Showing 42001 words to 45000 words out of 90241 words
Chapter 15 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 k'aunar ta bud'e ido tayi tozali da ita, sai tayi ta korarta tana fad'in
 "ke 'yar Aljana matsa baya nace Kada kishigo ciki, koba haka nace maki ba?"
Har Afnan ta hak'ura ta daina shiga ciki, duk yanda zatayi ta kaucewa aikin da zaisa taje sashensu shi takeyi."
Idan tana yiwa tumakai wanka, zata shiga jero masu wak'ok'i cikin sautin muryarta mai dad'in sauraro,
 cikin k'ank'anin lokaci duk tumakin dake wurin ta sanya masu suna."
Cikin k'ank'anin lokaci suka saba da ita, da zarar sunji sautin wak'arta, zasu zo su zagayeta suna kukan jin dad'in ganin ta."
Ta d'ebo abincin su da ruwa taba basu, tashige cikinsu taita kallonsu tana shafarsu, ita kanta bata san tana son dabbobi  ba sai yanzun."
 
      Dokin Yarima fari ne yana shan wanka a wurin Afnan. Sun saba da ita sosai idan kaji tana fira dasu sai kace da mutum takeyi."
     Dabba kamar mutum take Hankalin ne kad'ai ya rabasu da mutum, idan zasuyi kashi haka zasu ja jiki sutafi can gefe suyi."
Masu gyaran wurin da sunzo sai su kwashe a kai lambu a zuba."
A cikin lambun Afnan take samun kayan itace kala kala, taita tsinkowa tana sha, har ya kai tasaba da 'yan lambun sosai, wautar da takeyi masu ita take sanya su dariya."
Yanzun ta ba kanta hak'uri ta rage tunanin Kaka sosai, idan taji tunanin yana son zo mata sai tayi saurin kauda shi, taci gaba da ma'a malarta."
'Yan mazan wurin suna ganin girmanta saboda takama kanta, shiyasa ko da wasa babu Wanda yatab'a tun kararta da magar banza."
Kwanciyar hankali tasanyawa kanta yaba ta damar cikowa tayi b'ul b'ul da ita kyawonta sai kuma fitowa yakeyi."
Wata rana Bassam yashiga wurin dabbobi, kasan cewarsa yana son dabbobi wannan dalilin ne yasan yashi ya ke kiyonsu."
A lokacin da yashiga wurin yaga wurin ya canza mashi yayi fes fes dashi ga tumakai yagani tsaf tsaf da su musamman dokinsa a dayake fari  har wani haske yakeyi."
Mamaki yashigayi, a can k'asan lambu yaji wata murya mai dad'i mai kuma zak'i kamar sarewa tana rera wak'a, 
   Da sauri ya haye kan dokinsa ya  gangara zuwa  lambun."
Haka ya dinga biyar sautin muryar har ya iso gaf da sautin muryar ke fitowa, tsayawa yayi yana sauraren muryar yana lumshi ido, bai tab'a tunanin Afnan bace, lumshe idon da yakeyi sautin muryan na ratsashi ta ko ina."
Jin da yayi Wanda ke wak'ar yayi shuru, 
   Ya sanya shi saurin bud'e idonsa  yashiga wai ge waige."
A can bayanshi kuma inda yafito wurin kiyo a can ya kuma jin wak'ar natashi."
Sauka yayi a kan dokinsa yashiga takawa a k'afa a hankali ya dinga bin sautin muryar yana tafiya har ya iso wurin."
 gabansa ne ya fad'i da yayi tuzali  da Afnan tana yiwa tumakai wanka tana wak'a tare da karkad'a k'ugunta, tana watsa masu ruwa a jikinsu, tana kyalkyalar dariya cikin sautinta mai dad'i."
Shagala yayi da kallonta yana sauke wani murmushi a fuskarsa Wanda bai San yanayin saba."
Ko me yatuna da sauri yaja tsaki ya bar wurin yana mamakin ko mema yasan yashi ya tsaya kallonta."
Komawa yayi sashinsa amma kunnuwan sa basu daina jiyo masa sautin muryar Afnan ba, idonsa bai daina hasko masa k'ugunta ba, da take karkad'awa."
