Showing 96001 words to 99000 words out of 182942 words
Chapter 33 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
canji ki kirani ki fad'amin Kinji, sannan banda yawan shan magani barkatai
Ibtisam dariya tayi tare da fad'in Toh zama akan wani dalili zansha magani? Tunda ba ciwo nake ba, ibtisam dai bata gane inda Granny ta dosa ba, dan haka sukai sallama suka wuce
Abba drop ya d'aukar ma ibtisam, sannan ya bata kud'i yace ta ri'ke..
Tace Abba inada kud'i fah
Abba yace eh ki k'ara
Amsa tayi tare da fad'in nagode
Sannan ta shiga motar suka wuce shima abba ya tafi kasuwa.
Ibtisam ta riga Zarah zuwa, tana zuwa ta Tarar su Aisha an dawo da HAUWA
Hauwa tace manya, tunda kuka tafi ko waya, ni nace Bari in kiraki amma number d'inki kullum a kashe
AISHA ta cabe da fad'in Wlh kuwa, ni muna waya da Zarah kodan NAJEEB AI dole inkira inji
Dariya HAUWA ta saki Tana fad'in Wlh kina da aiki
AISHA tace ke dan baki ganshi bane Wlh ya had'u, ki tambayi ibtisam kiji.... Kallon ibtisam tayi tare da fad'in fad'a mata dan Allah ibtisam
Ibtisam uhm kawai tace, tare da dan murmushi cikin ranta tace ni ban taba ganin had'uwan najeeb ba, bai taba burgeni ba, hasali ma ni bana ganin kayanshi sai muninshi da kuma mugun halinshi wanda inka ganshi zaka d'auka na arziki ne, ga rashin kunya da rashin tarbiya, ga shan giya, Wa'iyazubillah gaskiya rayuwar NAJEEB Abun muni ne ga mace ya kawo ya ajiye a gida wacce ni ban Masan zaman Mai takeyi dashi ba, Hmmm Allah dai ya kyauta.....
Shigowan Zarah yasa ibtisam dawowa daka duniyar tunanin data fad'a, tare da sakin ihu ta rungumeta, Zarah itama ihun take Tana fad'in Amarya bakya laifi
Aysha tace Amarya?
Hauwa tace nima abunda naji tace kenan, aure kikayi bamu sani ba??
Zarah tace eh anyi bikinta da muka koma Gida
AISHA tace Wlh baku da kirki, gaskiya baku San zaman tare da Wlh
HAUWA tace Wlh baku d'aukemu yanda muka d'aukeku ba wlh..
Zarah tace a'a ba haka bane Wlh, kuyi mana uzuri, itama bata san da auren ba, saida ta koma
Kuma ita anyi saita Gama karatu amma aka canza, koda akai bikin bata cikin hayyacinta sai yasa batai gayyaba..
AISHA tace Kai, irin abun nan babu dad'i, wlh nafi son inyi karatu in Gama sai inyi aure
Ibtisam tace Kedai bari ai hakan yafi dad'i Wlh, amma mu kaddara tazo mana a haka..
Nan dai sukai ta fira
Zarah taba ibtisam kud'i wanda Mum tace a Kawo mata, dubu hamsin ne.
Ibtisam tace dole taje ta bud'e account gaskiya, domin bata son ajiye kudi a hannunta
Ibtisam da Zarah tashi sukayi suka fita, domin zarah nason mata magana akan ciwon goshinta, duk da plaster din ya fita
Bayan sun fita Zarah tace ibtisam ina fatan dai komai normal koh? Wlh kullum da tunaninki nake tashi, ina tsoran irin halin da zaki shiga keda NAJEEB, Ina fatan bai cutar dake ba, musamman wannan ciwon dana gani na goshinki
Ibtisam tace Zarah NAJEEB ya cuceni, hawaye ta Fara zubarwa tare da fad'in Zarah duk duniya dake d'aya na yarda, sai yasa zan fad'a miki sirri na, duk da nasan babu kyau, amma fad'a miki da zanyi shine zaisa in samu sauk'i daka rad'adin da yake damuna, wlh Zarah NAJEEB ya cutar dani, ya lalata min rayuwa
Zarah cikin tsoro da tashin hankali tace maiya miki ibtisam??
