Showing 24001 words to 27000 words out of 90241 words

Chapter 9 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9821

fad'i jin an ambaci Yarima, amma kuma sai ta dake saboda karsu fahimci wani abu a tare da ita,
tace "kuna iya shigowa ta kauce tabasu hanya suka shiga d'akin."


Talatu tafad'a toilet domin had'a mata ruwanka_
Indo kuma tashiga gyaran d'aki had'ida goge goge,


Tsaye tayi tana kallonsu, sai dai muryar Talatu taji tana fad'in ranki ya dad'e komai ya kammala ke kad'ai ake jira, kishiga kiyi wanka."


Kallo tabisu dashi tace nagode Talatu."


Suka sunkuyar da kai alamar girmamawa suka ce "ki daina yimana godiya ranki ya dad'e aikinmu dolene muyi maki bauta,
Suka fita suka tsaya pallo suna jiran tafito wankan su shiryata."


Cikin minti talati ta kammala wanka
tafito, sunajin fitowarta suka nufota suka shiga yimata kwalliya."


Kwalliya sukayi mata irin ta 'ya'yan sarauta tasha Alkyabba tayi kyau sosai suka take mata baya suka mufi wurin cin abinci da ita."


Break fast ne aka shirya mata, abinci ne iri iri aka shirya mata kowane daga ciki saida aka zuzzuba mata shi a plate,
Mamaki tashigayi tana fad'i a zuciyarta lallai masu kud'i sunajin dad'insu,
Wannan irin daula haka da mulki inama auren soyayya ne aka yimasu?"
Inama ace masoyinta ne ya Sayyadi aka aura mata suke cikin wannan daula haka."


Nan take zuciyarta ta karye da ta tuna da masoyinta Malam Nura, idonta yacika da hawaye, tayi saurin gogewa saboda karsu talatu su lura da hakan."


Abincin tashiga cakud'a tanaci a hankali, sai muryar jakadiya taji tanayiwa su Talatu magana tana fad'in "yauwa Talatu kunshirya ta kenan?


Suka runsuna sukace mungama ranki ya dad'e,
Sannan tace "ina shi Yarima yake?"


Zasuyi magana kenan yak'araso wurin yace "gani Jakadiya."


Ta kalleshi taganshi sanye da jallabiya ko wanka beyiba tace "ina katafi ko wanka bakayiba kuma kasan Afnan zataje gaida maimartaba kasan kuma tare zaku tafi."


Sai lokacin ya lura da Afnan dake zauna akan dining table tana cin abinci,
Harara ya warga mata sai a kan idon Jakadiya,
A zuciyarsa kuma yana fad'in wannan Aljanar yarinya tasamu sake diba yanda takecin abinci kamar ba 'yar matsiyataba."


Jakadiya tace idan ka gama hararar mutane Yarima saika wuce kaje kayi wanka muna jiranka."


Kallon jakadiya yayi yace "wai Jakadiya dole ne sai anjeni wurin maimartaba dani ne?


Tabashi amsa da "Eh atare zakuje domin yasanya maku albarka."


Be kuma yin magana ba yasanya kai yayi tafiyarshi."


Jakadiya ta maida kallonta ga Afnan tace taso kizo nan 'yata."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com










*21*








Afnan ta tako a hankali ta zauna a kusa da Jakadiya."


Jakadiya tace " ki natsu ki kwantar da hankalinki ki d'auki nan gidan kamar gidanku ne."


Kiyi hak'uri da halin mijinki domin kuwa Yarima Baud'and'an hali gareshi, wanda ko Sarki wani lokaci yakan rasa gane kansa."


Ki d'aukeni a matsayin Uwa domin tun lokacin da kika shigo gidan nan naji kinshiga raina, kuma nayaba da zab'enki da Yarima yayi a matsayinki na matar aurenshi."


domin tun lokacin da Allah ya karb'i ran Mahaifiyar Yarima, nice na reneshi na kula dashi har lokacin da karatu ya rabamu dashi."

