Showing 63001 words to 66000 words out of 90241 words

Chapter 22 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9837

shiga cikin wani yanayi na azababben ciyon ciki da kuma zubar da jini cikin k'ank'anin lokaci ciwo ya d'auke."


"Tabbas anyi haka tana gama shan maganin da hajiya zainab ta bata ne abun ya faru."


Kuka tasaki wiwi har da buga hannunta a kan kujerar mulkinta."


"Hajiya zainab ta d'auke mata jin dad'in rayuwa kenan, ta b'ata mata ma haifa, kuma tayi mata asiri bata iya zuwa kusa da mijinta,
ashe yau dararta tayi?"


Tayi Alk'awarin d'aukar fansa, ta lura a duniyar nan babu Wanda takeso kamar Yazeed,
Zatayi sanadinsa sai tasan zafin yau darar da tayi Mata."


Ta dubi jabo tace "kina iya kisa?"


"Kisa ranki ya dad'e?"
Wannan ba aiki na bane sai dai na tura masa da sammu."


Zai zamo dashi da babu duk d'aya?"


Inno tace "haka ne ranki ya dad'e ki yarda a dasa mata bak'in cikin da baya gushewa har ta mutu tanaji tana gani amma ba yarda zatayi."


Kukan da saratu takeyi ta daina."


Tace shikenan yanzun takaini ta baro yarinyar can ita zata haifi 'ya'ya bandani."


"Ranki ya dad'e ki kwantar da hankalinki, ai kema ramawa zakiyi, mulki ya gaji haka, dole sai an zubar da jini sannan sai an d'auki mataki kwankwara sai ancima buri."


Saratu tace duk abunda mukeyi a tsaka ninmu ya zama sirri."


"Angama ranki ya dade."


Jibo yanZun warin da suka saka min ya za'ayi dashi?"


Ganin tulu tayi jibo ta d'auko. Tsoro ya kama saratu."


Jibo tace "asirin da sukayi maki ne, ranki ya dad'e cikin rijiya suka jefashi,
Za'a zuba ruwa a cikin tulun nan ki mayar dashi ruwan shanki insha Allah zaki warke."


Ganin hakan sai ta wangale baki, cike da jin dad'i."


Saratu tace "zaki iya damk'a min yarima a hannuna sai yanda nayi dashi."


Jibo tayi shuru ta kasa magana, saboda abun da kamar wuya."


Tace ranki ya dad'e bari mu gama da aikin da kika ce a fara a kan Yazeed d'an hajiya zainab."


Haka ne taji dad'i a ranta,
Bata da wani buri a yanzun sai ganin bayan hajiya zainab, tunda tayi mata lahani ta rasa mahaifar da zata haifawa yarima d'a Wanda zai gaji sarauta a gaba."


Ta fad'i da k'arfi tace hajiya zainab bakisan ko wacece saratu ba sai kinyi nadamar abunda kika aikata min."


******************


Saratu ke tafiya cike da k'asaita zata nufi sashin hajiya Zainab,

Alhaji Aminu ya kira wayarta yake CE mata "ya yaji shuru kwana biyu bata nemeshi ba, kuma bayan ta d'and'ana masa."


Cewa tayi "Alhaji Aminu ka d'an saurara min kwana biyu domin kuwa yanzun yarima ya dawo,
Koni kaina ina kewarka da yawa, yanzun haka wayar da mukeyi da kai duk ka d'aga min hankali najini cikin wani yanayi wanda a yanzun haka duk najik'e pant d'ina."


Alhaji Aminu yasaki wata dariya ta yaudara har da wani Jan iska a bakinsa a kunnenta,
kamar Wanda yaci yaji, sai gaba d'aya hankalin saratu ya tashi sai da tanemi wuri ta zauna kusan minti Biyar ta samu natsuwa sannan ta mik'e taci gaba da tafiya ta nufi wurin hajiya zainab."


Kai tsaye tashiga d'akin hajiya zainab batare da sallama ba.
Ta Tarar da hajiya zainab zaune a kan kujerar mulkinta,
Kai tsaye gefen kujerar da hajiya zainab take zaune ta tafi ta zauna. Tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya."


Saratu ta gaida hajiya zainab,
Cike da mamaki hajiya zainab ke kallonta, tashiga tunanin wata k'ila tasamu lafiyar jikinta Dan haka take d'agawa da lafiyarta."