Ibtisam tace Zarah NAJEEB fyad'e yayi min
Zarah dariya taso tayi amma saita dake tare da fad'in fyad'e? Kaman ya?
Ibtisam tace Hmmm Zarah NAJEEB yayi raping d'ina, ba tare daya Sani ba
Zarah tace kaman ya kwaya yasha Kome??
Ibtisam tace kin San yana Shane dama??
Zarah tace a'a, naji kince yayi raping d'inki ba tare da saninshi ba shine abun ya bani mamaki sai kace wanda yasha kwaya
Ibtisam tace eh yasha kwaya, domin NAJEEB yana shan alcohol.....
Da sauri Zarah ta tashi tsaye tare da fad'in what cikin tsoro da razana
Ibtisam kamata tayi ta zaunar da ita tare da fad'in, wlh....
Zarah tace kodai wine kika gani kika d'auka giya ce???
Ibtisam duk da Tana hawaye saida tayi murmushin takaici tace ko d'aya, tare da danna wayarta ta nuna ma Zarah hotan kwalban alcohol din
Salati Zarah ta saki tare da fad'in Wlh wine with alcohol ne, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, Najeeb giya?
Nan ibtisam ta Fara bata Labarin abunda yayi mata harda kwanciyarta a asibiti, da yanda ta dawo gida, da kuma yanda ta fad'a musu Granny duka ibtisam bata boye ma Zarah komai ba, saida ta fad'a mata
Zarah hawaye ne ya zubo mata a ido tare da rungume ibtisam tace Wlh NAJEEB ya cuceki, daya miki irin wannan Abun, amma koda yake bake ya cuta ba kanshi ya cuta, domin Allah Baya zalinci wlh, yanzu Abun nashi harda shan giya, gashi gashi harda neman mata.....
Ibtisam tace bance yana neman mata ba, tunda banga yayi ba
Zarah tace toh inba nemanta yake ba uban Mai yasa ya ajiyeta a gidansa?? Wlh saina fad'ama su Dad
Ibtisam tace kar kiyi haka, domin idan kika fad'a ni kika tona ma asiri, sannan bawai na fad'a miki bane danki fad'a musu ba, ni dake akwai sirrin da zamu dinga ajiyewa ba tare da sanin iyayenmu ba
Zarah tace amma ibtisam wlh bai kyauta ma kanshi da rayuwarshi ba ko kad'an, ace kana dan musulmai ka dinga shan giya, wacce haramun ce, kai IInnalillahi'wa inna ilaihirajiun, wlh Najeeb ya cuci kanshi da rayuwarshi, gaba d'aya sai yasa baya ganin kimar kowa, ya d'auki halin turawa yasa ma kanshi tsaki taja cikin k'unan rai
Ibtisam shuru tayi tana tunanin mafita, domin tun jjya take kiran Layin KABIR switch off, Tana matukar son yin magana dashi, ita burinta taji ko yana lafiya, gashi bata da number din wani nashi
Zarah tace tashi mu koma ciki.
Tashi ibtisam tayi suka shiga ciki..
Washe gari suna da lecture dukansu kuma time d'aya harda Zarah karfe 7 Dan haka tare suka fita, ita dai AISHA tace babu inda zata, domin lecturer din mutuminta ne bata da matsala dashi
Hauwa kam ba'a skul ta kwana ba,
Sun tafi lecture inda ko wanne yayi department d'insu
Ibtisam shiga lecture tayi inda bata dad'e ba suna cikin fira da Salees saiga lecturer din ya shigo, nan Ya fara musu lecture
Sai 10 ya fita inda ibtisam ta zauna ba tare data fita ba, tana ta dialing din number din kabir amma har yanzu a kashe, cikin ranta tace May be ma ya canza layi ne.... Kai no kabir bazai canza layi ba, na tabbata irin sonda yake min bazai canza layi ba
Am sure wani abu ya faru dashi, sai yasa wayarshi baya shiga
Salees ne ya katse mata tunani da fad'in Yadai? Naga tun d'azu sai faman danna waya kike cikin damuwa..
