Showing 6001 words to 9000 words out of 90241 words
Chapter 3 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 yafi yiwa Hajiya zainab bak'in ciki arayuwa domin d'aki tashiga tadinga kuka kamar wadda uwarta ta mutu."
      
________________________________
*Bassam* na kammala secondry a lokacin yanada shekara 16, Maimartaba ya turashi England karatu domin yana lura da Hajiya Zainab a kullum burinta d'aya taga bayan d'anshi tilo d'aya."
Tafiyar *Bassam* England karatu da abota da k'awaye yasan yashi ya fara shaye shaye da Neman mata, amma ko mace mako wace yake ma'amala da itaba sai mai aji."
Domin *Bassam* akwai aji, ga kuma kud'i, domin maimarta a koda yaushe cikin turo mashi kud'i yake a account d'inshi kuma yamashi gargad'in cewa "karya kuskura yadawo Nigeria har sai ya kammala karatunshi gaba d'aya,"
Domin a ganin Sarki wannan kariyace yake mashi daga shairin Hajiya Zainab."
Shine bedawo gida Nijeria ba saida ya kammala degree d'inshi da masters, sannan Sarki ya bashi umurnin yadawo k'asarshi."
     A lokacin sai Maimartaba ya gina mashi b'angarenshi ya kuma bashi umurni da cewa "duk wanda be yarda dashiba, to karya bari yashigar mashi b'angare."
  
 lokacin da yadawo gida Nigeria *Bassam* ya girma sosai yazama namijin gaske, gashi da gwarjini a fuska da kuma rik'on addini, 
     Domin duk wanda yayi ido biyu dashi sai yaji shayin ya tunkareshi, saboda ba wasa a fuskarshi."
Sarki nason *Bassam* sosai domin ya yaba da hankalin shi da kuma tarbiyar shi,
       Domin a tunanin sarki, *Bassam* ko goro bayaci bare azo ga giya."
Wanda shima yake kiyaye duk wata hanya da zai sanya sarki ya fahimci wata b'araka ko rashin tarbiya daga gareshi."
  
sai dai idan dare yayi yaja motar shi yanufi club yasha giyarshi ya holewar shi da 'yan  matanshi,   sannan yadawo gida babu wanda yasani."
Shinefa bayan yadawo daga club d'in a buge yabiyo ta unguwarsu *Afnan* har yaci karo da ita tadawo daga islamiya, cikin maye yaga tayi mashi kama da budurwanshi *Basma* yanemi ya fad'a mata."
       Wannan kenan."
_________________________________
 Tafiya yakeyi yana sak'e sak'en a zuciyarshi irin hukuncin da zai d'aukarma *Afnan* tareda wannan tsuhun Wanda yake gani kamar mahaifinta ne,
      Murmushi mugunta yayi a zuciyar yace " idan nasanya aka d'aukomun wannan tsuhun hukuncin da zanyi mashi sanyawa zanyi a gutsire mashi wannan k'azamin  hannun nashi, da yanuna ni dashi."
Yana daf da shiga b'angarenshi yaji ana kwala mashi kinashiga nesa, 
 Dajin muryanta ya gane ko wacece,  Hajar ce, d'iyar k'aunar Hajiya zainab datake mutuwar sonshi,
 shi kuma a duniyar nan babu abunda ya tsana kamar Hajiya Zainab da duk wani Abu da yafito daga hannunta,
Bai juya ba,  be kuma tsayaba, yayi  shigewar shi b'angaren shi."
Tana zuwa daf da k'ofar b'angaren nashi taja burki ta tsaye, domin tasan duk fad'in gidan babu Wanda yake gigin shigar mashi b'angaren  daga Sarki sai *Fulani* sai kuma jakadiya."
      Bayan wad'an nan babu wanda ya isa yashigar mashi b'angare, koda  sarki ne ya aikosu."
Dashi garshi d'akin nashi kai tsaye toilet ya fad'a domin yin wanna."
 shiri yakeyi babu abunda yake gani sai fuskar *Afnan* lokacin da tasanya hannu ta mareshi,
Idonsa suka rikid'e sukayi jajir, da Sauri ya d'auki key d'in motarshi yanufi unguwarsu *Afnan*
π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
             *6*
Tafiya sukeyi sai fira sukeyi mai dad'i, *Afnan* tareda masoyinta malam *Nura*
        Daga makaranta tafito, shine yayo mata rakiya zuwa gida,
  Domin yanada labarin duk abunda yafaru tsakaninta da prince *Bassam* 
Kasan cewar yau *Maryam* bataje makarantarba saka makon ciyon kai da take fama dashi."
