Showing 72001 words to 75000 words out of 90241 words

Chapter 25 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9839

👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*60*












Takai gurfane a gaban Sarki idonta yana mai zubar da hawaye tace "ranka ya dad'e ka taimaka min Yazeed ya farka ya kuma yashiga cikin wani sabon yanayi, ka taimaka min mukaishi asibiti."


Maimartaba ya mik'e tsaye da sauri, ya kalli yarima dake zaune yace "tashi mutafi yarima."


Sai a lokacin hajiya zainab ta lura da yarima zaune a wurin, ido biyu sukayi sai da taji gabanta ya yanke ya fad'i."


Yarima ya mik'e tsaye yabi bayan mahaifin nashi suka nufi sashin hajiya zainab."


Yanayin da sukaga yazeed cikinsa abun ya firgita su, musamman maimartaba yace hajiya zainab wai meke faruwa da wannan yaron ne?" Meyasa meshi?


Yarima kuma yana gefe baiyi magana ba, a zuciyarsa yana fad'in "kad'an kikagani, tunda a zuciyarki mugunta kika sanya a gaba, babu Allah a cikinta."


Maimartaba bai rufe bakiba, sarkin gida yashigo da gudunsa,
Ganin maimartaba yasa yaja ya tsaya wuri d'aya had'ida zubewa k'asa yana gaisuwa."


Maimartaba ya cika da mamaki yabi sarkin gida da ido, yace
"sarkin gida a d'akin hajiya zainab batare da neman ixiniba?"


Ya dokawa sarkin gida tsawa yace "waye ya baka izinin shigowa har cikin nan." Lallai yau zansanya a hukunta ka."


Jikinsa na rawa zaiyi magana, hajiya zainab tayi karaf tace "ranka ya dad'e nice na aika akira munshi,
ba laifinsa bane nice nabashi izinin shigowa


Sai a lokacin Bassam yayi gyaran murya yayi magana yace
"Abba kabarshi kawai akan yanda tace, mu fuskanci abunda ke gabanmu."


Maimartaba ya maida kallonsa ga Bassam yace "yanzun d'aukarshi za'ayi akaishi asibiti kenan a dubashi likitici su fahimci abunda ke damunsa?"


Bassam ya girgiza kai yace "A'a Abba ciwon Yazeed bana asibity bane, adai nema masa maganin gargajiya."


Sarki yace, "to meye mafita yarima?"


Hajiya zainab babu abunda takeyi sai zafgawa yarima harara idan taga zasu had'a ido sai ta waske ta k'ak'aro murmushin dole."


Duk abunda takeyi yarima na kallonta ta gefen idonsa."


Yace "Abba ninasan wani mai bada magani, irin wannan ciwon da yazeed yakeyi,
Kuma hajiya zainab tasan shi,
Sarkin gida ma yasanshi."


Da hajiya zainab da sarkin gida, suka kashe kunne suna sauraron Bassam."


Bassam ya kalli hajiya zainab yace "kicewa sarki gida ya d'aukeshi ya kaishi wurin wanzam."
kinsan yafi kowa sanin yana aiki sosai aikinsa kamar yankan wuk'a."


Zaro ido sukayi waje a tare, duk da sanyin Ac dake d'akin bai hana hajiya zainab fitar da zufaba,
A ranta take cewa "wannan yaron akwai abunda yake nufi damu a gidan nan,
Kar dai ace duk abunda mukeyi yana sane dashi."


Maimartaba yace "Alhmdulillah Abu yazo gidan sauk'i kenan hajiya zainab sai ya d'aukeshi a had'ashi da fadawa sutafi a kaishi, Allah yabaka lafiya yazeed,"


Bakinsu na rawa suka amsa da Amin."


Bassam ya kuma kallon sarkin gida, dayaketa zarar ido kamar wadda yayi k'arya, sai zufa yake fitarwa yace "nayi magana bakace komai ba,
Ko ka manta wanzam d'in danake nufi ne?
nafad'a maka shi dala dala, yanda zaku fahimta."


Sarkin gida yace Allah ya taimakeka ya k'ara maka lafiya mungane shi, ba sai ka fad'eshi ba."


Bassam yayi murmushin mugunta yace "yawwa tunda kaganeshi a can zaka kaishi,
Ya kalli maimartaba yace Abba mutafi kawai, sun fahimceni, zasu maganci matsalar."


Sarki yabiyo bassam suka fito yana Sanya mashi Albarka, suka rabu da juna kowa ya nufi sashinsa."


