Showing 138001 words to 141000 words out of 182942 words

Chapter 47 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

ta Fara fad'in najeeb na tsaneka har abada bazan taba Sonka ba, wlh even for a minute ban son ganinka, plz am begging you just stay away from me...


Lokaci d'aya idonshi ya kad'e domin a duniya ya tsani wannan Kalman Nata, yanda take nuna Mai kiyayya, yace ibtisam am your husband so dole inzo inda kike


Tace you are not my husband, najeeb..... Sai kuma tayi shuru tana kuka...


Kokarin matsawa yayi ya kamota tace don't touch me.....


Ido ya bita dashi tare da kallonta


Ibtisam tace najeeb am not your wife karka manta ka sakeni..... Oh na manta how will you knw that u divorce me?? Tunda kana cikin Maye.....


Ina tayaka murna ka rabu da enemy din'ka and Nima Ina taya kaina...... Kuka yaci karfinta


Shi kam NAJEEB gaba d'aya d'auke wuta yayi data furta Mai Kalman cewa ya saketa Bayan yasha giya, wani irin sarawa yaji kanshi yayi,.... Lokaci d'aya magananta ya fara mishi yawo a Kai wanda take fad'in am not your wife don't touch me...... Kenan alcohol d'in da yasha last a America shine ya furta Kalman ya saketa?? Tunawa yayi a ranan ya ganta kaman bata da lafiya.....


Kallonta yayi tare da kamota ya rungumota yace ibtisam plz don't tell anyone akan cewa na rabu dake bazan iya barin Uwar d'ana ta auri wani ba, plz just for our child keep this as Secret......


Da sauri ta tureshi tare da fad'in ni inada ilimi Nasan abunda nakeyi, sannan nasan abunda Allah ya hana da kuma wanda Allah yayi hani dashi, lallai Kai tarin laifin naka kullum k'aruwa yake Bayan manyan laifin da kake aikatawa shine kake Son k'ara wani? Lallai babu komai a ranka sai duniya baka tuna Allah inda kana tuna Allah Wlh bazaka fad'i haka ba, ni ba irin matan da kake bi bane, ni nasan abunda nakeyi kuma daka yau kar I.....


Yace enough ibtisam komai zai faru am still your husband and keep this on your mind yana fad'in haka ya fita Fuuuuu


Ibtisam kam ganin najeeb ya fita ranta wani irin tafarfasa yake mata, da sauri ta d'auko ledan maganinta Wanda aka bata a hspt ta bud'e su duka maganin suna da yawa ta watsa a bakinta ta shanye su duka, tana murmushi tare da fad'in nasan tunda nasha wannan maganan wannan cikin zai zube and daka ya zube shikenan kowa ya huta.......










Kabir ne zaune a office yana danna system d'inshi wayarshi ce tayi K'ara, alaman kira yana shigowa, d'auka yayi ya duba ganin Sunan hafsat yayi akan wayar


D'auka yayi tare da sawa a kunnenshi yace madam ya akayi??..


Ta gefenta tace lafiya, when zaka dawo??


Yace did you miss me ne??.


Murmushi tayi tare da fad'in alot I really miss you, and I cook your favorite food....


Tun kafin ta k'arasa yace oh I have told you, ki daina shiga kitchen kina bama kanki aiki, but baki ji abunda nace ba, kina son wahalar min da baby


Hafsat tace am sorry, kasan Mai irin Lalura na ana son ta dinga yin aiki yanda inta tashi haiyuwa zaizo mata da sau'ki


Yace but nidai banso, tunda baiyi kwari Sosai ba, and gani nan zuwa right now


Tace OK


Bayan sun kashe wayar kabir murmushi yayi domin duk wannan Abun da yakeyi yana yine domin kar Allah ya kamashi and yasan yanzu ibtisam tayi aure shima dole ya sauke hakkinshi dake kansa akan matarshi, amma so d'aya ne yaba ma ibtisam har yanzu yana Sonta Sosai, sai dai yakan ro'ki Allah akan ya cire Mai Sonta ya amshi tashi kaddaran amma Abun mamaki kullum kaman Sonta K'ara k'aruwa yake a cikin ranshi, har tausayin hafsat yake yanda take nuna Mai kulawa amma shi gaba d'aya zuciyarshi baya wajanta ko kad'an