Firar su, sukeyi ta masoya kwanin ban sha'awa duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki kuma sona son junansu."
Anan ne malam *Nura* ke shaida mata da cewa "da zarar yadawo Madina karatu, gaskiya ya gaji da zama ahaka zaije yayiwa *Kaka* magana a gaggata yin auren su saboda gaskiya yaga nawar su mallaki junansu."
*Afnan* dariya tashigayi had'ida rufe fuska cike da jin kunya."
Karya kwanan da zasuyi da zata kaisu gida, tafiya sukeyi cike da farin ciki."
*Bassam* kuma da tun d'azun ya iso, unguwar, gaba d'aya gidansu *Afnan* ya b'ace masa, 
      Sai dai yasamu wuri yayi parking d'in motarshi a gefen unguwar, yafito sanye da wani bak'in glass a fuskarshi, ya haye kan mota ya zauna cike da b'acin rai,    yana kallon duk mai wanda ya wuce d'aya bayan d'aya."
A can ya hango *Afnan* tare da malam *Nura* sun karyo kwana."
Wani tsalle yayi ya doro kan motar, yanufesu, 
       Gabansu ya tara ya tsaya yana k'are masu kallo d'aya bayan d'aya."
*Afnan* na ganinshi sai da gabanta ya fad'i, amma ta dake, ta kalli malam *Nura* tace "ya Sayyadi ka barni daga nan ka koma gida ko."
Kallonta malam *Nura* yayi had'ida murmushi, 
sukayi kamar basu lura da prince a wurin ba, 
yace "a'a mutafi kawai na k'arasa dake gida Gimbiyata."
Rab'a *Bassam*sukayi, har sun d'an gotashi kad'an 
   Saiji tayi anjanye mata hijabi, saida tacire gaba d'aya, yana fad'in ke 'yar matsiyata, ina matsiyacin ubanki yake, yau sai kunyi nadamar abunda kuka aikatawa yarima d'an sarki."
      Zan nuna maku Ku matsiyata ne, kuma talaka wa, dake da mahaifinki nayi alk'awarin saina azabtar daku, a zaba mai tsanani."
Afnan ranta idan yayi dubu ya b'aci idonta ya cika da hawaye batasan lokacin da ta d'aga hannu ta kwad'a mashi mari, a karo na biyu, tana magana tana kuka tana fad'in "kai wane irin dabbane wanda bakasan darajar d'an Adam ba, anfad'a maka mulki hauka ne ko sarauta haukace to kasani Allah yana tare damu."
Kallo *Bassam* yabita dashi dafe da kunci, cike da mamaki."
Saiji yayi malam *Nura* na fad'in "good *Afnan* kinburgeni, wannan shine hukuncin da ya dace ki d'aukarwa azzalumi irin wannan."
Ya duk'a ya d'auko mata hijabinta yabata tasanya, sannan ya kuma kallon *Bassam* yace "idan ka isa, kasanya bindiga ka harbemu mubar duniyar idan katashi."
Suka rab'a ta gefenshi sukayi tafiyarsu."
*Bassam* tsaye yayi yana kallonsu domin yanzun abun mamaki yake bashi, kallo yabisu dashi beyi mgnaba, har *Malam Nura* ya kaita  gida, sukayi sallama ya juyo ya dawo."
Ta gaban *Bassam* ya rab'a ya wuce *Bassam* betan kashiba, saida yayi nisa sosai sannan *Bassam* yabishi a baya, saida yaga gidan da yashige sannan ya juyo,
    Yashiga motarshi da k'arfi ya figeta, ya fita a unguwar ranshi a b'ace."