Hajiya zainab na ganin fitarsu, ta sauke ajiyar zuciya. Ta had'e rai
ta kalli sarkin gida tace "sarkin gida ina zarginka da ballasa sirrinmu a wurin yarima."


Sarkin gida, ya kai gabanta ya gurfana yace "wlh tallahi bantab'a ballasa sirrinki ga kowa ba, ki yarda dani."


Na dad'e ina fad'a maki halin yarima wanda baki saniba ranki ya dad'e."
Zaki nefa, wlh har yafi zaki bala'i,
Ni ina ganin kamar da Aljanu yake yawo masu d'auko masa rahoto."


Hajiya zainab ta mik'e tsaye ranta b'ace "tace idan shi zakine to ni damisa ce, bada Aljanu yake yawoba ko da ifirito sarkin Aljanun, yake yawo
na rantse da Allah sai naga bayan shi."


Kuma muje zuwa dani dashi,
har da Aljanar matarsa, ita kuma abunda nayiwa saratu sai na lunka mata biyunshi."


Sarkin gida yace "ranki ya dad'e kibi komai a sannu kar muje wurin Neman gira murasa ido kisani komai lokaci gareshi."


Ta daka masa tsawa tace "yi mun shuru!!
Lokacina bazai tab'a wucewa ba a cikin gidan nan nagaji saurata gaba da baya, don haka dole ne najuya gidan nan da abunda ke cikinsa, yanda naga dama."


Sarkin gida ya had'iye miyau masu zafi a mak'oshinsa shi dai yasan abunda yake hangowa a wurin yarima."


Yace "haka ne Allah ya huci zuciyar sarauniya."


Yayi mata sallama ya fita,
kwata kwata ya manta da abunda ya kawoshi wurinta."


***************


Afnan na wurin Anna kwance yau batajin dad'in jikinta.
Anna tabata magani tasha dakyar tasamu zazzab'in ya lafa tasamu damar yin barci."


Farkawar da zatayi, taji a duniya babu abunda takeso sai k'amshin turaren Bassam."


Mik'ewa zaune tayi, Anna tace "d'iyata kintashi?"
To ya jikin naki?"


Tace naji sauk'i Anna,
Bara na shiga daga ciki nayi wanka sainayi sallah."


Anna tace "to afito lafiya."


Cikin tafiyarta mai cike da natsuwa,
ta isa d'akin nasu,
Ta tarar da bassam kwance akan gado yayi rufda ciki da Alama ya jima da dawowa."


K'amshin turaren jikinta yajiya ya tabbatarwa kansa itace,
Ya tashi zaune had'ida bud'e hannayensa alamar tazo gareshi."


Da sauri ta isa wurinshi ya maida hannunsa ya rufe, ya rungumeta,
dama tanaso tashak'i k'amshin turaren jikinsa."


Tana rungume dashi tayi lamo a jikinsa tana shak'ar daddad'an k'amshin jikinsa, tana lumshi idonta,
Shi kuma sai kissing d'inta yakeyi a wuya a kuma baki da kuncinta, yana Neman cire mata riga yasha Brest


Idonta ya sauka akan kwalbar giyar dake gefen gado ajiye da alamar yanzun ya k'are shanta."


Ta yunk'a ta kwace jikinta daga jikinsa, a dai lokacin da ya fara fita daga hayyacinsa, yana Neman zuge mata zif d'in rigarta."


Tashiga ja da baya idonta na zubar da hawaye,
Nufota yayi yana fad'in Angel meke faruwa?"
Pls karki gujeni a dai dai wannan lokacin,
Mena maki?" Me kike so?"


Angel kina Azaftar dani da soyayyarki, shin har yanzun baki yafe min abunda nayi maki ba?"


Kizama mai yafiya gareni, nayi maki Alk'awarin duk yanda kikeso ki ganni na zama zan zama in har zaki daina guduna."


Sai a lokacin hawayen fuskarta suka tsaya cak, ta tsureshi da ido, ta tabbatar da abunda yake fad'i da gaske yakeyi har cikin zuciyarsa yake fitowa."


Yabata tausayi sosai, taje kusa dashi ta zauna."


Yabita da ido yana kallonta.
Yace "Angel kin Amince dani bazaki k'ara gudunaba?"


Ta d'aga kanta alamar "Eh."


Tace "Amma da sharad'in bazaka kuma shan wannan abarba ta nuna masa kwalbar giya."


Ya tsurawa kwalbar giyar ido yana kallonta,
yana tuna lokacin da yafara shanta tun yana England makaranta,
Dama bak'in ciki da b'acin rai yake sanyashi ya shata."
Mudun ta Amince dashi ta tarairayeshi ta nuna masa so a gaban kowa babu abunda zai kuma yi da giya."