Kenan ta gano ita tayi mata asiri kenan?"


Hajiya zainab tacewa saratu "lafiya."


Saratu tace "lafiya ta wuce haka mekike son gani?"


Maganar ta bata haushi, amma tace mata "har yanzun cikin baisamu ba?"


Saratu tayi murmushin ta kaici tace "ai ciki lokaci gareshi."


Hajiya zainab tace "naji ance yarima aure zaiyi?"


Murmushi saratu ya kau ranta ya kuma b'aci tace " ta dubi hajiya zainab cikin ido tace "tazo mana ai yanada damar yin haka tunda har kwarori yana iya ajiyewa,
Kuma ni bazan juya masu mahaifa ba Dan karsu haihu da yarima."


Hajiya zainab ta har zuk'a tace "magana zaki fad'a min?"
Na d'auka kinxo ne Dan musan shirin da zamuyiwa kishiyarki Dan naji ance kyaunta tamkar...."
Ki kwantar da hankali in taimakeki."
[3/5, 9:33 PM] Ummu Safwan WS P1: πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*54*












Dariyar da saratu keyi ne, shi ya dakatar da hajiya zainab da zancan ta."


"Kina nufin wurinki zan nemi taimako?"
Lallai ma kuwa to kicanza tunani, Auren yarima kuma da auren sa ya aure ni ko baki da labari ne hajiya zainab?"


Hakan ya nemoni bani na nemoshi ba, ya aure ni saboda da so da k'aunar da yake Mani."


Mik'ewar da hajiya zainab tayi shiyasa Saratu tayi shuru tana hararar ta."


Itama saratu ta mik'e tsaye sukayi gaba da gaba, saratu tace " har kingaji da jin maganata, to ni zan wuce,
Maganata ta k'arshe dake itace ki kula da *zuciyarki*."
Sannan saratu ta fito a fusace."


Hajiya zainab ranta yayi bak'ik'irin kamar bak'in leda. Tashiga tunanin kalaman da saratu ta fad'a mata. Bare kalmarta ta k'arshe *kikula da zuciyar ki* me take nufi zatayi?"


Da sauri tasa aka kira mata sarkin gida. Yashigo da sauri ya zube."


"Ranki ya dad'e gani."


Saratu tazo sashin nan yanzun, tayi min wulak'anci har da yimin gatse!!
wai in kula da zuciyata.
Me take nufi da hakan?"


"Ranki ya dad'e ba komai so take ta gaya maki kifita a harkarta, saboda ranki zaita b'aci da irin matsayin da zaita k'arayi."


"Oh shi yasa naganta cikin k'asaita ga komai warwas, lallai ina ganin ta fara samun lafiya."


"Zan tarwatsa ta, zan ganar da ita ni ba abunkiyar yinta bace,
Yarinya k'arama ta neme gasa min gyad'a a hannu."
Me ya kamata inyi yanzun?"


Dawa take ma'amala yanzun Dan na lura tasan komai a kanmu, naga tafara ji da kanta, inason musguna mata...."


"Ranki ya dad'e ki natsu. Da kyau kadda saratu ta tayar maki da hankali ita d'in banza."


Yau d'in nan ba sai ankwana ba muna iya sanyawa tabar duniyar gaba d'aya."


Hajiya zainab ranta yayi fari tasaki dariya mai sauti."


****************


Anna tashigo da k'ofi a hannunta, ta mik'awa Afnan tace ongo karb'i ki shanye."


Afnan ta k'arb'a tana turo baki, alamar shagwab'a ta shanye,


Anna ta kuma zube wani garin magani cikin k'ofi ta d'auko Zuma da Lipton ta zuba ruwan zafi, ta girgije ta kuma mik'a mata,
Shanye wannan yanzun."


Ta k'arb'a ta rik'e tak'i kaiwa bakinta.
"Anna ki barni yau in huta dan Allah."


"Hutu."


Inkikaga kin huta to sainaga an kaiki kinsamu ciki."


Afnan ta turo baki tace a ranta "ni Anna ba wannan ya dameniba yarima baya sona."


Anna tace "sha mana tawan, kinsan inaji dake Afnan ina maki sha'awar yarima."


nan da nan taji son yarima da k'aunar shi tare da ita, batasan lokacin da tafara sonshi ba."


Ta tuna da ranar farko da tafara ganinshi. Bata tab'a jin tsoro wani mutum ba sai a kanshi."