Ibtisam ajiyan zuciya ta sauke tare da fad'in lafiya
Salees yace number din wa kike nema ya'ki shiga, kona wanda yayi min kwace ne?..
Murmushi tayi tare da fad'in kaman ka sani wlh
Salees yace gaskiya ana son wannan guy din Sosai, yayi Sa'a fah Sosai
Ibtisam dad'i takeji tana murmushi domin ita a duniya Tana son taji ana mata maganan Kabir, ko firan daya shafeshi
Salees yace ina Aisha bata shigo ba, kodai bata dawo daka hutun bane???
Ibtisam tace ta dawo, bacci takeyi tace bazata iya zuwa ba
Dariya Salees yayi tare da fad'in kai AISHA matsala, Allah ya kyauta
Tunda ibtisam ta dawo take karatu Sosai, amma kullum da tunanin kabir take kwana take tashi, duk ta rame
Yau Bayan sun fito daka lecture tana zaune wajan wata bishiya saiga Dr jibril Wanda tunda suka dawo Bai shigo musu ba, sannan bata ganshi ba
Kiran sunanta yayi da Amina.
D'ago dakai tayi tare da kallonshi, lokaci d'aya kuma ta saki murmushi, tare da fad'in sir
Dr jibril yace Ykk?
Tace lafiya sir, kwana biyu? Tunda na dawo ban ganka ba?
Dr jibril yace shine baki kirani ba? inda kina son ganina I you have to call me
Murmushi kawai tayi tare da Dan Sosa kanta
Ido yad'an kura ma fuskanta, lokaci d'aya Yace Kinji ciwo ne? Maiya samu goshinki??
Taba goshin tayi tare da fad'in na buge ne da window
Yace eyya sorry Allah ya kyauta, tare dayin gaba
Ibtisam ganin ya tafi yasa tayi dan murmushi tare da barin wajan itama
*AMERICA*
saida kabir ya k'ara sati d'aya aka sallameshi, shima danya matsa ne, dole aka sallameshi domin jikin da sauk'i, kawai dai kafarshi ce da yake dan dingishi, shima Dr yace a hankali zai daina
KABIR sun had'a kayansu inda suka biyo jirgi suka tawo gida Nigeria
Gefen NAJEEB kam, tunda ya tabbatar ibtisam ta tafi, hankalinshi yad'an kwanta amma Abu d'aya ya tsaya mishi a rai shine dawa take hulda a skul, duk da Baya son ibtisam shiba Wawan namiji bane, domin yana da kishin abunda ya zama mallakinshi, balle wacce aka d'aura mishi
Najwa kam tun sanda NAJEEB ya kirata akan taje hospital taga ibtisam ta'ki zuwa, tare da barin k'asar domin tasan tabbas akwai abunda ya shiga tsakanin NAJEEB da yarinyar, domin kuwa koda ranan da tasha giya AI tasan a daki ta farasha, sannan ta ganta a falo, kuma taga kayan NAJEEB a kitchen daka ganin alama yayi wani abu da yarinyar Wacce haka kawai taji bata Sonta....
*NIGERIA ZARIA*
ibtisam suna zaune suna lecture, kanta taji yana mata ciwo kaman tana jin jiri, ga kirjinta dake mata zafi, lokaci d'aya taji cikinta yana murd'a mata kaman zatai period....
Dr jibril ganin yanda takeyi yasa ya kira sunanta da fad'in Amina what wrong with you??
Duka y'an class din suka k'ura mata ido,
Kanta ta nuna mishi alaman shine ke mata ciwo
Dr jibril yace kije kisha magani
AISHA ta tashi tare da fad'in Bari in taimaka Mata in kaita d'aki in dawo..