Ya kalleta yace Angel nayi maki Alk'awari daga yau daga yanzun bazan k'arashan barasaba, in dai hakan zai sanyaki farin ciki."


Batasan lokacin da ta rungumeshi ba, tashiga aika masa da kiss kota ina."

Shima yashiga mayar mata dama a buk'ace yake, nan da nan ya cire mata kayan jikinta, shima ya cire nashi, ya haye kanta yashiga aikin nashi."


Ba laifi Afnan tayi dauriya, wadda bassam da kansa sai da yayi mamakinta."


Bayan sun gama, bassam yaji dad'i sosai ya kuma samu gamsuwa,


yaji wani sabon sonta da k'aunarta sun k'aru a zuciyarsa,
Ya jawota ya rungumeta, yace nagode maki Angel hak'ik'a ke Alherice a rayuwata."


Kinsan Albishir d'in da zan maki?"


Ta rufe fuskarta had'ida girgiza kai alamar "A'a."


Yace "gobe ki shirya zankaiki wurin kaka da kaina,
Ki ganota.
Dolene a jijjinawa Kaka tareda yimata babban kyauta, Allah ya biyata yasa ta gama da duniya lafiya."


Sann kuma Albishir na biyu. Nayi maki _passport_ zamuje England kihuta."


Afnan taji dad'i ta kuma rungumeshi tace "Nagode my prince,
Allah ya barmu tare."


Daren yau sunfarantawa junansu sunji yarda junansu dad'i Wanda Afnan dauriya ce kawai takeyi, Dan ta jigata sosai."


Haka sukayi barci cikin farin ciki Afnan ta matsu safiya ta waye mata."


****************


Shiri sukeyi Bassam cikin dakakkiyar shadda ruwan Zuma ya sanya hula itama ruwan Zuma da ogogon gwal sanye a hannunshi yayi kyau matuk'a."


Itama Afnan taci ado da gwala gwalai tasanya super English Atamfa tayi mata kyau, ta d'auko Alkyabbarta ruwan zuma ta sanya, sunyi kyau matuk'a,
Basaam yace "Angel kinganki kuwa kinyi kyau, inajin kishin kadda wani ya gane min ke a haka."


Tayi murmushi tace "ai kafini kyau prince,
Ta kawar da maganar da cewa "amma ya kamata muje muyiwa Anna sallama."


Haka suka jera suka fito gwananin ban sha'awa."


Suka shiga d'akin Anna sukayi mata sallama,
Ta dubesu kwanin ban sha'awa, tayi masu Addu'ar dawowa lafiya, had'ida bawa Afnan turamin Atamfofi takaiwa Anna saura kuma ta rabawa yan uwa da abokanan arzik'i."
Ta d'ur k'usa k'asa tashiga godiya ga Anna,
Anna ta mik'ar da ita tsaye tace "ki daina yimin godiya Afnan a rayuwata babu abunda bazan makiba."
Kicewa Kaka ina gaida ita saina zo."


Haka suka fito d'akin Anna cike da murna, suka nufi wurin maimartaba, tsakanin sashin su Dana maimartaba akwai 'yar tafiya,
Suna tafiya suna hira cike da nishad'i."


Saratu sukaci karo da ita tafito wani lungu sai waige waige takeyi kamar bara gaskiya."


Wuri d'aya taja ta tsaya ganin yarima ya tsaya yana kallonta cike da tuhuma,


Har ga Allah ya manta da ita, idan ba ganinta yayiba,
Kuma duk lokacin da ya ganta saiya tsinci kansa cikin yanayin rashin yarda da ita.
itama ta daina bibiyarshi kamar yanda tasaba."


Cike da tuhuma yake kallonta yace "daga INA kika fito a nan?"


Ta dake tace "ranka ya dad'e nafito ne domin nasha iska."


Ya kafeta da ido yana karanto rashin gskya a tare da ita."


Afnan nan gefe tana kallonsu kishi duk yacika mata zuciya, jitakeyi kamar ta fashe."


Inda yaga tafito nan ya maida idonsa yana kallo,
Wani mutum ya hango ya juya baya yana tafiya,


Ko a mafarki yaga mutumin yasan kowaye, shi,
Alhaji Aminu ne, ko dayake bayansa kad'ai yagani."


Yayi murmushin nan nashi na gefen baki yace "wancan fa?
Waye shi?
Daga INA yafito?"


