Showing 60001 words to 63000 words out of 182942 words

Chapter 21 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

bridal shower, da kamu, so duka a hall za'ayi, sai kuma dinner


Tahir yace bridal shower ango na zuwa?


Ibtisam tace a'a baya zuwa only amarya da friends dinta ne


Tahir yace Toh naki a canza mana, ango yazo


Dariya sukayi shida kabir


KABIR yace a'ah baza'ayi haka ba, dinner kawai za'ayi duka da amarya da ango, amma duka biyun kamu da bridal shower babu wanda zani


Ibtisam tace amma ango na zuwa kamu AI, shida abokai suzo suyi spraying su tafi


KABIR yace my ibti ki bari ranan dinner kawai, ban so suyi ta kallonki


Tahir yace au hakane? Toh dad'in Abun Muma munada mata balle a mana gori


Ibtisam tace ba gori bane gaskiya ya fad'a


Tahir yace taran dangi zakuyi min?


KABIR yace a'a kasan nida ita komai namu d'aya ne, "d'auko wata Leda yayi na waya ya mi'ka ma ibtisam yace gashi


Tace bana fad'a maka Abba ya Aiko min da wacce ka siya min ba


KABIR yace kin fad'a min, ni kuma Na riga Na siya wannan sanda kika fad'a, toh kinga saiki had'a biyu, "wannan iPhone7 ne Kinga wancan Samsung ne saiki had'a, dama naga ku mata wayarku kenan iPhone


Dariya tayi tare da fad'in ni Wlh daka barshi


Kabir yace Kinga amsa dan bazan ri'ke ba


Amsa tayi tare da fad'in nagode Allah k'ara budi


Tahir dake gaban motar har cikin ranshi yaji dad'in addu'an da ibtisam tama kabir, wanda yanzu mata saika musu Abu babu godiya wata rainawa ma zatayi


Sun dad'e suna fira Kafin kabir yace zasu tafi, ibtisam fita tayi Bayan tayi ma Tahir sallama, shima KABIR fitowa yayi tare da matsawa inda take yana fad'in my ibti plz banda biyema friend plz Kinji?


Kaita d'aga mishi alaman toh


Yace sai yaushe kuma?


Tace sanda kazo


Yace OK ana ta aikin gidanki


Tace Allah ya taimaka


Ya amsa da Ameen


Dr jibril tun daka nesa ya hango su lokacin da kabir yama ibtisam sallama ya shige mota suka tafi dai dai lokacin Dr kabir ya k'araso kallon ledan wayar dake hannun ibtisam yayi tare dayin gaba tana gaidashi bai ko bata amsa ba ya wuce ya shiga motarshi.....














Read and leave it, dnt share to anyone






*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
















Ibtisam kam hakan da yayi mata sai bataji dad'i ba, Koba komai tunda ta gaidashi ya kamata ya amsa bawai ya shareta ba"haka ta nufi d'akinsu jiki a sanyaye domin babu dad'i ka gaida mutun kuma kasan yaji yayi banza dakai


Koda ta isa d'akinsu babu wanda ya dawo, dan haka shiga tayi tasa wayar da kabir ya bata a caji tare da kwanciya, bata dad'e ba bacci yayi gaba da ita


Zarah sai wajan 6 suka fito daka lecture Kai tsaye d'akinsu ta nufa taita nocking shuru saida ta dad'e "ibtisam dake bacci ta farka taji k'aran ana nocking sannan ta tashi ta nufi kofar tare da tambaya Waye?


Zarah tace bud'e nice


Bud'e kofar ibtisam tayi Zarah ta shigo tana fad'in haba ashe bacci kikeyi sai yasa naji shuru inata nocking


Ibtisam tace Wlh bacci ya D'aukeni....


Katseta Zarah tayi tare da fad'in wannan wayar Waye a caji?


Ibtisam tace nawa


Zarah tace waya baki?


ibtisam tace KABIR yaban shine ya kawo min wayar


Zarah tace yazo ne KABIR din?


