Showing 150001 words to 153000 words out of 182942 words

Chapter 51 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

bata irin rayuwar Banza kallonta ake bata Waye ba, wacce take iskanci ita ake ma kallon wacce ta Waye, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun,


Wlh ya kamata muji tsoran Allah, mu tashi daga turban shaidan, babu Waye wa irin mace ta suturta jikinta sannan ta kame kanta, wannan itace Waye wa, bawai fitar da tsiraici ba, da rayuwar Banza ba, da yawa mutane sun amsa kiran shaidan wanda yayi nasara a kansu, sai yasa a kullum ake son bawa Ya nemi tsari daga tsaida na'a nanne


Kubra tace lallai yau na gane rayuwa na kuma k'ara yarda, duk abokin da bazai fad'a maka abunda Allah yace ba, tabbas ba Aboki bane, duk abokin da zai dinga kaika hanyar halaka ka guji wannan abokin, ibtisam wlh Nayi nadaman sanin mutane da yawa a rayuwa ta, wanda sune suka k'ara Sani cikin wannan banzar hanyar, wlh babu rayuwa Mai dad'i kaman bin abunda Allah yace, sannan Kak'i abunda yayi hani dashi .... Sannan yau kawai na gane babu mutunci ga mace face gidan aurenta, domin da yawa abunda yake cutan mu sai muce sai mun gama karatu za muyi aure, muna mantawa aure baya hana komai, yanzu na tabbata inda inada aure da yawa bazanyi wani abu ba, koda kuwa Ina son inyi, saboda koda banji tsoran Allah ba zan dinga jin tsoran kar wannan mijin nawa ya ganni ko a Kai mishi labari, amma da yake banda aure yin Abu nake iya son rai na, ban damu da kowa ba, tunda iyayena ba a nan suke ba.....


Ibtisam tace hakane, amma rashin aure bashi bane kesa mata yin iskanci a jami'a ba, abun tsoran Allah ne kawai, ki duba zarah ai gata bata da aure, zan iya cewa bata kula samari ma, Kinga ta kame kanta, akwai ma ire irenta Wanda suka kame kansu basa irin wannan rayuwar, saboda sun ri'ke addini kuma suna tsoran Allah, dan Sun San komai suka aikata in wani Bai gansu ba, toh Allah ya gansu, kuma shine mai sakayya, mai hukunta bawa dai dai da abunda ya aikata


Kubra tace hakane, mudai munbi rudin duniya, amma yanzu Alhmdlh Allah ya ganar dani, kuma indai har inada rai ban mutu ba, zan zama cikakkiyar musulma Mai bauta ma Allah, tare da kame kaina sannan inna samu miji inyi aure duk da nasan kona samu mijin in yaji ba budurwa bace ni, zansha wulakanci amma zanyi hakuri in jure, dama duk Wanda ya zabi hanyar sabon Allah zaiga ba dai dai ba a rayuwa


Ibtisam tace ku tashi mu shiga ciki


Tashi sukayi suka shiga ciki, inda ibtisam tace kubra ta kunna wayarta


Kubra tace wlh Ina jin tsoro Karya kira


Ibtisam tace karki damu ki kunna


Kunna wayar tayi Aiko tana kunnawa saiga kiran mutumin nan ya shigo tace kin gani koh??


Amsan wayar ibtisam tayi tare da dannawa tasa a speaker


Mutumin yace hello kubra


Ibtisam tayi mata alama da tayi magana


Kubra dakyar tace inaji.....


Yace har yanzu baki mutu ba.....


Ibtisam ta fusge wayar tare da fad'in bata mutu ba, kaine zaka mutu insha Allah.....


Kit wayar ta mutu alaman ya kashe wayar


Kubra kam babu abunda take sai kuka tare da fad'in Kun gani koh, kunji abunda yace koh?? Na shiga uku


Ibtisam tace miye haka kubra?? Bayan d'azu kika ce koda kin.....


Tun Kafin ibtisam ta k'arasa kubra tace hakane, nan ta Fara addu'a cikin ranta, da sauri ta bud'e data tare da shiga play store tayi downloading app na complete qur'an audio, nan ta saka ta Fara ji, ikon Allah uhm lallai babu wani sarki face Allah, shine sarki kuma Mai jin kai.


