Showing 156001 words to 159000 words out of 182942 words
Chapter 53 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
gobe saimu tafi da safe ai, kaci abinci ko saina zuba maka ne??
Dariya yayi tare da fad'in tunda y'ar autarki bata nan yau nine autan sai a zuba min din kawai
Mum tayi dariya tare da zuba mai, nan suka zauna suna ta fira Inda NAJEEB yace Mum yanzu nasan ina rayuwa wanda da gaba d'aya ba rayuwa nake ba
Mum tace kaman ya??..
Yace Nasan addini na, Mum da gaba d'aya Ina amsa sunan ni musulmi ne amma ban San miye addini ba, amma a yanzu Alhmdlh Nasan abubuwa da dama kuma ina kan koya
Mum cikin mamaki tace najeeb a Ina ka koya??..
Murmushi yayi tare da bata labarin abubuwan daya faru Bayan tafiyar shi
Mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da tashi ta rungumeshi ta baya tana kuka tare da fad'in Alhmdlh Alhmdlh Alhmdlh yau nafi kowa murna yau Ina cike da farin ciki d'ana ya fara neman ilimin addini, najeeb Wlh baka ga yanda naji dad'i ba, abunda yake ranmu kenan akan muyi maka magana sai gashi kaida kanka ka Fara koya Wlh ji nake yau kamun anyi min kyauta Mafi girma a duniya
Najeeb yayi murmushi tare da fad'in Mum nima yanzu baki ji yanda nake jin dad'i ba, nasan miye rayuwa nasan yanda zan tafiyar da rayuwa domin samun tsira wanda da duk ban sani ba yanzu kam Alhmdlh
Mum tace najeeb Allah yayi maka albarka
Tashi yayi tare da kamo hannun Mum Ya ri'ke tare da fad'in mum plz ina son duk wani abu dana miki na rashin tarbiya ki yafe min, Dan Allah domin na gane da ba'a akan dai dai nake ba
Mum ta rungumo shi tare da fad'in na yafe maka duniya da lahira, Wlh najeeb komai kayi min ban taba ri'keka ba cos ni uwa ce sannan nasan duk wannan abunda kakeyi ina maka uzuri duba da irin kasar daka taso a cikinta
Wani irin hawaye ne ya zubo a fuskanshi wanda yayi sauri ya goge, lallai uwa uwace, shida kanshi yana jin kunyar abubuwan daya musu baya amma gashi yanzu tace bata rik'eshi ba, Allah sarki rayuwa duk Wanda bai mutunta iyayenshi ba yayi Asara, kun dai ga irin abubuwan da najeeb yayi amma Mum tace bata ri'ke shi ba, waye Zaima wannan inba Uwar data haifeka ba
Jin kiran sallah magrib yasa najeeb nufa masallaci
Su dad sun k'arasa Kano wajan karfe 9 da wani abu, kai tsaye asibitin suka nufa wanda koda Dr ya fito baiyi musu wani bayani akan abunda yake damunta ba, yadai ce jikin da sauk'i sannan suna kan gwaje gwaje akan abunda ke damunta, sannan har yanzu bata farka ba
Hankalin kowa ya tashi da wannan ciwon na Granny, ibtisam gaba d'aya sai kuka take, inda Zarah take ta rarrashinta, wajan k'arfe Goma Ummi tace ya kamata su tafi gida ita zata kwana da Granny....
