko a'ah, wlh saboda rashin sharhi gaba d'aya bana jin dad'in typing din, daka na Fara sai inji na gaji, amma in kuna sharhi Zan gane kuna fahimta*




*Pls masu samun sticker a whatsapp in Nayi posting ku daina, wlh da kisa min sticker gwara ki karanta baki cemin komai ba yafi min dad'i, indai kin San zaki dinga samun sticker ki ri'ke sticker d'inki bana so*


*facebook kuma ina bukatan sharhi ba thanks ba, wasu ko thanks dinma basa iya karasawa sai dai susa maka T, haba for god sake taya writers za suji dad'in muku posting kullum kaman yanda kuke bu'kata, gskya in bakwa sharhi zan daina posting kullum sai naga dama zanyi, tunda comment din da baifi 30 second ba inya dad'e minti d'aya ya gagara taya nida nake zama wajan awa biyu uku Ina typing sannan inji dad'in muku posting kullum, kunga hakan bazai yihu ba, duk da Nasan akwai masuyi Sosai so Ina magana akan masu samun thanks ko T, plz ku gyara*






















~MARYAM OBAM~




*NAJEEB*




*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*




*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*




*http://WWW.Maryamobamnovels.com*


*Wattpad@ Maryam-obam*


*Instagram@maryam_obam*






*DEDICATED TO.....*


*MY LOVELY MUM*








*PAGE 9*














Mum kam ita duk wannan abunda sukeyi, ita bata ganin zata yarda, " Ayi ma d'anta haka, "dan ita gaskiya bazata yarda a d'aura ma d'anta wa Innan matan ba, haba ai wannan ba adalci bane ko kad'an, "taya yaron daya taso a waje, yayi karatu a can, ace za'a aura Mai wa Innan matan, gaskiya da sake, inshi Dad yayi shuru gaskiya ita bazata yarda a cuci d'anta ba, 'In ma auren akeso yayi sai a Bari ya zaba da kanshi bawai a Kawo mishi wa Innan y'an kauyen ba, ai sai a matsa Mai ya kawo mata a aura Mai indai haka akeji.


Dad tashi yayi "yana fad'in saida safe Bari inje in huta.


Granny tace "Allah ya tashemu lafiya.


Ya amsa da Ameen sannan ya wuce "itama Mum ta tashi tabi bayanshi


Ibtisam da zarah da Granny suka rage "Granny ta kalli ibtisam "tace wai yaushe shima kabirun zai turo ne? "naji shuru ya kamata dai ya turo "musan halinda muke ciki.


Ibtisam tace "haba Granny aikya Bari in warke koh, "kuma Kinga ga yaya Najeeb baiyi aure ba, ya kamata injira in yayi nima sai inyi hakan zaifi.


Granny ta tsuke baki, "can tace ke nifa so nake a had'a bikin duka, dan ban son Ayi ta hidima kan hidima aita abu a rarrabe, gwara a had'a, zaifi, " saiki fad'a ma Kabiru ya turo, inbai shirya ba mu sani. "kallon zarah tayi tace kema ya kamata in kina da manemi anayin nasu Kema kice ya turo, nida so samu ne duka basai a had'a ba.


Ibtisam tace ni saida safe tare da tashi tabar wajan.


Granny tace " oh ni Amina yara basa son zancen aure, daka an fara saisu tashi, kaman masu iska, "Zarah Anya bakya tunanin suna da aljanu kuwa? Granny ta jefo ma Zarah wannan tambayan.


Zarah dariya tayi tare da biye ma Granny "tace ashe bani d'aya nake tunanin haka ba, "Granny tace haba ashe Kema kina tunani kai na shiga uku, "Kinga miskili shi tunda yaji zancen aure yabar gidan har yanzu bai dawo ba.


Zarah tace "Granny nifa ina tunanin wannan matan ne baya so, " inda zaki canza mishi wasu da hakan yafi, ko kice ya kawo wanda yake so.


Granny tace "sam wannan ba abu mai yihuwa bane, "koso kike a maidani karamar mutum?


Zarah tace "kaman ya Granny?


Granny tace "inje in kwaso Mata har hud'u, sannan ace bai d'auki ko guda d'aya ba, "inna koma Mai zance ma iyayen yaran? "Kinga tashi kije ki kwanta, "Granny tashi tayi tana fad'in saida safe, "miskili d'an banza ya'ki dawowa.


