Showing 81001 words to 84000 words out of 90241 words

Chapter 28 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9843

kanta, tashiga turashi k'asa sai da ya fad'o daga kan gadon."


Sarki ya doki gaba cikin tashin hankali yace "Alhaji Aminu da matar d'ana yarima?"
Aminina a kan shinfid'ar d'ana yana cimasa Amana?" Kaico duniya."


A tare suka jawo zanen gado suka rufe jikinsu. Fuskokinsu cike da tashin hankali."


Afnan tanajin sarki yace Alhaji Aminu ta kuma duban shi da kyau, ta tabbatar da tabbas shine azzalumin da tadad'e tana Neman Allah ya cika mata burinta a kanshi."


Ta matso kusa gareshi idonta yana zubar da hawaye, tace "Allah ya kamaka azzalumi ma yaudari basik'i Wanda bai d'auki zalunci da cin amana a bakin komaiba."


Ta juya ta kalli maimartaba ta d'an russuna, tace "ranka ya dad'e wannan azzalumin Wanda kake kira da Amininka shine yaci Amanarmu ya ha incemu ya kwace dukiyar mahaifina yace dukiyarsa ce sannan daga k'arshe ya kwace mana gidan da muke ciki ya koromu garin kano mukadawo gombe da zama." Ina ma Kaka zata ganka a cikin wannan halin da tayi alawaddai da rayuwa irin ta."


Bassam ya jawota ya rungumeta yana bubbugar bayanta alamar tayi shuru."


Dakyar kaka tasamu ta kutso cikin taron mutanen dake k'ofar d'aki sunyi cincirindo."


Tana shigowa taci karo da Alhaji Aminu tace "dama mai hali baya fasa halinshi, duk inda Azzalumi yake k'arshinsa jin kunya."


Tad'aga kai sukayi ido biyu da Sarki. Tace Alhaji Ahmad!! Yace Mama!! Dama Afnan 'yar gidan Alhaji Aminu ce?"


Ya kuma juyawa ya kalli Alhaji Aminu yace "tabbas kacika babban macuci maciye Amana." Kaci Amanata kaci Amanar d'ana kaci Amanar Aminta ka kuma ci Amanar marainiyar Allah wadda kake k'arya da ita kana amsa kud'i a hannununa, sannan kuma kaci Amanar kanka, Dan wlh na rantse da Allah sai na hukuntaka hukunci mai tsanani, dakai da wannan mummunar abar."


Babu abunda idon saratu da Alhaji Aminu yake fitarwa sai hawayen nadama."


Ya dubi Saratu yace d'an Adma butulu. Kina matsayin baiwa kinsamu yanci d'an sarki ya aureki har kike iya cin Amanarsa."


Dama makircin da kike k'ullawa kenan tun yarima yana da rai kenan,
Jikin saratu sai karkarwa yakeyi kamar mai jin zazzab'i, idanunta sunyi jajir sun k'ank'ance, "ranka ya dad'e kayi min rai don girman Allah na tuba." Bai kulata ba ya dubi Alhaji Aminu yace


"Tun yaushe kuke tare?"
Ya kasa magana ya had'a hannayensa guda biyu yana rok'on gafara"


Sarki yace "bakaji tambayata ba?"


D'aya daga cikin fadawan yadaka masa tsawa yace bakaji tambayar sarki ba, maciye Amana."


Jikinsa na rawa yace "najiya, mun dad'e tare da ita, budurwa tace tun a kano,
Na d'auki kusan shekara biyar bangantaba sai lokacin da nakawo maka ziyara naci karo da ita a nan gidan, nayi mmki da tace Yarima take aure saboda saratu tsohuwar yar barikice tsohuwar karuwace, tasan dad'in d'iya maza."




Marinda yarima ya kwad'a mashi shiyasanyashi yaja bakinshi yayi shuru."


Hajiya zainab ta matso kusa da dad'inSaratu ta zungureta tace "ni dama tunda wannan Abar tashigo gidan nan naji ban natso da itaba, naji na tsaneta
Nayi mamakin da yarima yaganeta yaji yana sonta har ya aure,
ta kai mata mari tace munafuka kawai yau k'aryarki ta k'are."


Sai a lokacin Yarima yayi gyaran murya yayi magana yana rungume da Afnan, ya dubi Fadawa yace " tallabesu kufitar mun dasu acan gaban fada, Ku ajiye munso tsakar fili,
Kucewa sarkin hukunci yafara yimasu bulala dubu dubu tare da hukunci mai tsananani kafin safiya ta waye a zartar masu da hukunci dai dai laifinsu, kuma a basu kaya susa a barsu haka."


Sukace Angama ranka ya dad'e, suka tallabesu suka sanyasu gaba cikin zanen gado d'aya suna tafiya fadawa na tsine masu Albarka."