Nan ibtisam tace ina, ita zata kwana da ita, saida ummi tayi dagaske Kafin ibtisam ta yarda harta suka wuce suda Zarah da abba inda Dad ya tafi hotel shima Bayan ya sai musu su madara ruwan roba da duk wani abu da zasu bukata sannan yaba Ummi kud'i yace ko za'a bukata
Koda su ibtisam suka je gida sai kuka take tana fad'in Wlh Ina jin tsoran wani abu ya samu granny ina matukar Sonta da yawa, Wlh baki ji yanda nake jiba na shiga uku Granny na
Zarah tace haba ibtisam babu abunda zai sameta addu'a za muyi mata, ki daina fad'in haka insha Allah komai zai wuce sannan granny zata warke Kinji
Ibtisam shuru tayi tana sauraran zarah
Zarah tace ki tashi kije kiyi wanka, kinga duk Fuskanki ya tashi idonki ya kumbura kaman wacce tayi shekaru gidan yari
Ibtisam tace hmm zarah Wlh hankalina a tashe yake ban son wani abu ya samu granny Wlh ko kad'an
Nan zarah tace babu abunda zai sameta maza tashi kije kiyi wanka Kinji
Ibtisam tashi tayi ta fad'a toilet tayi wanka, koda ta fito zarah bata d'akin can saiga zarah tazo da tea a hannunta da kazan da abba ya siya musu
Ta ajiye ma ibtisam tace gashi Nima Bari inje in had'a nawa tea din
Tashi tayi ta nufi kitchen inda itama ta had'o tea d'inta ta dawo ta Fara sha ibtisam kam kasa sha tayi
Zarah tace wai miye haka ibtisam kisha mana, ibtisam tace Wlh zarah bana son sha
Zarah tace Indai baki shaba Nima Wlh bazan shaba.....
Ibtisam tace ke nifa bana jin yunwa gwara kici
Zarah tsaki tayi tare da fad'in kinga saida safe
.ganin dagaske take yasa ibtisam fad'in zo kici Nima zanci
Jin haka yasa Zarah ta zauna tare da d'aukan cup din tea din ta farasha tare da kazan
Bayan sun kammala, itama Zarah wanka tayi tazo ta kwanta
Washe gari tunda sukai sallah asuba suka shiga kitchen inda suka d'aura abinci domin sukai asibti, Bayan sun kammala sukai breakfast suka nufi asibitin Wanda suka tarar har yanzu Granny bata farka ba ga oxygen ansa Mata.
Ibtisam hawaye ta farayi domin tausayi, taji Granny ta bata, tare da furta ciwon lokaci d'aya jiba jiya Uwar haka lafiyanta kalau amma kalla yanzu ko numfashi saida aka sa mata oxygen, kai ikon Allah, fita tayi waje tana kuka domin tausayin halin da Granny d'inta ke ciki
Zarah ce ta biyota inda ta zauna kusa da ita Tana fad'in ibtisam hakuri zakiyi kibar wannan kukan, inba haka ba kanki ne zaiyi ta miki ciwo....
Zuwan Dad ne yasa Zarah fad'in Ina kwana dad? Da fatan an tashi lafiya
Dad yace lafiya yamai jiki??
Tace da sauki
Itama ibtisam gaida Dad tayi inda yace har yanzu kina wannan kukan mamana
Ibtisam hannu tasa tare da share hawayen idonta
Murmushi Dad yayi sannan yace yauwa gwara kibar wannan kukan
Dad ya kalli Zarah yace Mum d'inki bata k'araso ba??
Zarah tace eh
Dad yace a'ah tace min fah tun d'azu sun shigo Kano bari in kirata d'auko wayarshi yayi yana k'okarin kira Zarah tace ga sunan
Nan Dad ya nufesu inda sukai gaba shida mum bayan ibtisam ta gaidata, d'ago kanta tayi sukai ido biyu da najeeb wani irin faduwan gaba taji wanda bata taba jiba sai yau, najeeb kam kallo d'aya yayi mata ya kauda kai tare da kallon Zarah yace yamai jiki hope da sau'ki??
Zarah tace toh har yanzu bata farka ba dai.....
Mum ce tazo tana fad'in ibtisam kuna ina kuzo Granny na kiranku NAJEEB kaima tawo
Da gudu ibtisam ta nufi d'akin inda taga Granny tana kallon sama hawaye na zuba a idonta, jin muryan ibtisam yasa Granny kallonta ibtisam nufan Granny tayi tana kuka tare da kamo hannunta
Granny cikin murya tana hardewa tace ina na je bu
Mum tace najeeb jeka mana
Najeeb kusa da gadon yaje inda Granny ta Kamo hannunshi Tana mishi murmushi, shima murmushin ya sakar mata, had'a hannunshi tayi dana ibtisam ta Fara magana najeeb Ina son ku kasance kaida ibtisam a haka har karshen rayuw..... Kallon mum tayi tace fad'a mishi abunda nake fad'a nan Mum ta Fara fad'a mishi abunda Granny take fad'a..... Granny tace naso inga yaranku amma Allah bai nufa ba.....