Har yanzu zuciyarshi bata cire mishi cewan zai samu ibtisam ba, sau da yawa yakan k'okarin ya cire tunanin ta in yanayi amma ya kasa sai yasa yake keeping kanshi busy saboda baya son bata lokaci wajan tunani


Lokaci d'aya ya tashi tare da fita kai tsaye waje yayi inda ya nufi wajan motarshi ya shiga ya tada..... Tuk'i yake yana lafiya wani Mota ne yake ta mishi horn alaman ya tsaya


Kaman bazai tsaya ba, lokaci d'aya ya faka tare da fitowa, inda motar itama ta faka a gaban nashi


Wani mutumi ne ya fito cikin motar kiran golf inda ya nufi kabir din ya bashi hannu suka gaisa


Kabir yace lafiya??


Mutumin yace ai yau wajan kwana biyu inata so in ganka amma Allah baiyi ba, domin ina son fad'a maka wani abu mai muhimmanci tare da k'ara fad'a maka kayi a hankali akan mutanan da kake hulda dasu, and mutane ba Abun yarda bane, wanda bakai expecting ba sai yaci amanarka, wanda bakai tunani ba shine yaudaranka ya munafunceka....


Kabir ya Katseshi tare da fad'in wai maike faruwa ne plz fad'amin mai nene???


Mutumin yace nine wanda naje ranan daurin aurenka nace kana da HIV......


Kabir ru'ko mutumin yayi idonshi ya canza Kala..... Lokaci d'aya kuma ya saki mutumin tare da fad'in kasan Mai ka aikata kuwa!? Kasan irin laifin daka aikata kuwa?? Ka cuceni ka batamin rayuwa, har yau Ina fama da dakon son ibtisam......


Mutumin yace kayi hakuri KABIR Wlh nima sani akayi, ba komai bane ya kawo ni face in fad'a maka gaskiya domin Nima Wanda ya sani aikin ya yaudareni yaci amanata......


Yace KABIR wannan aikin ba kowa bane ya sani sai abokin ka Tahir


Kabir yace Tahir??


Wani irin kallo yama mutumin tare da fad'in karka kara mishi wannan k'azafin domin har abada Tahir bazai taba min wannan Abun ba.....


Mutumin yace Allah sarki, haka masu kyakyawan zuciya suke dama, kuna da saurin yarda, gashi ana saurin cin amanarku, Wlh Allah d'aya ne koh?? Toh Wlh Tahir yasa ni saboda yana son yarinyar, ya Turani inje ince kana da HIV domin in an fasa auren shi yace tunda hakane zai aureta sai akai rashin Sa'a go slow ya rik'eshi a hanya har aka d'aura auren yarinyar da wani


Wanda haushin wannan Abun yasa ya hanani sauran kud'in aiki na, da naga haka shine nace Zan fad'a maka gaskiya domin mu irin mu bamu da amana indai Mun ri'ke amana Toh ka bamu hakkin mu


Dan haka saika kiyaye dashi, yana fad'in haka mutumin yayi gaba abunsa


Kabir kam gaba d'aya wani irin dum yaji a kansa mamaki yake Tahir taya Tahir zai mishi haka!?? Lallai inko ya tabbata shi dinne yaci amanarshi, domin a yanda ya d'auki Tahir duk yanda yakai da son Abu Indai yace yana so zai bashi amma...... kai hannu ya d'aura a kanshi tare da lumshe ido yana jin wani irin jiri


Dakyar ya samu ya bud'e motarshi ya shiga inda ya figa da gudu Kai tsaye office din Tahir ya nufa koda ya shiga


Tahir yace a'a angon hafsat


Kabir zama yayi tare da kallon Tahir yace Mai yasa kamin haka Tahir??