Tsaki yaja ya mirgina gefen gado yayi tufda ciki, yana tunani."
Saratu tashigo d'akin kai tsaye ta fad'a kan jikinsa kamar yanda tasaba, tana fad'in "honey yaushe kashigo?"
    ina can ina nemanka narasa inda kashiga."
      Tasanya hannunta a k'irjinsa tashiga shafawa."
          Saratu akwai jarabarbiya tsiya☹."
Tsawa ya daka mata wadda bai tab'a yimata irinta ba, yace
 "tashi kifita ina muk'atar kad'ai cewa ni kad'ai na hutu."
Zaro ido tayi had'ida turo k'aton bakinta alamar shagwab'a,
     Zata bud'e baki tayi magana yace "karki ce  min komai pls tashi kifita." had'ida nuna mata hanyar waje."
Mik'ewa tayi jiki ba kwari ta fita, kallo yabita dashi, yana harararta🙄 ya furta a ransa "kai wannan abar akwai muni😂
[3/5, 4:48 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *38*
Juyi kawai yakeyi akan gadon sa, amma  fuskar Afnan kawai yake gani tare da d'an k'ugunta da take ta faman  karkad'awa tana rawa."
Dogon tsaki yaja ya kuma juya  kwanciyarsa, daga rigingine zuwa rufda ciki yaja wata doguwar ajiyar  zuciya tare da fitar da  wani kalar numfashi a bakinsa."
Can kuma yaja wani dogon tsaki had'ida  runtse idonsa, a zuciyarsa yana  fad'in "  meyasa fuskar yarinyar nan tak'i  fita a ido na?"
         Indai kyau ne tana da kyau,
 amma kyauwon banza ne domin babu abun ke tare da macce kyakkyawa sai mugunta, da iya sharri."
Tunawa yayi da abunda yafaru a tsakaninsu, farkon shigarta sashinsa,  lokacin da yaka mata a d'akinsa."
 Tunawa yayi da  Laushin fatar jikinta  tareda d'an k'aramin bakinta da yashiga tsotsa kamar sweet."
Kuma mirginawa yayi had'ida lashe bakinsa, gaba d'aya Jiyayi tsikar jikinsa  natashi  kamar anyi mashi shocking."
 filo ya lalubo ya rungume had'ida  sauke numfashi a hankali tare da lumshi idon shi."
daga nan har barci b'arawo yayi awon gaba dashi amma Afnan ce a idonsa."
*Sarkin gida*a gaban Hajiya zainab  durk'u she yana jera mata kirari."
Murmushi tabishi dashi alamar ta amsa."
domin da zarar taga sarkin gida cikin wannan yanayin tasan ansamo nasara wurin boka."
Sarkin gida ya kalli Hajiya Zainab yace "ranki ya dad'e ansamo nasara, ya mik'a mata k'ullin magani k'ulli  biyu, yace "wannan aikin nakine ranki ya dad'e domin boka yace "so akeyi ta shanye shi, ya kuma tabbatar min da cewa da zarar ta shanye maganin zata koma Salaf kamar miya ba gishiri."
   Kinga duk rawar k'afar da Yarima yakeyi a kanta zai daina."
  Dan na lura da ita a gidan nan so takeyi ta wuce ki a mulki."
Hajiya zainab tasaki wata irin dariyar mugunta tace " nagode sarkin gida dan haka nake sonka duk a cikin fadawa na."
     Ta d'ebo kud'i masu yawa ta mik'a masa tace "wannan nakane."
Ya amsa yana godiya had'ida zuba mata kirari sannan ya fita."
Saratu ce cikin shiga ta alfarma tafiya takeyi kuyanginta suntake mata baya, ta nufi sashin Hajiya Zainab."
Da shigarta ta tarar da hajiya Zainab a zaune a kan kujera tana bawa Yazeed abinci."
Batabi takan hajiya zainab ba ta jawo kujera ta zauna cike da mulki da  isa,
 ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta shiga  kallon hajiya zainab tana  jefa mata da habaici."
Hajiya zainab  tashiga ramawa, tace "dibeki ba ciki ba goyo, Allah yasa Yarima ba juya ce ya kwasowa Kansa ba, kamar sauran matan ubansa."