Najeeb bai farka ba sai wajan d'ayan dare, "tashi yayi yaji gaba d'aya jikinshi yayi mishi nauyi Sosai, "Kai tsaye ya nufi toilet yayi wanka tare dayin alwala yazo yana rama bashin sallah, Allah dai ya kyauta, "bayan ya idar ya tashi ya d'auki key din motarshi yabar hotel din, " Kai tsaye gida ya nufa inda yayi horn Mai security suka bud'e Mai kofar ya shiga part d'inshi ya nufa direct, "Bayan ya shiga gaba d'aya kayan jikinshi ya cire yasa jallabiya tare da kwanciya bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi


Washe gari da safe tunda Granny tayi sallah asuba, ta fito falo ta zauna "wai miskili bai kwana a gida ba Tana jiran ya dawo taji gidan uban wa ya kwana, sai gyangyad'i takeyi, "amma ta'ki tashi tana nan zaune Wai tana jiran miskili, " a haka bacci ya bingirar da ita a nan Hhhhh, "shi dama bacci barawo ne gashi ya sace granny.


Wajan karfe 10 mum ta fito falo "ganin Granny kwance akan kujera tana ta shakar bacci,abun yaba mum dariya, "tare da fad'in badai a nan ta kwana ba? Har zata tasheta ta fasa dan in Granny ce sai tace ta katse mata bacci, dan haka ta Fasa tare da wucewa kitchen taga mai masu aikinta suke dafa musu, "koda mum ta nufi kitchen "gaidata masu aikin suka farayi cikin girmama a harshen turanci ,"Mum tace an kammala komai kenan?


Suka amsa da yes ma


Fita Mum tayi ta koma falo inda ta Tarar da Granny zaune tana hamma "Mum tace ina kwana mama


Granny tace "lafiya an tashi lafiya?


Mum tace lafiya Alhmdlh.


Granny tace "Ina nan tun dazu ai ina jiran dawowan wannan Yaron, tun jiya bai shigo gida ba, saiya fad'amin inda ya kwana, kallon Mum tayi "tace Wlh kuna bani mamaki ace d'anki bai kwana a gida ba amma ku ko a jikinku, baku ma sani ba, kai Wlh wannan halin naku yana bani mamaki.


Mum dai shuru tayi dan bata da abun fad'a, inma tana dashi bazata iya jayya da Granny ba, tunda Uwar mijinta ce, dole itama ta d'auketa matsayin uwa, "Abu d'aya Mum take ganin za tayi jayayya da Granny shine ace Najeeb ya auri matan data kawo, sai dai in shine yace yana So, shine zanyi shuru.


Granny sai faman fad'a takeyi ta inda take shiga ba tanan take fita ba "ace yaro saurayi ya kwana a waje ba tare da saninku ba, wannan wace irin tarbiya ce? "Haya niyan Granny shine ya tashi Dad Wanda ya fito falon da sauri, ganinshi yasa Granny tace yauwa gwara da kazo


Yanzu d'anku ace ya kwana a waje, amma baku damu ba?


Dad yace mama kiyi hakuri Najeeb ba yaro bane, sannan shida yake wata k'asar da bama ganinshi ma, "Allah ne yake karewa n.....


Dakata dakata Granny ta katse shi da fad'in haka, sannan tace "can daban nan daban, Niko can Ameka din da yake aiki baso nake ba, andai fi karfina ne, saboda y'an Ameka basa ji wlh, suko kunyan taba junansu basayi, kai duniya ta lalace, ku ko tsoro bakwayi ya kwaso irin halin..... Shuru tayi na wani lokaci sannan taci gaba da fad'in "koda yake shi miskili bazai yi wannan iskancin ba, yaushe wannan miskilancin nashi zai Bari ya kula wasu, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya "koya yake k'arewa da abokan aikinsa oho? "Nifa ina ganin an canza shi a Ameka, Inba haka ba taya yaro zai'ki son aure? "daka maganan aure sai yabar gida tun jiya, " na taba ji ance a Ameka suna canza ma mutum halitta koso kwashe jinin mutum susa Mai wani, Anya basu ma Najeebu haka ba kuwa?