Ta juya ta kalli wurinda yake nufi, hango Alhaji Aminu da tayi shiyasa gabanta ya fad'i,
Amma dayake 'yar duniya ce,
Ta dake tace "ranka ya dad'e ni banga kowaba, bayan wancan mutumin dake tafiya."


kuma a rayuwata bantab'a ganin halitta irin tashiba sai yanzun da ka nuna minshi."


Ya kuma yin murmushi yace "karki damu kishiga ciki,
Fita zanyi da Angel idan muka dawo, inaso zanyi mgna dake."


Bata bashi amsa ba, tarab'ashi ta wuce cike da jin zafinshi, yana nuna fifiko a tsakaninsu da wancan Aljanar."
[3/6, 9:47 AM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*61*




_hmm mutum ba'a iya masa, halin mutum sai shi_
_ina ganin fa rubuta littafin nan ba wani yasanya niba, nice naga dama na sanya kaina, labarina a rubuce yake nariga da natsara abuna. To meyasa akeson ayimin haka ne?_
_pls dan Allah kurabu dani kubarni naci gaba a yanda natsara labari_
_idan kuma kinka inda baiyi dai da yanda kikesoba, to ki kyara a ranki."_
_ko kuma ki rubuta naki_ _labarin, amma idan aka nemi a takemin duga dugai to gskya za'a samu Matsala danifa, saboda bana da hak'urin da juriya ina gani aneme shige min a hanci_ _afa kiyayeni ehe_😎












Ya juya kalli Afnan dake tsaye nesa dasu dan gudun karta jiyowa kunnenta abunda zai b'ata mata rayuwa,


Yaga taci magani. Ta had'e fuska ba fara'a a tare da ita,
ya k'araso wurinta ya rik'a hannuta had'ida d'an matsashi kad'an yace "Angel meye abun had'e rai kuma?"


Bata tanka mashiba illah ma ta fisge hannunta, ta shige gaba,
Murmushi yayi yabita a baya, yanajin dad'i a ransa saboda ya hango kishinsa k'arara a idonta."


Gabda zasu shiga fada, taja ta tsaya ya cimmata suka jera gaba d'aya fadawa na ganinsu suka take masu baya had'ida zuba masu kirari."


A gaban maimartaba suka zube, suna gaisuwa."


Cikin jin dad'i da murmushi d'auke a fuskar sarki yake amsa gaisuwarsu
Tareda sanya masu Albarka."


Kallon Afnan sarki yakeyi yana anyanawa a zuciyarshi yana fad'i "ikon Allah, Allah mai yanda yaso, a duniya ana kama,
Da ace 'yar Alhaji ibrahim na k'asar nan,
da babu wanda zai Hana ya rik'e Afnan yace itace."


Saboda suna matuk'ar kama da Amininsa har dariyarsu iri d'aya da d'an murmushin da Alhaji Ibrahim yakeyi idan suka je wurin da yakejin kunya,
Sak irinshi Afnan takeyi, Allah mai yanda yaso, aduniya ana kama."


Bassam ya katse masa tunani yace "Abba zamutafi gidan kaka yanzun kayi mana Addu'a, sannan kuma na shirya komai gobe zamu wuce England, jirgin k'arfe 8:am zamubi."


Maimartaba yace Allah ya tsareku ya kareku a duk inda kuke ya kuma duban Afnan yace "d'iyata a dawo lafiya."
Suka fito tare da fadawa wad'anda zasuyi masu rakiya."


Motoci hud'u aka cika da fadawa masu rakiya gamida motar su yarima biyar kenan."


Motarsu Afnan ce tsakiya sannan gabansu da bayansu duk motocin fadawa ne, sai jiniya ake masu."


Isarda sukayi k'ofar gidansu kaka cike yake da mutanen d'auren Auren malam Nura da Maryam."


Jin jiniyar da sukayi ne yasa kowa ya raja'a ya maida hankalinshi wurin kallon motocin, ganin *tambarin sarauta* lik'e a kowace mota ya tabbatar masu da yayan gidan sarauta ne."


Malam Nura dake tsaye tareda abokanansa yana ganin motocin gidan sarauta sai da gabansa ya yanke ya fad'i."


Tsayawar motarsu yarima fadawa suka fito da gudu suka nufi motarsu, suka zagayo wurin yarima suka bud'e mashi yafito cike da k'asaita,
Zasu zagaya subud'ewa Afnan yarima yad'a masu hannu dasu dakata."