Kai tsaye club ya nufa yasanya akayi masa odar giya, sai d'aga kwalba yakeyi yana shan yewa yana jifa da gwalbar gefe, saijin k'arar fashewar kwalma mutane keji ba halin ayi masa magana,
Amma darar ka  ganshi kasan a cikin b'acin rai yake."
duk abun nan dayakeyi *Basma* na gefe tana kallonshi tana zubar mashi da hawaye domin Allah yajarabeta da masifar sonshi."
 ganinshi datayi cikin wannan yanayin ne yasan yata bata tunkaroshi ba domin tasan halin *Bassam* sarai mudun yana cikin b'acin rai tanufo shi domin ta lallasheshi, to a ranar zataci dukan tsiya, saita rasa wadda zai taimaketa, gata Kuma Allah ya d'ora mata masifar sonshi kamar ta had'iyeshi takeji."
Ganin shi tayi ya kuma d'aukar kwalba ta 5  zai kai bakinshi, tayi saurin  zuwa gabanshi da d'an gudunta, ta rik'e mashi hannu idonta cike da hawayen tausayinshi, tace haba " *Bassam* meye hakan kake aikatawa?" Kadiba ga ganifa, kwalba  ta biyar kenan kake Neman shanyewa, meyasa kake neman b'ata rayuwarka a wurin giya?" Pls *Bassam* yi hak'uri ajiye kwalbar, tana amsar kwalbar ya mik'e tsaye cikin maye yana kallonta saiji tayi ya d'auketa da mari har sau biyu,
       Yana fad'in ni zaki Mara?" Waye ke?" Waye ubanki?" A fad'in duniyar nan?"
*Kuyi hakuri da wannan*,
       *ummu safwan*
               07066214433
π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
________________________________
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
   
           ππππππππππππππππππ
*Happy Birthday Faty Azland Allah yasanyawa Rayuwarki Albarka, ya k'aro shekaru masu Albarka*πππππππππ
           *7*
"Tsura mashi ido tayi dafe da kunci tana mai zubar da hawaye,
      Ganin  zai kuma tunkarota alamar zai hauta da duka yasanyata yin saurin ja da baya tana zubar da hawaye."
Wurin wasu samari tanufa dake cikin club d'in, suna shek'e ayarsu,
    Tayi masu magana tace  "Dan Allah su taimaka mata, su rik'o mata *prince Bassam* su shigo mata dashi Rom 12 ko nawa ne zata biyasu."
Jin kud'i yasa samarin yin wata irin shewa, sukace "angama Baby *Basma* bakida matsala indai wannan ne."
Cikin dabara suka rik'o " *Bassam* dayasha giya tayi mashi over suka sanyashi a d'aki had'ida kwantar dashi a kan kado."
Kud'i ta d'ebo a jaka Wanda itama kanta bata San ko nawa neba, ta dank'a masu a hannunsu, murna suka shigayi suna k'ara jinjina mata sannan suka fita."
Wurin da aka kwantar da *Bassam* tanufa  kwance yake yayi d'aid'ai akan gado barci mai nauyi yayi awon gaba dashi,
  tashiga zage mashi talkamin dake sanye a  k'afarshi, ta kuma gyara mashi kwanciya had'ida lullub'eshi da bargo, ta tsura mashi ido tana kallonshi cike da so da k'auna, ita dai a duniyar nan babu abunda takeso sama da *Bassam*."
Ahaka tasanyashi a gaba tana kallonshi had'ida shafa gefen fuskarshi har barci b'arawo yayi awon gaba da ita."
________________________________
*Afnan* nashiga gida kai tsaye d'akinta  ta nufa, ta fad'a kan katifarta, tashiga rusar kuka, tana tuna irin wulak'ancin da *Bassam* yayi mata yacire mata hijabi a gaban bainar jama'a, me Tatare mashi a rayuwa, meta yimashi?
 Hasalima bata tab'a ganinshi ba, kuma bata tab'a ganin fuskarshiba amma yakeso yashiga rayuwarta domin ya tuzartata, Dan yaga bata da gata, 
    Ta kuma fashewa da kuka tana fad'in "gatana shine Allah kuma nasan zai taimakeni ya kuma tsaremi ga dukan Wanda keso yaga ya tuzartani."
*Kaka* dake tsakar gida tajiyo sautin kukan *Afnan* da sauri tanufo d'akin tana fad'in *Afnan* lafiya meya sameki  kike kuka hakan?"
*Afnan* tayi saurin goge hawayen fuskarta tace "bakomai  *Kaka* kaina ne kiyimun ciyo sosai."
