Showing 75001 words to 78000 words out of 182942 words
Chapter 26 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
isa kace sai munyi shawara dakai Kafin mu yanke hukunci? Baka isaba sannan kayi kad'an
Najeeb yace plz Mum ki daina sa baki am respecting you
Kallon Dad yayi yace Dad I won't accept this marriage
Dad yace ko kaso ko kar kaso wannan ba damuwa ta bace, amma Abu d'aya nake son ka sani idan ka cutar da ita zan manta nine mahaifinka Wlh koda sau d'aya tace kayi Mata wani abu I will make sure to punish you.
Najeeb fita yayi daka gidan cikin fushi lallai Dad ya raina shi, eh ya raina shi mana akan wani dalili zai aura mishi wannan karamar yarinyar kuma mara kunya, wace bata da komai, kai tsaye wani club yaje duk da yanzu yamma ne giya ya bu'kaci a bashi yasha inda ya amshi kwalban giyan ya farasha
Najeeb giya yake sha Sosai a kalla yasha kwalba wajan biyar, wanda bai taba shayuwa irin haka ba tunda yake, gaba d'aya ya bugu a nan ya fad'i Bayan ya gama surutai barkatai
Najeeb bacci yayi a nan ganin haka suka daukeshi sukai ciki dashi, dama akwai d'aki ga Wanda suka sha giya suka bugu sai a kaisu nan in bacci ya d'aukesu
Dad Bayan fitan NAJEEB zama yayi cikin bacin rai, lallai najeeb yayi nisa, har zamu dinga fad'a yana fad'a? Lallai duniya ta lalace d'an daka haifa ya dinga fad'a maka haka
Mum ganin irin halin da mijinta ya shiga yasa ta Fara bashi baki tare da fad'in kayi hakuri da halin najeeb, gaba d'aya baya kyautawa, na rasa irin wannan halin nashi
Dad yace karki damu, I will teach him a lesson very soon, zanyi maganin rashin tarbiyanshi
Mum tace Allah ya kyauta
Ibtisam dake d'aki duk taji abunda ya faru, tunda abun ya faru sai yau tayi murmushi tare da fad'in lallai tasan NAJEEB zai iya sakinta tunda baya son auren, wani irin dad'i taji domin tasan zata koma ma kabir d'inta....
*KANO NIGERIA*
Kabir yau kwananshi biyar a asibiti amma babu wani ci gaba, domin har yanzu jiya I yau ne, abun gwanin tausayi kallo d'aya zaka mishi kaga ya canza yayi wani fayau dashi, lallai in baka mutu ba, ba'a gama maka halitta ba, kabir gaba d'aya ya sauya kaman bashi ba
Family d'inshi suna cikin tashin hankali, Hafsat itama tana asibitin duk ta shiga cikin duniyar tunani tare da damuwa, wanda ita tun tuni take son kabir amma bata taba fad'a ba sai gashi Allah ya bata shi, gashi kuma tana k'okarin rasa shi
Ganin irin halin da yake ciki babu wani ci gaba yasa suka yanke shawaran su kaishi waje kawai domin hakan shine suke ganin zaifi
Koda suka ma Dr magana bai musa ba, domin yasan can Sun fisu kwarewa inda ya rubuta musu takarda na neman yarda a fitar dashi domin a duba lafiyanshi a America
Washe garin ranan aka tafi da kabir cikin masu tafiyan harda hafsat da wani k'anin Kabir din sai mahaifiyarshi suka wuce inda zasu sauka a hotel in sunje domin can ba kaman nan bane inda za'ace za'a kwana da mara lafiya, su ba'a kwana da mutum
Koda suka isa America an amshi Kabir inda suka fara sabon gwaje gwaje akanshi domin su gano miye matsalar duk da sun duba takardan asibitin da suka fara dubashi a Nigeria amma basu wani gamsu dashi ba, dan haka yasa suka fara sabon nasu binciken
Najeeb bashi ya tashi ba sai washe gari wajan karfe 1 da wani abu, mi'ka yayi tare dajin ya manta duk wata damuwa dake tare dashi, kai tsaye tashi yayi ya fara kallon d'akin da yake ciki, da sauri ya tashi tare da tunanin maiya Kawo shi nan?