Saratu tayi shuru tana nazari domin bata tab'a tunanin haihuwa ba sai yanzun da hajiya zainab tayi mata gori."
Ranta ya sosu tashiga tunanin  abunda zata cewa hajiya zainab domin ta huce abunda ta furta mata, amma tarasa kalma ko d'aya."
Mik'ewa tayi tsaye cike da takaici zata fita."
Hajiya zainab ta kalle ta, 
 tace "har kintashi zaki tafiya?"
    Na aza kinzo ne domin muyi fira."
Saratu tayi shuru ta  bita da kallo batayi magana ba."
     Illah ta koma ta zaune."
Hajiya zainab ta kuma kallon ta, tayi murmushin cin nasara, tace "Anya saratu baki buk'atar taimakon manya?"
     Anyi aure kusan shekara d'aya da rabi amma babu ciki?"
Jikin saratu yayi sanyi, ta manta da ita maiyin maganar shekararta nawa da yin auren kamin ta haihu?"
   
Ta sunkuyar da kanta k'asa domin maganar hajiya zainab ta fara shigarta,
       Hajiya zainab ta gano tayi nasara a kan saratu, don haka ta kwatar da Yazeed, ta taso ta matso kusa ga saratu ta saka mata k'ullin magani a cikin tafin hannunta ta rife tana murmushin da bai kai cikiba."
Tace "kinsan na d'auki shekaru a gidan nan ban haihuba, amma daga baya dana tashi tsaye da Neman magani bagashi na haihu ba, kuma na haifi d'a namiji."
Saratu ta katseta da cewa "eh nasa ni."
Hajiya zainab tace "kije kiyi k'ok'arin samun ciki, "wannan maganin dana baki zai taimaka maki ki wuri samun ciki, sannan kuma ki haifi d'a namiji."
Saratu taji dad'i cikin murna tace "da gaske?"
Hajiya zainab tace "jeki ki kwada mana bari in k'aro miki idan kika fara amfani dashi kada ki tsaya sai kin tabbatar da ciki yashiga jikinki."
Saratu taji dad'i sosai tace wa hajiya zainab "kiyi hak'uri da rashin kunyar da nake maki, ranki ya dad'e, idan na tuna da irin wahalar da nasha ne a hannunki sai intajin ba dad'i."
Hajiya zainab tace "banga laifinki ba, saratu kada ki damu kanki ai yanzun munzama d'aya,
    Kisaki jikinki dani zan koya maki abubuwa da yawa wadda zai sanya mijinki ya k'ara gamsuwa dake a b'angaren auratayyah."
Murmushin jin dad'i saratu takeyi."
Hajiya zainab tace "banaji ance kina ihu ba, idan kina tare da Yarima me yake yine haka da bazaki iya danne jin dad'inki ba har sai kinyita ihu?"
Saratu tace "haka aka ce maki?"
Hajiya zainab tace oh baki sani bane?"
Kunya ta kama saratu,
    Ta shiga tunanin kwana nan kwata kwata Yarima d'in ya canza mata wurin kwanciya, jiya ma yana kanta yana farawa ya sauka ya tallabe kansa, 
tayi masa tambayar duniya abun da ke damunsa?"
Sai  yace mata "babu komai."
Haka suka kwana babu abinda ya kuma shiga tsakaninsu,
    Kuma tasan da ba haka yake ba."
       Tasan da yana matuk'ar son ya kasance tare da ita."
Ajiyar zuciya taja mai k'arfi, ta kalli hajiya zainab tace "zantafi sashina nagode kwarai da kulawarki gareni."
Hajiya zainab ta d'auko wani galan na wani nau'in maganin ta mik'a mata tace "wannan zai taimaka maki zaki matse a can k'asa."
Saratu taji dad'i sosai kamar hajiya zainab ta gano matsalar ta a bud'e take, batajin kanta gam to koshi yasa Yarima ke nisanta kanshi da ita ?"
Hajiya zainab ta dafa kafa d'arta tace "kada kidamu komai zai zama normal."
Saratu tace "nagode ranki ya dad'e, nagode kwarai da gaske Ashe ban San kece mai tai makona ba........