Allahu Akbar Allah mai rahma mai gafara ga bayinsa wanda suka tuba, mutum yayi ma Allah babban laifi sannan Idan ya nemi gafara Allah ya yafe masa....


Mai yasa mu muke ri'ke da y'an uwanmu musulmai?? Ya kamata Muma mu dinga yafiya, idan aka mana abu, idan ka yafe kaima sai Allah ya yafe maka


Kubra jin karatun al'qur'ani yasa gaba d'aya taji nutsuwa a tare da ita, duk wani firgici da takeji sai taji duk ta daina, ga wani tsoran Allah da taji yana k'ara shiganta, lallai maganin ko wace cuta da nasiba tana cikin al'qur'ani Mai girma


Kubra haka ta zauna a dakin su ibtisam har dare yayi inda tace itafa a nan zata dinga kwana, domin a d'akinsu babu na Allah ko wacce tayi nisa, tare da fad'in Tana zargin d'ayan ma ta shiga cult


Koda su Aisha suka shigo d'akin suka ji kubra ana jin karatun al'qur'ani, abun ya basu mamaki, hauwa kasa hakuri tayi tace yau duk yanda akayi Kinji wa'azi a wani wajan wanda ya ratsaki kikai tuban mazuru....


Dariya Aisha ta saki tare da kallon kubra tace Nima fah Abun yaban mamaki, bandai fad'a bane kawai, wai kubra yau kodai kin had'u da wani sabon guy USTAZ ne yayi miki wa'azi


Kubra tace uhm, ban had'u da USTAZ ba sai dai na had'u da Wanda yayi niyan zama ajalina nan ta basu labari


Dariya suka saki tara da fad'in Wlh wannan k'arya ne


Kubra jin haka tayi banza dasu tare dayi musu fatan shiriya domin ita yanzu Allah ya ganar da ita gaskiya kuma ta gane


AISHA ta kalli Zarah tace nidai dan uwanki nake so, inda zai aureni dana daina harkan banzan nan.....


Ibtisam jin wani abu tayi ya tsaya mata a wuya da taji abunda Aisha ke fad'i........




















Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*


*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*


3138831065 Firstbank Maryam Alhassan


*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*


*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*




AISHA taci gaba da fad'in Wlh zarah inda yayanki zai yarda ya aureni..... Hmmm da naji dad'in rayuwa, ni aida na more da nafi ko wace mace Sa'a.....


Hauwa ta Katseta da fad'in nidai Ina son ganin wannan guy din da kike ta wasa wa haka Wlh


Aisha tace uhm, Aini tsoran ki ganshi ma nake wlh, baki ga yanda ya had'u ba


Hauwa tace yakai zarah kyau??


Tsaki Aisha taja, tace ina itafa Zarah ba'ka ce, wannan sak Balarabe, baki ji zarah tace mamansu ya d'auko ba, Kai Wlh ya had'u namiji iya namiji, Kinga Wlh zaiyi kwazo.....


Dariya suka saki tare da shewa


Ibtisam gaba d'aya ji tayi ranta na baci, jin bazata iya sauraransu ba yasa ta tashi tayi waje abunta, koda ta fita tsaki taja tare da fad'in aikin Banza dana hofi, waima NAJEEB suke wani kuzantawa, tsaki taja tare da fad'in inda Sun San halinshi da basu bata lokacin suba, Wlh, gaba d'aya ranta taji babu dad'i.


Gaba tayi tana tafiya, ranta gaba d'aya a jagule yake


mota ce ta tsaya a gabanta, wanda hasken motar ya kashe mata ido, tsaki taja tare da fad'in duba yanda suke wani haska mutum saboda iskanci


Har zata gota wajan motar taji muryan Dr jibril yana fad'in am so sorry plz, na kashe miki ido, sai Ina haka??