Ibtisam cikin kuka tace Granny ki daina fad'in haka dan Allah na ro'keki
Granny tace ibtisam ni nasan bazan tashi ba, wannan ciwon bazai barni ba, dan Allah najeeb ku koma ku zauna kaida ibtisam hakan zaisa koda na mutu in mutu cikin salama, wlh Ina takaicin rashin jituwan ku,, ina so kumin alkawari zaku zauna a tare har abada......
Da sauri najeeb yace I promise Granny kin gani tare da K'ara matse hannun ibtisam duk mum na fassara Mata
Granny wani irin murmushi tayi lokaci d'aya ta saki hannunsu Tana salati wanda dai dai lokacin oxygen din da aka saka mata yake k'okarin d'aukewa.......
Plz I don't tin gobe zanyi posting coz gobe gaba d'aya Ina busy sai yasa na muku yau but inna samu time may be inyi koda babu yawa
Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
Lokaci d'aya oxygen din ya tsaya cak........
Ibtisam gaba d'aya k'asa tayi ta fad'i bata san ta fad'i ba, gaba d'aya hawayen dake idonta lokaci d'aya ya tsaya cak....
Dr ne ya shigo inda ya fara dubata amma ina rai yayi halinsa, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun abunda Dr ya iya fad'a kenan tare da fad'in Allah ya amshi rayuwarta
Zarah kuka ta saki ita dasu Mum suko su Dad da abba kukan zuci suke, najeeb kam gaba d'aya wani irin yanayi ya shiga Mai wuyan misaltuwa, lokaci d'aya hawaye ya fara zuba a idonshi lallai sunyi babban rashi a family d'insu
Ibtisam kam gaba d'aya ko kukan ta kasayi ma, zan iya cewa kaman tunaninta ya dauke Domin gaba d'aya ta daina jin komai, ita gadai ta nan ne kawai
Nan aka d'auki Granny bayan Mum ta d'aga ibtisam tare da ri'keta suka nufi Gida inda aka ma granny wanka domin kaita gidanta na gaskiya, kafin kace Mai mutane har sunji kabarin mutuwar lallai Granny tayi mutane sosai sai dai muce Allah yaji kanta lallai ciwon ajali kenan, wanda ya kama Granny lokaci d'aya ashe ciwon bana tashi bane Anata amsan gaisuwa.....
Ibtisam kam gaba d'aya ta kasa kuka, magana ba ta kasa furta komai, ganin haka yasa hankalin Mum ya tashi inda taita fad'in ibtisam kiyi kuka domin rashin kukanki akwai matsala.....
Ibtisam ido ta bita dashi tana kallonta kaman wata mara wayau yanda takeyi da idonta
Mum ganin haka yasa ta janyota jikinta tana fad'in ibtisam Granny ta rasu kiyi kuka, duk wannan abunda Mum take fad'i tana fad'a ne domin ibtisam tayi kuka amma ta'ki yi.
Koda Ummi tazo taga Mum na fama da ita akan tayi kuka amma ta kiyi kaman ma bata jin mum din, sai taji ibtisam din ta bata tausayi lallai dole tayi kuka domin kuwa ibtisam tayi mugun sabo da Granny, sunyi mugun shakuwa Sosai
Ummi itama babu yanda batayi ba amma ibtisam taki yin kuka, gaba d'aya su duka sun shiga cikin wani hali, zarah itama tayi tayi amma ta'ki kuka
Mum ta kalli ummi tace rashin kukanta Akwai matsala babba, inaga ko zan kaita hspt ne??
