Showing 93001 words to 96000 words out of 182942 words
Chapter 32 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
zan fito zan tawo da ita
Dr yace OK, tare da fad'in ka kawota da wuri domin daka duka alama tana jin jiki Sosai
Najeeb ba komai bane yasa ya'ki yarda tabi Dr d'inba sai dan baiso ya taba ibtisam amma yasan duk da ana nemanshi emergycy a office inya kaita hospital din daukanta za'ayi a Keken marasa lafiya tunda kaman bata san inda kanta yake ba, Najeeb kaya yasa cikin sauri yana gama shiri ya d'auketa Kai tsaye yayi mota da ita, Najwa dake falo Abun ya d'aure Mata Kai, gashi taga najeeb cikin shiri wanda hakan ya tabbatar Mata da airport zashi, ranta taji ya baci
Shiko NAJEEB saka ibtisam yayi a mota ya tada sukai hospital din, daukanta akayi akai ciki da ita cikin abun tura mutane.
Najeeb yaso ya shiga amma Anata kiranshi a office Wanda yasa dole ya wuce da niyan zaije ya dawo
Ita kam ciki akai da ita inda aka fara dubata, tare da Mata taimakon gaggawa
Najeeb kam tuk'i yake yana tunanin maiya sameta? Shi babban abunda yafi damunshi ya akayi taji ciwo a goshinta? Kodai ita taji ma kanta da gangan? Kai no taya mutum zaiji ma kansa ciwo, kai no way akwai wani dalilin dai, but Zan bincika inji
Koda ya k'arasa airport Kai tsaye ya shiga inda yaje ya tadda abunda ya jagula Mai lissafi domin wai wanda zai tashi jirgi zuwa k'asar Spain yana hanyar zuwa airport yayi accident shine aka kira NAJEEB, haka dole ya zauna badan yaso ba, sai dai Dan babu yanda zaiyi, dan tsaki yayi tare da kiran Najwa
D'auka tayi tace hello
Najeeb yace Najwa zani Spain right now am in airport....
Katseshi tayi da fad'in inzo ne mu tafi tare?
Najeeb yace no, tare da fad'in ina son kije hospital din da ibtisam take kiga ya jikinta yake sannan ki dinga zuwa Kafin in dawo kar a barta ita d'aya
Najwa tace why? Mai yasa zani
Najeeb yace saboda na saki
Najwa tace plz Najeeb nifa I hate that girl....
Baiko tsaya ya gama sauraranta ba Ya kashe wayarshi tare dajan tsaki, kiran Dr din yayi amma baiyi picking ba, ya kirashi wajan sau uku ba'a d'auka ba, dole ya tashi ya shiga cikin jirgi badan yaso ba
Lokacin Tashin jirgin nayi ya d'aga suka bar k'asar
Ibtisam kam gaba d'aya bata san inda kanta ke mata ciwo ba, an saka mata drive, lokacin da ruwan ya k'are a lokacin ta farka tare da bud'e ido da yake mata dishi dishi, ganinta a asibiti yasa ta k'ara wage idonta tare da tunanin maiya sameta? Lokaci d'aya ta Fara tunawa sai kuma ta saki kuka Sosai
Dr ne ya shigo cikin d'akin inda ya kura mata ido tare da fad'in ta daina kukan ta fad'a mishi inda yake mata ciwo, cikin harshen turanci yake maganan
Dakyar ta samu tayi shuru tare dayi ma Dr bayanin yanda jikinta yake mata zafi, da kuma rad'adi, ciki harda kafafunta dake mata zafi.....
Bayan ta gama fad'a mishi Dr din yace anyi sex dake ba tare da kina so bako? Right
Ibtisam shuru tayi tana jin nauyin bashi amsa
Yace what I mean anyi raping d'inki ne??
Ganin bazata iya bashi amsa ba, yasa ta kwanta wanda ya danna wani abu saiga wata Dr ta shigo ita da nurse Wanda duka turawa ne
Kallon Dr din yayi tare da fad'a mata yana son ta duba ibtisam domin yana tunanin anyi raping d'inta ne
Dr din duba ibtisam tayi, taga anji mata ciwo, kallonta tayi tare da fad'in how many guy sukai raping d'inki? Sannan kin zubar da blood lokacin da sukai miki hakan?
