Showing 9001 words to 12000 words out of 182942 words

Chapter 4 - NAJEEB COMPLETE BOOK Document writing Maryam Obama.txt

duba mishi Mata wacce zata dinga koya mishi fulatanci.


Ibtisam dariya take Sosai cikin ranta, tare da ro'kan Allah yasa ayi mishi hakan.


Granny tace toh ke ya Magananki da kabir? Ina fatan kin amince koh?


Ibtisam tasan ta gama magana da kabir, dan haka tace na amince Granny Indai zaki ma Najeeb aure, amma ina son a fara nashi Kafin nawa, tunda Kinga ya girmeni Sosai, ban so In rigashi aure


Granny cikin jin dad'i da murnan ibtisam ta yarda zatai aure tace karki damu, gobe ni dake zamu habuja din inga audullahi muyi magana.


Koda ummi ta dawo ta kira ibtisam, Bayan ibtisam tazo, ummi tace Waye yazo nemanki?


Ibtisam tace ummi shine wanda ya rage mana hanya shekaran jiya, nan taba ummi labarin yanda suka had'u.


Ummi tace naga kaman ya baki, Leda, ban San amshe amshen kayan samari, Indai kin San ba auranshi zakiyi ba gwara ki sallameshi, ban son fitina


A hankali tace toh ummi, tare da tashi ta fita


Washe gari da safe ibtisam ta shirya ita da granny Wanda Abba bai San da tafiyar Granny ba, sai ganinta yayi da safe ita da ibtisam, yace mama zaki rakata garage ne?


Tace miye kuma wani garan?


Yace ina nufin tasha.


Tace wani rakiya? Tare da ita zamu, muje ka sauke mu tasha sai mu shiga mota


Yace mama tare kuma zaku?


Tace eh ko saina tambayi izini ne, Kafin a barni inje inda nake so?


Yace a'ah kiyi hakuri mama ba haka nake nufi ba, naga tun jiya baki ce zaki jeba sai yanzu.


D'aure fuska tayi tare da fad'in Ummaru zaka kaimu tasha ko mu tafi da kammu?


Yace a'ah muje in saukeku, ummi ta basu kayan miya sukai ma mum tare dasu gurasa da sauransu, sannan ta musu Allah kiyaye hanya suka fita.


Saida Abba ya biya ATM ya cira kud'i sannan sukai hanyar garage, inda ya d'aukan musu shatan mota su biyu, nan ya biya kud'in motan, sannan ya bama Granny kud'i itama ibtisam ya bata, saida suka wuce sannan ya shiga tashi motar ya wuce kasuwa.


Sai wajan 3 da wani abu suka isa Abuja, dai dai kofar gidan alh Abdullahi aka saukesu, inda suka nufi gate din gidan suka fara nocking, wani soja ne ya le'ko yana fad'in 'who is that? Ibtisam tace mune cikin harshen turanci take bashi amsa.


Granny tace Mai yace? Ibtisam tace tambaya yake su Waye? Granny tace oh yanzu har sai an tambaya, kai dan ubanka zoka bud'e Uwar Mai gidan ce,


Dai dai lokacin sojan ya bud'e karamin kofar gate din, inda mutum zai shiga Inba da mota bane.


Kallonsu yayi sannan yace wa kuke nema?


Ibtisam ta bashi amsa da fad'in Munzo wajan matar gidan ne?


Yace tasan da zuwanku?


Ibtisam na k'okarin bashi amsa, Granny tace wai Mai yake cewa ne?


Nan ibtisam ta fad'a mata, Granny ta kalleshi cikin jin haushin tambayar da yake musu, tace Kai Dallah bamu waje mu shige tare da k'okarin tusa kanta cikin gidan.


Sojan yayi sauri ya tareta tare da magana cikin gurbattaciyar hausan shi yace mama inane zaka? Ka kira ajiya sai in Barka ka ciga, lokaci d'aya kuma ya kalli ibtisam yace ki kira madam a waya in tace in barku saiku shiga.


Granny kam in banda faman surfa bala'i tare da fad'in audullahi yasa Anci min zarafi yanzu in banda iskanci In za'a zo gidansa sai an kirasu a waya, har dani uwarsa.