Dr jibril yace yes plz help her
Koda suka fita Dr jibril yaci gaba da lecture
Ibtisam ta tsaya tare da kallon Aisha tace dan Allah ruwan sanyi
Aysha tace zauna bari in siyo miki
Koda aysha ta Kawo ruwan ibtisam amsa tayi ta kafa kanta a goran ruwan ta farasha kaman hauka take kwankwadan ruwan
Bayan ta gama sha ta cire Tana sauke ajiyan zuciya tare da fad'in kai har naji komai normal da nasha wannan ruwan
Aisha tace sannu
Tace yauwa Bari inje in kwanta, ki koma kawai zan iya zuwa yanzu am OK
AISHA tace OK
Ibtisam komawa tayi daki, inda ta kwanta ta rasa mai yasa take yawan jin jiri kwana biyu, gashi cikinta saiya murd'a kaman zatai period gashi ba period din bane tsaki taja tare da d'auko wayarta taga misscall
Dubawa tayi ta tashi da sauri, domin ganin kiran KABIR ne har guda biyar......
Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Ibtisam bayan ta tashi dialing din number din kabir tayi wanda yake ta ringing ba'a d'auka ba
Kabir kam tunda ya kira batai picking ba ya ajiye wayar ya shiga toilet domin yayi wanka, koda ya fito shima ganin misscall din ibtisam yayi da sauri ya kirata ringing d'aya ta d'auka tare da sawa a kunnenta
Kuka ta saki tare da fad'in mai yasa ka kashe wayarka? Mai yasa kayi nesa dani? Kasan irin halinda na shiga kuwa Mai..... Kuka yaci karfinta Sosai wanda hakan yasa ta kasa k'arasa abunda tayi niyan fad'a
Kabir kiran sunanta yayi da ibti
Cikin kuka tace uhm
Yace plz ki daina kuka Ina son ki bani dama inyi miki bayanin abunda ya faru
Dan shuru tayi domin tana son ta saurareshi
Yace ibti ranan da nazo gidanku ranan daurin aurenmu bayan na dawo naji abunda ya faru, Naje hospital anyi min test inda daka nan nazo gidanku wajan Abba na nuna mishi k'arya ne sharri akamun yace inje zai nemeni, a hanyata ta komawa nayi accident wanda har saida aka fitar dani waje, ina sauka Kena Fara nema
Ibtisam kuka take tana fad'in dama jikina ya bani akwai wani abu daya faru dakai, wlh jikina ya bani, Ina fatan kana lafiya yanzu
Yace ibti lafiya? Sai dai na musulunci.... Canza maganan yayi da fad'in ina asibiti a America naga wata kaman ke....
Tace America a wani hspt?
Nan ya fad'a Mata, tace Wlh nice nice dama kaima nan aka kaika??
Kabir yace eh, Mai kikaje yi a can??
Tace KABIR an kaini wajan NAJEEB.... Sai kuma tayi shuru tare da saka kuka can taci gaba da fad'in KABIR Ina cikin wani hali dan Allah kazo ka d'aukeni mu gudu, wlh bazan iya zama da kowa ba inba kaiba dan Allah kazo mu gudu muje muyi aure na ro'keka
Kabir shuru yayi wanda sai yanzu ya tabbatar daya rasa ibtisam domin tunda tace an kaita wajan NAJEEB, lallai ya rasata kenan, wani irin hawaye ne ya zubo mishi Mai zafi tare da fad'in ibtisam Ina son kiyi hakuri ki rungumi aurenki hannu bibbiyu domin yanzu ke matar wani ce
Ina miki fatan Sa'a a rayuwa, sai dai Ina son ki sani zuciya ta Kece a ciki har abada, Indai na cireki a ciki toh daka ranan nabar duniya.... Yana fad'in haka ya kashe wayar domin yanda yake jin zafi cikin ranshi lallai yasan abune Mai wuya ya iya cire ibtisam a cikin ranshi, amma koh Waye ya mishi wannan Sharrin ya gama dashi
Ibtisam kam jin ya kashe wayar yasa ta k'ara fashewa da kuka tare da fad'in Wlh KABIR Nima bazan Barka ba, lallai dole NAJEEB ya sakeni, bazan iya rayuwa ba tare dakai ba....
Zarah da tun d'azu ta shigo d'akin ta tsaya bakin kofa domin jin ibtisam na kiran sunan KABIR, shigowa tayi tare da kiran sunan ibtisam
Ibtisam bata d'ago ba balle ta amsa mata kiran da tayi mata
Zarah hakan bai dameta ba, ta Fara magana da fad'in ina son kiji tsoran Allah, karki manta ke matar aurece bai kamata ki dinga magana da kabir b....