Ibtisam cikin kuka tace ba raping d'ina akayi ba, Dr din ta kura mata ido, tare da fad'in that mean anyi sex dake da karfi??
Ibtisam shuru tayi ganin haka yasa dr din tunanin tunda tayi shuru hakane, nan dai aka fara bata magani, ta farasha
Kwananta Biyu babu wanda ya le'ko dama batai tunanin NAJEEB zaizo ba, tama gode Allah daya kawota hospital din tunda gashi yanzu ciwon kafar da takeji ya daina, da kuma ciwon kai wanda duk stress ne yasa take jin hakan
Kwanan ibtisam hud'u a hospital din, sune suke bata abinci, domin suna bama patient d'insu abinci a hspt din, duk cikin kudinku ne kuke ci
Gaba d'aya babu abunda ke damunta yanzu ta warke tayi garau abunta, har yau da Dr yazo ta buk'aci ta koma Gida, domin a gobe zata koma Nigeria, Dr ya dubata babu wani matsala inda aka bata magani Wanda zata dinga sha, ta ro'ki Dr akan yasa a kaita gida domin bata san hanya ba, gashi bata da kud'i, hakan ko akayi Dr yace tazo a kaita tare da fad'in mai takeyi gidan pilot NAJEEB?
Ibtisam tace ita sister d'inshi ce, domin bata son dogon tambaya balle harta dan ganta NAJEEB da sunan mijinta, tir Allah ya kyauta ta fad'a cikin ranta
Dr yace muje koh, koda suka fito suna tafiya dr na baya ita Tana gaba, kabir dake zaune domin yanzu yakan zauna sai dai bai cika magana ba, kawai yaga ibtisam da sauri ya tashi tsaye yana goge idonshi, fita yayi da sauri amma koda ya fita Bai ganta ba, abun mamaki ya bashi kodai imagination ne? Kai dole inbar k'asar nan yau ko gobe bazan iya zama a nan ba, gwara in koma Nigeria domin in banga ibtisam ba akwai matsala Sosai
Zama yayi a wani kujera dake wajan tare da d'aura Hannu akai
Ibtisam kam Dr yaba driver ya kaita gida, koda suka k'arasa ibtisam ta ro'ki driver din akan yayi hakuri ya jirata ta dibo kayanta ya kaita airport
Driver din yace OK
Shiga cikin gidan tayi Kai tsaye bata ga kowa ba, hakan yayi mata dad'i tafiya take a lambo kaman barauniya, harta isa d'akinta inda ta zuba kayanta cikin akwati tare da saka jallabiya ta canza kaya ta yafa gyalen jallabiyan ta d'auki su passport d'inta tayi waje, kai tsaye motar ta shiga driver din ya kaita airport tare da sauketa
Shiga tayi inda taga wasu kujeru masu kyau ga sanyi wajan, dan gobe ne tafiyanta kuma jirgin 10 zata hau, ibtisam dai a nan ta kwana, sannan harta sallah a nan tayi, duk da turai ne babu ruwan wani da wani amma sunyi mamaki da suka ga tana sallah a nan, wasu harda daukanta video
Koda Dr ya dawo ciki yaga KABIR zaune shi d'aya, dr mamaki abun ya bashi, ta wani gefen kuma dad'i yaji daya ganshi haka, kenan shida kanshi ya tashi harya fito yazo nan ya zauna
Dr yace wow badai kaika fito da kanka ba??
KABIR ya d'ago tare da sakin murmushi yace nina fito da kaina, na gaji da zama a nan ina bukatar in koma Gida
Dr murmushi yayi tare da fad'in tashi kayi tafiya mu gani
Tashi kabir yayi yana dingishi domin inmai karatu bai manta ba, sanda yayi accident k'arfe ya bula Mai k'afa Wanda shine yasa yake d'ingishi
Dr yace kafarka har yanzu tana bukatar samun kulawa
KABIR yace eh, but ni kawai Ina son a sallameni, zanci gaba da kula dashi inna koma Nigeria
Dr yace ya Bari ya k'ara kwanaki Kafin a sallameshi
Amma KABIR ya dage akan shifa dole gida zai koma, so yake a sallameshi
Dr yace OK za'a sallameshi amma yayi hakuri nan da kwana biyu
Haka kabir ya amince badan yaso ba
Koda su hafsat suka zo asibitin da mamanshi da kaninshi, sunyi mamaki da suka ganshi ya fito hakan kuma yayi musu dad'i Sosai
Hafsat kallon kabir tayi cikin so da kauna, tace sannu ya jikin naka?