Hajiya zainab ta katseta da "kada kidamu na fad'a maki mun zama d'aya."
Saratu ta dawo sashinta tasa aka tafasa mata k'ullin maganin da hajiya zainab tabata,
     Haka ma tsimin gaba d'aya takafa kai ta shanye tayi wurgi da galan d'in tsakar d'aki, kuyangi suka d'auke suka fitar dashi waje."
Aka kawo mata na k'ullin shima ta kafa kai ta shanye."
Tashiga tunanin ita tasan akwai canji tsakanin ta da mijinta, da har murna yakeyi idan ya ganta, amma yanzun sai tayi tayi masa magana amma bai d'aga ido ya kalleta bare ya amsa mata."
Ko d'an zaman da sukeyi a lambu yanzun ya daina gayyatar ta." Ita tarasa abunda ke damunsa kwana biyun nan ko son kallonta bayayi."
Can taji ciyo ya tsikareta k'asan mararta, a kwance take ta mik'e zaune, jitayi marar ta tayi mata wani irin juyi na azaba sai da tasaki wata irin k'ara ta azaba."
Kuyangu suka shigo Suna cewa " ranki ya dad'e lafiya?"
Ganin ta sukayi tafad'i k'asa tana murk'usoso tana juyawa, itama kanta bata san tanayi ba, saboda azaba da take ji."
       Can sai wani kalar jini ya fara fita bak'ik'irin  gudaje gudaje ga wasu irin Abu a ciki kamar dakakken nama haka."
Jini sai zuba yakeyi kamar ruwa a famfo can kuma sai ya daina, jakadiya ta shigo tana kallon ikon Allah."
"Bari ne ko?" Inji jadiya ta tambaya."
       "Allah sarki sannu."
Saratu ta zaro ido tace "bari fa kika ce dama ina da ciki?"
Jakadiya tace "to ya b'are ranki ya dad'e."
Saratu ta fashe da kuka tace "yi shuru jakadiya ta aza hannu a kai tace "nashiga uku."
Ba'a dad'e ba aka gyara ta tsab aka kwashe komai duk wani ciwo da takeji taji yatafi,  sannan jinin da ke zuba ya tsaya tsaf ko d'igo babu."
     Wannan Abu da mamaki yake🤔
[3/5, 4:53 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
       
*Kuyi hak'uri masoya Tambarin sarauta jiya kunji ni shuru gidan biki ta tafi shiyasa bansamu damar yi maku typing ba*
            *39*
 A Yanzun Bassam bashi da wurin da yake zama domin  shan iska sai wurin kiyon dabbobi,
 inda yasan yana iya hango duk abunda  Afnan takeyi."
      Yana murmushi wani abun kuma yasanya shi dariya, amma kuma baya barin ta ganshi saboda karta rainashi."
      
Shi dai yasan yana zuwa ne domin yaga dabbobin sa saboda shi ma'a bucin son dabbane."
Afnan kuma bata San yanayi ba domin ita har ga Allah har mantawa takeyi dashi a rayuwarta,
   Ita dai burin ta d'aya ne duk lokacin da tayi sallah take addu'ar Allah ya fitar da ita cikin wannan gidan ta koma gaban mahaifanta."
Yau ma hakan taka sance Bassam yayi wanka yasanya wani kaftani mai dogon hannu yayi kyau matuk'a, ya fito yanufi inda yake zama domin nishad'in rayuwarsa."
Tafiya yakeyi Audu na biye dashi yana zuba masa kirari."
 sai da suka zo inda yake zama,  anyi masa shinfid'a ta alfarma, kai tsaye yaje ya zauna."
Audu ya kalleshi yace "ranka ya dad'e ina da tambaya?"
Bassam bai kalli Audu ba yace "ina saurarenka Audu yi tambayar ka."
Audu yace "ranka ya dade lafiya kake kuwa a kwanankin nan?"
    naga tunda aka keb'e wurin kiyon dabbobi a cikin gidan  nan baka tab'a zuwa ba."
 Nayi mamakin ganinka danake yi a nan a koda yaushe,
Kuma ranka ya dad'e naga  ka maida wajen wurin hutawarka sab'anin lambu da kake zama."