Ibtisam tsayawa tayi cak tare da fad'in ina wuni sir


Yace lafiya, tare da kallonta lokaci d'aya kuma ya fito daka cikin motar ya nufi inda take


Murmushi ya sakar mata tare da fad'in Amina dare yayi ina zaki??


Tace sir na fito insha iska ne


Yace Ok, ya exam din??


Tace Alhmdlh


Yace Bari in gudu, so Kema ki koma ciki, domin bai kamata kina yawo ke d'aya yanzu ba, domin lokaci ne da yara marasa ji ke zanyar fita


Ibtisam tace toh tare da fad'in saida safe


Yace OK motarshi ya nufa tare da barin skul din


Itama hanyar komawa tayi, domin gaskiya ya fad'a mata, domin taga irin motocin dake shigowa suna d'iban y'an Mata, ga kuma y'an Mata sai fita ake, Allah dai ya kyauta ya kuma shirya....


Ta kusa zuwa kofar d'akinsu ta hango zarah Tana tawowa, tsayawa tayi har Zarah ta k'araso inda take


Ibtisam tace sai Ina??


Zarah tace ke nazo nema, ina kika je??? Kodai duk kishin najeeb dinne yasa kika fita


Tsaki taja tare da fad'in Allah ya kiyaye akan mai zanyi kishin shi. Wlh kina bani haushi Idan kina fad'in haka, saifa kana son mutum kake kishin shi, in baka son mutum kishin Mai zakayi nashi??


Zarah tace toh mai yasa kika fita sanda ake maganan najeeb??


Ibtisam shuru tayi kaman tana tunanin abunda zata ce, can tace saboda haka nayi ra'ayi, keda kanki kin San bana son yayanki Mai zanyi dashi? Kinga dan Allah ki barni haka inji da abunda ke damuna na exam d'ina, gashi gobe zan Gama paper amma gaba d'aya na kasa zama inyi karatu nidai wannan semester din gaba d'aya sai a hankali Wlh


Zarah tace ai dole, tunda kin d'auki Abu kinsa ma ranki, ibtisam karki ce zanyi miki wannan maganan dan najeeb yayana ne, karki manta Kema y'ar uwata ce, sannan kuma abokiyar shawarata, Nasan a baya bakya son NAJEEB, amma a yanzu na tabbata kina sonshi, domin kuwa a da yanda kike yawan nuna tsananshi k'arara a ranki yanzu ba haka bane, gaba d'aya tsanar da kike Mai ya ragu, kibar yaudaran kanki, ki amshi mijinki hannu bibbiyu......


ibtisam wani harara ta sakar ma Zarah tare da fad'in baki da hankali sannan tayi gaba cikin fushi tana fad'in akan me Zata ce tana son NAJEEB, ai koda zanso mutum bazan so wanda ya tsaneni ba, mutumin da baya so na shine zanso?? Allah ya kyauta, mai zanyi dashi, mutumin da yake zina, tare dashan giya wanda baya tsoran Allah, aini har abada bazan taba sonshi ba, yaje can ya zauna da matanshi Wanda ya saba dasu, domin zama da irinshi wata rana saiya kwaso ma mutum cuta ya manna Mai, tunda shi neman Mata yasa gaba, d'aki ta shiga, tana shiga daga su Aisha Anata surutu da HAUWA, ko kallonsu batayi ba, domin gaba d'aya ji tayi haushi suke bata, nufa gadonta tayi wanda kubra ke kwance tana jin karatu bacci ya d'auketa, kashe karatun tayi domin su Aisha Nata surutu ga karatu, itama kwanciya tayi a kusa da kubra, amma gaba d'aya ta kasa bacci, har yau abunda najeeb yayi ya tsaya mata a rai yanda ta kamashi da Najwa suna sex, wani hawaye Mai zafi taji yana zubar mata, lallai najeeb ba mijin zama bane, har yau abun ya tsaya mata a rai ta kasa Manta abun kuma wani abun mamaki ta kasa fad'ama kowa, daga tazo fad'a saita fasa, ta rasa dalili, ita dai ranta yana bata ta rufa Mai asiri.....