Afnan na kusa da Anna gyarata akeyi kullum saita sha maganin tsari irin Wanda take bawa yarima. Duk muguntar mutum sai dai ya buga ya barsu."


Afnan kullum tunanin Bassam takeyi, tun lokacin da aka sanya masu rana bata sake ganinsa ba har yanzun da yarage saura sati d'aya a kaita."


Tana yawan tunawa da irin salon soyayyarsa,
Lokacin da yasamesu lambu ita da sadi."


Sadi na yawan tambayarta wai meye tsakaninsu da yarima, sai dai tayi masa dariya tace bakomai."


Tayi murmushi da ta tuna lokacin da ta fad'awa Sadi zata tare a gidan yarima a matsayin matar sa."


Yayi fushi sosai, yace "ke dai Aminiya fushi nakeyi dake,


Duk tsawon lokacin da muke tare kink'i fad'a min yarima mijinki ne,
Yanda naga yarima yana shige maki nayi tunanin sonki yakeyi har nafara jimaki dad'i. Ashe mijinki ne gaba d'aya."

Tace "yi hak'uri Amini labarin yana da tsayi. Kabari sai mungama hidiba zan gaya maka komai."


Sai a lokacin yayi dariya yace "na hakura Aminiya, ya shirye shiryen biki kinsan gobe ne za'ayi dinner


*Ranar dinner* an shirya a lokacin Bassam kasa b'oye farin cikinsa yayi, duk Wanda yaganshi yasan yana cikin farin ciki Wanda ba'a tab'a ganinsa a fuskarshi ba."


Abokanan shi da sukayi karatu a England duk sun hallara duk wani aboki nashi ko wani Amininsa ya gaiyatosa domin su shaida Afnan a matsayin matarshi."


Haka maimartaba, ya gayyato yan uwa da abokanan arziki."


Amarya Afnan ansha gyara sai wani shege takeyi, kusan wata d'aya ana gyarata. Sai da Anna tace "kar ayi mata halawa saboda yanayin fatar ta."


Taci ado cikin wani material pink and blue, doguwar riga, sai wani gyalli yake fitarwa, gaba d'aya jikinta gwala gwalai ne aka yimata ado dasu."
Duk Wanda yaga Afnan a wannan lokacin bazai ganeta ba. Saboda tayi kyau har ta gaji."


Anna sai yaba kyaun 'yarta takeyi tana zuba mata kirari."


Bassam shima ya shirya tare da abokanansa yasanya wata dakakkiyar shidda blue ya sanya hula pink da takalmi da agogo,
Kuzo kuga bassam yanda yayi kyau kunsan dama kyakkyawa ne."


A cikin gidan sarautar maimartaba ya shirya masu dinner, kowa ya hallara Amarya da Ango kawai ake jira."


A can na hango Bassam rungume da Afnan suna k'arasowa, gaba d'aya kallon ya koma kansu.


Yan jarida da yan sa ido kowa sai d'aukarsu photo akeyi."


Wurin zamansu suka nufa na Alfarma suka zauna, ko wannensu zuciyarshi cike da farin ciki.


Maimartaba dake zaune gefe d'aya akan kujerarsa ta mulki tare da abokanansa sarakuna, kowa sai yaba zab'en yarima yakeyi, maimartaba yaji dad'i sosai."


Hajiya zainab bata tab'a ganin Afnan ba amma dai tanajin labarin irin kyawonta,
Sai yanzun da tayi ido biyu da ita, sai da gabanta ya fad'i saboda yanda take hasashenta ba haka ta gantaba."


Wani bak'in ciki ya taso mata,
Ta mik'e da sauri ta bar wurin domin bazata kuma k'ara kallontaba,
Tabbas akwai Jan aiki gabanta,
Idan tayi wasa wannan matar yarima sai ta amshe mata kujerar ta ta sarauniya a gidan nan."


Tashiga kwad'awa sarkin gida kira."


*********
Saratu kuma babu abunda takeyi sai aikin kuka,
Inno na kusa da ita tana bata hak'uri,


Inno tace "ranki ya dad'e kitashi ki shirya ki d'au kwanliya nasan babu abunda matar yarima zata nuna maki."


Haka kuwa akayi saratu ta shirya takira mai kwalliya tayi mata, tare da yan rakiyarta suka nufi wurin dinner."