********************


Kafin safiya ta waye sarki ya tura fadawa garin kano gaba d'aya aka tattaro dukiyar Alhaji Aminu a ka kawo masa."


Daren ranar labari ya gauraye gidan sarautar ankama matar yarima da kwarto tana cin Amanar sa."
Yarima ya sanya shela gobe da safe misalin k'arfe "8:am kowa ya hallara gaban fada za'a zartar masu da hukunci."


Ba wanda ya runtsa yayi barci daga sarki har yarima. Mussam Afnan da taketa kukan dad'i tana tsakiyar Anna da Kaka zaune suna hira, kaka tana bawa Anna labarin irin cin Amanar da Alhaji Aminu yayi masu."


Safiya na wayewa misalin k'arfe 8:am kowa ya hallara gaban fada, kuyangu da bayi kai duk wani mai aiki a cikin gidan sai da ya hallara, gasu tsakar fili kowa yana kallonsu."


Sarki ya fito tare da yarima ya tsaya, yayi kyaran murya, ya fara magana."


" Aminu a bisa cuta da cin Amana daka aikata min, ka daffareni kud'ad'e da dama wad'anda nake baka kana cewa kana taimakawa iyalan Alhaji Ibrahim bisa k'arya kakeyi. To ni nayafe maka."


Amma dukiyar marainiya baza'a tab'a yafe maka ba,


Jiya kafin safiya ta waye, natura garin kano an d'auko min duk wani Abu da nasan Alhaji Ibrahim ya mallaka a zo min dashi, Dan haka za a bawa marainiya hak'inta gadon mahaifinta Wanda ya mutu ya bar mata kasa k'afa ka danne saboda kana Azzalumi."


yanuna masa wata jaka yace "wannan itace kaddarar Afnan, ya kira Afnan da Kaka ya mik'a mata gaban mutane, Afnan ta runsuna ta karb'a tana godiya had'ida zubar da hawaye."


Sarki ya dubi yarima yace sauran "hukunci kuma ya na hannunka magajin sarki."


Yarima ya matso ya dubi fuskar Saratu cikin tsana da bak'in ciki, ya kuma d'aga kai ya dubi bayinta da kuyangunta yace Ku matso kusa duk Wanda yasan wannan mummunar ta tab'a cin amanarsa ko zaluntarsa ni nace kuyi mata dukan tsiya har sai kunrama abunda tayi maku
, Ku had'a harda wancan muna fukin."


Aikuwa suka hausu da duka, baji bagani, saida suka fitar masu da jini sannan yarima yayi gyaran murya yace
"Kugyalesu haka. Ya dubi jakadiya yace "
"Jakadiya d'auko masu kayan bayi kibasu su sanya."


Aka d'auko masu, suka tub'e gaban bainar jama'a suka sanya."


Yarima yace "sarkin hukunci ya matso yace "Naam ranka ya dad'e."


Yace ku d'aukesu kubar garin nan dasu Ku kaisu can cikin daji Inda ake zuwa kama bayi,
Akamasu atafi dasu can wata masarautar suyi aikin bauta, su wulak'anta su zama abun tausayi."


Ya kuma kallon Saratu ya matso kusa da ita ya sauke mata bari biyu masu kyau yace na sakeki saki uku Kada Allah ya kuma had'ani da mummunar fuskarki ko a lahira."


Yace kud'aukesu kutafi dasu Ku wurgar dasu can na daina ganinsu."


Haka aka d'aukesu aka wurgasu cikin motar d'aukar dabbobi aka tafi dasu."










Bye bye Sarah Baby😂😂😂😂😂
[3/6, 10:35 AM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*65*










Ana tafiya dasu kowa ya watse ya kama gabansa suna la'antarsu tareda tsine masu Albarka."


Fada maimartaba ya nufa, yayi wa yarima magana da Afnan da Kaka yace "su biyoshi yanaso zaiyi magana dasu."


Fada sarki a kan kujerar mulkinsa,
Gaba d'aya suna k'asa sun zauna had'ida sunkuyar da kansu."


Yayi murmushi yace "Mama kiyi hak'uri na banzar da rayuwarku, Ban rik'e Amana da Aminta dake tsakanina da babban Aminina Alhaji Ibrahim ba."


Nayi sakaci dana bar rayuwarku cikin garari kuna ta wahala a wurin wancan Azzalumin."


Kuyafe min, daga yau k'arshen wahalarku da k'unci yazo k'arshe, Ku d'auka cewa Alhaji Ibrahim ya mutu, kuma ya dawo."


Kaka tace "mungode Ranka ya dad'e, ko hakan kabarmu burinmu ya cika, munga k'arshen Azzalumi."


Kuma burin 'yarka Afnan ya cika domin a duniya bata da wani buri illah ta kwato dukiyarta a hannun Azzalumi Alhaji Aminu."