Ibtisam dake k'okarin kiran mum tace Granny dan Allah kiyi shuru, shifa wannan bai San ke maman uncle bace, inda ya sani Aida ya Bari kin shiga, kuma daka gani sabon zuwa ne, dan duk zuwan da nake ban taba ganinshi ba.


Granny ta galla mata harara tare da fad'in Dallah ni kirata Ina jin fitsari kaman marata zata fashe


Kiran mum tayi, bayan mum ta d'auka tace ibtisam Kun zone, Ashe da Granny kuka tawo, yanzu na gama waya da abbanki.


Ibtisam tace Munzo muna Gate, ance mu kiraki.


Mi'ka ma Sojan wayarta tayi Mai tocilan, ya amsa tare da sakawa a kunne, naji yana fad'in ok ma, ok ma, lokaci d'aya kuma ya fara sorry ma, tare da kashe wayan ya mi'ka ma ibtisam, ya fara basu hakuri, cikin harshen turanci tare da cewa ibtisam taba granny hakuri bai San Maman oga bace.


Nan ibtisam ta fad'a ma Granny abunda yace, Granny ta kalleshi tare da fad'in Dallah bani waje, munafuki, da sauri ya matsa suka shiga, tun Kafin su k'arasa wata yarinya Doguwa chocolate colour kyakyawa ta rugo da gudu ta rungume ibtisam tare da fad'in oyoyo, lokaci d'aya kuma ta saki ibtisam ta rungume granny


Granny tace Dallah sakeni karki Karya ni, saida kika gama rungume y'ar uwarki sannan zaki zo kaina.


Ibtisam tace zarah Kinga kyaleta zomu shige


Granny tace zanyi maganinku Wlh, yara duk sun girma Sun Fara tsufa amma babu aure, ji yanda zarah ta k'ara fashewa, nidai Amina wani laifi na muku babu maganan aure a tsarinku, kwafa tayi sannan ta shige ciki ta barsu nan tsaye suna murnan ganin juna, sun dad'e a nan Kafin suka shiga ciki inda suka tarar da mum a falo ita d'aya.


Ibtisam gaida mum tayi, mum ta amsa cikin sakin fuska tare da fad'in ya hanya?


Ibtisam tace Alhmdlh, sai dai rigiman Granny, duk ta isheni dariya suka saka, mum kana kallonta Kaga balarabiya sak ita NAJEEB ya d'auko sai dai wasu sukan ce farinta ya d'auko yafi kama da dad d'inshi wasu suce da ita yake Kama, mum in kaji hausarta saika d'auka ba Hausa takeyi ba dan in tanayi kaman tana larabci


Granny ce ta fito cikin tan'kamemen falon Tana gyara zani tare da fad'in ku komai naku daban dana mutane, Kun tashi kun ajiye mara mutunci a bakin gate.


Zarah tace Kai granny maiya miki kuma?


Tace ban sani ba, in banda wulakanci in za'a shigo gidan sai ace sai an kira a waya, in mutum baida Kati fah, ko in bashi da wayan gaba d'aya fah?


Zarah tace saiya koma, Granny ko a addinance anaso in mutum zaizo wajanka ya Sanar dakai, bawai yazo kai tsaye ba K....


Granny tsaki taja tare da fad'in tunda bakwa son mutane ba, ai dole ki Kawo maganan addini..


Dariya suka saka, mum tace mama muje kuci abinci ku huta


Granny tashi tayi aka nufi k'aton dinning table, harta zauna, lokaci d'aya kuma ta tashi tare da fad'in nifa wannan abubuwan ban cika sonshi ba, in mutum zaici abinci saiya wani zauna a kujera kaman Maye, ni kusa min in zauna a k'asa Inci


Zarah da ibtisam babu abunda suke sai dariya


Granny tace uwarku kuke ma dariya, akan Mai yasa za'a ce cin abinci sai an hau saman kujera maima kuke kiran kujeran Denis ne ko Mai ohon muku


Zarah saboda dariya har dayin k'asa tace miye kuma Denis dan Allah granny kar kisa cikina ya fashe saboda dariya. Tsaki Granny taja tare da zama ta mi'ke k'afa a k'asa tana fad'in nidai ban hawa Denis din nan wlh


Mum da itama take ta dariya k'asa k'asa ta Fara zuba ma Granny abinci, Bayan ta gama ta ajiye mata a k'asa inda ta zauna, Granny Fara cin abinci akayi ana mamula baki.