   Kuma ranka ya dad'e sai naga kamar kana tsurawa wuri d'aya ido kana kallo, kana  murmushi  a fuskarka."
Basaam ya juyo ya kalli Audu Yace "yaushe ka fara sanya min ido a harakokina?"
Audu yayi saurin kaiwa k'asa yace "ayi hak'uri ranka ya dad'e tuba nakeyi."
Bassam yace "tashi katafi  sai na nemeka."
Audu ya mik'e yana fad'in "godiya nake ranka ya dad'e a gafar ceni."
Bayan tafiyar Audu, Bassam yashiga tunanin maganar da Audu ya fad'a masa, tabbas gaskiya ya fad'a, shima yana mamakin zuwan da yake a nan."
       Idon safiya ta waye baya samun farin ciki, baya jinsa cikin nishad'i har sai yazo wurin nan yayi tozali da dabbobinsa da kuma mai kula dasu, to meyasa?"
   Yashiga tambayar kansa."
Wata zuciyar tace masa "saboda mai kula dasu ta iya tafiyar da dabbobi yanda ya kamata."
Wata zuciyar kuma tace " ba saboda dabbobi kake yazama wurin nan ba saboda kayi tozali da kyakkyawar mace wadda a yanzun da ita kake kwana da ita kake tashi a ranka."
Da sauri ya kawar da wannan tunanin yana fad'in "k'arya ne babu wata mace da ta isa a duniya na tsaya b'ata lokaci na nayi tunanin ta
, bare wancan abar mai kama da Aljanu." Allah yatsare yaja dogon tsaki."
Ya shiga kallon wurin ko zai ganta, amma bai ganta ba, tunda ya zauna wurin yake zuba ido a inda yasan take zama amma bai gantaba."
Sai tunanin sa ya canza yashiga tunanin" ko lafiya?" Mai yasa meta wanda har yanzun bata fito ba?"
Mik'ewa tsaye yayi yanufi wurin dabbobin ko Allah zai Sa ya ganta, yaji dalilin da yasa bai ganta a  dai dai wannan lokacin Dan  tabawa dabbobin sa abinci da ruwa."
Wurin yanufa bai ganta ba, waige waige yashiga yi, koda zai ganta amma bai gantaba."
     Lambu ya nufa da sake sake a ransa wanda bai masan yanayi ba, yana fad'in "Allah dai yasa lafiya take."
   
Yayi saurin kauda wannan tunanin  ya furta a fili,  "wannan bai dameni kuma ba matsala ta bace,
 ko bata da lafiya sai ta fito ta aiwatar da aikin da ya zamar mata dole."
Afnan na lambu taje tsinko mangwaro, tana hango Bassam ya nufo wurin da sauri tashige k'arkashin bayan wani icce ta b'oye."
Tana kallonsa, yayi kyau, domin bata tab'a k'are masa kallo ba sai yanzun."
       Tace "kudibe sa kamar mutumin arziki, amma babu komai a tare dashi sai mugunta, da zalunci da kuma rashin tausayi."
Lura tayi dashi  sai waige waige yake alamar akwai abunda yake nema, taja dogon tsaki had'ida murgud'a bakin kamar yana ganinta tace "yanzun haka wannan mummunan matar tasa mai kama da agwa_gwa yake nema."
        Gani tayi ya tunkaro inda take taja jinin jikinta ta b'oye."
sai da yazo dai dai inda  take   yayi tsaye, yaci gaba kallon ko ina yana waige."
Kuyangi masu gadin wurin basu lura da shigowarsa ba, suna can zaune a gefe d'aya suna fira." d'aya daga cikinsu ya hango shi, ya nuna wa 'yan uwansa shi."
Da gudu suka nufo wurinsa suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, suna fad'in ranka ya dad'e a ga farcemu ayi mana afuwa bamu San kazo ba,
      Ranka ya dad'e mekake nema?"
Rasa amsar da zaibasu yayi, ya kallesu yace "ba komai kuyi tafiyar Ku."
Da sauri suka mik'e suka nufi wurin aikin su."
Ganin sun wuce, shima ya bar wurin, saboda karsu fahimci wani Abu a tare dashi tafiya yakeyi amma kalle kalle yakeyi 