KABIR bai kalleta ba, ya amsa da lafiya kalau, Alhmdlh, jiki da sauk'i
Mamanshi zama tayi kusa dashi tana fad'in kaika fito ko fito dakai akayi?
KABIR murmushi yayi tare da fad'in dakai na, nah fito, domin naji sau'ki yanzu so nake ma in koma Gida, na gaji da zama a nan, ina son in koma inje inga mahaifin ibtis......
Sai kuma yayi shuru
Hafsat wani irin hawaye ne Mai zafi ya zubo mata, da sauri tasa hannu ta goge domin karsu gani
Maman Kabir tace KABIR bazaka koma ba har sai ka warke, domin bazan bari kayi wasa da rayuwarka ba, kasan lafiya shine komai, dan haka dole ka nemeta
KABIR shuru yayi ba tare da yace komai ba, lokaci d'aya kuma ya tashi yana dingisawa tare da shiga cikin d'akin da yake danya kwanta, koda ya shiga ya kwanta akan gadonshi na marasa lafiya, ba komai yake ba sai tunanin ibtisam, wani irin hawaye Mai zafi ya zubo mishi. Lallai Kabir yana son ibtisam Sosai, Abu mai wuya ne kaga namiji yana zubda hawaye, amma gashi akan son ibtisam yanayi, lallai so dafi ne, sannan shi so baya tsufa, duk girman mutum ko kankantarsa yana kamashi, shi so babu ruwanshi
Hafsat kam zama tayi a nan inda kabir ya tashi, mahaifiyar kabir ta lura da hafsat, irin halin data shiga.
Nan ta zauna ta Fara fad'in hafsat ina son kiyi hakuri dan Allah, shi rayuwa komai Mai wuce wane, Idan kikai hakuri komai zai wuce insha Allah
Hafsat dai bata ce komai ba, domin ita da kanta tasan son maso wani takeyi, domin so d'aya dai KABIR yaba yarinyar da yake so
Washe gari wani irin sanyi ibtisam keji ga yunwa, amma haka tayi hakuri tare da kudundune jikinta, tana nan zaune har lokaci ya kusa ta tashi ta shiga Bayan an duba passport d'inta tare da jakarta, sannan ta wuce ciKi inda passenger ke zaune suna jira a Fara shiga cikin jirgi
Bata wani dad'e ba, aka fara shiga cikin jirgin, ibtisam kam ganinta cikin jirgin yasa ta lumshe ido cikin jin dad'i, domin gani take kaman taga Kabir, lokaci d'aya ta Fara hawaye Domin tunawa da abunda Najeeb yayi mata, yanzu wani irin kallo kabir zai Mata? Anya KABIR zai yafe mata kuwa? Bazai ce taci amanarshi ba kuwa? Jin maganan ana fad'in su saka belt, tare da musu bayani akan koda jirgi yayi hatsari ga tai makon da za suyi ma kansu wajan saka saukan lema, ibtisam share kwallan dake idonta tayi, lokaci d'aya jirgi ya d'aga
Ibtisam jin jirgi ya d'aga ta sauke ajiyan zuciya, cikin jin dad'i cikin ranta tace nida k'asar nan har abada, domin na barta kenan, sai dai Inba nida KABIR nazo ba
Najeeb Washe gari zasu dawo America, gaba d'aya inda yake bai samu ya rintsa ba, gashi yana son yin waya da Dr yaji ya jikin ibtisam amma bashi da Layin k'asar Spain din, amma Abu d'aya ya Sani Yadai San Tana hospital kuma ya tabbata komai zaizo da sauk'i, wannan tunanin da yayi yasa ya d'an rage tunani, sai Abu d'aya daya tsaya mishi a rai, shine irin kayan dake jikinta sanda ya kaita hspt, wanda ya tabbata sai sun cire mata hijab, lokaci d'aya ya lumshe ido tare da Fatan gobe yayi yabar k'asar ya huta....