Ibtisam tace eh yazo bai dad'e da tafiya bama


Nan Zarah ta d'auki wayar tana fad'in a'ah Amarya wajan barrister Kabir gaskiya yana ji dake fa Sosai, "irin wannan wayoyi har guda biyu manya ga iPhone ga Samsung


Ibtisam dariya tayi tare da fad'in uhm bari kiga in fad'ama Ummi kar ta gani in shiga uku


Zarah dariya tayi tare da fad'in Aikam, kin tuna abunda ya faru kenan?


Ibtisam tace ai ban manta ba, saboda waya aka hanani zuwa skul gashi saboda Abun yasa zanyi aure ba tare dana kammala karatu ba, kaman yanda naso Nayi ba tun Farko.... D'aukar wayar da ummi tayi ne yasa ibtisam fad'in ummi Ina wuni?


Ummi tace lafiya kalau ya karatu?


Ibtisam tace lafiya kalau ummi.,"dama na kira in fad'a miki dazu KABIR yazo ya Kawo min wata waya, nace ya Bari tunda ga wanda yaban yace a'a wai yariga ya siya


Ummi tace mutumin da yake hidiman aure shine yake wani K'ara siyan miki waya? Kai Allah ya kyauta, shikenan saiki ajiye d'aya kar ki ri'ke biyun a sace


Ibtisam dariya tayi tare da fad'in haba Ummi sai kace autanki Ahamd


Ummi tace au shikenan, "Ina Zarah


Mi'ka ma Zarah wayar ibtisam tayi


Gaida ummi Zarah tayi cikin girmamawa, Ummi tace ya karatun fatan dai komai lafiya?


Zarah tace lafiya kalau ummi karatu Alhmdlh


Ummi tace toh Masha Allah, sai a dage sannan a k'ara tsare mutunci banda kawayen banza


Zarah tace insha Allah


Sallama sukayi Bayan ummi ta kashe wayan Zarah ta kalli ibtisam tace Wai Mai kika dafa ne?


Ibtisam tace Shinkafa da miya


Nan Zarah ta tashi ta d'auko plate ta zuba abincin tare da d'auko Titus ta fasa ta zuba akan abincin ta Fara ci


Ibtisam ita danna wayarta take abunda


Zarah tace abincin yayi dad'i fah, gaskiya kin iya girki Sosai


Ibtisam tace uhm Kedai kawai kice Kinji yunwa


Washe gari ibtisam Nada lecture karfe 8 dai dai, dan haka da wuri ta shirya ita d'aya ta tafi domin har yanzu su Aisha basu dawo ba.


Ibtisam basu fito daka lecture ba sai karfe 10, "zama tayi akan wani dakali, dan tasan kota koma Zarah bata nan dan tace mata 10 suma suke da lecture


Ibtisam na zaune tana danna wayarta gaba d'aya hankalinta nakan wayarta "sai jin muryan mutum tayi kaman daka sama ana fad'in madam danna waya


Da sauri ta d'ago kanta taga salis ne."murmushi ta saki tare da fad'in banga zuwanka bafa, kawai na daiji magananka daka sama


Salis yace yaushe zaki ji, tunda kina Bussy wajan danna waya, kina chatting


Tace uhm wani chatting, game nakeyi a wayar


Yace yau banga Aisha ta shigo lecture ba?


Ibtisam tace eh bata nan


Yace ok su Aisha manya indai mutum ya ganta a lecture Toh na Dr jibril ne, dan tasan baya wasa


Ibtisam bata ce komai ba, tana dai sauraranshi


Salis ya kira sunanta da fad'in ibtisam


Tace na'am


Yace ina son fad'a miki wata magana in babu damuwa


Tace ka fad'a karka samu damuwa


Yace OK...


Lokaci d'aya ya fara magana kaman haka, ibtisam tun sanda na ganki na yaba da hankalinki da kuma nutsuwarki, "duk da d'akinku d'aya dasu Aisha amma sai naga ke dasu ba irin halinku d'aya bane, kuna da banbanci Sosai


Ibtisam jinshi take


Yace tun sanda na ganki naji Ina sonki, sai dai nasan bazan samu karbuwa ba, may be kice Nayi miki k'arami ko kice muna karatu tare, naso Nayi shuru na boye abunda ke raina sai naga is better in fad'a May be in dace


Ibtisam tayi shuru Kafin tace"nagode da kauna, sai dai ina Mai baka hakuri akan biki na saura wata hudu da sati d'aya


Salis yace kai aure?


