Showing 3001 words to 6000 words out of 90241 words

Chapter 2 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9819




Kuma kasani mutuwa nakan kowa, sai dai idan lokaci bayeba, kaima zatazo kanka, kuma nasan saikayi nadama a lokacin da bata da amfani."


Tana kaiwa nan tafashe da kuka ta mik'e tsaye ta goya *Afnan* dake ta barcinta,
Ta kuma kallon *Aminu* dake zaune ba abunda ke damunsa ko ajikinshi🤷🏻‍♂


Ta kuma cewa "ina sauran kud'in dasuka rage a account d'in nashi bayan angama biyan kowa bashinsa?"


Ya mik'a hannu wurin 'yan sanda aka mik'o mashi wata jakar kud'i miliyan shidda ke cikinta, ya mik'awa *Hajjah* had'ida da cewa "wad'an nan kud'in su kad'ai suka rage a cikin dukiyar Alhaji *Ibrahim*."


Tayi saurin d'aga mashi hannu tace "naji na kuma fahimta,
Amma sai dai maganar tashi daga gidan nan ayi min hak'uri sai gobe zan had'a kayana sai na natashi."


Wani kalar murmushi ya saki Alhaji *Aminu* had'ida sosa gemunshi, sannan yace "bakomai *Hajjah* ai da yau da gobe duk d'aya amma Dan Allah ki tabbatar da gobe zuwa k'arfe hud'u kintashi, domin inada buk'atar ayimin kyarekyare domin anan zandawo da iyalina."


Bata tanka mashiba tayi shigewarta d'aki tana zubar da hawaye😭 Domin sai a lokacin ta kuma tabbatar da cewa tabbas Alhaji *Ibrahim* shine gatan ta."


Safiya na wayewa tashiga had'a kayansu gaba d'aya, ta goya *Afnan* suka nufi tasha, tashiga mota sai Gombe."


Gidan wani k'aninta ta sauka Wanda shi kad'ai ya rage mata a duniya, tayi mashi bayanin duk abunda ke faruwa ya kuma tausaya mata sosai,
Anan tabashi kud'i tace "tanaso yasaya mata gida ma dai daici domin ta zauna taci gaba da renon marainiyar da aka barmata Amana."


Haka kuwa akayi ansa marmata gida madai daici aka saya mata Wanda yanzun suke zaune a cikinshi,
Sauran kud'inda suka rage kuma tadinga kasuwanci tana samun kud'in da zata dinga yiwa *Afnan* buk'atocinta na rayuwa."


Haka rayuwa taci gaba da tafiyar masu yau dad'i gobe k'unci, har Allah ya had'asu da wani mak'oci mai mutumci wato malam *Iron* mahaifin *Maryam* kenan."


Tun tashin *Afnan* malam *Iro* yaji yana tausayinta kasan cewar yaji labarin mareniya ce bata Uwa batada Uba."


Wannan dalilin ne yasa ya d'auki aniyar sai ya taimakawa rayuwarta domin duk Wanda yatai maki wani Allah zai taimakeshi."


Ya had'ata tareda *Maryam* 'yarshi yasanyasu makaranta d'aya, Arabic da boko."


________________________________




*Afnan* da *Maryam* Allah ya had'a jininsu sosai Wanda idan d'aya zaici abinnci dole saida d'aya na nan."


Tun tashin *Afnan* Allah yayi mata wata baiwa ta iya sarrafa computer domin ko a makaranta da zarar wani injin yasamu wata matsala ko computer cikin ikon Allah da zarar *Afnan* tasanya hannu to zaitashi, wannan dalilin ne yasanya makarantarsu suke alfahari da ita."


Tasha samun kyautuntuka akan wannan gyaran da takeyi Wanda yasa malan *Iro* da *Kaka* sukejin dad'i sosai."


Akwai wani lokaci a makarantarsu ta *Boko* anshirya bikin yaye d'alibai angayyato manya gari gwamnoni da sanatoci, taro yayi taro akunna jannareto domin kunawa mai girma gwamna famka yaji iska, ana tsaka da dirama jannareton ya tsaya haka kuma duk na'urorin da ake amfani dasu suma suka d'auke."


Kowa yashiga mamakin lafiya?" Meke faruwa?"
Anan take shugaban makaranta yaba fa umurnin akira mai gyara ya gyara sannan aci gaba da abunda akeyi."


