Showing 114001 words to 117000 words out of 182942 words
Chapter 39 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt
ba haka bane, kawai Ina mamakin Abunne, ni nasan cikin NAJEEB ne, domin Nasan koke wacece, sai dai abunda yake bani mamaki da kika ce yana shan giya
Wani hawaye Mai zafi ya fito Mata, tare da fad'in Granny Idan Nayi mishi sharri Riban Mai zanci???
Granny Wlh abunda na fad'a shine gaskiyan magana, amma koma dai miye za'ayi gwaji a gani Idan akayi DNA test za'a gane ko jinin Waye AI
Granny tace taya za'a gane Bayan yaro bai fito duniya ba???
Ibtisam tace za'a gane, kawai jinina ake bukata, sai nashi su za suyi gwajin su gane jinin na Waye
Granny tace ikon Allah kaga Abu iri iri dai a duniya
Ta gefen Mum kuma koda suka k'arasa ta Fara fad'ama Dad abunda yayi bai dace ba, domin abunda yayi ya nuna yana Bayan NAJEEB ne, kuma hakan bai dace ba, domin Wlh ni nafi yarda da maganan ibtisam din
Dad yace koma dai Mai zaki fad'a ni na yarda da NAJEEB, akan wani dalili zata kirashi da mashayin giya?? Wato ke baki ji komai ba akan an kira d'anki da mashayi ba koh???
Mum tace gaskiya kayi babban kuskure da ka yarda da NAJEEB, Bayan ko daka irin halin shi, ya kamata ka yarda cewa zai iya shan abunda yafi giya Indai akace yanayi, karka manta ko irin yanda najeeb yake......
Dakatar da Mum yayi tare da fad'in ya isa haka plz, I trust my son, so ban son wata magana plz koma dai miye gobe zamu tafi gaskiya zata fito and ina tunanin tunda basa son juna is better a raba auren
Mum salati ta saka tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, Mai kake fad'a haka?? Kana nufin akan d'anka har zaka iya yarda kayi fad'a da dan uwanka?? Ko kasan wannan abunda kakeyi zai iya Kawo rashin fahimta kaida k'anin ka? Yanzu kai saboda yaran da kuka haifa saiku yarda su raba muku zumunci K....
Dad ya Katseta da fad'in sai me?? Akan mai yasa bazai rabu da ita ba, Bayan tana binshi da sharri akan wani dalili zai zauna da ita??
Mum shuru tayi, lokaci d'aya tace ina guje maka abunda zaisa kazo nan gaba kana dana sani
Yace babu dana sanin da zanyi domin Nasan NAJEEB komai yayi zai fad'a Dan haka kibar wannan maganan ki barni in kwanta In huta
Mum shuru tayi tana mamakin yanda mijin Nata yadau zafi, ita bata ga abun d'aukan zafi ba, ita a yanda take kallon NAJEEB komai akace zaiyi zata yarda, domin su da kansu suka lalata rayuwar d'ansu da kansu, yaro sun D'aukeshi sun kaishi waje karatu ba tare da mai kwaba mishi ba, ai dole suga ba dai dai ba
Washe gari wajan karfe 9 tayi masu NAJEEB a gidansu ibtisam, koda suka zo ,Ummi ta Kawo musu abinci
Mum ce kadai taci amma shi Dad yaci abinci
Najeeb kam baici komai ba haka kawai yaji baya son cin abincin domin gaba d'aya baya cikin nutsuwa, Ummi kiran ibtisam tayi wacce ta fito cikin jallabiya tare da yafa k'aramin gyalen jallabiya din wanda yayi mata kyau Sosai
Najeeb tunda ta fito ya kura mata ido Lokaci d'aya ya kauda kanshi tare da jan gajeran tsaki
Ibtisam kam wani irin dad'i taji, domin tana shigowa kamshin turaren shi taji wanda ya sata nishad'i
Gaida su Mum tayi cikin girmamawa
Dad ya amsa babu yabo babu fallasa
Mum tace ibtisam sannu ya jikin naki??