Lokaci d'aya ya lumshe ido domin ya tuna da abunda ya faru, ido ya bud'e da sauri tare da fad'in kai impossible I won't accept that girl as my wife, tashi yayi ba tare da yayi sallah ba tun na jiya ya fita kai tsaye gidan ya koma, koda ya shiga baiga kowa a falo ba, dan haka Kai tsaye ya nufi part d'inshi inda ya shiga toilet yayi wanka, koda ya fito wanda yasa 3quater irin crazy jeans dinnan, sannan yasa riga mara hannu itama crazy shirt, gaba d'aya jikinshi kamshin turare yake tashi
Falon ya kuma fita inda ya iske Mum na fitowa daka kitchen, kallonta yayi tare da fad'in mum Ina Dad?
Banza dashi tayi ba tare da tace mishi komai ba, domin taji haushin abunda ya aikata jiya Sosai
Yace Mum am asking you Ina Dad yake?
Muryan Dad yaji yana fad'in kazo ka k'ara fad'amin magana ne?
Murmushi NAJEEB yayi tare da fad'in a'a but Ina son baka shawara ne
Dad zama yayi akan kujeran falon ba tare daya kuma cema NAJEEB komai ba
Najeeb yace Dad am I your real son?
Dad da sauri ya d'ago ya kalli NAJEEB tare da fad'in what kind of stupid questions is this?
Najeeb yace Dad Ina tantama akan niba d'anka bane, inda ni d'anka ne am sure baza min aure ba, ba tare Daka fad'amin ba, koda a waya ba, sai dai kawai ka zarce hukunci ba tare da sani naba
Dad I hate dat girl, wlh Dad gwara matan da Granny ta Kawo min akan ita, Mai zanyi da ita, wlh an cuceni
Dad yace NAJEEB itama kanta ibtisam din bawai tana son wannan auren bane, karka d'auka ko itama tana sone, ina tunanin ita ta fika tsanan wannan auren, domin na tabbata inda saki a hannunta yake da tuni ta sakeka, ni kaina da nake Mahaifinka nafi Sonta da kabir, akan Kai, domin ibtisam bata dace dakai ba dashi Kabir din ta dace, domin yana mata so Mai tsafta
Mum tace even me Wlh Ina son ibtisam da Kabir, domin Sun dace.....
Tsaki NAJEEB yaja tare da fad'in oh really? Saiku d'auketa kukai Mai ita
Mum tace you can say whatever, but ibtisam bata dace da mara kunya irinka ba
Najeeb tsaki yayi tare da tashi yabar musu falon gaba d'aya yayi gaba Abunsa
D'akinshi ya Shige inda ya rufe kofar ya d'auko kwalban alcohol d'inshi ya fara sha, lokaci d'aya yaji ranshi ya fara sanyi tare da manta abunda ya faru
Ita kam ibtisam dama take nema domin tayi magana da NAJEEB domin duk abunda suke fad'a tana ji, ta tabbata zai iya sakinta
Kwanan su Mum biyar suka fara shirin tafiya gida, ana gobe zasu tafi Mum ta shiga kasuwa da ibtisam wacce ta Fara sakewa yanzu domin tasan dole ma najeeb ya saketa ta auri KABIR d'inta tunda baya Sonta, kaman yanda itama bata sonshi.