Ai kuwa mai gyara uku aka kira amma babu Wanda yayi nasarar gyaran na urar, sai can shugaban makarantar ya tuna da *Afnan* aikuwa da sauri aka shiga cikin d'alibai nemanta,
Kasan cewar *Afnan* batason hayaniyar mutane sosai, kuma batason yawan magana shiya sanya ta komawarta cikin aji tayi zamanta tana karatu"


Anan shugaban makarantar ya nemota yafad'a mata duk abunda ke faruwa,
Murmushi tayi tace "bakomai Malam bara ni nagwada sa'ata, Allah yasa adace."


Haka kuwa akayi tana sanya hannunta, tana tab'a wani abu saiga haske ya bayyana komai yatashi lafiya galau yafara aiki."


Murna wurin malamai abun ba'a magana,
Anan ne gwamna yace "ya d'auki nauyin karatunta har iya rayuwar ta."


_______________________________


Haka rayuwa taci gaba da sakancewa *Afnan* kullum sai k'ara girma takeyi halittar jikinta na kuma koma sak mahaifiyarta wani zuben kuma mahaifinta, domin gaba d'ayansu kyawawa ne."


Allah ya horewa *Afnan* farin jini Wanda da zarar tafita waje ko zuwa makaranta ne sai maza sunyita bibiyarta.


Tun tana kuka *Maryam* na lallashinta har takai ta daina domin idan da sabo yakamata ta saba.
Dan dai *Afnan* din ba mai yawan suruto bace, kuma batason damuwa,


Namiji d'aya take tsayawa dashi suyi magana wato malam *Nura* koshi tun lokacin da yasamu labarinta ya tausaya mata matuk'a ya kuma d'auki niyar saiya taimaka mata a karatunta."


A duk lokacin da taje makarantar Arabic Malam Nura shike mata karatu har sai yaga ta fahimta sosai sannan yake kyaleta,


A haka soyayya mai k'arfe ta shiga tsakanin malam Nura da Afnan har sukayiwa kansu Alk'awarin aure.'


_____//////////////_________//////_________




A yanzun Tunanin Afnan d'aya ne aduk lokacin da ta zauna shine Allah yacika mata burinta tayi karatu mai zurfi domin takwato dukiyarsu a hannun Azzalumi Alhaji *Aminu*


______________________________


A b'angaren *Bassam* kuma
Yana komawa gida a guje yashigar da motarshi a parking space d'in harabar masarautar,


dafe da kunci yafito motar,
Bayi da kuyangi sai zuwa sukeyi a guje suna zubewa suna kwasar gaisuwa amma baya kulasu."


Kai tsaye b'angarenshi yanufa aka bud'e mashi k'ofa yashiga kai tsaye saman wani katafaren gado yafad'a Wanda yaji bargo na more rayuwa."


Fad'awa yayi rumda ciki dafe da kunci dai dai inda Afnan ta maareshi,


Rufe idonshi yayi yana kuma tunanin fuskar Afnan a lokacin da tad'aga hannu ta kwad'a mashi mari."


Wani murmushin mugunta yasaki a lokacin da yatuna da wani tsoho da yayi tsaye gabanshi yana fad'a mashi maganganu wad'anda da alama zaginshi yakeyi."


Tashi tsaye yayi domin mayen giyar yasakeshi, amma kuma babu abunda yafi tsaya mashi a rai ilah marin da wata 'yar matsiyata ta kwad'a mashi a fuska."


Ya kuma girgiza kai yace "tabbas saina wulak'antaki wulak'anci mai tsanani,
Saina ladabtar da wannan tsohon har saiya kai da rayuwarshi amma baya iya more mata."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com








*4*








Mik'ewa tsaye yayi a fusace, yanufi b'angaren Maimartaba,
Kai tsaya yashiga fada batareda da yajira anbashi iziniba,
Domin idan da sabo fadawa masu gadin k'ofar fadar sun saba da halin Prince *Bassam*


Kai tsaye yashiga fadar, yatarar da sarki kishingid'e yana diba jarida a hannunshi, ganin shigowar yarima *Bassan* yasan shi ajiye jaridar ya maida hankalinshi wurinshi,


*Bassam* tsaye yayi ya hard'e hannuwa had'ida sunkuyar da kansa k'asa alamar baya da niyar magana."