Ibtisam tace Alhmdlh
Najeeb yace Dad mu kama hanya 10 jirgin zai tashi
Gaba d'aya tashi sukayi, suka fita cikin masu tafiyan harda Granny yau zata Ameka
Koda suka k'arasa airport suka shiga jirgi granny dai ba wannan bane farkon shigarta jirgi ba, kar kuji batai kauyanci ba Hhhhh
Bayan kowa Ya gama shiga jirgi ya d'aga zuwa America koda suka sauka Kai tsaye mota suka shiga inda NAJEEB yace shifa bai yarda aje Gida ba sai an fara zuwa anyi DNA test din hakan ko akayi
Suna tafiya a mota domin zuwa asibti Granny tace oh ikon Allah kalli yanda suke yawo kaman tsirara Kai dole mutun ya lalace idan yazo wannan k'asar Wlh, jiba wannan Abun kunyar har Ina fisabilillahi
Mum dariya tayi tare da fad'in Granny aisu ba musulmai bane, sannan Idan bakai wannan shigar ba su gani suke baka Waye ba
Granny dake zaune sanye da riga da hijab tace kenan ni sai su koreni daka k'asar kenan
Mum tace a'a sai dai ka zaman musu abun Kallo
Granny tace Allah shiryesu
Mum ta amsa da Ameen
Ita kam ibtisam bama jinsu take ba, ita burinta aje Ayi gwanin ta samu ta zubar da cikin kowa ya huta hankali kwance
Koda suka k'arasa asibitin ba tare da bata lokaci ba akama Dr bayani akan abunda suke bukata, nan aka d'iba jinin ibtisam aka d'iba na NAJEEB tare da fad'in sai nan da kwana biyu result zai fito
Nan sukayi gida Kai tsaye, suna isa Dad yayi kitchen domin Ruwa yake bukatar sha
Mum kam ciki suka shiga inda ibtisam tace d'aki d'aya zasu zauna da Granny hakan ko akayi
Gaba d'aya ibtisam bata fita koda falo ne, abinci sai dai Granny ta Kawo mata daki,balle yanzu da komai taci sai tayi amai bata ma cika ciba sai taji kanta na Mata mugun ciwo shine zata ci Dan dole shima tana gama ci sai amai gaba d'aya ta kosa result ya fito a cire mata cikin ta huta da wannan wahalan
Najeeb kam gaba d'aya baya zama a gidan tunda suka zo, domin aiki yayi mishi yawa sosai
Ibtisam tana d'aki zaune bata son jin komai sai kamshin turaren najeeb, ganin ba samu zatayi ba, yasa tasa kuka Sosai kaman ranta zai fita Dan takaici gashi gobe ne result zai fito, gashi gaba d'aya taga lokaci baya gudu
ibtisam na nan zaune taji kamshin turaren NAJEEB, da sauri ta d'aga Kai suka had'a ido, wani irin murmushi da bata san ya fito ba ta saki tare da sauke wani irin ajiyan zuciya
Najeeb wani irin kallo ya mata tare da fad'in gobe result zai fito you better tell them the truth tun kafin lokaci ya k'ure kiji kunya
Ibtisam tashi tayi tare da kallonshi tace najeeb nasan bazanji kunya ba, domin Nasan ban aikata abunda kake tunani ba am sure kaine zakai dana Sani
Wani irin shu'umin murmushi ya saki tare da fad'in we shall see tomorrow
Wani irin kallo ya watsa mata tare dayin gaba Zai fita har yayi nisa ya kusa fita, da sauri ta kira sunanshi da fad'in najeeb plz wait
Tsayawa yayi cak ba tare daya waigo ba
Nufanshi tayi tare da zuwa gabanshi tana fad'in dan Allah kaban..... Sai kuma tayi shuru alaman tana jin nauyin fad'an abunda take son cewa
Gira ya d'aga mata tare da fad'in zaki fad'amin Waye kwarton naki ne???