Hawaye take da yake ba kuka bane, kuma akwai huta ga k'aran fanka yasa su Aisha basu San mai takeyi ba, balle su Fara mata tambaya ko lafiya


Ido ta lumshe tana ganin yanda najeeb din ke fucking din Najwa, da sauri ta bud'e ido tare da tashi ta zauna tana sauke wani nishi, sama sama, lokaci d'aya kuma ta fita taje ta dauraye fuskanta, inda ta hango zarah Tana waya


Bayan ta dauraye fuskan Nata, ciki ta koma inda tahau gado ta kwanta, still tunanin nedai ya kuma dawo mata, duk yanda takai danta cire Abun a rai ta kasa gaba d'aya tunanin abun ne a ranta


Haka taita juyi akan gadon har zarah ta shigo d'akin Itama ta kwanta, ibtisam ta kasa bacci har su Aisha masu fira suma sukai bacci


Washe gari ibtisam idonta duk ya kumbura ga ciwon kai, domin batai bacci ba, ga exam 8 haka ta shirya ta nufi exam, Bayan sun fito daga exam dinne ta dawo dak'i inda ta samu kubra na zaune ta manne waje d'aya alaman zazzabi ke damunta


Ibtisam tace kubra bakya jin dad'i ne??


Kubra tace eh wlh fever ke damuna Sosai, plz ki bani paracetamol insha, ko zanji dama dama


Ibtisam tace Kai Wlh banda paracetamol, amma inaga ki tashi muje hspt sai a dubaki, a baki magani, Kinga is very risk kisha magani baki San maike damunki ba


Kubra tace hakane, bari muje, tashi kubra tayi ta d'auki babban hijab tasa suka fita ita da ibtisam, inda sukai cikin Shika domin taga Dr


Bayan taga Dr inda aka bata gwaji inda aka ga Malaria ne, nan aka rubuta Mata magani, suka biyo ta wajan emergency, inda suna tsaye domin wata mota ta wuce, aka faka wata mota kusa dasu, nan aka bud'e wani matashi ne wanda kallo d'aya zaka mishi kace lafiyanshi kalau, domin ko motsi bayayi amma sai wanda suka kawo shi sukace bazai iya tafiya ba, nan aka d'auko Keken guragu domin a sashi, nurse din na tabashi tace ai ya rasu......


Kubra wani irin ihu tasa yanda kuka san ta san yaron, kuka take tana fad'in ibtisam kalla kiga, wlh kaman kice ya tashi, kalla kiga ikon Allah Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, wayyo kai Allah yaji k'anka


Nan y'an uwan yaron suka bita da ido, domin ganin yanda ta nuna damuwa akan dan uwan nasu


Nan ibtisam ta jata sukai gaba


Kubra na hawaye tana fad'in ibtisam wannan kukan Inayi ne tare da tausaya ma kaina, wlh ibtisam tunani Nayi inda nice na mutu, mai zance ma Allah?? Gaba d'aya na bata rayuwa ta, na bijire ma Abun da ubangiji yace Ayi, nabi hudubar shaidan, amma yanzu na gode Allah daya ganar dani tun lokaci bai k'ure Ba, wlh gaba d'aya komai na duniya ya fitar min a kai, ina matukar jin tsoran in aikata Sabo yanzu, lallai ibtisam idan kana son ka k'ara jin tsoran Allah imani ya Kama ka kazo asibti ziyara, na tabbata inda mun shiga accident and emergency da munga abubuwa wanda tayu wani in muka gani bazamu iya bacci ba, saboda tausayi, ibtisam kalla wannan saurayin, jikinshi fresh kaman bai mutu ba, kaman kice Mai ya tashi, ya kuma tashi din, lallai duniya ba komai bace


Ibtisam tace hakane nima mutuwar shi ta tsaya min a rai tasa gaba d'aya jikina yayi sanyi..... Allah yaji k'anshi tare da sauran musulmai