Maimarta na ganin hakan ya fahimci cewa rayuwarshi a b'ace take,
Amma bazai masa maganaba har sai lokacin da yagaji da tsayuwar da yakeyi ya zauna sannan yafad'i abunda ke tafe dashi."
Dan haka shima yabishi da ido yana kallonshi "


Ganin Maimartaba baya da niyar tambayarshi abunda ke tafe dashi kamar yanda yasaba a duk lokacin da yaganshi ya shigo fadar,
Yasanya shi, d'aga kansa domin suyi ido biyu da shi,
Saima gani yayi Maimartaba yaci gaba da karatun jaridarshi."


Ransa ya kuma b'aci ya juya hard'e da hannu ya fita."


Maimartaba na ganin fitarshi yayi murmushi irin nasu na manya, yace "idan kamatso kaine mai dawowa kayi magana da bakinka."


*Bassam* nafita kai tsaye d'akin *Fulani* yashiga domin duk a cikin matan sarki da ita kad'ai yake shiri."


Kai tsaye yashiga d'akin *Fulani* batare da sallama ba, ya Tarar da *Fulani* tare da wata mahaukaciya mai suna *Rabi* wadda ta taimaketa ta nema mata magani kuma ba laifi sauk'i ya soma samuwa gareta,
*Fulani* Nayi mata tsifar kai."


Tana ganin *Bassam* yashigo cikin yanayin b'acin rai,
*Fulani* ta b'ata fuska tace "meke damun *Yarima* mai jiran gado,? Waye ya tab'a d'an sarki mai takalmin k'arfe yanzun hukunci ya hau kansa kowaye shi?"


*Bassam* yaji dad'in kirarin da *Fulani* tayi masa." ya kuma hard'e hannuwansa sannan yace " *Fulani* meye hukuncin Wanda ya mare d'an sarki?"


Sai *Rabi* mahauciya tayi karab, tace " idan mace ce ka aureta kawai karama marinka saika saketa, ta tuntsire da dariya."


*Bassam* yaji haushin maganar *Rabi* sosai,
Tsawa ya daka mata wadda sai da tayi saurin zabura tare da k'ank'ame jikinta, sannan yanuna mata hanyar waje yace "tashi kifita, mahaukaciya kawai masu hankali na magana kina Sanya masu baki."


Da sauri ta mik'e ta fita tana sosar kai."


Ya maida kallonshi ga *Fulani* batare da yayi magana ba, alamar ita yake sauraro."


*Fulani* tace " duk Wanda k'addara ta aikeshi ya sanya hannu ya mari d'an sarki, to tambas hukunci ne zai hau kanshi mai tsanani,
Domin za'a tura fadawa a d'aukoshi ko waye shi, akaishi gidan horo a yimashi horo mai tsanani had'ida azabtarwa mafi muni a gareshi."


Murmushin mugunta yayi, had'ida sosa gyamonshi, yace "Nagode *Fulani* sannan yafita daga b'angarenta."




________________________________








*Waye Bassam*?"


*Bassam* kenan d'an sarki mai takalmin k'arfe."


Shikad'ai ne d'a namiji a wurin sarki *Ahamad Moh'd Gombe* dan haka yake taka kowa yanda yakeso a gari."


Mahaifiyar *Bassam* Hajiya *Hadiza* uwar gidan Sarki, Allah yayi mata rasuwa tun a wurin haihuwar *Bassam* wannan dalilin ne yasanya Sarki ya d'auki son duniyar nan ya d'orashi a kan *Bassam* kuma shine d'anshi namiji wadda zai gaji kujerarshi."




_______________________________
*Sarki Ahmad Moh'd* shine sarki na bakwai a hawa kujerar sarautar *Gombe* shima ya gaji sarautar ne a wurin mahaifinshi,


Sarki *Ahmad* sarkine mai adalci mai taimakon tala kawanshi, tun lokacin da ya hau kujerar sarautar jama'ar gari suke murna da farin ciki domin babu abunda talaka zai nema ya rasa, a yanzun a masarautar *Gombe*

Masarautar *Gombe* tana da wasu gundun tarihi mai yawan gaske wanda tun sarki na d'aya da ya sauka akan kujerar mulki, sakamakon ciyo da yasameshi,
Shine kad'ai yasan sirrin tafiyar da mulkin masarautar, kuma shi kad'ai yasan kaddarori da dukiyar masarautar take dashi."