Bayan sun kammala, Granny tace audullahi bai dawo bane har yanzu?


Mum tace tun dazu yace Sun sauka, Nasan yana gab da gida yanzu


Tashi Granny tayi, tace ni bari in shiga in huta kafafuwana duk sunyi tsami, d'aki ta nufa


Ibtisam taba mum tsaraban da Ummi ta bata, mum taji dad'i Sosai tana ta godiya, inda zarah taja ibtisam sukai d'akinta, wanda d'akin yayi mugun had'uwa, komai dake d'akin pink ne, sai rasi rasin blue kad'an, zama sukai akan gadon d'akin Mai shape din mota, zarah tace kin Fara shirin zuwan mu skul kuwa?


Ibtisam tace na Fara mana, sai dai Granny ta sani gaba da maganan aure, kai wannan tsohuwar akwai jaraba


Zarah tace Niko Tana sani dariya wlh, dama ta mana wata biyu a nan


Ibtisam tace Aiko ko sati tayi a nan sai kince ta isheki, ko sanda take zuwa kina skul in kin dawo kin gaji, yanzu da kike zaman Gida ai wlh saita isheki, dariya zarah tasa inda suka fara tsara yanda za suyi a skul, wayan zarah dake wajan wardrobe d'inta ne ya fara K'ara, tashi tayi da sauri ta d'auka, ganin Mai kiran yasa tayi saurin d'auka tare da fad'in bros


Yace yakike? Cikin harshen turanci


Tace am fine my bros, sai dai nayi missing dinka


Murmushi yayi tare da fad'in gobe Zanzo Nigeria, make sure kisa a gyaramin part d'ina


Tace an gama bros, Granny tazo ma


Tsaki yaja tare da fad'in har yanzu bata mutu ba?


Zarah tace what? Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad'in Bari Dad ya jika, kana ma mum d'inshi fatan mutuwa.


Kashe wayan yayi ba tare daya kuma ce mata komai ba.


Kallon ibtisam tayi tare da fad'in bros gobe zai zo,, rabonshi da gida wajan wata hud'u kenan


Tabe baki ibtisam tayi tare da fad'in wannan ba damuwa ta bace.


Zarah dariya tayi tare da fad'in oh na manta Ashe enemy d'inki ne, sai kuma ta saki dariya tare da fad'in nima a waya yake sake min, inya dawo sai yayi ta d'aurewa kaman dodo, na rasa irin halinshi Wlh, zanso inga matarshi inya ya zai dinga mata.


Itbtisam tace lallai Aiko duk wacce ta auri wannan ta shiga uku, sunanta sorry, lokaci d'aya kuma ta tuna da abunda ya kawo Granny, cikin ranta tace Allah ya tabbatar inga yanda zaiyi.


Zarah tace dama Ayi auran zumunci ke dashi, tunda naga halinku d'aya K....


Da sauri tace aniyarki ta biki, da in auri wannan yayan naki gwara in mutu Banyi aure ba, wannan wani banzan tunani nema kikayi haka, tsaki ta saki cikin bacin rai.


Zarah tace Allah ya huci zuciyarki, wasa nake miki, ai nasan in aka had'aku wata rana k'ona gidan zakuyi


Itbtisam dake huci tace wannan Aiba wasa bane, in mala'iku suka amsa fah? Haba dan Allah, wlh gwara in mutu yau da ace na auri NAJEEB, dan Allah karki k'aramin wannan Wasan plz, wlh kinsa raina yayi mugun baci Sosai


Zarah tace ikon Allah, haka tsanan NAJEEB yayi girma cikin zuciyarki? Adai dinga hakuri d'an uwanki ne dai


Tsaki Itbtisam taja tare da tashi tana fad'in naga baki da wata firan arziki saina wannan yayan naki Kinga Bari inje wajan Granny n....