Ibtisam tace eh


Salis yace wow na tayaki murna, gwara kiyi auren domin shine darajan mace,"amma fa wlh kin burgeni da zakiyi aure tun yanzu, ba irin matan da za suce sai sun gama karatu ba, daka karshe samun mijin ya musu wuya ba


Ibtisam tace uhm ba tare da tace komai ba


Salis yace ya kamata dai yanzu tunda zakiyi aure kina da miji sai mu zama friends amma wanda zai aureki yayi Sa'a, yamin shigan sauri


Ibtisam dariya tayi domin maganan salis ta bata dariya yanda yace wanda zai aureta yayi mishi shigan sauri


Suna nan zaune suna fira ita da salis harya tashi yace Bari yaje ya amso sa'ko


Tace OK nima dai Bari inje in huta


Duka suka jera tare shiya Mike ita tasha kwana domin zuwa hostel, "koda ta koma d'akin taga su Aisha da hauwa da kubra a d'akin suna ta raban kud'i


Shigowan ibtisam yasa kubra fad'in matar Dr jibril


Ibtisam tace wa? Rufamin asiri dan Allah "tare da kallon su Aisha tace Sannunku


Aisha tace yauwa har an fito daka lecture din?


Ibtisam tace eh tare da fad'in harya bamu text baki shigo ba


Aisha tace bar shegen zanje in sameshi nasan Dan bai ganni bane ya bada text din, dan inje ya cini ne dan bura uba


Hauwa tace Waye?


Aisha tace Daniel mana


Hauwa tace tir harda Arne yake cinki? Aiko anyi Asara


Aisha tace Wlh banga Asara ba, wlh ki gwada bashi ya iya cin mace


Hauwa tace Allah ya kiyaye ai duk iskanci na, Banyi da wanda ba musulmi ba wlh


Kubra tace nima kaina ban hulda da Arne duk da ina yare, balle ku hausawa


Aisha tace kwaji dashi


ita kam ibtisam mamaki suke bata, yanda suke sakin zance anyhow babu boye boye ko tsoran Allah


Suko kunyar junansu basayi, kai Allah ya kyauta yasa mu dace


Nan suka zauna sunata fira


Kubra tace kun San Jamila fashion ta kusa da d'akin mu?


Hauwa tace eh na santa naji ance wai ta shiga cult dagaske ne?


Kubra tace gulman da zanyi muku kenan"ashe Kun sani?


Aisha tace nidai ban sani ba, sai yanzu, "haba sai yasa take shiga cikin manya manyan motoci Ashe ta shiga cult?


Aikam muna dan gaisawa zanyi taka tsan tsan da ita Wlh, kar taje ta bada jinina
.dariya suka saki su duka


Ibtisam kam Abun mamaki yake bata, dama an fad'a mata indai jami'a ne zata ga mutane iri iri, wasu y'an lesbians wasu bin maza, wasu y'an cult Ashe dagaske ne tunda gashi taji suna fad'i, "Aiko dole in dage da addu'a.


Washe gari su ibtisam karfe 8 suke da lecture kaman jiya, yau dr jibril ne zai shigo musu


Ibtisam da wuri ta isa tana shiga ita da Aisha shima ya shigo


Bai wani bata lokaci ba Ya basu text, Bayan sun gama ya k'ara basu assignment tare da fad'in 5mrk ne assignment din, text shima 5 duka 10mrk


Koda ya gama lecture fita yayi yabar ajin ba tare daya jira wani bayani daka bakin kowa ba


Aisha kallon ibtisam tayi tare da fad'in naga sai kallonki yake tayi daka na d'aga ido sai inga yana satar kallonki


Ibtisam tace Taya kika san ni yake kallo? Kenan Indai hakane Kema shi kike kallo


Aisha ta kwashe da dariya tare da fad'in Toh fah, kodai kishi kikeyi ne? "kawai inna d'ago ne sai inga yana kallonki


Ibtisam tace uhm Allah ya kyauta tare da tashi zata fita."salis yace ina zaki yanzu wani kecturer zaizo 10 dai dai gwara ki zauna


Zama tayi tare da fad'in au ai ban sani ba, nasha ko Mun gama babu Mai shigowa


Salis yace Tab yau fah muna da lecture 4 ma Akwai lecturer din da zaizo mana


Ibtisam tace Kai yau akwai zama..