Amma a kullum addu'ata d'ayace gareshi Allah yabashi mata tagari wadda zata kula da rayuwarshi domin rayuwar Yarima tana cikin hatsari a koda yaushe,


kasan cewa shikad'aine d'a d'aya tilo a wurin Maimartaba, gashi kuma maraya."


Afnan ta sunkuyar da kanta k'asa tana sauraren jakadiya, a zuciyarta kuma tana fad'in to ni meye nawa a ciki, aiko nima marainiyar ce amma ya rabani da kowa nawa harda masoyina ya d'aukoni ya kawoni wannan gidan, babu abunda yakeyi min sai zaluntana yana dukana."


Jakadiya ta katse mata tunani da cewa, yanzun zakuje ku gaida Sarki a tare dashi."


Inaso kinatsu da kyau, domin nasan kinada tarbiya."


Nan Jakadiya tadinga koya mata yanda zata gaida Sarki had'ida zuba mashi kirari cikin girmamawa."


Bassam kuma wanka yakeyi zuciyarshi tunkushe da jin haushi,


dole saiya jera tareda Aljanar Yarinyar can suntafi fada, wai halan basusan yanda ya tsaneta bane, kwata kwata bayaso ya bud'e ido ya ganta a kusa dashi bare har su jera a tare su tafi fada a cikin bainar jama'a a nunasu a matsayin aurata."


Wani dogon tsaki yaja had'ida fitowa toilet d'in yashiga shiryawa,
domin yasan halin jakadiya yanzun tana fara kwankwasa mashi k'ofa, a d'aga mashi hankali a banza, akan wacan abar."


Shifa ya lura tun zuwanta gidan nan kowa yafara raja'a akanta musamman Jakadiya wadda ya d'auketa tamkar mahaifiyarshi,
Ya lura da yau ko break fast bata damu data tambayeshi ko yayiba sab'anin yanda take mashi a da."
Ya lurada kwatakwata hankalinta baya gareshi yana wurin wancan abar."

Haka ya kammala shirinsa cikin wata Alkyabba ruwan madara wadda tafito mashi da kyanshi da maxantakarshi na jinin sarauta."


Jerawa sukayi a tare suna tafiya fadawa suka take masu baya suna zuba masu kirari suka rakasu har fad'a,"


Sarki cikin farin ciki da jin dad'i yake kallonsu yana murmushi, gaba d'ayansu suka duka gaban maimartaba,

Afnan tabud'a baki a hankali tana magana cikin nutsuwa, gaisuwa take jerowa maimarta."


Bassam najin hakan yasan aikin Jakadiya ne, ya tsura mata ido, ita kanta ta lura da irin kallon da yake mata amma bata yarda sukayi ido biyuba dashiba,
ta sunkuyar da kanta a k'asa."


Sarki yace "masha Allah Tubarakallah."
Ka iya zab'e d'an sarki Ashe ni ka gada gurin iya zab'en mata."
Yana maganar yana dariya.


Fadawa sai kirari suke mata."


sarki yace " saiki dage ki haifo mana 'ya'ya maza masu karamci irin na d'ana Bassam."


Bassam ya d'auke idonshi daga gareta, a ransa yace "Allah ya tsareni ya kiyayeni ni, aurenta ma danayi kaddara ce, akwai kuma dalili.......


Sarki yayi masu hud'ubba su zauna lafiya, sannan daga k'arshe ya basu umurni da sutafi."


Tarigashi yunk'urin tashi tayi gaba, ganin hakan Sarki yaja hannun Bassam ya rik'e cikin barkwanci yake kallon Bassam yace "banga alamar kaci amarci daren jiyaba, mekake jira?"


Murmushin da baikai cikiba Bassam ya saki yana kallon k'asa."


Domin yasan mahaifin nashi da son zolaya da barkwanci."