Tahir yace mai ya faru??


Kabir yace Mai yasa ka zama silan da yasa aka fasa aurena da ibtisam??


Da sauri Tahir ya tashi ya fara in Ina.....


Kabir ganin haka yasa ya tabbatar shi dinne, dan haka yasa yace Tahir kaci amanar amintaka inda ka d'aukeni yanda na d'aukeka bazaka min haka ba, just saboda kana son ibtisam Wlh ni nasan Ina son ibtisam but a yanda nake jin abokantakar mu zan iya hakura, but kaci amanata but babu komai is part of experience


Tahir yace KABIR Dan Allah kayi hakuri Wlh Sharrin shedan ne, daka baya Nayi nadama, musamman da ni ban sameta ba kaima baka sameta ba, Nasan tun sanda na ganta naji Ina sonta Wlh Sharrin zuciya ne kawai tare da shaidan dan Allah kabir kayi hakuri kar wannan Abun yasa ya zama silan abunda zai had'a zumuncin mu....


Kabir yace babu komai haka Allah ya nufa nayi imani da kaddara Allah yasa ba tawa bace yana fad'in haka ya fita yabar office din Tahir


Shi kam Tahir babu komai a ranshi sai tarin nadama tare dayin dana sani da abunda ya aikata wanda bai taba jin kunya a duniya ba irin yau, lallai son zuciya ya kaishi ga halaka lallai ya biye ma zuciyarshi Wanda gashi ta kaishi dayin dana sani Innalillahi'wa inna ilaihirajiun


Shi kam kabir koda ya nufi gida kai tsaye d'akinsa ya fad'a hafsat ganin haka yasa taji wani iri domin tasan indai ya fad'a irin wannan halin to tasan yaji magana akan ibtisam ne, ido ta lumshe gaba d'aya kishin ibtisam yana cinta wanda take ganin itace tasa mijin Nata ya kasa bata wani kulawa


Kai tsaye ta tashi ta nufi d'akin kabir din amma Abun mamaki yasa ma kofar key ya rufe, alaman baya bukatar a shigo a damesa


Wani hawaye ne ya gangaro mata a ido tare da ba'kin cikin wannan rayuwa, yaushe mijinta zai cire wannan ibtisam din cikin ransa? yaushe zai daina tunaninta? yaushe zai bata cikakkiyar kulawa?


Lokaci d'aya tabar kofar d'akin tana kuka ta nufi d'akinta, lallai tana fama da son maso wani koshin wahala, ita Tana masifar son kabir amma shi ibtisam yake so


Ibtisam bayan tasha maganin duka, lokaci d'aya cikinta ya fara murdawa da ciwo Sosai kaman zata mutu, ihu ta Fara saki wanda bata san tanayi ba, domin irin azaban da takeji gaba d'aya bata san inda kanta yake ba ihu take Tana kuka hannunta nakan cikinta.....


Najeeb a tare da Mum suka zo d'akin da gudu


Koda suka k'araso tayi k'asa hannunta na kan cikinta tana kuka.


Da sauri NAJEEB ya dauketa sukai hspt da ita inda akai emergency da ita sai ihu take Tana kuka


Najeeb gaba d'aya ya kasa samun sukuni domin a furgice yake tare da fargaban mai ya sameta??


Itama Mum ta kasa zama gaba d'aya hankalinta a tashe yake


Dr dai yana ciki gaba d'aya jikin ibtisam yayi weak babu kwari


Dr yayi wajan 40 mnt sannan ya fito inda yake fad'a musu tasha magani over Wanda hakan yasa take wannan ciwon, daka duka alamu tana son zubar da cikin dake jikinta amma yanzu ku gode Allah komai normal but if she try again zata iya samun matsala domin kuwa wannan maganin da tasha yasa mahaifarta tayi weak, is better tayi hakuri harta haifi abunda ke cikin Nata....