Zarah tace Bari dai a kira najeeb ya kaita tunda kuna amsan gaisuwa ku a nan
Zarah kiran najeeb tayi a waya ta fad'a mishi halin da ake ciki, kai tsaye yace Bari ya shigo cikin gidan
Shigowa yayi inda ya iske basa falo sai mutane wanda suka zo gaisuwa, ummi ce ta fito ganin najeeb yasa tace yauwa tana d'aki tare da nuna mai d'akin ya shiga
Koda NAJEEB ya shiga itama mum fita tayi Bayan tace ya kaita asibti, ganin haka yasa Zarah itama ta fita
Najeeb kallonta yayi gaba d'aya sai yaji ta bashi tausayi domin yasan sun shaku da Granny Sosai, gashi ta tafi ta barta bazata sake dawowa ba
Najeeb kusa da ita ya zauna tare da kallonta lokaci d'aya ya juya da ita tare da kallon fuskanta ya fara fad'in ibtisam kin tuna alkawarin da Granny tace mu d'aukar mata?? We don't love each other but we have to live together saboda munyi Mata promise, kin San bana sonki I.....
Kuka ta saki mai sauti tare da sauke idonta akanshi, wani irin abune ya tsaya mata a wuya Mai zafi
A hankali ta Fara kiran sunan Granny tare da fad'in shikenan na rasa ki, sai kuka Sosai wi wi wi......
Najeeb jin kukanta yake har cikin ranshi, Lokaci d'aya ya janyota jikinsa tare da rungumeta yana rarrashinta tare da fad'in ibtisam addu'a za muyi mata, ba kuka ba, wannan kukan baida amfani plz ki daina....
Cikin kuka tace ya zanyi?? Just muna fira nida ita ta fad'i ban taba kawo mata mutuwa ba, amma ta tafi, ban taba zaton zata mutu yanzu ba, amma gashi ta tafi ta barni, zuciya ta babu abunda take sai ciwo tare da rad'adi Innalillahi'wa inna ilaihirajiun
Ibtisam gaba d'aya ita tama manta ko wa take tare dashi, domin bata cikin yanayin da zata iya tunawa ko ganewa
Shi kam NAJEEB sai shafa mata baya yake alaman tayi shuru.....
Mum ce ta shigo d'akin domin taji shuru basu fito ba, ganin tana manne jikin najeeb tana kuka hakan yasa Mum jin dad'i tunda tana kukan
Itama Mum zama tayi a kusa data gefen ibtisam din, ganin haka yasa Najeeb tashi tare da fad'in tunda tayi kukan bari in fita waje
Tashi najeeb yayi ya fita tare da tausayawa ibtisam din
Mum ta kira sunanta da fad'in ibtisam
D'ago Kai tayi ta kalli mum wanda gaba d'aya idon ibtisam din ya canza yayi ja
Mum tace ki daina wannan kukan addu'a ya kamata ki mata domin shine babban gatan da zaki nuna mata a rayuwa, idan mutum ya mutu babu abunda yake bukata face addu'a
Ibtisam kaman an danna stop, gaba d'aya ta tsaya da kukan lokaci d'aya, inda ta kwantar da kanta akan gadon d'akin, gaba d'aya abubuwan daya faru ita da Granny taita tunawa, lokaci d'aya kuma ta Fara Mata addu'a tare da neman Allah ya gafarta mata zunubanta, lallai ibtisam taji wannan mutuwar Sosai.
Ibtisam gaba d'aya ta rame saita k'ara yin haske, fuskanta yayi fayau, Mum a gidan take kwana dad da najeeb kuma a hotel
Yau akayi sadakan uku
Ibtisam dai har yanzu ga tanan ne dai, gaba d'aya bata jin dad'in komai, rayuwa kenan, shikenan yanzu babu Granny a wannan duniyar
Sallama Dad ne da Abba da najeeb yasa ibtisam d'aga Kai tare da gaidasu ta tashi tabar falon
Najeeb da ido ya bita harta bace Mai
Shima kanshi najeeb din yayi mugun jin mutuwar Granny, wanda ya tabbata da yanzu tana nan yazo data Fara fad'a Mai magana, Allah sarki rayuwa kenan
Dad yace Yau zasu koma Abuja, dan haka saisu tashi su wuce
Abba ya kalli Dad yace zaku tafi da ibtisam, tunda mijinta yazo banga amfanin zamanta a nan ba....
