Showing 27001 words to 30000 words out of 90241 words
Chapter 10 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 tana fad'in "wai mutumin nan yasan Allah kuwa?"
           Muguntarsa ta yi yawa, a kullum burin shi yaga ya illatata, yayi mata tabo ajiki."
     Cigaba tayi da kuka, Talatu ce ta turo k'ofa tashigo, domin duk abun da ke faruwa a kan idon ta."
 tazo kawowa Afnan kayan  motsa baki, 
    Da Sauri  ta koma da baya, Allah yatsare  basuyi ido biyu da Bassam ba."
Matsota tayi ta durk'ushe k'asa ita ma hawaye sai fita yakeyi a idonta, sai ka ce ita a ka yiwa."
Afnan na ganinta tayi saurin mik'ewa tsaye a firgice, 
      Tana fad'in ina yake?"
Talatu tace "ya tafi ranki ya dad'e."
Afnan ta kuma rushewa da kuka, taci gaba da cewa,
    Sai ya kashe ni yau d'in nan in huta da wulak'aci da azzabtar da ni da ya keyi."
Hannun ta Talatu ta rik'e tana dibawa, tace "ranki ya dad'e wannan shaidar fa?"
Kukan ta ya tsanta tace " so yake ya gama b'ata min jiki da tabo,
   So yake yaga ya in latani sannan ya rabu dani."
Mulki hauka ne, ko saura ta hauka ce,
    Gara ma yasa a kashe ni ta,  idon ba hakan ba, zan ganar dashi mulkin macce a kwai banbanci sosai,
Domin bazanci gaba da  d'aukar  wulak'ancinsa ba, sai dai yayi gun duwa gun duwa da naman jikina."
_____________________________
 Cikin *Kunar Zuci* Bassam ya fita,
 kai tsaye chilly ya nufa, mashayar giya."
Basma yaci karo da ita zai shiga, ita kuma zata fita."
Kallon juna suka shigayi, cikin yana yin kuka ta rungume shi."
Bassam na ganin hakan ya zanye ta daga jikinshi cikin dabara suka nufi gefe d'aya inda mutane basa wuce wa."
 Basma ta fad'a a k'irjinshi ta fashe da kuka, tana fad'in "meyasa ka yau dare ni Prince?"
Kasan kai kad'ai nake so, kai kad'ai na mallakawa zuciya ta da jikina, amma kai ne mutum na farko da kafara yaudara ta."
Banta b'a sanin ko wane d'a namiji ba, sai a kanka, ka shayar da ni zumar soyayyar ka, wadda duk namijin da na tunkara, bayan rashin ka danayi, tamkar 'yar uwata mace  nake d'aukar shi." 
        Prince mena maka?"
 ka yau dare
 ni?"
Kamanta da ni, daga k'arshe sai  dai naji labarin auren ka a gari?"
Share mata hawaye ya shiga yi, cikin sigar lallashi,
 yana d'an dukan bayan ta, alamar tayi hak'uri tayi shuru."
Sannan tayi shuru ta d'aga kan ta, suka yi ido biyu, sannan ya samu da mar yi mata magana."
"Basma ki natsu ki saurare ni, ki kuma fahimce ni da kyau."
  Auren da kikaji labari  nayi,
 banyi shi ne ba domin na yau dareki, 
    Nayi shi ne domin d'aukar fansa."
Sannan  kuma na k'unta tawa rayuwar wasu masoya."
Har ga Allah bana son matar da kike cewa wai na aure ta, domin kwata kwata bata d'aya daga cikin jerin matan da nake mafarkin aure"
Sannan kuma yin aure na bashi ne yan kewar alak'a ta da ke ba."
 Basma, ke tawa ce ni naki ne, idan Allah ya k'addari ki zama mata ta, zaki zama."
 
 share mata wasu 'yan gun tayen  hawaye yashiga yi, yana kuma kwantar mata da hankali, 
     A nan take ya mantar da ita b'acin rain dake damun ta."
Fira sukeyi mai cike da so da k'auna, mussam Basma, domin Bassam biye mata kawai yakeyi domin ya samu ya  rabu da ita lafiya."