Washe gari Bayan NAJEEB ya sauka a k'asar America, tun a airport ya kira Dr, Dr Ya d'auka tare da fad'in pilot
Najeeb yace ina patient din daya kawo?
Dr yace aita dawo gida, nasa driver Ya Mai data....
Jin haka najeeb Ya kashe wayar tare da nufa gidan Kai tsaye, koda ya shiga gidan yaga duk yayi kura, tun a falo ya kira number din Mai aikin Gidan akan ta dawo taci gaba da aiki, yana fad'a mata ya kashe wayar
Najeeb Kai tsaye ciki ya shiga inda yaga kofar d'akin ibtisam a bud'e, shiga yayi amma yaga bata ciki, abun mamaki ya bashi tare da tambaya ina ta shiga ne haka?
Ganin wardrobe d'inta a bud'e yasa abun ya bashi mamaki, tare da tunanin ina ta shiga? Ganin kaman babu kaya cikin wardrobe din hakan ya nuna mishi tabar gidan ne, dan haka kiran Dr din yayi tare da k'ara tambaya kota dawo hospital dinne?
Dr yace a'a, tare da fad'in ina zuwa let me ask my driver domin shine Ya kaita, ya fad'a maka da kanshi
Dr din fita yayi inda yaga driver d'inshi ya bashi wayar
Najeeb Ya fara mishi tambaya ina ya ajiyeta?
Driver din yace na kaita gidan da aka fad'amin, daka nan kuma tace in tsaya in kaita airport t......
AI NAJEEB baima tsaya sauraranshi ba Ya kashe wayar, tare da fita, kai tsaye airport ya nufa inda Ya fara dube dube ko zai ganta amma babu ita balle Mai kama da ita, kai tsaye binciken Wanda suka tafi Nigeria yasa a mishi cikin satin nan
Aiko ana dubawa yaga hotan ibtisam wacce ta tafi jiya, hannunshi Biyu Ya buga tare da fad'in damn..
Ya dad'e a tsaye Kafin daka bisani ya kad'a kafad'a tare da fad'in let her go, I don't care
Fita yayi daka airport d'in inda ya koma Gida, yaga Mai aikinshi tazo Tana ta goge goge, gaidashi tayi ya amsa tare dayin ciki, danya samu yayi wanka
*NIGRRIA*
Koda ibtisam ta sauka a airport kunna wayarta tayi, har zata kira Abba ta fasa, kawai ta fita inda tahau mota ta shiga ta fad'a musu inda zasu kaita, kai tsaye gida aka kaita, ta shiga da sallama
Granny dake zaune ita d'aya a tsakar gida tace muryan wa nakeji kaman na ibtisam?
Sakar baki granny tayi tare da Mata kallon mamaki Tana fad'in Mai zan gani haka? Maiya samu goshinki aka saka miki plaster ?
Ibtisam tace Granny ki bani kud'i Inba Mai adai daita sahu
Granny ciki ta shiga cikin damuwa ganin ciwo a goshin ibtisam, taje d'auko mata kud'i, Bayan ta d'auko mata kud'in ta bata
Ibtisam fita tayi ta biya motar kud'inshi Sannan ta dawo ciki da kayanta
Granny tace wai Mai ya samu goshinki ne ibtisam???
Ibtisam tace maiko ya sameni, Inba jikanki dake neman illatani ba
Granny salati ta saki tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, garin yaya Toh??
Ibtisam ta saki kuka tare da fad'in Wlh Granny kasheni yake son yi, kin San Mai yamin kuwa? F.....
Da sauri tayi shuru domin kunyar abunda take son fad'a tayi, lallai bazata iya fad'an abunda ya shiga tsakaninta dashi ba, domin wlh abun kunya ne....
Granny duk da bata fad'a mata ba, ta fahimci abunda ibtisam keson fad'i, wato NAJEEB ya nemeta ta k'arfin tsiya, tayi mishi musu shine yasa mata karfi har taji ciwo
Granny wani irin dad'i taji da taji wannan Labarin lallai, jikarta ta zama babban mace yanzu, ji take kaman ta tashi ta taka rawa, cikin ranta tace Allah yasa an samu rabo
Ibtisam jin Granny tayi shuru yasata fad'in ina ummi???