Kayan sawa mum tasai ma ibtisam Sosai, kuma duk English wear sai jallabiya guda biyu da kuma kayan bacci, inda Mum tace zata had'a mata akwatin ta, Kafin ta dawo Nigeria insha Allah
Koda su Mum zasu tafi suka tara NAJEEB da ibtisam, inda Dad yayi ma najeeb warning akan idan yama ibtisam wani abu saiya hukunta shi
Itama ibtisam din dad yayi mata nasiha akan tabi mijinta sau da k'afa, tare da fad'a mata Mai nene aure da hakkokin mace akan miji, shima NAJEEB aka fada Mai hakkin mace akanshi
Najeeb tunda Dad yake magana baice komai ba, yanda yayi kaman yaji maganansu yanda yayi shuru
Ita kam ibtisam bama jinsu take ba, domin ita magana Indai bana kabir bane Toh bata ma saurara
Daka karshe Mum ta fad'ama najeeb kwanakin da ibtisam zatayi, saboda karatun ta
Ibtisam da NAJEEB duka suka tafi rakiya domin kai su Mum airport, saida jirgin su Mum ya d'aga sanna ibtisam ta tashi ta koma mota, wanda ta bud'e ta shiga gidan baya domin koda za suzo Dad ne a gaba
Najeeb bai zoba haka taita zama cikin motar, a kalla tayi wajan minti talatin tana jiranshi amma bai fito ba, gashi gaba d'aya ta gaji da zaman
Kwantar da kanta tayi akan kujeran motar, jin an bud'e motar yasa ta d'ago dakai, ganin najeeb yasa ta kuma kwantar da kanta
Muryanshi taji yana fad'in, uban wa kike so ya zama driver d'inki?
U better come front ko ki fita a motar kisan inda dare yayi miki idiot
Ibtisam da take a gajiye sannan bata da lokacin magana dashi yasa dole ta tashi ta bud'e kofar tare da fita ta koma gidan gaba
Tun Kafin ta rufe kofar yaja motar da gudu wanda hakan yasa tayi saurin rufe kofar, sanda yazo yin wata kwana saida ta buge kai domin yanda ya juya motar
Kai tsaye gidan suka koma inda yana faka motar ya bud'e ya shiga cikin gidan yana tsaki tare da fad'in Wlh an cuceshi yanzu an kawo mai abunda zai dinga takura mishi, tsaki yaja tare da fad'in I hate that girl ban San tunani ba amma tasa na Fara, haka ban San damuwa ba amma tasa na Fara I hate her with all my heart
Zama yayi a kujeran falon
Shigowan ibtisam falon yasa ya wurga Mata wani dan iskan kallo Mai cike da tsana
Ibtisam kam dashi da banza duk ta bada ajiyansu domin ita bata san ma yanayi ba
Shiko fad'i yake cikin ranshi yanzu da wannan karamar yarinyar aka had'ashi, gata mara kunya, ko uban Mai zan Mata oho K.....
Muryan ibtisam dinne ya Katseshi daga tunanin da yakeyi
Inda tace mishi ina son magana dakai
Kallonta yayi sannan ya kauda kai
Tace dan Allah Ina son ka taimaka ka sakeni
Wani irin kallo ya watsa mata sannan ya saki murmushi tare da fad'in kina tunanin ni NAJEEB ina sonki ne? Inma haka kike tunani you are wrong
Ibtisam tace Nasan baka sona, haka nima bana Sonka, shine dalilin da yasa nace ka sakeni.
Najeeb wani irin murmushin mugunta ya saki tare da kallonta a wulakance yace do you know what?
Bata bashi amsa ba, shima bai damu da hakan ba
Yace mistake din da akayi shine da aka d'aura miki ni a matsayin miji, you will leave hare as my servant, komai nawa ke zaki dinga yi daka yau, baki da wani hutu, domin ni banga abunda zakiyi min ba, Inba bauta ba
Ibtisam hawaye ne ya fara zuba a idonta tare da fad'in Dan Allah NAJEEB ka tausaya min ka sakeni in auri wanda nake so kuma yake Sona p.....