Domin ko giyar wake yake sha baya jin zai iya auren ta,
Macce da suka had'u a Club, yana ma kula tane, saboda yaga tana yi mashi wani mahaukacin so,
Amma dan tsabagen muna furci irin  na mace, harda wani kuka "wai ya san dai shi kad'ai ta fara kulawa."
Koda ya fara ma'amala da ita, tamkar k'ofar text yakejin, haka nan kawai yake biye mata."
[3/5, 4:34 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
           *24*
Haka ya samu da kyar ya lallashi Basma tare da kwatar mata da hankali da cewa idan Allah ya rubuto zasuyi aure tofa zasuyi shi."
Bayan Basma ta tafi."
ji yayi gaba d'aya komai ya fice mashi a rai, 
    Giyar ma yaji ba ya son sha."
Iyar da shigewa yayi cikin chilly d'in,
  ya sayi barasar da yake gurin baki d'aya irin wadda yake sha."
 yasa aka jera masa ita a bayan but d'insa."
Yashiga mota ya nufi gida da sak'e sak:e a ransa.'
" tabbas dole ne ya canza d'aki, Wanda zai dinga ajiye sirrinsa, domin ya fahimci wannan aljanar yarinyar su take tadinga shige masa a hanci."
   Yana tsayar da mota harabar gidan, fadawa suka taso kansa suna yimashi kirari,
      Kud'i ya fito dasu 'yan dubu dubu yashiga zubar masu. 
Yayi hakan ne dan su rabu dashi karsu hango abunda ke but d'inshi."
Ai kuwa da gudu suka shiga rugu guwar tsintar kud'in basu kuma bi takan shiba,
     Kuma matsawa yayi da motar shi kusa garesu, 
saiti d'aya
Window  d'akin nashi,
Nan  yakira wani Amintancen Bafadensa,  Wanda ya yarda dashi, ya kuma Amince masa,
 suka shiga d'aukar barasar ana shigar masa da ita ta bayan k'ofa, ba tare da kowa yasani ba, hankalinsa ya kwanta."
 
_______________________________
Washe gari,  sarki da Bassam, suna break fast, domin al'adar sarki ne baya cin abinci da kowa sai da tilon d'ansa ta nan yake jin damuwar d'an nasa." 
Afnan ce tashigo cikin shiga ta alfarma,
 ta durk'usa ta  gaida sarki cikin girmama wa."
Kallo maimartaba yabita dashi cike da jin dad'i ya amsa gaisuwarta."
domin tunda ya sanya ido ya ganta a matsayin matar d'ansa, 
yaji ya yaba da tarbiyar ta da kuma na tsuwarta, 
    Sannan duk ya kalle fuskarta  sai yaga tana yi mashi kama da wani babban aminin shi wato Alhaji Ibrahim Wanda yayi rashin sa shekaru da suka wuce", 
Wanda akoda yaushe idan ya tuna shi zaiji ba dad'i a ransa." saboda ke warshi da ke damunshi."
Bassam kuma na kishingid'e gefe d'aya ga fulalluka ya jera yana cin dabino,
   Ko kallon bata ishisa ba, 
       Sai cewa yake lallai yarinyar tasamu sake, har fada take zuwa gaida maimartaba dan tsabagen muna furci."
Can kuma ya d'aga kai sukayi ido biyu da ita,
    Saiya tuna da lokacin da tad'aga hannu ta  mareshi"
Tuni haushin ta da takai cinta ya cika mashi zuciya, 
       Nan da nan nishad'insa ya kau, ya juya masu baya."
Shi kuma sarki sai  fira yake jan Afnan yana yi mata  tambayoyi ."
Jin haka da Bassam yayi, yaji baya iya zama wurin, 
   Mik'ewa yayi ya bar wurin."
 sarki kuma ya lura da yanayin sa, ya kuma fahimci  tambas akwai abunda ke damunsa,  ya kyaleshi bai ce masa ko mai ba."
Maimartaba yaci gaba da jan Afnan da fira, domin yanaso ya fahimci wani Abu game da ita."