Tunda Dr ya fara bayani idon NAJEEB ya kad'a yayi ja, lallai ya tabbatar da irin tsanar da take mishi lallai ya tabbatar tunda har Da gaske zatai yunkurin kashe abunda ke cikinta ya tabbatar zata iya kasheshi Fuuuuu ya fita daka hspt din mum na kiranshi amma ina kota ita bai bi ba Kai tsaye inda ake siyar da alcohol ya nufa inda ya siya wajan kwalba goma ya nufi gida


Koda ya k'arasa key yaba driver tare da fad'in ya koma hspt ya jira mum


D'akinshi ya shiga ranshi a bace har wani duhu duhu yake gani, bud'e bottle din alcohol d'in yayi yana k'okarin sawa a baki ya tuna da maganan ibtisam din I hate you duk wasu manya laifi ka had'a, you are drinker womanizer.... Ido ya lumshe tare da kafa kwalban a baki ya fara sha yana surutai yana fad'in even I, I hate you shan alcohol d'inshi yake kaman hauka yana surutai tare da jefar da bottle din ya fashe a d'akin a kalla yasha wajan bottle hud'u kuma duk ya fashe bottle din a d'akin lokaci d'aya ya fad'a kan bottle din a k'asa.......




Mum a asibti ta kwana ita da ibtisam wacce take a kwance har yanzu bata farka ba


Ibtisam sai wajan asuba ta farka tare da bud'e idonta Wanda yake a kumbure ta Fara kallon d'akin, ganinta a asibti ga Mum na sallah ta gane an kawo ta hospital ne, lokaci d'aya abunda ya faru ya fara dawo mata wani irin Abu taji yazo mata tare da fatan Allah yasa cikin ya zube tunda tasha magani da yawa.....


Jin muryan mum tayi tana fad'in kin tashi ne??


Ibtisam cikin dashewan murya tace eh


Ibtisam tashi tayi amma jikinta babu kwari, Mum tace Bari in taimaka miki kar abun drip din ya goce... Ko da yake bari in kira su domin naga ya kusa k'arewa ma, fita Mum tayi ibtisam taba cikinta tayi wanda ya dan Fara tashi saboda yawan cin abincin da takeyi sosai, jin alaman har yanzu yana nan yasa ta saki wani irin kuka tare da fad'in duk wannan wahalan da nasha?? Wannan wani irin jarabban ciki ne haka?? Wlh in bai fita ta sauk'i ba zanje a wanke shi ta yanda zai fita da hujja


Shigowan mum da nurse yasa tayi saurin goge hawayen idonta, nan nurse ta cire mata drip din Bayan mum ta tambaya ko akwai wanda za'a k'ara mata??


Nurse din tace a'a sai dai in dr yazo


Ibtisam toilet ta shiga inda tayi alwala tare dayin sallah, Bayan ta idar ta koma kan gadon ta kwanta wanda Tana tafiyan ne dakyar


Mum Tana zaune har Dr yazo ya duba ibtisam


Dr Ya kalli ibtisam yace ya jikin??


Tace da sau'ki


Yace ibtisam Mai yasa kika sha magani da yawa haka?? Kina son cikin ya zuba NE??


Ibtisam shuru tayi ba tare da tace komai ba, wanda ta tabbata Mum tasan komai wani irin kunya taji Sosai


Dr yace ina son in baki shawara Idan kika k'ara yunkurin yin hakan zaki iya samun matsala domin mahaifarki bata da kwari, so you have to be very careful Indai kina son rayuwarki


Nan Dr yace zata zauna na kwana biyu a nan, inda Mum tace bazasu iya tafiya gida ba


Dr yace zasu iya but tana bukatar hutu sosai, koda Kun koma Karta dinga aikin komai


Nan Mum tace shikenan inda Dr ya sallamesu suka koma Gida, koda suka isa Gida mum saida ta had'ama ibtisam ruwan dumi a cikin bath sannan tace taje tayi wanka