Yace keep quiet stupid, kina tunanin zan sakeki? You are wrong, duk wani abu da aka danganta shi dani har aka kirashi nawa ne, toh is only mine alone
Let me tell you something Ina son kisan wannan Abun inma kina tunanin ni NAJEEB zan sakeki kinyi kuskure, nasan am not your type har Abada niba ajinki bane, nafi karfinki, but tunda Sun cuceni Sun aura min ke duniya tasan you are my wife dole in zauna dake but not as my wife but as my servant
Sannan abunda yasa bazan sakeki ba, karki d'auka ko am in love with you.... Murmushi ya saki tare da fad'in god forbid never
Idan na sakeki in an tashi kwatance za'ace tsohuwar matar NAJEEB, wannan ne kadai yasa zaki zauna dani har ki koma ga Allah domin bazan bar haka ta faru ba, I won't allow anyone to call you with my ex wife that is d reason da yasa bazan sakeki ba.......
Read and leave it, dnt share to anyone
*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Ibtisam hawaye take Sosai tare da tsugunnawa tana fad'in dan Allah NAJEEB kayi hakuri ni nasan bama son juna ni dakai, ka duba girman Allah ka rabu dani inje in auri wanda nake so, na ro'keka K.....
Yace keep your mouth shut
Ibtisam kuka take Sosai, tare da zama a k'asa
Najeeb tsaki yaja tare da shiga d'akinshi ya barta nan zaune tana kuka, wanda shi tsanar kukan nata yake and baya son ji, ya rasa mai yasa gaba d'aya baya son yarinyar
Ibtisam kam kuka taci Sosai, har kanta ya fara ciwo, bata taba tunani a rayuwa zata fuskanci wannan halin ba, bata taba tunanin irin wannan ranan zaizo mata ba, wai yau itace matar NAJEEB
Gaba d'aya ji tayi ta tsani duniya da abunda ke cikinta, wlh da tasan hakan zai faru da tayi fatan ta mutu, lokaci d'aya ta goge hawayen idonta tare da tashi tana fad'in inna koma Nigeria dole insan abunyi domin bazan yarda da wannan auren ba, bazan iya zama da wani namiji a matsayin miji ba, Indai kabir na cikin wannan duniyar Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, mai yasa haka ta faru dani? Why me why why, zan iya hakura da komai Amma wanda Kabir kuka ta kuma saki lokaci d'aya tayi d'akinta tana shiga ta fad'a gado tana kuka wi wi gwanin tausayi
Najeeb Bayan tafiyan su Mum yaci gaba da abunda yakeyi, ba tare da tsoro ba, ko fargaba, kaman yau yana zaune a falo d'auke da kwalban giyanshi yana sha ibtisam ta fito wanda bata cika fita ba sai jefi jefi, sannan tunda su Mum suka tafi bata K'ara ganinshi ba sai yau
Kallo d'aya ya mata tare da kauda kanshi, yaci gaba dashan alcohol d'inshi
Ibtisam kam ko kallo bai isheta ba, kai tsaye kitchen ta nufa inda taga mai aikin gidan wacce baturiya ce tana ta faman goge goge, "gaida ibtisam tayi cikin harshen turanci
Ibtisam amsawa tayi tare da fad'in lafiya, sannan ta bud'e fridge lokaci d'aya tayi tsaki mara sauti tare da rufewa, tea kawai ta had'a tana k'okarin fita saiga Najeeb yazo kofar kitchen din ya tsaya tare dasa hannunshi ya Kare kofar
Kallon Mai aikin yayi tare da fad'in daka yau karki k'ara zuwa na baki hutun 2week
Nan Mai aikin ta amsa da OK
Kallon ibtisam yayi wacce take tsaye Tana jira ya matsa ta wuce yace daka yau ke zaki fara aikin Gidan nan, domin banga amfanin zamanki a nan ba, so just get ready and start d work tomorrow morning and ban son kazanta, in naga wani Abu dabai min ba I will punish you
Ibtisam wani irin kallo tamai na raini sannan ta kauda kanta gefe alaman baka da hanakli
Najeeb idonshi na kanta ganin irin kallon da tayi Mai yasa yace ma Mai aikin tazo ta wuce
Mai aikin fita tayi itama ibtisam tazo zata fita, ru'ko Mata hannu yayi tare da komar da ita kitchen din yayi baya da ita
Ibtisam wani irin kallo ta wurga Mai, Mai kama da miye haka
Najeeb ganin Mai aikin tabar gidan yasa ya matsa gab da ita tare da janyo mata riganta wanda yasa ta saki cup din tea din dake hannunta ya zubar mishi a jiki, da yake akwai zafi yasa ya saketa, Aiko ta fita da gudu tabar kitchen din
Tsayawa tayi bayan ta fita ganin ya kunna famfo din dake kitchen din yana wanke hannunshi tace nafi karfin inyi maka bauta, gwara ka dawo da wacce take maka aiki, tsaki taja tayi gaba da sauri ta shige d'akinta tasa key dan karya shigo mata
Shiko NAJEEB bayan ya kashe famfo din, abun mamaki ya bashi, lokaci d'aya kuma yayi dariya tare da fad'in I will teach her a lesson ina tunanin ta manta who I am, sai yasa take fad'amin magana.