Sarki ya kuma kallon Bassam cikin zolaya yace "ni dai a iya sanina magajin sarki jarumi ne ba ragoba."


Kunyace ta cika Bassam yatashi tsam yana dariya yabar fadar, shima sarkin dariya yakeyi."


Da sauri take tafiya domin tasamu ta isa b'angaren nasu kamin Bassam ya yafito daga fada, domin tasan idan ta tsaya jiranshi su tafi a tare to kamin sukai ya zalunceta yayi mata illah."


Kai tsaye ta isa b'angarensu a kayi sa'a Bata tarar da Jakadiyaba,
Bedroom tafad'a kai tsaye ta haye a kan gado ta kwanta tana sauki ajiyar zuciya a hankali."
Anan take sai tunani Kaka ya fad'o mata a rai ko a wane irin hali take a yanzun?"


Can kuma taji gabanta ya fad'i da tuna da Ya Sayyadi,idonta ya cika da hawaye, wayarta ta laluba a jakarta domin takira gida."


Taji bata jitaba, da Sauri tashiga lalubin d'akin har k'ark'ashin gado ko Allah zai sanya tafad'a amma bata gantaba, saima taci karo dawani k'aton kwali da alamar akwai abunda Bassam yake b'oyewa a cikinshi."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com










*22*










Jawo kwalin ta shiga yi a hankali, da kyar ta samu ta jawoshi.
saboda nauyin da ke gareshi,
Da sauri tashiga bud'e wa domin ganin abunda ke ciki."


Karo taci da kwalaben giya, cike da kwalin,
Zaro ido tayi cike da Mamaki, tashiga fad'in "wato wannan mugun mutumin har a gida yake shan giyar kenan."


Dogon tsaki taja, tace "Allah yaraba mu da rashin tarbiya."
had'ida tallafar kwalin da kyar saboda nauyin kwalabin dake cikinsa."




window tanufa sai da ta fara lek'a kanta,
taga ba kowa ga alama mutane basu cika wucewa ta wurin ba,
sannan ta kinkimi kwalin tajefa, saijin k'arar fashewar kwalabe kakeji."


sannan ta rufe window tana murmushin jin dad'i domin ko ba komai tasan idan ya nemeta be gantaba rayuwarsa saita b'aci, ita kuma zataji dad'i idan ta ganshi a cikin wannan yanayin kodan saboda marin da yayi ta kwad'a mata a daren jiya."


ta kai dubanta a k'afarta inda ya taketa ta murgud'a baki tace "Allah ya isa,
azzalumi kawai, kuma duk muguntar da zakayi min a sannu zan rama."


Ta hayewar ta a kan makeken gadonta barci mai dauyi yayi a won gaba da ita."






Tafe yake amma ranshi idan yayi dubu ya b'aci, Zuwan da sukayi fada tare da Afnan, har sarki yake masa zancen jikoki, Allah ya tsareshi da ya had'a zuri'a da wan can marar kunyar, ko mata sunk'are a duniya yanajin ba zai tab'a son wancan abar ba mai sunfar Aljanu."


Shifa a duniya babu mace da ya tsana kamar kyakkyawar mace domin a cewarsa, duk macce mai kyau babu abunda ke gareta sai mugunta."


Domin yagani a wurin matan maimarta, musamman Hajiya Zainab da yayi laka'ari da dukansu tafisu kyau."


Dan haka yake k'arajin tsanar Afnan a ranshi, dan haka burinshi a kullum yaga ya musguna mata, hardai idan ya tuna da hannunta da ta d'aga ta kwad'a mashi mari. A gaban bainar jama'a."


B'angarensu ya nufa da saurin shi, domin rayuwar shi ta farfasa takeyi babu abunda ke wanke masa rayuwa yaji sanyi, sai giya."