Bayan ibtisam ta shiga toilet mum direct d'akin NAJEEB ta shiga inda ta ganshi a k'asa ga jini dake zuba a jikinshi wani irin ihu ta saki mai firgitarwa da sauri ta nufeshi ta juyo dashi domin ta kife ya fad'i cikin mayen giyar da yasha inda ya fad'a akan kwalba Wanda ya sokeshi a cikin sa, Bayan ta juyo dashi ta Fara kuka ganin kwalba da sauri ta d'auki wayarta tana kuka lokaci d'aya ta kira Dr inda ta fad'a mishi yazo da kayan aiki kwalba ya sokar mata da a ciki


Ciki ta koma inda sai a sannan ta lura dako numfashi bayayi..... Wani irin ihu ta kurma mai ban tsoro wanda yasa ibtisam dake d'aki itama ta fito da sauri ta nufi gefen da taji ihun da yake a bud'e mum tabar kofar ibtisam itama shigowa tayi ganin halin da yake ciki yasa itama ta tsorata ganin jini a daskare Wanda da duka alama ya dad'e shine ya fara bushewa, Wanda ga wani shima yana zuba lokaci d'aya taji tana jin jiri ita dafa bangon d'akin tayi ta sulale tayi k'asa itama........


























Read and leave it, dnt share to anyone......*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*














Mum ganin haka yasa ta kuma rud'ewa tare da salati, cikin tashin hankali ta nufeta, Shigowan dad ne yasa ya tsaya yana kallon ikon Allah, gaba d'aya kasa magana yayi sai kallo da yake binsu dashi ga NAJEEB kwance jini na zuba ga ibtisam itama kwance, lokaci d'aya yayi karfin halin ciro wayarshi ya fara kiran Dr.....


Jin sallama a falon yasa Dad fita, Dr ne yazo inda Dad ya mishi Iso har cikin d'akin najeeb din, inda Dr yaga kwalban daya sokeshi da kuma irin ciwon da yaji, nan take dr yace dole sai anje hspt, Mum fita tayi ta kira masu aikinta inda aka Kama ibtisam su Dad kuma suka Kama najeeb Wanda gaba d'aya basu San a wani hali yake ba


Kai tsaye hspt aka nufa dasu, inda duka aikai emergency dasu, Dr har uku suka shiga tare da nurse domin ceto rayuwarsu


Dad da Mum kam gaba d'aya sunyi zugum, musamman Dad yau da yaga abunda ya firgita shi, Domin kwalban giyan daya gani a dakin najeeb din, wanda bai shaba da kuma wanda ya fasa yaji mai wannan raunin, yau kawai for the first time yaji ya aikata babban kuskure na tura d'ansa waje karatu, ba tare da mai kula dashi ba, yau ne rana ta farko da Dad yaji ibtisam bata dace da d'ansa ba, yau ne rana ta farko yayi dana sani...... Wani irin fargaba yakeyi tare da tsoran yanzu idan dan nasa ya mutu Mai zaice ma Allah wanda ya tabbata giya yasha har yayi yawa yasa ya fad'a cikin wannan halin, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun. Lallai ya cuci kansa tare da d'ansa gaba d'aya bai bashi ilimin addini ba, baima taba Ankara da kula da irin yanda yake gudanar da abunda addini yace ba, shidai d'ansa kawai yayi karatun boko, domin shine yake ganin hanyar data dace bana addini ba......


Mum ce ta katse ma Dad tunani cikin kuka tare da fad'in yanzu ka gani koh?? Ka tabbatar ma kanka koh??? Ka gani da idonka abunda d'anka yake aikatawa, wanda son d'anka da kuma rashin yarda da abun da wani ya fad'a maka saina wanda d'anka ya fad'a gashi yanzu ka gani da idonka, yanzu idan ya mutu Mai zaice ma Allah?? Kwata kwata babu ruwanka da irin rayuwar da d'anka yakeyi Kai komai ya fad'a a wajanka shine dai dai, wlh ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login