Fitar da yayi daga fada kai tsaye d'akin shi ya nufa Wanda ya koma babu wanda ya isa ya shigesa sai shi kad'ai."
Sai da ya fara sanyawa d'akin key sannan, ya bud'e prege ya d'auko kwalbar giyar shi ya shiga sha,
 domin duk lokacin da yayi tuzali da fuskar Afnan sai ya tuna marin da tayi mashi, 
zaiji rayuwarshi tana suya, babu abunda yake wanke masa b'acin rai kamar giya."
Haka Afnan ta kamalla fira da Maimartaba,daga k'arshe yq bata izini   taje ta huta."
Tafiya takeyi sai d'in girsa k'afa takeyi inda Bassam ya taka ta har yanzun wurin ciyo yake mata ga kuma hannunta shima da yake mata zugi."
gab da zata shiga d'akin barcinta,
taci Karo  da Jakadiya tare da indo sunfito daga wani d'aki, 
Jakadiya ta lura da d'in gisa k'afar da takeyi,
Ta rik'o hannunta mai ciwon tana kallo,
     Cikin mamaki, tace Afnan meya sameki a hannu da k'afa? 
Zuciyar Afnan ta  k'arye, a nan take ta fashe da kuka."
Jakadiya ta juya ta kalli indo domin tasan suke kula da lafiyar ta,
    Tace "indo me ya same ta?
Tuni indo ta zube k'asa tana inda inda, bata iya cewa ga abunda ya faruba,
     Domin Bassam ya fi k'arfin a kai k'ararsa, domin sanin halinsa."
Afnan ta raunana muryarta tace "Bassam ne !"
 
Jakadiya ta dubeta cike da mamaki, tace "Bassam ya jimaki?" akan me?"
Ta kuma fashewa da kuka tace " yana ta tambayata ajiyarsa dan nace bangani ba shine yayi ta buguna."
Jakadiya tayi ta lallashinta, taja ta  tashigar da ita d'aki tayi ta kwantar mata da hankali, sannan tafito tabata wuri domin ta huta."
Jakadiya tarasa gane abunda ke tsakanin Bassam da Afnan."
Tayi juyin duniyar nan Afnan tak'i bari ta gano wani Abu a tsakanin su, haka shima Bassam."
Dan haka ta d'auki alwashin sai ta yi k'ok'ari ta gano abunda ke tsakaninsu, cikin hikima irin tasu."
Zata yi k'ok'arin hana shi dukanta dan kada yajiwa yarinyar mutane ciwo, saboda jikinta baiyi kama da na duka ba."
_____________________________
Jin k'arar bud'e  k'ofa dayaji yasan yashi yin saurin mik'ewa ya d'auki kwalbar barasarsa ya b'oye a bayan kujera, domin yasan babu Wanda ya isa ya shigo masa d'aki sai jakadiya, Wanda yake jinta tamkar mahaifiyarshi.'
Jakadiya ce ta shigo, ya saki murmushin dole. Yace " Anna nemana kikeyi?"
Anna shine sunan da yake kiranta dashi tun yana yaro."
Ta kalleshi babu wasa a fuskarta, tace "Eh."
Sannan taci gaba da cewa wace Ajiya ce kake nema?"
Tambayar tazo masa bazata, yarasa abunda zai ce, shuru yayi."
Anna ta dibeshi tace "Akan me zaka doki Afnan har kaji mata ciwo?"
Jin an ambaci sunan Afnan nan da nan ya b'ata fuska, yace 'ni ban dake taba."
"Haka kace?"
     Afnan CE zatayi maka k'arya?"
To shaidar da nagani a k'afarta da kuma hannunta, ta meye?"
Shuru yayi yana susar kai."
"Haba Bassam akan ajiyarka ta banza, zaka doke matarka har ka jimata ciyo?"
Tun kana k'ara minka nasanka da tausayin 'ya mace Bassam meyasa kake son k'untatawa Yarinyar nan ne?"
Sunkuyar da kansa yayi yace "kiyi hak'uri bazan sakeba."