Da sauri *kaka* tace "Subahanallahi."
 tashiga d'akinta ta d'auko mata maganin ciyon kai, had'ida d'ebo mata ruwa tabata tasha, had'ida tufeta da Addu'oi sannan tace "ki d'an kwanta *Afnan* zuwa ajima zakiji ciyon  yasakeki kuma kidaina kuka kidinga addu'a saikiji sauki yazo maki."  
*Afnan* tayi murmushin k'arfin hali tace "na daina *kaka* Allah yak'ara maki tsawon rai da lafiya."
Kaka tayi murmushi tace "Amin *Adman* yar gidan *kaka*."
______________________________
 
Hankalin Marmartaba yatashi matuk'a *Bassam* be kwana a gidaba, duk inda ake tunani yana can, andibashi babu labarin shi, idan aka kira wayarshi a kashe akejinta."
       Anan take hankalin masarauta yatashi ko ina anbaza fadawa sun tafi nemanshi."
Hajiya *Zainab* kuma sai murna takeyi tanajin dad'i tana kuma k'ara addu'ar Allah yasa ya b'ata bacewa ta har abada, dama ko be b'aceba ta k'arb'o wani magani Wanda yau d'in nan zata sanya mashi a abinci da zarar yaci sai dai wani bashi ba."
     To kuma saigashi an hutar da ita yama b'ace gaba d'aya, Allah yasa kar a ganshi."
Agaban maimartaba kuma tafi kowa nuna bak'in cikin rashin ganinshi da ba'ayiba domin har kukan muna furci takeyi."
*Fulani* kuma kallonta kawai takeyi domin tasan halin Hajiya *Zainab* sarai macece makira mai tsananin mugunta matuk'a."
Farkawar da *Bassam* zaiyi ya Ganshi rungume a jikin *Basma* tana barci, kallo yabita dashi, yana tuna abunda yafaru dashi jiya, 
Sauri yayi yashafa  gefen fuskarshi inda *Afnan* ta mareshi, ranshi ya kuma b'aci, 
Ya kuma yadiba a gogon hannunshi yaga 8:am ya tuna a nan kenan ya kwana,
A hankali ya kwantar da *Basma* domin karta tashi,
   Ya ayyana a zuciyarshi cewa "duk inda maimartaba yake yasan yanzun hankalinshi na can atashe rashin ganinshi da beyiba."
A hankali ya sauko daga kan gadon, yasanya talkaminshi had'ida d'aukar key d'in motarshi yafito yanufi gida."
Ta unguwar su *Afnan* yabi aikowa yayi sa'ar tafito tanye da uniform zata makaranta, malam *Nura* na rik'e da jakarta suna tafiya cikin nishad'i
Tagabansu yawuce ya fige mota da k'arfi gaba d'aya ya wanke masu jiki da ruwan kwata yayi tafiyarshi."
π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
_____________________________
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
          *8*
Tsaye *Afnan* tayi tsamo tsamo jik'e da kwata, haka shima malam *Nura*  gaba d'aya jikinshi har fuskarshi duk ya b'aci da kwatar,
kallon ta kuma bin malam *Nura* dashi cike da tausayin shi  domin  tasan itace silar  janyo mashi wannan wulak'ancin hakan."
      Idonta cike da hawaye tace "Dan Allah Ya sayyadi kayi hak'uri nasan duk a sanadiyata hakan ta faru da kai."
D'aga mata hannu yayi yace "kidaina bani hakuri *Afnan* nasan abunda *Bassam* yake nufi dake, kuma nayi alk'awari indai akankine nafiso narasa Rayuwata wurin kare maki mutuncinki."
Ya mik'a mata jakarta littafanta yace "ki koma gida kiyi hak'uri da zuwa makarantar a yau kibari sai  gobe kitafi, 
Ta k'arb'i  jakar tana mai zubar da hawaye."
A nan sukayi sallama suka rabu da juna kowane daga cikinsu ranshi a b'ace yake musamman *Afnan* da aka wulak'anta mata masoyi da ruwan kwata, 
     Domin ita bata tunanin kanta saboda tasan bata batada gata abunda yafi wannan ma zai iya faruwa da ita."