Sukayi saurin jada baya,
Da kanshi ya zagaya mazauninta ya bud'e mata k'ofa ta fito,


Rumgumeta yayi a jikinsa batare da yadamu da taron mutanen dake wurin ba."
Ya kara bakinshi a kunnenta yace "muddun kikayi k'ok'arin kwace kanki gareni, bazan kuma kawoki kiga Kaka ba."
Aikuwa Afnan najin haka ta kuma lafewa a jikinsa, ta tura kanta a k'irjinshi tana shak'ar k'amshin turaren shi."


Aikuwa kallo yadawo kansu kowa sai mamaki sukeyi wasunsu na fad'in
"waccan kuwa Afnan ce?"


Wasu nakiran "eh itace amma gskya ta canza kama kamar ba itaba."


wani yace "aidama Afnan matar manyace. Karanbani ne kawai yakai malam Nura soyayya da ita."


Malam Nura dake tsaye gefe d'aya sanye da manya kaya abokanansa sun zagayeshi,
Yana ganin fitowar Afnan rungume da yarima sai da Idonshi yacika da hawaye, yayi saurin maidasu."
Ido biyu Bassam yayi da malam Nura yasakar mashi murmushi ya kuma rungume Afnan d'inshi kamar wadda za'a kwacewa ita, suka shiga gidan."


Afnan batayi mamakin sabon gidan da kaka da malam iro suke cikinsaba, dama tanajin labarinsu a wurin Anna. Wadda ita kuma Anna maimartaba yake gaya mata komai."


Tana rungume dashi suka shiga gidan, ganin taron mutane cike da gidan yasa gabanta fad'uwa tayi saurin kwace jikinta daga gareshi."


Ta kutsa cikin taron mutanen tana kiran "Kaka!!"


Kaka dake falonta zaune tareda abokanan Maryam suna barkwanci tajiyo sautin muryar Afnan tana kiranta,
Da sauri ta zabura ta mik'e tsaye tace "muryar wa nakeji kamar ta Afnan dina."


Afnan ta rugo da gudu ta rungume Kaka tana sauke ajiyar zuciya,
Kaka tace "oyoyo Afnan suka kai zaune cike da murna."


Maryam da abokananta mutuwar tsaye sukayi da suga yanda Afnan ta canxa masu." Kasa yimata magana sukayi saboda mamaki."


Sallamar da Bassam yayi ya shigo, ita yasanya kowa ya watse yabar d'akin."


Bassam ya kai gurfane gaban kaka yana gaida ita,
Kaka rungume da Afnan tana murmushi cike da jin dad'i take amsa mashi, had'ida cewa


"Bassam anshigo d'aurin auren?"


Munga abun Arziki Allah yabiya yasaka maka da Alheri yabaku zuri'a tagari."


Afnan tasaki baki tana mamaki, "Auren waye akeyi?"
Shin dama yana zuwa gidan kaka ne baitab'a fad'a mata ba?"


Ya katse mata tunani da cewa "kaka bari naje wurin d'aurin auren can, nasan yanzun hakan ni ake jira ga sadakin nan a wurina."


Kaka ta zaro ido tace "yarima abun ba'a gajiya harda sadakin kaine zaka biya?"
"Anfa gode Allah yabaku wad'anda zasuyi maku kuma."


Yace "Amin had'ida kallon Afnan yayi murmushi ya tashi ya fita."


Afnan na ganin fitarshi. Tace "kaka ni duk abun ya d'aure min kai shin wai auren waye akeyi a gidan nan?"


Dama yarima yana zuwa gidan nan ne?"


Kaka tayi dariya tace "ai Yarima yazama d'an gidan nan kwana ne kad'ai ne bayayi a gidan nan, duk matakin da kikaga mun taka to aikin yarima ne a yanzun danida malam iro babu abunda zamu iya cewa Yarima sai Allah yayi mashi Albarka ya bashi zuri'a ta kwarai."


Sannan mutanen da kikagani a waje yau ake d'auren auren malam Nura da Maryam, Wanda Bassam ne ya d'auki nauyin komai har sadaki da kuma gidan da zasu zauna."


Allah sarki Ya Sayyadi, ta furta a fili. Tace "kaka naso naga Ya Sayyadi naga yanda ya koma, nabashi hak'uri abunda ya faru."


Kaka tace "karki damu malam Nura ya dad'e da yafemaki, dama Allah baiyi kece matarsa ba."


Fira sukeyi mai cike da farin ciki da yaushe rabo."


Afnan ta zama abar kwatance a cikin mutane kowa sai nunata yakeyi."


An d'aura auren malam Nura da Maryam akan sadaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login