Kubra ta amsa da Ameen, tare da fad'in Wlh ibtisam ke Kinji dad'i kina da aure, rayuwarki Abun sha'awa, baki da wani fargaba, amma mu gashi babu aure ga sabon Allah, gashi karatun bama bashi muhimmanci tunda yawon mu kawai muke, in mun dawo mubi lecturer su kwanta damu, dan karsu fadar damu, kai Wlh babu komai cikin raina sai tarin dana sani, gobe zan koma Gida tunda na Gama paper, ina son koda na koma Kafin hutu ya Kare zamu dinga waya ina tambayarki abunda ya shige min duhu


Ibtisam tace karki damu kubra, insha Allah, duk sanda kike da tambaya ki kirani kawai


Nan sukai gaba, inda suka koma cikin skul


Koda suka shiga d'akinsu a kwance suka tarar da zarah


Ganin Sun shigo yasa Zarah fad'in Ina kukayi


Ibtisam tace hspt na raka kubra ganin Dr, ya paper din??


Zarah tace hmm, Alhmdlh, tare da kallon kubra tace bakya jin dad'i ne? Ko duk maganan mutumin nan ne?? Kubra tace a'a kawai zazzabi naji Inayi


Zarah tace Allah ya sawake


Washe gari duka suka watse sukai gida, Zarah taso ibtisam ta bita suyi abuja amma ta'ki, dole ta hakura ta tafi abuja ibtisam tayi Kano


Ibtisam ta isa Gida wajan 1 Tana shiga ta iske Ummi bata nan sai granny dake sallah, Dan haka itama alwala taje tayi inda ta Fara sallah


Bayan ta idar, ta kalli Granny dake zaune tace ina ummi??


Granny tace ta tafi anguwa, ya naga kin dawo, ko baki da lafiya ne? Naga duk kin rame


Ibtisam tace Hmmm granny ba dole ba, exam babu dad'i Wlh, munyi hutu ne sai yasa na dawo


Granny tace auwo tare da gatsan goranta tana ci tana gurus gurus


Ibtisam tace wai ba zaki daina cin wannan goran ba?? An fad'a miki yana da Illa, Amma kin k'i, wlh Granny ki shafa mana lafiya ki daina, kar kije kici abunda zaisa Musha wuya, gwara ki mutu cikin salama ba tare da wahalan jinya ba......


Granny tace dallah Rufamin baki, AI sai a kasheni, naga bakan mutum nake ba, in naci goro ya kashe ni, jiki na ko naki, haba yara sai iyayi komai ace yana da Illa shi kenan mutum kar yaji dad'in rayuwa, haba ni ban taba jin inda akace goro nada Illa ba


Ibtisam tace ai sai kiyi taci tunda an fad'a miki kin dage, nidai in ciwo ya kama ki bazanyi jinya ba, tunda na fad'a


Granny ta tsuke baki tare da fad'in shirmen banza da hofi, dama wake bukatar ki? AI na tabbata babu abun arzikin da zaki iya, Aini da kiyi jinyata gwara in zauna ni d'aya yafi min, wannan ba'kar zuciya taki, gashi mijin naki kin kasa hakuri dashi.....


Granny jin ibtisam tayi shuru yasa ta kalleta, ganinta tayi tana hawaye....


Granny tace miye haka kuma?? Haba takwarata maiya faru? cikin sigar rarrashi take tambayarta


Ibtisam kallon Granny tayi tare da fad'in yanzu Granny komai najeeb yayi ba'a ga laifinshi ba sai nawa???


Granny tace ba haka nake nufi ba, abunda nake nufi kin kasa hakuri dashi.....


Ibtisam tace taya zanyi hakuri dashi?? Granny karki manta ni mace ce, an d'aura min najeeb ba tare da sanina ba, infact ma ban taba tunanin zan aureshi ba, gaba d'aya nasa rai za muyi aure da kabir sai naji an d'aura da wani, yau najeeb Koba dan uwana bane shi, dole yanda naji babu dad'i hakan zanyi, anyi min wannan a matsayina na mace, wanda ya zama dole in hakura in zauna dashi, Wanda nasan igiyar auren shine keda ikon tsinkata, sannan shi namiji ne, Ance in za suyi adalci su Fara daga Biyu.....


Kinga Mata biyu akace ba d'aya ba, kinga yana da ikon k'ara auren wacce yake so, amma nifa?? Bani dashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login