Granny tace taje kasuwa, amma Nasan ta kusa dawowa
Granny tace ina najeeb din??
Ibtisam kaman tace ban sani ba, amma inta fad'i hakan za'ayi zargin wani abu, domin in aka zargi wani abu za'a sata ta fad'i abunda ya faru har a gano yayi mata wani abu
Ibtisam tace yana can America
Granny tace y'an Ameka, ai Kema kinsha Ameka din Sosai
Tashi ibtisam tayi ta shiga ciki domin ita yunwa takeji Sosai..
Kitchen ta shiga ta had'a tea tasha tare da bread, Bayan tasha sannan tasha maganinta
Kai tsaye toilet ta shiga tayi wanka, koda ta fito ummi ta dawo, ibtisam fitowa tayi tare da gaida Ummi, ummi kallonta tayi sai taga tayi fayau
Inda badan Granny ta fad'a mata Karta tambayi ibtisam ba, danta fad'a mata dalilin ciwon Nata, amma sai taga kaman ibtisam din ta rame ta k'ara haske, lokaci d'aya kuma saita kawar da tunanin tunawa da tayi tana cikin tashin hankalin rashin kabir dole ta rame
Ummi tace ansha hanya, ina NAJEEB din?
Ibtisam tace yana can
Ibtisam ganin Ummi bata tambayeta dalilin jin ciwonta ba yasa taji dad'i tare da sakewa Anata fira
Koda Abba ya dawo shima bai tambaya ba, domin ummi ta mishi bayani shima
Wajan karfe tara ibtisam na daki saiga kiran Zarah Ya shigo cikin wayarta
D'auka tayi da sauri tare da fad'in baki da kirki Wlh Zarah
Zarah dariya tayi tare da fad'in Ashe dagaske kin dawo?
Ibtisam tace eh na dawo, kin San mun koma skul fah
Zarah tace eh nima gobe zan wuce
Ibtisam tace OK ya zamuyi? Ko mu had'e a skul din kawai
Zarah tace eh hakan zaifi
Nan suka fara fira inda Zarah take tambayarta ya amarci
Ibtisam tsaki taja tare da kashe wayar tana fad'in a'a angonci ne ba amarci ba
Zarah ganin ta kashe wayan tasan halin ibtisam sarai Dan haka ta gane tayi fushi ne, dariya tayi Sosai
Washe gari da wuri ibtisam ta shirya, bayan sunfi breakfast take shaida ma Abba akan yau zata koma makaranta
Abba yace daka dawowa?
Tace ai mun koma ne Abba kuma ban son a wuce ni.
Abba yace OK saiki zo muje in ajiyeki a garage ki tafi
Tace toh tare da tashi danta d'auko kayanta
Granny tsaki taja tare da fad'in ni wannan karatun Wlh na rasa amfanin shi ko kad'an Wlh
Abba yace Toh ya za'ayi mama tunda mijinta ya amince ai Kinga sai dai muyi musu fatan alkairi
Granny tsuke baki tayi
Koda ibtisam ta fito ummi ta kira sunanta tare da fad'in zo nan
Zama ibtisam tayi a kusa da ummi
Ummi tace inaso ki sani, yanzu da, dah ba d'aya bane, a da baki da aure a yanzu kuma kina da aure, ibtisam Nasan keba jahila bace, domin mun baki ilimi dai dai gwargwado, Nasan kin San abunda nake son in fad'a miki, bana bukatar ince miki wani abu sai dai in miki tuni, da kiji tsoran Allah aduk inda kike, sannan ki kare mutuncin aurenki.
Ibtisam tace insha Allah ummi
Abba yace Toh kayan abinci fah??
Tace Abba sai nace can, ibtisam akwai kudi a wajanta wanda ta manta dasu, saida taje Tana had'a kaya ta gansu, domin kud'in da ta dawo dashi ne da sukai hutu a skul
Tashi abba yayi yace muje
Granny tace tsaya inada magana
Ibtisam tace Kai granny tun d'azu bakiyi ba sai yanzu
Granny tace saboda yanzu naga daman yi
Ibtisam tace uhm inaji
Granny tace in kika tafi sai yaushe kuma??
Ibtisam tace sai munyi hutu
Granny tace Allah ya kyauta, ki dinga kula da kanki daka Kinji wani