"Ita dai zaka bawa hak'uri,
  Tunda aka kawota gidan nan na lura baka damu da itaba, idan kasa k'afa kafita sai kaga dama kake dawowa daga k'arshe ma karaba d'aki da ita."
To idan baka kyautatawa matarka ba, ni zanfita daga lamarinka innemi alfarma wurin maimartaba ya canza min wurin zama."
Saurin d'aga kai yayi cikin tashin hankali, yayi saurin matsowa kusa da ita, 
   Yace " Haba Anna daina fad'ar hakan don Allah daga yanzun ba zan sake ba wallahi."
Fita tayi tace " Allah yasa ka gyara."
Tana fita Bassam ya d'auko barasarsa yaci gaba da sha,
Yana fad'i a zuciyarsa zai ganar da yarinyar nan shi ba'a kai k'ararsa, lallai ma yarinyar nan saina koya mata hankali."
_________________________________
A b'angaren *Malam Nura* kuma........
       
*Wash hannu na nagaji*
[3/5, 4:34 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
            *25*
*Malam Nura* kuma Alhmdulillah,
Sauk'i yasa mu, ya kuma san yawa zuciyar shi dan gana."
 Amma kuma, a kullum cikin tunin Afnan d'in shi yake."
Domin a koda yaushe yana sanya ido akan  Afnan d'inshi zata dawo gare shi."
Domin yasan Afnan 
 shi take so, ba Bassam ba, kuma 
    A kwai babban dalilin da ya sanya ta Amince da Auren Bassam."
Dan ya shai dawa kansa cewa,  a duniyar nan idan aka cire Kaka to babu wanda Afnan take so sama da shi." Dan haka a kullum yake sanya zuba ido zata dawo gare shi."
       Dan haka kullum yana gidan *Kaka* 
      Babu abun da ke raba shi da gidan *Kaka* sai barci, sai kuma idan ya tafi wurin aiki."
Domin zama gidan *Kaka* yana k'ara d'ebe mashi kewar Afnan, d'in shi,
          Musammam idan yayi tuzali da d'akin ta, Wanda tayi rayuwa a cikin sa,
       
Sannan kuma *Kaka* bata da firar da take masa sai ta Afnan, wata firar yayi dariya wata kuma yaji wani sabon son ta, da son yasan halin da take ciki a yanzun."
*KAKA* Kuma tunda akayi auren Afnan kullum sai maimartaba ya aiko fadawa, da kayan abinci, da cefa ne, da duk wani Abu na kyauta tawa, rayuwarta, da ita da malam Iro."
Sannan kuma daga k'arshe yace "a sheda mata, jikan yarta, tana cikin k'oshin lafiya, zai san ya ranar da fadawa zasu zo a d'auke a tafi da ita taga Afnan."
Sai a lokacin hankalin Kaka da Malam Iro ya kwanta ganin hidimar da Sarki yake masu da kansa,
    Hakan ya kuma tabbatar masu da cewa Afnan tana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali, 
    Hankalin *Kaka* ya kwanta tasaki jikinta tana cin arziki daga gidan Sarauta."
______________________________
Gida Wanda ya amsa sunan sa, gida ne irin na 'ya 'yan sarauta, kai ko a cikin 'ya'yan sarauta 'ya 'yan gata akeyi wa wannan kalar ginin gidan."
Sarki ne ya d'ebi wani babban fili a cikin yan kin cikin gidan sarautar ya sanya aka ginawa d'an sa kwaya d'aya tilo, Yarima kuma sarki mai jiran gado, domin yaci Amarci tare da gimbiya Afnan."
Gida ne Wanda Sarki  da kansa yake zuwa domin yaga shirin da ake tsarawa a cikin gidan."
Tun a waje zaka san an kashi dukiya, saboda masu tsaro ne, da wad'an da zasu kula da Yarima tare da gimbiya, ga sunan birjik, a ko ina kowa na hidimar gabansa."
A babban k'ofar da zaka shiga anyi babban gate an buruta sashen *Yarima Bassam Ahmad Moh'd* 
    Daga can gefe d'aya kuma sashen Afnan ne tare da kuyan ginta masuyi mata hidima."