Tana zuwa wurin tayi ido biyu da yarima da Afnan zaune fuskokinsu cike da farin ciki suna kallon wasan gishiri da maimartaba yasanya aka shirya kamin a fara gudanar da dinner din."


Saratu na ganin Afnan batasan lokacin da hawaye ya fara zuba a idontaba
Juyowar da Bassam zaiyi sukayi ido biyu da ita, ta juya da sauri ta bar wurin idonta sai zubar hawaye sukeyi."


Afnan ta lura da inda yake kallo taji kishi ya kamata,
Ta rik'o hannunshi ta matse da karfi, sai da yad'an runtse idonsa, yana kallonta, cikin magana kasa kasa yace menayi kuma?"


Bata kulashi ba saima hararasa data warga masa, wadda ta k'ara mata kyau."


Yayi murmushi, yace "ayi hak'uri amarya yarima tuba nakeyi idan laifi nayi."


Bata kulashi ba, ta kawar da kanta gefe."
Yasan kishine ke damunta, saima yaji dad'i a zuciyarsa yace " a she tana sona."


Anci Ansha an zubar da naira biki na d'angata." Yarima bassam


A can na hango yan group din ummu safwan hausa novels
Dana
Tambarin sarauta friends
Sai wasar baki sukeyi suna so suje suyi sulfie da Afnan amma fadawa sun hanasu k'arasawa wurin,


Nida ke kusa da Afnan ina d'auko rahoto sai gwalo nake masu😜


A can na hangosu sunyi group wuri d'aya asanya shinkafa a tsakiya da naman kaji saici sukeyi suna dariya. Su ooo da ooo d'an kwalin kansu da gyalen jikinsu duk sun cire basu saniba."


🀣🀣🀣🀣🀣
[3/6, 8:11 AM] Ummu Safwan WS P1: πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*55*












Amarya Afnan gobe dai za'a kaita gidan Bassam gyara kam tashashi a wurin Anna."


Maimartaba yaturo a kira masa Anna,
Bata b'ata lokaci ba ta isa wurin maimartaba."


Yana fada zaune tare da manyan bak'insa. Yana ganin tafowar Anna ya mik'e yanufi wani babban falo."


Anna na ganin hakan tabi bayanshi domin tasan zancanda zasuyi ba k'arami bane, kuma yana da muhimmaci."


Ta zube tana gaida sarki, ya saki fara'a sosai."


Sannan yace "ina d'an naki?"


Tace "yana lafiya ranka ya dad'e."


"Kinsanfa yarima nakine zurfin ciki yake min bansan gabansa ba
ban kuma san bayansa ba." Natsuwar sa da hankalinsa a kullum ina maki godiya domin kece kika d'ora shi a kan tarbiya mai kyau."


Babu abunda zan saka maki dashi Anna sai dai intayi maki godiya da addu'ar har zuwa ranar da zanbar duniya."


"Nadamu kwarai da rashin haihuwar da baiyi ba har yanzun."


Matarsa tayi shekaru biyu amma yanzun shuru bata haihuba."


Yarinyar nan Afnan ta kwanta min a rai kamar yadda naga kema ta kwanta maki."


Tun lokacin da aka kawota a gidan nan ina sane dashi ya banzartar da ita baya kulata, bansan manufarsa akantaba, bana so yaje ya cutar da ita,
Na lura yarinyar nan tana da wauta sosai

Ina Neman Alfarma a wurinki. Ki taimaka da taimakon da kika saba kibita can sashinta Ku zauna har ta saba da gurin."


Kuma kisamin ido da abubuwan da ke faruwa saboda take taken hajiya zainab ya fara bani tsoro."


Anna dai shuru tayi duk halayyar Bassam da ya zayyana mata itama abun na damunta,
Amma hakan da ya yanke yayi mata dad'i, saboda ita ma tana son sanin abunda ake ciki."


Zatayi k'ok'arin Kare Afnan daga shairin hajiya zainab, tana jin haushinta yanzun kuma lokaci yayi da zata dakatar da ita daga mugun nufinta,
Shiyasa ta duk'ufa wurin bawa Afnan maganin kariya Wanda take bawa yarima."


Sun rabu da sarki a kan zasuyi abun cikin sirri dama jiran hakan Anna takeyi tashiga fadar sarki da hujja maik'arfi."


*****************


Yarima ya kira sadi yace "ya gaya masa matar da yake so ya aura."