Ibtisam baki ta cije alaman taji zafin abunda ya fad'a amma saita basar tare da fad'in turaren ka nake son ka bani plz wanda kake sawa....
Ido ya kura mata yana kallonta lokaci d'aya kuma ya saki murmushi tare da d'aure fuska yace shi d'an iskan da yayi miki cikin nashi baiyi miki bane???
Ibtisam tace plz ka bani ban son dogon magana plz
Najeeb wani kallo ya k'ara watsa mata tare da fad'in kije uban cikin naki ya baki shi saurayin naki
Cikin bacin rai tace OK zanje ya bani amma ina son ka sakeni sai in koma waj......
D'aga hannunshi yayi zai mareta alaman bacin rai ga idonshi da yayi ja, lokaci d'aya ya sauke hannun tare da cije baki ya fita fuuuu.
Bai dad'e da fita ba, sai gashi ya Kawo mata turare wajan Kala 8, tare da watsa mata akan gadon d'akin
Har zai fita ibtisam tace babu shi a ciki wanda kake sawa shi nake so, dan Allah ka bani ka tausaya min ka bani sai kuma ta saki kuka......
Plz kuyi manage zazzabin mura ya kamani dakyar nayi wannan
Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*
*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*
3138831065 Firstbank Maryam Alhassan
*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*
*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*
NAJEEB waigowa yayi tare da kallonta, yanda take kuka, "duk Da yana jin haushinta Sosai yanda take kukan sai yaji ta dan bashi tausayi kad'an
Tashi tayi tazo inda yake tare da fad'in Wanda kasa a jikinka shi nake so, wanda nake jin kamshin shi yanzu tana maganan ne cikin kuka
Ido najeeb ya k'ara kura mata yana mamaki, lokaci d'aya kuma yayi murmushi tare da fad'in heey enough stop making and excuse da zaki dinga zuwa kusa da inda nake, kina wani kina son perfumes d'ina, gashi na baki sai me kuma? Mai kike so kuma??? Tell me what do you want?? Inma kina wannan Abunne danna tabaki you are mad,..... Yeah sai yanzu na fahimta kina manne min Dan inyi sex dake right wani irin dariya ya saki tare da fad'in that is your problem Nigerians girl, kuna da naci, nacin ku yayi yawa, ga jaraba daya muku yawa, small rat like you shine kike son Wai Kimin taku da dabara tare da k'arya Wai kina son turare ne, na baki turaren kinzo kince babu shi a ciki, saboda ba turaren kike bukata ba, ni kike bukata me, just come out and say it ni kike bukata, cije lips d'inshi yayi tare da d'an murmushin ba'kin ciki wanda zuciyarshi bata komai sai tafarfasa da zugi tare dajin takaicin abunda ta aikata, tazo mishi gida da cikin wani....
ibtisam ce ta Katse mishi tunani da fad'in najeeb ban taba tunanin inyi wani abu dakai ba a rayuwa ta, amma sai gashi ka cuceni kayi min abunda har in mutu bazan manta ba, kayi min irin abunda ko.... Sai kuma tasa kuka tare da fad'in ka cuceni.....