Bebi takan kowa ba, bedroom ya fad'a kai tsaye idonshi rufe bema lura da ita a kwance tana barciba,


K'arkashin gado yashiga dibawa amma wa yam, babu abunda ya ajiye da sunan b'oyo, dibe dibe yashiga yi idonshi ya rikid'e ya koma launin ja, yasan babu Wanda zai iya yimashi bincike ya gano inda ya ajiye abarsa sai Afnan domin ya lura idonta a tsaitsaye suke cike da rashin kunya."


D'aga rinannun idonshi yayi,
Yaci karo da ita kwance akan gado tana barci."


Ya matsa kusa da ita cikin zafin rai, yana kallon halittar da Allah yayi mata...


Cikin zafin nama yajawo hannunta ya d'aga hannu ya kwad'a mata mari."


A firgice ta bud'e idonta tsoro na tashin hankali ya bayyana a fuskarta, tayi k'arfin halin d'aga kai ta kalleshi dafe da kunci idonta cike da hawaye tace
Tace "lafiya?" Me namaka?"


Kallonta ya kuma yi cike da tsana da jin haushi, yace "OK tambayata ma kikeyi saboda rain in hankali,
ya kuma d'aga hannu zai kuma kwad'a mata wani marin ta goce besa metaba."


Yashiga cewa ina ajiyar da nayi a k'ark'ashin gado?"


Kallonshi tayi tace "wace irin ajiya kuma?"


Nuna mata wurin yayi yace "a can na ajiye ina kika kai min kayana?"


Kamota yayi ya mikek'ar da ita tsaye ya matseta gam a bango,
Yana tambayarta ina takai mashi kayanshi?"




Matsar da yayi wa hannunta ne ya sa ta yin hawaye, tare da kai d'ayan hannunta ta rik'e tana fad'in
"Wayyo hannuna nashiga uku."


Yasaki hannun nata tareda ture ta ta fad'a kan gadon, kuka taci gaba dayi, a hankali tana kuma bashi hak'uri, domin ta ganshi a yanayin da bata tab'a ganinshi ba."👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






*23*








"Kifad'a min inda kika kai mun ajiya ta kona b'anb'ala maki hannu."


Kuka ta kuma fashewa dashi, tana fad'in ban san in da ka a jiye kayan ka ba, ni ka daina tambaya na."


Kuma kusan to ta yayi yana zare idonsa, kamar ya had'iye ta, yakeji saboda jin haushi."


Amma hakan bai sa ta daina ce masa ita bata ga kayan sa ba."


Fita yayi yana huci, tana ganin ya fita,
Ta kalli hannun ta wurin da ya rik'eta, wurin yayi jajir sai masifar zafi yake mata."


Wani sabon kuka ta fashe dashi, tana fad'in "wai mutumin nan yasan Allah kuwa?"
Muguntarsa ta yi yawa, a kullum burin shi yaga ya illatata, yayi mata tabo ajiki."




Cigaba tayi da kuka, Talatu ce ta turo k'ofa tashigo, domin duk abun da ke faruwa a kan idon ta."
tazo kawowa Afnan kayan motsa baki,
Da Sauri ta koma da baya, Allah yatsare basuyi ido biyu da Bassam ba."


Matsota tayi ta durk'ushe k'asa ita ma hawaye sai fita yakeyi a idonta, sai ka ce ita a ka yiwa."


Afnan na ganinta tayi saurin mik'ewa tsaye a firgice,
Tana fad'in ina yake?"


Talatu tace "ya tafi ranki ya dad'e."


Afnan ta kuma rushewa da kuka, taci gaba da cewa,
Sai ya kashe ni yau d'in nan in huta da wulak'aci da azzabtar da ni da ya keyi."


Hannun ta Talatu ta rik'e tana dibawa, tace "ranki ya dad'e wannan shaidar fa?"


Kukan ta ya tsanta tace " so yake ya gama b'ata min jiki da tabo,
So yake yaga ya in latani sannan ya rabu dani."