Najeeb d'akinshi ya nufa inda yayi wanka tare da canza kaya domin zashi k'asar Germany kuma shi zai tu'ka jirgin, shiryawa yayi ya d'iba kaya cikin k'aramin akwati Domim kwana uku zaiyi ya dawo America, koda ya gama fita yayi yabar gidan ba tare daya fad'ama ibtisam ba, ko ya nemeta
Ibtisam kam tunda ta shiga d'aki bata fito ba, ga yunwa na damunta, gashi tana tsoran ta fita NAJEEB ya kamata ya bugi banza, dan bamai kwatanta, tunda daka ita sai shi, jin yunwa na neman illata ta yasa ta tashi ta bud'e kofarta a hankali tare dayin lam'bo tana le'kawa ko zata hangoshi ta koma, ganin baya nan yasa ta shiga kitchen din ta k'ara had'a tea a gaggauce, tana Gama had'awa ta koma da sauri tare da rufe kofarta
Asibiti kuwa KABIR an dan samu canji ba kaman daba, domin kuwa yanzu har ya fara bud'e idonshi yana rufewa, sai dai abu d'aya da yake basu mamaki shine idan ya bud'e idon nashi baya komai sai hawaye, dake zuba cikin idon nashi, likitoci suna iya kokarinsu akan kabir
Hafsat yanda ta damu kaman tafi kowa shiga cikin wani hali, domin tana matukar tausayin mijin Nata Sosai da Sosai, kullum burinta taga ya tashi, amma har yanzu
Ta gefen mahaifiyar Kabir kam, gaba d'aya Abun duniya ya isheta domin ita gani take kaman zata rasa d'anta
K'anin KABIR mai suna faruk yana matukar k'okari dasu tare da musu kalamai Mai dad'i akan ku su kwantar da hankalinsu insha Allah zai tashi,suyi ta addu'a
Ita dai hafsat in yana magana jinshi kawai take, amma tana matukar tsorata da yanayin kabir din, mutum baya iya ko motsa jikinshi balle yayi magana, sai dai ya bud'e ido ya rufe, KABIR ya sauya yanda kuka san an canza mishi halitta, lallai dan Adam ba komai bane, sannan ba'a gama ma mutum halitta sai ranan daya bar duniya
Najeeb bayan ya sauka a k'asar Germany Wanda kai tsaye d'akin da aka tanada dominsu dake cikin airport d'in ya nufa inda ya shiga ya kwanta domin ya huta, dai dad'e ba bacci yayi gaba dashi
Koda NAJEEB ya farka tashi yayi ya fad'a toilet tare da fitowa yasa kaya ya d'auki wayarshi ya wanda yasa sim din k'asar Germany din ya kira Najwa tare da fad'in where are you?
Tace am in the airport, tun dazu naita jiran kiranka