NAJEEB yace or nine na cuceki?? You are mad infact you are stupid, let me tell you something, ko sanda Nayi sex dake Nayi regretting duk da shima kena taimaka domin naga kina bukata, and I try to help you cos naga kin Fara fita out of control..... Shuru yayi sannan yace "But.... Shima shurun ya kar'ayi yana kallonta sannan yace 'you cheat me kin Sa Nayi sex dake da dattin wani k'ato a cikin ki, you cheat me and I will never forgive you, I will make sure to make your life miserable, I will make you regret what you did to me... Ibtisam I hate you I so much hate you I never hate person in my life like the way I hate you, kinyi min babban laifi a rayuwa and kin fake da abunda nake aikatawa kina son Yimin sharri, kince nasha alcohol Nayi sex dake..... Shuru yayi tare da lumshe ido Lokaci d'aya kuma ya bud'e idon tare da fad'in why me? Why? Mai yasa kika zaba ki cutar dani? Mai yasa tun Farko baki fad'ama parent d'inki kinyi sex da wani ba, sai yasa kika shiga shock sanda akace saurayinki yana da HIV..... Shuru yayi tare da dafe Kai yace oh my god I have to do HIV test.... Kallon ibtisam yayi tare da fad'in duk da ance bai dashi I will go for HIV test domin ban yarda dashi ba, and Ina jira gobe yayi kowa yaga result at that time zanyi punishing d'inki zanyi miki abunda baki taba expecting ba, just wait and watch, Allah ya kaimu gobe..... Fita yayi Fuuuuu tare da barin gidan wanda su Mum suma basa nan sun fita harda Granny
Ibtisam k'asa tayi tana kuka tare da Alla wadai da wannan auren da aka mata, lallai NAJEEB ba miji bane, lallai an cuceta Wlh, an d'aura mata mashayi Wanda bai San darajan Dan Adam ba, Wanda baya mutunta kowa, gashi yanzu yayi mata ciki yana fad'in ba nashi bane, wlh Idan har result ya fito dole in zubar da wannan cikin, ibtisam wani irin tsanar abunda ke cikin Nata takeji Domin tunawa da cewa jinin najeeb ne a cikinta, lallai zata iya aikata komai a yanda take jin kanta yanzu domin taga wannan cikin ya zube, dan bazata iya yarda ta had'a zuri'a da NAJEEB ba, kuka take sosai tare da tsanan kanta da tun Farko da akai Mata auren Mai yasa bata gudu ba
NAJEEB kam Kai tsaye hospital ya nufa inda ya bu'kaci a mishi HIV test a dubashi ya gani wanda dama yanayi every 6month amma wannan karan lokacin daya kamata yayi bai kaiba, yazo a dubashi dan kawai yayi sex da ibtisam Wanda yake tunanin tana da HIV kabir ya saka mata, shi gaba d'aya bai yarda da kabir d'inba duk da ance mishi baida shi sharri aka mishi, domin najeeb a duniya in aka cire ibtisam babu wanda baya kaunar ya gani kaman KABIR din, wanda tun farkon ganinshi da ibtisam din yaji guy din gaba d'aya baiyi mishi ba, yaji ya tsani kabir, musamman da yake ganin yana zuwa wajan ibtisam Wanda yake ganin kaman ya bada maza, domin yana zuwa wajan karamar yarinya wacce bata kaiba.... Lokaci d'aya najeeb yayi tsaki tare da fad'in ai dole ya nace mata kullum sai yazo munafuki Ashe yasan abunda ya kunsa mata, Bari gobe yayi in tabbatar Wlh sai nasa an d'aureshi
NAJEEB na nan zaune har aka bashi result d'inshi yaga negative alaman bai dashi, ido ya lumshe tare da barin hospital din, koda ya fita gidan ya koma direct inda ya tadda har yanzu su mum basu dawo ba, tsaki yaja tare da nufa d'akinshi ya shige tare da rufe kofar d'akin
Kallo d'aya zaka masa ka gane yana cikin tashin hankali tare da kunan rai, domin gaba d'aya inda mutum zai ganshi daka jiya zuwa yau, zai gane yana cikin tashin hankali har wata y'ar rama yayi na kwana d'aya, gaba d'aya tunanin abunda ibtisam tayi shike mishi yawo a Kai, ji yake kaman ya hadiyi zuciya ya mutu dan ba'kin ciki, wai matar da aka d'aura mai itace tazo da ciki Kai Wlh an cuceni, ganin kanshi yana mishi ciwo saboda tunani yasa ya tashi ya d'auko kwalban alcohol d'inshi wanda ya boye a wardrobe d'inshi saboda Kar iyayenshi su gani, ya fara sha, najeeb gaba d'aya Wanda ya rage baida yawa domin ranshi a matukar bace yake, idonshi yayi ja gashi yanda yake shan alcohol din duk ya zubar mishi a jiki, tashi yayi yana ganin jiri tafiya ya farayi wanda baya cikin hayyacinshi balle yaga inda yake son dosa, bugewa yayi da wardrobe d'in d'akin Wanda hakan yasa ya fad'i ya fara bacci a nan
Ibtisam kam gaba daya kanta taji yana mata ciwo tare da jiri, wanda tasan ba komai bane yake damunta sai yunwa, ga kuma tunani Wanda ta tabba inda za'a gwada jininta za'a fad'a mata cewa yahau Sosai, lallai yau lokaci baya mata sauri ita yanzu burinta gobe yayi kowa ya gane itace keda gaskiya tasa a zubar da cikin ta koma skul ita wannan shine burinta kawai
Granny ce ta shigo d'akin ta ganta tana rusgan kuka, granny tace ibtisam, "lafiya kike wannan kukan kaman wanda akace wani naki ya rasu??..