Ba mum ba harta Dad saida maganan Granny ya basu dariya, "su Zarah da surutun Granny ya ishesu suma suka fito, gaida iyayen nasu sukayi "sannan zarah tace Granny Wlh kin hana mutane bacci,.


Granny tace "aikya fad'i haka, kina zaune a gida hankali kwance babu maganan aure, "wai kai audullahi baka ganin girman yaran nan ne, da suke gabanka?


Dad shuru yayi domin yasan abun Granny harda tsufa, koda yake tsufan ne ma, sai anyi hakuri, kwata kwata kwaya nawa Yaran suke? " yaushe suka taso da Granny zata Fara maganan Ayi musu aure.....


Maganan Granny ne ya dawo da Dad daka duniyar tunanin daya fad'a "inda take cema ibtisam ya hannun?


Ibtisam tace Alhmdlh da sauk'i, "sai dai har yanzu ina jin zafi Sosai "Mum tace sannu yarinyata zai daina a hankali Kinji? Allah ya k'ara sauk'i my dear


Ibtisam ta amsa da Ameen mum, "shima Dad ya mata Allah k'ara sauk'i.


Granny tace ni yunwa nakeji wlh, "shi miskili zai dawo ya tarar dani, "ke Zarah jeki kira yaran da nazo dasu..... Fitowan Najeeb yasa Granny sakan ba'ki "lokaci d'aya kuma tace yaushe ka dawo?


Najeeb daba jin abunda tace yayi ba ya banka Mata harara, tare da gaida iyayenshi cikin harshen Hausa Wanda bai kware ba, "Ina kwanan ku ya furta a gajarce tare da nufa dinning dan yayi breakfast.


Granny tace miskili koda idonka zai fad'o k'asa harshen harara sai kayi aure ja'iri, ke Zarah jeki kira matan nan ya zaba a ciki "Zarah ta amsa da toh tare da tafiya kiransu


Shiko Najeeb abinci ya fara ci, " Ibtisam dake tsaye ta kalleshi cikin ranta tace mugu azzalumi, wlh abunda kamin saina rama, Koba yanzu ba "shi Najeeb bai masan tana wajan ba dan bata su yake ba, so yake ya koma America danya gaji da wannan tsohuwar Sosai take takura mishi.


Granny nufanshi tayi tana fad'in ja'iri dama ka iya Hausa? "harda wani Ina kwanan ku. "toh Bari kaji Nasan kana jina Wlh ka zabi d'aya cikin matan dana kawo, "koka auresu duka.


Najeeb ko kallonta baiyi ba "ji yayi kaman ya bugeta dan haushi take bashi, shi yanzu a duniya ya yarda ta gama raina mishi wayau, "Toh Inba haka ba taya zata kawo mishi wa Innan Buran tace ya aura, ko Dad d'inshi da yake tsoho balarabiya ya aura, balle shi yaro dashi, wanda yasha nonon balarabiya saita kwaso mishi wa Innan masu Kama da Buran, munana y'an kauye kai wannan tsohuwar ta gama dani, amma zan koya Mata hankali wlh


Granny tace baka jina ne?


Tsaki yaja tare da banka Mata harara, cikin harshen turanci yace "Wlh Granny ki kama kanki da tsufanki tun Kafin inyi miki babu dad'i.


Dad yace kana da hankali kuwa Najeeb? Cikin harshen turanci yake Mai maganan, "yace Uwar tawa kake fad'ama haka?


Yace Dad nifa gaskiya na gaji da halin wannan tsohuwar haba, koku bakwamin abunda takemin haba, gaskiya na gaji, tana gab da kaini bango Wlh, ka Mata warning ta fita harka na, ko a kanta nake da zata takura min? Ta tashi ta kwaso Mata wai in zaba in Aura for god sake ance mata Ina bukata ne, ko me? Ya k'arasa maganan cikin zafin rai


Granny daba jin abunda suke fad'a tayi ba, "tace wai Mai kuke fad'a ne haka? Ku fad'amin inji.


Najeeb tsaki yaja tare da ture plate din dake gabanshi na chips din da yakeci tare da tashi yana k'okarin barin wajan


Cikin fushi Dad yace koma ka zauna, mutumin banza,"zama yayi rai a bace tare da tamke fuska


Granny tace ikon Allah, yau naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login