Kamin ya mutu sai da Ya bar wasiya da cewa "idan ya rasu, duk Wanda zai hau kujerar sarautar mudun idan ba Dan *Allah* zaiyi mulkiba akwai wata manufa a zuciyarshi to tabbas babu wani Abu da zai kuma amfani a cikin masarautar har sai lokacin da akasamu sarkimai adalci sannan masarauta zatadawo dai dai,
Ya kuma nuna wani *Tambari sarautar* dake lik'e a cikin fadar masarautar, kamar agogo shiba kuma computer ba,
Amma yanaso yayi kama da agogo sai dai yafi agogo girma sosai,
Sannan yanuna wasu na'urori masu kama da computer dake ajiye a cikin wani d'aki Wanda ba Wanda ke shiga d'akin sai shi sarkin."


yaci gaba da cewa "wad'an nan dakuke gani bayan na mutu idan adalin sarki ya hau kujerata, to sune zasu nuna mashi irin k'undin tsarin mulkin masarautar nan, kuma sune zasu nuna mashi iya dukiyar da masarautar nan ta mallaka da duk wani Abu da yakeso yasani game da sarauta."


"Amma kusani duk sarkin da zaiyi mulki in har bada niya zuciya d'aya zaiyi mulkiba toko shekara nawa zaiyi bazasu tab'a amfaniba in har bada zuciya d'aya zaka mulki al'umma ba."
Yana kawowa nan yayi shahada ya rasu."




Hakan kuwa akayi bayan rasuwar sarki na d'aya, duk sarkin da ya hau kujerar mulki, sai yayi ta Neman *Tambarin sarauta* yatashi domin yasan iya dukiyar da masarauta ta mallaka Dan yasata yayi abunda ya ga dama dasu, amma tambari bazai tashiba."


Koda sarki na hud'u ya hau kujerar mulkin,
komai sai ya kuma lalacewa domin har gwala gwalai da zinari da a kayiwa fada ado dasu, suna bada haske gwanin ban sha'awa yana hawa kujerarshi komai ya tsaya suka daina bada haske."


Kowa mamaki yashigayi, aikuwa hankalin sarki na hud'u ya tashi, yatura fadawa k'asar waje "duk inda mai gyara yake azo mashi dashi ya gyaramashi har *tambarin sarautar* zai biyashi ko nawane."


Haka kuwa akayi, ankira masu gyara k'asa k'asa amma babu abunda ya sauya."


Anan sarki na hud'u yaba da umurnin duk wani jinin sarautar *Gombe* yana buk'atarshi da ya dinga amfani da photon *Tambarin sarauta* a riga ko a hula, ko agogo?"


Bayi da kuyangi kuma bayan rigarsu aka zana masu k'aton photo *Tambarin sarauta*
Maza kuma har hular Kansu tana d'auke da photon *Tambarin*


Wannan dalilin ne yasanya duk inda akaci karo da photon *Tambarin sarauta* ajikin wani to basai ka tambayaba kasan jinin masarautar *Gombe ne*


Tun daga sarki na biyu har zuwa sarki na bakwai *Tambarin sarauta* be kuma tashiba, sai duk Wanda ya hau kujerar mulki saiya d'auko masu gyara domin yagwada sa'a ko zaitashi amma ko alama babu,
Har zuwa sarki na bakwai wato sarki *Ahmad moh'd,*
mahaifin *Bassam* kenan Wanda shi kwata kwata kujerar sarauta bata gabanshi, asalima ba da son ranshi aka nad'ashi sarautarba sai Dan mutanin gari sun zab'eshi kuma yayi alk'awarin tunda suka zab'eshi shima zai faranta masu kowanensu sai sunyi dariya bazasuyi kuka dashi."




*wash hannuna nagaji kuzo muje zuwa masoyana*
*ummu safwan CE*
07066214433
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






*5*








*Alhaji Ahmad Moh'd* yana da mata hud'u mahaifiyar *Bassam* Itace uwar gida, Sarki na matuk'ar sonta domin tsayuwa da ta a kan gaskiyarta,


Sannan ta biyu kuma sunanta Amina sai zainab da kuma Maryam, dukansu babu Wanda Allah yabawa haihuwa, kullum addu'a sukeyi "Allah yabasu ciki su haihu, su kuma haifi d'a namiji domin ya gaji sarautar mahaifinshi."


kwatsam saiga Hajiya Hadiza uwar gidan sarki Allah yabata ciki,


Lokacin da tasamu ciki, murna a wurin Sarki abun ba'a magana, ya kuma d'auki son dukiyar nan ya d'orashi a kan abunda zata haifa, yin hakan ya kuma sanyawa abokanin zamanta k'iyayyarta da abunda ke cikinta."