Koda tashiga gida, tsamo tsamo jike da kwata, *Kaka*ta rafka Salati cike da kulawa tace *Afnan* meyafaru hakan naga jikinki duk yajik'e da kwata?"
Ta k'ak'aro murmushin dole tace "muna tafiya tareda ya Sayyadi domin ya Samar min abun hawa, saiji nayi na fad'a kwata.*
*Kaka* tace "Subahanallahi, to Allah ya tsare gaba wuce kishaga ban d'aki,
 kicire kayan jikinki sai kiyi wanka, kin  arziki da bakiji ciyoba."
__________________________________
*Bassam* kuma ranshi ya d'anyi mashi dad'i, domin ko ba komai yasan ya bak'anta masu rayuwa a yanda yagansu cike da farin ciki."
      Wani dogon nishi yaja adaidai lokacin da zai shigar da motarshi get d'in gidansu, ya tuna da lokacin da *Afnan* take furtawa  wannan ustazun saurayin  cewa
 "nagode ya Sayyadi ka barni a nan na iyar da k'arasawa da kaina."
     Har wani murmushi take masa, shima hakan,  wato da ala masoyane kenan kuma alamu yanuna suna tsananin son junansu matuk'a."
       yayi wani murmushin mugunta, sannan yayi parking d'in motarshi yafito."
Babu Wanda yaga shigowarshi domin gaba d'aya hankalin kowa a tashe yake na rashin ganinshi da ba'ayiba,
Bebi takan kowaba kai tsaye b'angarenshi yanufa, a cewarshi sai yayi wanka sannan yatafi wurin Maimartaba yasan k'aryar da zai shirya mashi na rashin kwanan da baiyi a gidaba jiya."
Kai tsaye d'akinshi yanufa, fadawa da kuyangi masu kula da komai nashi na rayuwa, suna ganinshi cike da murna sunata zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa had'ida yimashi kirari."
Ba laifi ya d'an saki fuska ya amsa masu sab'anin ya yanda yake masu."
 Sannan daga k'arshe yaja masu kunne da cewa "kar Wanda yafad'awa sarki cewa yadawo har sai ya kintsa ya huta sannan ya kai kansa fada."
Cike da girmama suka amsa da "angama yarima Allah ya taimakeka ya tsare mana lafiyarka."
Sannan kowa ya watse yanufi inda yake aikinsa,
Ashe tun lokacin da yarima yashigo gida, akan idon Hajiya Zainab, tayi bak'in ciki matuk'a da yadawo batare da ya b'ace b'at ba."
tacije Baki tace " tunda kadawo baka b'ataba, ni bari Nazo nak'arasa da kai lafira matsiyacin yaron mai taurin ran tsiya."
 duk maganun nunkan da nake k'arbowa babu wanda yatab'a yin tasiri a kan wancan tsinanin yaron, bari naje nakwada wannan nagani boko yabani tambacin mudun yaci abincin da aka zubashi a ciki to sai dai wani bashiba." 
             Tamik'e tanufi b'angaren nashi."
Dashigar shi d'akinshi, kai tsaye kan makeken gadonshi ya fad'a, yayi ale,ale fuskarshi na kallon silin, babu abunda yake tunani sai hanyoyin da zaibi yaga ya wulak'anta Aljanar yarin can, a yanda yake cewa *Afnan* burinshi ya wulak'antata ya musguna mata yaga ya hanata  farin ciki a doron k'asa."
Tunawa yayi dayaga yanda Malam *Nura* ya rik'o mata jaka suna tafiya cikin nishad'i ko ba'a fad'aba kasan masoya ne,
    
Sai maganar Maryam mahauciya ta fad'o mashi a rai datace "ka aureta idan karama marinda tayi maka saika saketa."
Yaja dogon tsaki yace "No Allah ya tsareni na auri zuri'ar Aljanu,
Wata zuciyar kuma tace "aiba sonta kakeyiba, idan ka aureta ka wulak'antata da ita duk wata zuri'arsu, saika saketa ka kuma koresu gaba d'aya a garin, yanda zaka manta da tarihinta a doron k'asa."
Ko bayan haka, idan ka aureta ai karabata da masoyinta, yin haka kuma ba k'aramin bak'in ciki bane kadasawa