Aisha tace ba kadan ba..


Suna nan zaune lecturer din ya shigo yayi musu lecture shima ya basu assignment ya fita


Ibtisam tashi tayi ta fita domin kabir ya kirata, tafiya take tana waya ita da Masoyin Nata cikin shauki da kaunar juna, "tun tube taci zata fad'i ji tayi an ri'keta Wanda idonta a lumshe yake gaba d'aya ta sadakar ta fad'i k'asa, "jin an ri'keta yasa ta bud'e ido a hankali ganin wanda ya ri'keta yasa ta tashi daka jikinshi da sauri


Dr jibril yace ki dinga kallon gabanki


A hankali cikin jin kunya tace ngd


Jin maganan Kabir yana hello hello


Yasa ta maida wayar kunnanta tare dayin gaba, Tana waya


Shiko Dr jibril gaba yayi abunsa






*BAYAN 3MONTH*


ibtisam da Zarah sun fuskanci abubuwa iri iri daka kawayen zamansu, inda suka dinga tura musu ra'ayi akan rayuwar banza, amma basu biye musu ba.


Shiko salis da ibtisam sunyi mugun sabo domin yana taimaka mata Sosai ta fannin karatu, "ganin haka ibtisam yasa ta sake dashi suke shiri Sosai dashi


Sannan ta gefen Dr jibril yana bama ibtisam shawara Sosai, tare da fad'a mata ta kame kanta daka kawayen banza, sau da yawa inya ganta dasu Aisha saiya kirata akan ta rage hulda dasu, "duk da ta fad'a mishi dakinsu d'aya dasu


Duk wanda ka gani a skul din zaka gansa yana karatu domin Sun kusa Fara exam, karatu suke Sosai Babu wasa.


Zarah da ibtisam dasu salis suna zaune a wajan wani bishiya wayar Zarah tayi k'ara d'auka tayi taga Najeeb mamaki ya rufeta ganin number d'inshi na Nigeria, "tace yaushe yazo k'asar?


D'auka tayi tare da fad'in bros yaushe kazo k'asar?


Najeeb cikin hausarshi wacce ya dan Fara koya saboda granny yace kwana 3,"sai kuma ya sauya zuwa English yace come out Ina skul d'inku


K'ara ta saki tare da fad'in kana ta wajan ina?


Fad'a mata inda yake yayi, "tashi tayi ta Fara tafiya da sauri kai tsaye inda Najeeb ya fad'a mata ta nufa


Hango wata mota tayi Prado tasan kuma ta gidansu ce, kai tsaye motar ta nufa tare da bud'e motar "k'ara ta saki ganin Mum da Najeeb


Tace mum dama har dake?


Fitowa Mum tayi suka rungume juna ita da Zarah sannan suka koma cikin motar zarah tace driver yaja su k'ara gaba


Zarah gaida Najeeb tayi tare da fad'in bros Nayi missing din'ka. Ya America?


Najeeb fine kawai yace tare daci gaba da danna wayarshi


Gab da inda su ibtisam suke zaune ita da salis suka faka motar, "Wanda dai dai lokacin Najeeb ya d'ago kansa Wanda idonshi ya sauka a kansu,"lokaci d'aya ya saki murmushi tare da fad'in wai ita ta shiga university har an fara wayewa tare da fira dako wani namiji


Bud'e kofar motar din Mum tayi suka fita ita da Zarah.


Ibtisam hango Mum yasa ta tashi tare da nufan Mum da sauri tayi hugging d'inta tana fad'in sannu da zuwa Mum


Mum cikin dariya tace yauwa ibtisam, y'an jami'a. " Ya karatun naku?