Ibtisam ta taso cikin zafin rai tare da fad'in nayi magana dashi din, sai me? Wlh bazan daina magana dashi ba, sannan karki k'ara kirana inada aure domin da wannan auren gwara babu, Abu d'aya zakiyi shine kisa yayanki ya sakeni
Zarah kallonta ta tsaya yi cikin mamaki, lokaci d'aya kuma tayi murmushi irin na takaici tare da fad'in ibtisam Nasan ranki a bace yake, musamman na rabaki da Wanda kike so, wanda bada gangan akai miki hakan ba, kowa ya soki da kabir amma Allah yasa bashi bane mijinki, duk da anyi mishi kazafi ne, so ina son ki amshi kaddara kiyi hakuri ki amshi abunda Allah ya baki d.....
Ibtisam cikin kuka tace ai dole kice haka, tunda dan uwanki ne, dole ki dinga bin bayanshi, wlh Zarah koda zaki kwana kina wannan maganan naki, baji zanyi ba domin bazan taba son NAJEEB ba har abada, so d'aya ne, naba ma kabir dan haka kibar bata bakinki wajan Kare Dan uwanki da bai San hakkin Dan Adam ba
Zarah ganin yanda ibtisam tayi zafi Sosai yasa tace Allah ya baki hakuri ibtisam ni bana goyan bayan NAJEEB hasali ma ke nake goyan baya, wlh bance kiso NAJEEB ba, haka bazan tursasaki ki soshi ba, but abunda na Sani Kema y'ar uwarshi ce kaman yanda n....
Ibtisam tace Allah ya kyauta, wlh ba dan uwana bane, kima daina had'ani dashi
Zarah tace nidai ina baki shawara kiji tsoran Allah kina da aure, ki daina waya da kabir domin karki bata lahirarki Ina fad'a miki hakan ne badan Ina son NAJEEB bane dake ko d'aya sai dan kiji tsoran Allah ki kuma tuna kina da aure
Ibtisam juya mata baya tayi taci gaba da kukanta, ba komai ke mata yawo a Kai ba sai irin yanda KABIR yake fad'a mata Idan ya rasata bai San wani hali zai shiga ba, da irin kalaman soyayya da yake fad'a mata, tuna ranan da yayi kissing d'inta yayi da sauri ta tashi Tana fad'in NAJEEB ka cuceni sai kuma ta fashe da wani sabon kuka mai sauti.....
Zarah janyota tayi jikinta tana fad'in haba ibtisam, Ina iliminki yake? Ina saninki yake? Duk ina kika kaisu? So yana son ki kasa yarda da kaddaran da Allah ya baki cikin rayuwarki? Ibtisam ko kin manta kowa da irin tashi jarabawan? Mai yasa kika kasa yarda da wannan jarabawan? Ko kin San Allah yana jaraba bayinsa domin yaga imaninsu.....
Ibtisam cikin kuka tace hakane Zarah, wlh Ina son kabir, baki ji yanda nake ji bane, inda Kece a matsayina da zaki fahimci irin halin dana shiga, wlh Zarah son kabir yamin yawa, bana son kabir bazan iya bashi girman da mace zata iya Bama miji ba, zarah miye amfanin zamana da NAJEEB? Bayan baya sona nima bana sonshi? Wlh na tabbata in naci gaba da zama dashi zanyi ta jefa kaina cikin halaka, domin bazan iya bashi girman da mata ya kamata taba miji ba, gaba d'aya ko ganin fuskan NAJEEB bana sonyi inna tuna da abunda yayi min sai inji kaman in kashe kaina dan ba'kin ciki,.
Zarah ki duba yanda mace ke ririta kanta domin takai mutuncinta gidan miji, danta samu daraja, ki duba yanda nake ta kame kaina, amma at the end ki duba yanda akai dis virging d'ina a wulakance, bama tare da saninshi ba, inda Nasan haka zan rasa budurcina da tuni na barar a titi da....
Baki Zarah ta toshe ma ibtisam tare da fad'in ya isa haka Idan rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba, ina so kiyi hakuri Kibi komai