Mulki hauka ne, ko saura ta hauka ce,
Gara ma yasa a kashe ni ta, idon ba hakan ba, zan ganar dashi mulkin macce a kwai banbanci sosai,
Domin bazanci gaba da d'aukar wulak'ancinsa ba, sai dai yayi gun duwa gun duwa da naman jikina."


_____________________________






Cikin *Kunar Zuci* Bassam ya fita,
kai tsaye chilly ya nufa, mashayar giya."


Basma yaci karo da ita zai shiga, ita kuma zata fita."


Kallon juna suka shigayi, cikin yana yin kuka ta rungume shi."


Bassam na ganin hakan ya zanye ta daga jikinshi cikin dabara suka nufi gefe d'aya inda mutane basa wuce wa."


Basma ta fad'a a k'irjinshi ta fashe da kuka, tana fad'in "meyasa ka yau dare ni Prince?"


Kasan kai kad'ai nake so, kai kad'ai na mallakawa zuciya ta da jikina, amma kai ne mutum na farko da kafara yaudara ta."


Banta b'a sanin ko wane d'a namiji ba, sai a kanka, ka shayar da ni zumar soyayyar ka, wadda duk namijin da na tunkara, bayan rashin ka danayi, tamkar 'yar uwata mace nake d'aukar shi."
Prince mena maka?"
ka yau dare
ni?"


Kamanta da ni, daga k'arshe sai dai naji labarin auren ka a gari?"


Share mata hawaye ya shiga yi, cikin sigar lallashi,
yana d'an dukan bayan ta, alamar tayi hak'uri tayi shuru."


Sannan tayi shuru ta d'aga kan ta, suka yi ido biyu, sannan ya samu da mar yi mata magana."


"Basma ki natsu ki saurare ni, ki kuma fahimce ni da kyau."


Auren da kikaji labari nayi,
banyi shi ne ba domin na yau dareki,
Nayi shi ne domin d'aukar fansa."
Sannan kuma na k'unta tawa rayuwar wasu masoya."


Har ga Allah bana son matar da kike cewa wai na aure ta, domin kwata kwata bata d'aya daga cikin jerin matan da nake mafarkin aure"


Sannan kuma yin aure na bashi ne yan kewar alak'a ta da ke ba."


Basma, ke tawa ce ni naki ne, idan Allah ya k'addari ki zama mata ta, zaki zama."

share mata wasu 'yan gun tayen hawaye yashiga yi, yana kuma kwantar mata da hankali,
A nan take ya mantar da ita b'acin rain dake damun ta."


Fira sukeyi mai cike da so da k'auna, mussam Basma, domin Bassam biye mata kawai yakeyi domin ya samu ya rabu da ita lafiya."


Domin ko giyar wake yake sha baya jin zai iya auren ta,


Macce da suka had'u a Club, yana ma kula tane, saboda yaga tana yi mashi wani mahaukacin so,


Amma dan tsabagen muna furci irin na mace, harda wani kuka "wai ya san dai shi kad'ai ta fara kulawa."


Koda ya fara ma'amala da ita, tamkar k'ofar text yakejin, haka nan kawai yake biye mata."




[3/5, 4:34 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






*23*








"Kifad'a min inda kika kai mun ajiya ta kona b'anb'ala maki hannu."


Kuka ta kuma fashewa dashi, tana fad'in ban san in da ka a jiye kayan ka ba, ni ka daina tambaya na."


Kuma kusan to ta yayi yana zare idonsa, kamar ya had'iye ta, yakeji saboda jin haushi."


Amma hakan bai sa ta daina ce masa ita bata ga kayan sa ba."


Fita yayi yana huci, tana ganin ya fita,
Ta kalli hannun ta wurin da ya rik'eta, wurin yayi jajir sai masifar zafi yake mata."


Wani sabon kuka ta fashe dashi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login