   Wannan aiki ya yiwa Bassam dad'i, koba komai, nashi b'angare da ban yake,
 yanda zai ci ka renshi babu babbaka  yan da ransa yake so batare da sa ido ba ko kuma ta kura."
Afnan kuma ta k'ank'ame Jakadiya sai kuka take yi, domin kuwa Sarki yace" bada Anna za'a koma ba, ita tayi zamanta a tsohon gida, domin ta kula dashi."
Anna sai hak'uri take ba Afnan da cewa "ai ba rabuwa sukayi ba, kullum zata dinga zuwa tana diba lafiyar su, kasan cewar Anna ta sanya ido akan su ta fahimci babu jituwa tsaka ninsu,
      Dan haka ta d'auki d'amarar sai ta sanya jituwa  a tsakanin su, cikin hikima da daba ra."
Hakan suka tare a sabon gidan, inda gaba d'aya an zuba sabbin ma'aika ta da kuyangi."
 Bassam na b'an garen shi, ita ma Afnan tana b'an garin ta,
    Gidan yayi wa, Afnan kyau matuk'a, sai dai matsala d'aya babu kwanciyar hankali."
Kwanan su d'aya a gida tajita a takure, gashi gaba d'aya ma'aikan ta da aka zuba 
Bata wani  saba dasu ba."
Fitowa tayi domin ta zagaya gidan, ta d'ebewa idon ta  kewa."
     Wani b'angare tagani a can daban, Wanda aka rubuta masa sashen "Yarima Bassam Ahmad moh'd."
Get d'in wurin ya k'awatar da ita sosai, sai ta tsinci kanta da son shiga taga yan da b'angaren nasa yake."
Tafiya takeyi a hankali har ta isa bakin get d'in taja ta tsaya, domin a tunanin ta babu Wanda yasan ta a cikin basu gadin k'ofar."
Saiji tayi d'aya daga cikin su,yace "ranki ya dad'e barka da zuwa, yanzu yan zun nan kuwa yarima yafita."
Ajiyar zuciya taja tace " nasani dama akwai abun da zanyi a ciki."
Suka bata hanya ta Shige, tun daga hara bar b'angaren Afnan ta fara zuba ido tana kallo, a zuciyarta tana fad'in cab lallai masu kud'i suna abunda suke so."
Wata k'ofa tagani a ruf'e, wadda abun da aka rufe k'ofar dashi abun ka tsaya kayi ta kallo ne."  
Cikin rashin tsoro ta murd'a murfin k'ofar sai gani tayi ta bud'e,
    Sai da ta fara lek'a k'anta, domin ganin ko dai Bassam na ciki, cewa yayi ace baya nan."
Bata hango kowa ba, sannan ta shiga, har da 'yar Sallamarta d'auke a bakinta cikin siririyar muryan ta."
Mutuwar tsaye tayi ganin had'uwar falon, tsayawa lissafa abun da ke cikin falon b'ata lokaci ne, domin duk yanda naso na zayyane maku shi masu karatu, bama zan iyaba lol😜
Tafiya kawai take a falon tana kallo, tana fad'in Aljannar duniya, tana jinjinawa Sarki, sai yanzun ta tambatar da maimartaba ba k'ara min so yake yiwa Bassam ba."
Wasu k'ofofi ta hango har guda uku da alamar dukan su bedromm ne, sai ta tsinci kanta da son shiga kowa ne daga cikin d'akin domin ganin abun da ke cikinsu."
Bedromm na farko ta fara bud'ewa a hankali, ta fara lek'a kanta, ganin bata ga kowa a cikinsa ba, yasa ta kutsa ta shiga kai tsaye."
Mamaki ta shiga yi, tabbas an zuba dukiya wurin nan, tunda Allah ya halicce ta, bata tab'a ganin kayan d'aki irin wad'an nan ba."
Wani k'aton fridge taga ni a gefe d'aya Wanda yaja han kalinta domin frege d'in ya matuk'ar burge ta."
Wurin fridge d'in ta nufa tana kallo, hannun ta tasanya ta bud'e shi domin ganin