Ibtisam rungume Granny tayi tana kuka tare da fad'in Granny Wlh wannan cikin ya isheni, ya takura min gaba d'aya yasa na kasa samun sakat, ga ciwon kai ga son kamshin turaren da bazan samu ba, Wlh Granny Ina cikin wani hali na gaji na gaji...... Kuka ta kuma fashewa dashi wi wi wi wi
Granny shafa mata baya ta farayi alaman tana rarrashinta tayi hakuri, granny Tana jin tausayin ibtisam jin kukan nata take har cikin ranta, domin tana son ibtisam Sosai
Granny tace ibtisam kiyi shuru Kinji fad'amin sunan turaren da kike so, zan saka a si..... Shuru Granny tayi tare da fad'in a'ah ga turare can na gani da yawa, babu wanda kike so a ciki??
Ibtisam tace Granny babu irin wanda nake so, ni wanda nake so baya ciki
Granny tace toh ya sunan wanda kike so??
Tace Granny ni wanda n..... Sai kuma tayi shuru tana kuka
Granny tace zoki zauna Kinji
Zama sukayi sannan granny tace fad'amin inji
Ibtisam tace ki barshi kawai Granny
Granny tace Allah ya kyauta, yanzu dai gashi, Leda taba ibtisam tare da fad'in gashi nan na siyo miki
Amsa ibtisam tayi tare da bud'e ledan Tana kallon abunda ke ciki, kayan fruit ne a ciki, ibtisam tace Granny mai yakon ki kai kitchen.
Tashi ibtisam tayi tare da fad'in Bari inkai kitchen
Granny itama Tashin tayi tace muje, Kai tsaye falon suka nufa inda suka ga Dad a falon, ibtisam gaida dad tayi
Amsawa yayi cikin sakin fuska tare da fad'in ya jikin naki??
Tace da sauk'i Alhmdlh
Kai tsaye kitchen ta nufa inda taga mum na aiki, ibtisam tayi ma mum sannu da aiki
Mum ta amsa tare da fad'in Granny ta baki kayan fruit koh?..
Ibtisam tayi murmushi tare da fad'in eh ta bani gashi nan, ajiye kayan fruit din tayi tare da d'aukan carrot ta Fara kankare ma mum
Mum tace a'ah Kinga barshi kije ki huta
Ibtisam tace a'ah Mum zan iya
Ganin yanda ta dage yasa Mum barinta domin ta tayata din duk da ba wani aiki bane, Sosai
Mum sunayi Tana d'an jan ibtisam da fira, domin ta lura ibtisam din kaman tunani yayi mata yawa, tana son ta cire komai a ranta domin ta sake dan haka Mum tai ta janta da fira, Sosai
Ibtisam tun bata sakewa harta dan saki jikinta da Mum, suna cikin aiki taji Tashin