Da sauri zarah ta janyota Tana fad'in na daina miki firanshi, amma kudaina wannan abun babu kyau Wlh, duk da Nasan laifin bros NAJEEB ne, yana da shegen miskilanci da raini wlh, kodan ya girma mutane ne oho, wlh koni hakuri nake dashi, ga Dad komai yace saiya biye mishi tsaki taja


Itbtisam tace Kema kenan, balle ni ki.... Karan wayarta ne yasa bata k'arasa abunda tayi niya ba, d'auka tayi taga kabir ne wanda a jiya tayi saving number d'inshi, sawa tayi a kunne tare da fad'in hello


Ta gefenshi yace ibti Barka da yamma, sorry ban kiraki ba, aiki yamin yawa, yanzu nace gaskiya sai naji muryanki, ya kano?


Tace uhm lafiya kalau, nima bana Kano Ina Abuja


Da sauri yace yaushe kika zo Abuja?


Tace d'azu nazo nida Granny gidan uncle d'ina


Kabir yace shine baki fad'amin jiya ba, muzo tare


Tace naga hakan bai kamata ba, bai dace in bika ba har zuwa wani gari, hakan ba dai dai bane


Murmushi yayi tare da fad'in hakane, my ibti, tare da fad'in na gode ma Allah daya had'ani dake, ina Mai farin ciki, Allah ya tabbatar yasa ki zama mallaki na


Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.


Yace anjima zan kiraki, ina fatan zaki bani dama inzo in ganki a nan?


Tace babu damuwa tare da fad'in sai anjima, ta kashe wayan.


Zarah dake zaune kusa da ita, tace ke dawa haka? Daka ji saurayinki ne yanda kike wani kashe murya


Ibtisam takai Mata duka tare da fad'in ta ina na kashe murya?kina da sharri Wlh


Zarah tace fad'amim Waye inji tare da d'aga mata gira


Nan ibtisam ta bata Labarin inda suka had'u


Zarah saida tayi dariya Sosai tare da fad'in Wlh Granny tana da matsala, Tab gaskiya ki daina fita da ita.


Uhm kawai ibtisam tace


zarah tace Amma inda nice ke Wlh zan yarda in aureshi, tunda muda zamu karatu kaduna, shi kuma yana Abuja, Kinga zaki samu daman karatu, yanzu fah maza tsada suke sai kiga mata da yawa babu mijin aure, wlh ibtisam inka samu dama Kar kayi wasa dashi, kyace ya jiraki shekara hud'u ai yayi yawa wlh, kina da tabbacin zai iya jiranki har shekara hud'u, haba ibtisam Wlh nima da badan Dad ba da yake son inyi karatu ba Aida aure zanyi Wlh, nifa aure nake so, Amma Dad ya'ki fahimta inaga saina fito na fad'a musu


Dukanta da wasa ibtisam tayi tare da fad'in amma dai da kin cika mara kunya number d'aya, Tabdi Niko Wlh karatu ne a gaba na, Kinga mazan yanzu basu da tabbas, wlh gwara koda zanyi auran saina gama karatu in samu aiki sannan inyi, dan ban son ina bin namiji Ina bani yana min wulakanci, gwara in tsaya da kafafuna, Suma yanzu mazan basu cika auran zauna gari banza ba, dan basa son wahala


Zarah tace uhm, ni Wlh aure nake so, ke nifa wannan karatun kaman dole ne, amma Wlh Ina bala'in son inyi aure, Kinga in Nayi sai inyi karatun a d'aki na, hankali kwance, amma hakan bazai yihu ba, Allah yaban iyaye duka y'an boko, ko wanne zai ka'ida, ba mum ba, ba Dad ba, yanzu koda wasa ban isa ince Ina son aure ba, wai dana shiga uku, ko bros NAJEEB baiyi ba shida yake aiki sai ni, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya


Ibtisam tace zarah kin San muhimmancin ilimin mace kuwa? Inda za'a tambayeni tsakanin mace dana miji waya kamata a fi bama ilimi? Zance mace ya kamata, kin San mai yasa? Mace itace tushen gida Mace itace take zama a gida ita da yara ta basu tarbiya tare da duk wata kulawa, in mace bata da ilimi taya za tayi hakan? Da yawa yaran da zaki gani suna rashin ji Toh uwarsu bata da ilimi, sannan yana dakyau mata a dinga basu ilimi domin ko ina a dinga damawa damu, ki kalla aikin soja akwai mata Kinga wannan abun alfahari ne, ki duba fannin Siyasa akwai mata wanda da ana ma mace y'ar Siyasa kallon y'ar iska, amma yanzu an fara fahimta, inda babu Mata a Siyasa da baza'a dinga bamu hakkin mu ba, bazan musan miye Siyasa ba, sannan mune dai mukaci jefa ruwan kuri'a, sannan yana dakyau mata su dinga karatu kodan su zama likitoci, yanzu Idan mace tazo haiyuwa namiji zai amshi haiyuwar tayu ba musulmi bane, Kinga inda mata suna karatu Sosai da an huta, komai mu ana tauye mu, daka munyi aure shikenan, in namiji yace ba zamuyi ba shikenan ta zauna, bayan ilimi shine ginshikin rayuwa, wlh zarah in Kinga yanda in naga mace take burgeni in naga tana karatu ko aiki sai Kinji mamaki, zan iya bama mace tallafin komai nake dashi dan tayi karatu domin Nasan al'umma zasu amfana da ita, yana dakyau komai a dinga saka mata, ana bamu y'ancin mu, Idan kika duba yanzu zamani ya canza duniya ta canza, ilimi both na addini dana zamani is like kaman ya zama dole mace tayi, indai Tana son ganin ci gaba da taimakon Al'umma.


Zarah tace bank'i taki ba, shima auren yana da muhimmanci, sannan aure baya hana karatu, nidai Ina baki shawara a matsayina na y'ar uwarki, indai kabir dagaske yake kice Ya fito Wlh, Kinga kyaci gaba da karatun a d'akin ki, amma baki da wani hujja kice saboda karatu k'iki yin aure, Abba Nasan shi zai miki aure amma nikam Dad Nasan Wlh koda wasa saina gama wannan karatun zaimin aure, har shekara hud'u ta k'arasa maganan cikin tausayin kanta.


Muryan Granny sukaji Tana fad'in kuna inane haka?


Zarah tace Granny gamu a nan, Granny shigowa tayi ta saki baki Tana fad'in yanzu wannan kaman mota, motar nan taya akayi ta shigo wannan d'akin, naga dai kofar karama ce, ni ban taba ganin irin wannan motar ba Wlh, mota harda katifa, ya ake tukata?


Dariya suka saki su duka sannan zarah tace Granny gado nefa


Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad'in yanzu bakya tsoran wannan abun, salan kina bacci ya fara tu'ka kanshi? Ina gadonki Nada?


Zarah tace Kai granny wannan fah ba mota bane, gado ne mai shape din mota, gadona Nada anbama Mai aiki takai gidanta da aka canza min wannan.


Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad'in naji kince gado ne mai chape din mota, miye chape?


Dariya suka saki, itbisam tace haba Granny Tana nufin gado ne mai fasalin mota, yanzu kin gane?


Tace Hmmm wanna ai iskanci ne, in banda asaran dukiya, ace gado za'a saka a d'aki Mai fasalin mota da haka a siya motar mana a ajiye, yanzu wannan gadon nawa aka siya?


Zarah tace million biyu da rabi


Salati Granny ta saki tare da fad'in audullahi yana tunanin mutuwa kuwa? Yanzu gadon da zaki kwanta ki tashi shine har million biyu da rabi, oh ni Aminatu, wannan asaran dukiya haka Kai audullahi zai gamu dani, dama aure yayi miki keda wancan dan banzan, koda yake Bari in Gama da munafukin yayanki da wannan ta nuna ibtisam, sannan in dawo kanki, bari audullahi ya fito naji ance ya dawo yana hutawa


Zarah cikin jin dad'in maganan Granny tace Granny gobe ma zai zo gida NAJEEB din


Granny tace yauwa Alhmdlh Nima zani yola, dan Wlh wannan karan da Mata zai koma dan banza, sai na mishi iya shege, tunda bashi da niyan aure, inma aljana ce ta aureshi zata rabu dashi in na saka aka d'aura mai aure, zan zabo mata guda uku cikin dangi in tawo dasu ya zaba d'aya, inma duka yake so ya auresu dan banza kawai....... Muje zuwa muga had'uwan Granny da miskili, sannan muga ya zata kaya in aka zabo ma NAJEEB mata har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login