Mum tace hakane duba da irin yanayin data shiga, Indai tana nan zatai ta tunani, musamman yanda ta saba da Granny kwana tare sukeyi yau ta bud'e ido ta ganta ita d'aya Abun akwai ban tausayi
Dad yace hakane tare da fad'in Ina ibtisam din ku kirata
Mum tashi tayi inda ta nufi d'akinsu ta gansu ita da zarah duka sunyi jigum babu Mai magana
Mum tace ibtisam zo ana kira
Ibtisam tashi tayi tare dasa hijab tabi Mum inda sukai falo
Bayan ta zauna, Abba yace ibtisam inaso ki shirya zaku wuce abuja yau, za Kibi mijinki ku tafi, ina son kiyi hakuri ki zamo Mai biyayya, sannan karki manta abunda mama ta fad'a kafin ta rasu....
Kuka ta farayi domin ta tuna da abunda granny tace, tana son su kasance ita da najeeb har abada.......
Abba ne ya Katseta da yake fad'in ibtisam Nima Ina neman alfarma dan Allah....
Da sauri tace Abba karka nema alfarma a wajena ka bani umarni, zanbi ni y'arka ce komai kace inyi nimai biyayya ce a gareka
Idon najeeb na kanta ya rasa mai yasa take bashi tausayi Sosai, kodan saboda halin data shiga ne oho
Abba yace Allah yayi miki albarka, ina son ki zauna da mijinki lafiya, sannan ina son ki sani shifa aure bauta ne, sannan hakuri ne, duk abunda hakuri bai baka ba, toh rashin shi bazai baka ba, Kibi mijinki sauda k'afa, domin aljannanki tana k'asan kafarshi, sannan ki kasance mace Mai rufa ma mijinki a asiri, karki zama d'aya daga cikin mata masu fad'ama kawaye sirrin miji, komai mijinki yace kiyi, toh ki tabbata kinyi indai bai saba ma Shari'a ba, sannan karki manta najeeb dan uwanki ne, idan kika ga yayi abunda ba dai dai ba ina son ki daurashi a kan hanya, wannan Abun shine kawai nake nema a gareki ina fatan zan samu
Kuka take Sosai, bata samu ta iya bama Abba amsa ba sai kukan da takeyi Mai cin rai, yanzu shikenan kaddaranta ta soma daga yanzu, domin a wannan karan tasan dole ta zauna da najeeb, duba da yadda Granny ta nemi alfarma kuma wannan itace magananta na karshe kafin tabar duniya, inda tace tana son su kasance tare har abada, yanzu shikenan gaba d'aya rayuwarta zata koma irin rayuwar da sukai baya, za suyi rayuwa irin wacce sukai da, cikin kunci da rashin ganin girman kowa, amma babu komai zanyi k'okarin in cinye wannan jarabawan insha Allah,....
Ummi ce ta katse mata tunani tare da fad'in saiki tashi kije ki had'a kayanki.
Ibtisam tashi tayi jiki a sanyaye inda ta nufi d'akinta wanda Zarah ke zaune nan ta Fara hada kaya itama Zarah tayata ta farayi, idon ibtisam yakai wajan kayan granny da sauri ta nufi wajan kayan tare da rungumo kayan Tana kuka Sosai, tana fad'in wayyo granny shikenan yanzu kin tafi kin barni, ina nan ina kewarki Mai yasa kika tafi?? Yanzu kinsa gaba d'aya bana jin dad'in komai na rayuwa kuka take Sosai tare da shessheka
Dakyar Zarah ta rarrasheta tayi shuru inda Mum ta shigo ta kira Zarah domin tazo su tafi, motar su Dad mum da Zarah suka shiga
Ibtisam kam ita da najeeb Mota daya, duka suna baya, driver ya tada motar suka Kama hanya, ibtisam naji an tada motar ta kuma sakin sabon kuka, najeeb na jinta baice mata komai ba sai wayarshi daya d'auko yasa ear piece a kunne
Ibtisam kuka take Sosai har kanta ya fara ciwo, bata san lokacin da bacci ya d'auketa ba, ta dai farka ta