Ibtisam tace lafiya kalau Mum Alhmdlh


Muje ciki Mum


Mum tace toh har sunyi gaba ibtisam tace ah Zarah kuje ina zuwa, wayoyina yana wajan salis bari in amso


Zarah tace ok sukai gaba ita da Mum


Kai tsaye ibtisam wajan salis ta nufa inda ta ganshi yana k'okarin tashi, "tace Ina zaka ga wayoyina a kusa dakai


Kallon wayoyin yayi tare da fad'in kai Wlh ban Lura ba, kice dana tafi da wani ya samu


Dariya ta saki Tana fad'in dana shiga uku


Salis shima dariya yayi tare da fad'in keda sai miki akeyi a free, ai baki da matsala


Duk wannan abunda suke idon Najeeb na kansu, "tsaki ya danja ya tsana yaga mace tana sakewa dako wani namiji, "jiba yanda take mishi dariya kaman wani d'an uwanta


Ibtisam tace Bari inje sai munyi magana Ltr


Yace OK tare dayin gaba


K'aran da wayarta keyi ne yasa ta d'auka ganin Mum ce


Bayan ta d'auka mum tace ibtisam kice Najeeb yazo mana yana Mota


Ibtisam kallon motar tayi wanda ita bata san dashi aka zoba, "amsa mum tayi da Toh, jiyo muryan Zarah tayi tana fad'in Mum maza basa shiga hostel d'in mata muje dai waje wani restaurant


Mum tace ok ibtisam barshi Bari mu fito ma
.ibtisam dad'i taji, domin bata tunanin zata iya mishi magana, "ita Tama manta da wani Najeeb tunda hannunta ya warke, "amma jin an kira sunansu sai taji wani sabon tsanarshi cikin ranta, domin tunawa da abunda yayi mata


Cikin ranta tace mugu azzalumi sai Allah ya saka min.


Zama tayi a wajan tana jiran su Mum su k'araso


Bayan su mum sun k'araso ibtisam ta tashi, Mum tace suje suci abinci


Zarah tace suje wani restaurant a cikin skul din


Zarah ta nufi mota tace Najeeb ya fito suje


Kaman bazai fito ba, komai ya tuna kuma saiya fito


Ibtisam ganin ya fito ta tamke fuska tare da kawar da kanta gefe


Tafiya suka farayi kai tsaye har cikin restaurant din, matan dake wajan sai kallon Najeeb suke


NAJEEB daya lura da hakan sai yaji abun ya bashi haushi, tare da fad'in matsalan matan Nigeria kenan, basu da aji


Ibtisam tace ita bata cin komai, a koshe take.


Mum ta kalli Najeeb tace kaifa Mai zaka ci?


Yace nothing


Mum tace cikinku


Mum fried rice tace a bata, Zarah kuma tuwo tace ita Tana so


Mum tace a k'aro wani rice takeaway akai ma driver shima


Ibtisam tace a kawo takai Mai Bayan an kawo abincin domin bata son zama inda Najeeb yake ko kad'an.


Amsan abincin tayi ta fita waje Kai tsaye driver taba abincin da ruwa, inda ya amsa yana mata godiya


Aisha ce tazo inda ibtisam take tana fad'in ina kika samo wannan Mai k'aton motar haka? Ko Sanata kika samo?


Ibtisam tace Rufamin asiri dan Allah


Aisha tace toh na daiga kaman daka motar kika fito


Ibtisam tace ba daga ita na fito ba sa'ko na bada


Aisha ta kalli motar sabuwa fil tana she'ki tace ibtisam Waye mai motar plz?


Dariya Aisha tana ibtisam domin yanda duk ta wani rud'e take tambaya Waye mai motar


Aisha tace tsarki ya tabbata ga Allah kalla wani guy hadadd'e, wannan daka ganinshi Balarabe ne


Waigawa ibtisam tayi taga Najeeb ne wanda suka had'a ido, ta saki tsaki tare da Waigowa


Ta gabansu yazo ya wuce "Aisha tace kai Kinji kamshi wayyo ya barmu da kamshin turare amma wannan guy din ya had'u.... Shuru tayi tare da sakan baki ganin Najeeb ya shiga motar da ibtisam tace ta bada sa'ko


Aisha tace dama shine mai motar?


Ibtisam tace yayan Zarah ne fah


Aisha tace kina nufin Dan uwan Zarah ne?


Ibtisam tace eh


Aisha tace kai Wlh sai naje na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login