Hajiya Hadiza macece mai hak'uri da sanin ya kamata, duk abunda za'ayi mata bazata tab'a d'aga kai ta kalli mutum ba bare ta nuna rayuwarta ta b'aci."


Irin wad'an nan halayen nata ne, sarki yake masifar sonta."


Cikinta ya kai wata tara, likitoci suka tabbatar mata da cewa "d'a miji zata haifa,
Ai kuwa Sarki yadinga murna, saboda jin dad'i be iya b'oye farin cikinshi ba, ya dawo gida ya tara matanshi gaba d'ayansu yake shaida masu abunda likita ya fad'a, cewa "Da namiji Hajiya Hadiza zata haifa, dan haka sutayashi da addu'a zai samu magaji."


A zahiri sun nuna farin cikinsu, a zuciyarsu kuma babu wanda ya kaisu bak'in ciki musamman ta uku Hajiya Zainab domin duk tafiso bala'i da tungo a gidan."


Ta d'auki d'amarar cewa "indai tana da rai da lafiya, Hajiya Hadiza bazata haifi d'a namiji a gidan nan ba."


Aikuwa ta tashi tsaye ta dinga shiga bokaye da malamai domin ganin an salwantar da cikin Hajiya Hadiza."


Kwatsam wata rana nak'uda ta kama Hajiya Hadiza, hankalin Maimartaba ya tashi sosai, yakira likita cikin gaggawa domin ya taimaketa."


Tun 12:am take nak'uda itace bata haihuba sai 12:pm nasha wahala sosai, tana haihuwa tace ga garinku nan ta rasu."


Sarki yaji mutuwar uwargidanshi mace mai hak'uri da dantako,
kuka yakeyi sosai kamar k'aramin yaro."


Haka akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya."


Hajiya Zainab kuma tayi bak'in cikin mutuwar Hajiya Hadiza ita kad'ai batare da abunda ta haifaba, ta kuma d'auki alwashin mudun tana raye aduniya saita ga bayan *Bassam* a doron k'asa."


Haka rayuwar Bassam taci gaba da tafiya a hannun jakadiya itake renonshi take mashi wanka, gaba d'aya dai ita ke d'awainiya dashi."


Sannan kuma tunda ta fahimci burin Hajiya Zainab shi taga bayan *Bassam* a koda yaushe sai ta yimashi addu'ar tsari ajikinshi, domin *Bassam* kyakkyawane bafulatani ne, sak mahaifiyarshi ya biyo."


Girma yakeyi sai k'ara kyau yakeyi, duk inda ya gifta mutane sai maganar shi akeyi, gashi da saurin sabo, da fasaha, idan yafad'i wata magana saika d'auka fad'a mashi ita akayi, Allah ya horewa *Bassam* saurin fahimtar abu tun yana k'araminshi."


Wanda hakan ne yasa ya kuma shiga ran sarki, yanaji dashi sosai."


Wanda ita kuma Hajiya Zainab a kullum tana wurin boka neman maganin da zai raba *Bassam* da duniyar gaba d'aya."


Ita kuma Hajiya Amina ta zubar da makaman k'iyayyarta ga *Bassam* burinta d'aya ne Allah yabata ciki itama ta haifi nata d'an namiji."


Inda itama Hajiya maryam tun lokacin da mahaifiyar *Bassam* ta rasu Allah ya d'ora mata son *Bassam* a rayuwar ta."


Gaba d'aya renonshi yadawo a hannunta abunda ke rabasu da *Bassam* barci, domin wurin jakadiya yake kwana."


Duk abunda ke faruwa a gidan sarki yana sane dashi, yana kuma lura da duk wani mai kyautatawa *Bassam* da mai musguna mashi,
Yana kuma jin dad'in irin yanda Hajiya Maryam ke nuna kulawarta ga *Bassam* kamar itace ta haifeshi, wannan dalilin ne yasanya yabata matsayin marigayiya na *Fulani*


Cikin kwana uku aka d'ata a matsayin *Fulani* Nad'inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login