Rufe idonsaπŸ™ˆ yayi wai yaji kunya

Bassam yaja dogon tsaki "mts!!


Ka gani bana son sakarci, ka fad'a min gobe zan sa a d'aura maku Ku dukanku, ko ba ka so?"


Ya rik'e hannayensa wuri d'aya tare da nuna murna da ya bayyana a fuskarsa.


Yace "ranka ya dad'e mairo da talatu sunake so."


Yarima yace
" kuyangun Afnan?"


"Eh ranka ya dad'e."


"To angama gobe zasu zama naka, sai dai inaso ka shirya yanda zasu rik'a zuwa wurin Afnan kullum."


"Angama ranka ya dad'e godiya nakeyi."


Yarima yace "kadai canza hali mata ba'a sake masu fuska sai su neme hallakaka."


A'a nikam wasa zamu rik'a yi muna rawadasu,
ina zan iya rayuwa ina had'e sai kace su ba mutane bane."


Bassam yaja dogon tsaki yace shikenan matsalata da kai baka ganewa."


Abunda nakeso da kai karka yarda ka mayar da sashin Afnan daddalin hirarka, idan hira kakeso kazo muyi, Dan bazan dauki iskancinka ba."


"Dariya Sadi yayi yace "ai kagama mai wuyar tunda kabani abunda nakeso."


*Washe gari anshirya k'ayataccen biki tarewar Afnan gidan yarima a ranar kowa ya tabbatar yanzun yarima yayi auren kyau,


Ansan manya da auren mata masu kyau,
Musamman ake shiga gari neman zuri'a masu kyau, domin. A zo a bawa sarki labari aje kuma a auresu." Amma abun mmki Dan sarki ya auri macce mai suffar biriπŸ’


Talatu da mairo an d'aura masu aure da Sadi, kowa yana cikin murna da farin ciki."


Anshirya Afnan cikin lace ne ko material ne baza gane ba.


Purple ne da peach ta sha kwallita mai kyau. Ita kanta data ganta a madubi sai da taji tsoro, saboda bata gane kantaba."
Kyanta yayi yawa."


Anna sai nasiha take mata na yanda zata zauna a gidan mijinta lafiya.


Taci gaba da nuna mata yanda zata tarbi yarima idan yashigo da bincin sa da duk wani abu da tasan hak'k'ine a kan mata tayiwa mijinta, mussam yarima da bakasanin gaban sa bare bayansa."


Kuka takeyi sosai ta rik'e Anna,
Anna tace ki daina kuka Afnan zan sameki a can domin a tare zamu zauna."


Babu abunda yake damun Afnan sai kishin saratu, idan ta tuna da yanda taga yarima a wurin dinner ya tsurawa saratu ido, sai ta dinga jin wani zafi a ranta."


Cikin wannan tsananin damuwar ne aka d'auki Afnan aka kaita sashin yarima."


Gabaki d'aya taga ancanza alatun tsarin wurin.


Can k'urya aka kaita aka zaunar da ita kan kilishin da ke shimfid'e k'asa ga tuntu zube a gurin masu laushi, kamshi kawai ke tashi."


Taji lokacin da Anna tace "wai ina yarima?" Aka ce yana tare da saratu.'


Ta d'aga murya tace "agaya masa Amarya ta iso."


Wani bak'in kishi da haushi yarima ya kama Afnan."


Duk k'ok'arinta da tayi Dan kada tayi kuka abun ya gagara hawaye suka zubo mata sharrr a kan fuskarta. Babu Wanda yagani saboda jikinta a yafe yake babu Inda ake ganin fatarta."
[3/6, 8:19 AM] Ummu Safwan WS P1: πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*56*










Yarima a d'akin saratu, sai lallashin ta yakeyi, yana nuna mata da cewa ta kwatar da hankalinta bazai tab'a wulak'an tataba."


Babu abunda takeyi sai aikin kuka."


Tana kuma marairacewa a jikinsa,
Wanda jinginawar da tayi a jikinsa,
jinshi yakeyi kamar an d'ora masa wani k'aton dutse jiki."


Ganin bata da niyar hak'ura yasan yashi zame jikinsa daga gareta. Ya mik'e tsaye, yace mata sai da safe, idan kingama kukan kiyi Addu'a ki kwanta, bai kuma bi takantaba yayi fitowar shi."


Karo yaci da bayi wad'anda Anna ta aikosu kirashi."


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login