Ya dubi Afnan yace "matso nan 'yata ta matso kusa dashi tana murmushi. Yace tun lokacin da nasanya idona akanki nakeji a jikina cewa ke jinin Aminina ce,
Amma Wancan Azzalumin yake kawar min da tunanin hakan, sai nake d'auka wata k'ila kamace kukayi dashi."


Ya dubi zoben hannunta ya dubi zoben hannunshi iri d'aya danashi, yayi murmushi yace "Allahu Akbar, wannan zuben dake hannuki 'yata lokacin da mukatafi aikin Hajji da Alhaji ibrahim muka sayeshi a tare."


Lokacin ya d'auki Alk'awarin cewa da zarar yayi aure ya haihu, to duk abunda aka Haifa masa sai ya sanya wannan Zuben a hannunshi."


Kaka ta matso hawaye tace "tabbas anyi hakan, lokacin da zaiyi tafiya dubai kamar yasan ba zai dawoba, ya iskoni har cikin d'akina ya ciro Zoben yabani yace "mama gashi ki ajiye min a wurinki nasan kinfini iya ajiya, idan aka haifa min "ya Mace ko namiji, a sanya masa a hannunshi, akuma shaida mashi cewa babanshi yana sonshi."


Afnan ta fashe da kuka tana fad'in "Abba nima ina sonka Allah ya jik'anka ya haskaka ma kwancinka."


Suka Amsa da "Amin."


Bassam ya dawo kusa gareta ya kamata ya kwantar da ita a kafad'arsa yana d'an bubbugar bayanta alamar tayi shuru."


Sarki da Kaka suka bisu da Kallo suna murmushi."


Sarki yakira sunan Yarima,
Yace "yarima ga Amana nabaka ta k'aunarka kuma 'yar uwarka,
Ka Kula da ita kabata farin ciki Wanda zaisanya nayi Alfahari daku."


Yarima ya runsunar da kai yace to Abba na karb'i Amanarka in Allah ya yarda Afnan bazata tab'a kokawa ba."


"Allah yayi maku Albarka, sarki ya fad'a."


Suka amsa da "Amin."


Sarki yace "sai maganar dukiyar Afnan, wannan jakar dana bata takardune na kamfanonin Da takardun gidaje da filaye, dakuma chark na kud'i kusan biliyan hamsin da uku, to ya kuke ganin za'ayi?"


Kaka tace "duk hukuncin da kayanke ranka ya dad'e duk d'aya."


Sarki ya dubi Afnan yace "'yata zab'i na wurinki ki fad'I duk abunda kikeso ko kike da buri da zakiyi da dukiyar ki."


Afnan ta sunkuyar da kai tace "Abba burina na farko shine na taimaki marayu marasa k'arfi. Na ginawa mahaifana masallaci da makarantu, Allah ya kai lada a cikin kabarinsu."


Sannan daga k'arshe sauran kud'in a bawa yarima, shi yasan abunda ya dace yayi min dasu, da duk wani Abu nawa."


Kaka tace "tabbas kinkawo shawara mai kyau Allah yajik'an wad'anda suka rasu."


Sarki yace "Yarima Allah yabaka ikon kula da dukiyar marainiy."


Suka amsa da "Amin gaba d"ayansu."


Sannan kaka ta mik'e tayi masu sallama zata koma gida."


Afnan da yarima suka shiga yimata magiya a kan tayi zamanta kusa dasu, tace "bazata zaunaba."


Suka dube sarki a kan ya tayasu rok'onta akan ta zauna."


Zai magana kenan yaji tace "zan zauna amma ba yanzun ba, sai kin haihu."


Suka sanya dariya sukace "to Kaka Allah yanuna mana."


Anan sukayi sallama sarki ya Sanya aka kaita gida aka kuma cika ta da kayan more rayuwa."


**************


Tun a wannan ranar Afnan tazama 'yar gaban goshin Sarki, baya son ganin b'acin ranta."


Wanda hakan yana yiwa hajiya zainab bak'in ciki, tanaji tana gani Afnan zata amshe mata tauraruwa a gidan.


Duk inda kashiga bayi da kuyangu sai hirar Alherin Afnan kawai akeyi."


Gaba d'aya labarin Saratu yashafe a gidan kowa ya kama hidimar gabansa."


Wata sabuwar soyayya ce ta kuma shiga tsakanin prince da Angel, wanda sai tarairayarta yakeyi,
Da Zarar sunfara wasanni taga zai zarcewa zuwa wurin boos saitayi mashi dubara ta gudu tayi wurin Anna."


Shi kuma abun yana damunsa gashi mtum ne mai yawan buk'ata."
[3/6, 10:37 AM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*67*














Hakan yaci gaba da yimata, da zarar taci kifi sai labari ya canza salo."


Kusan sau hud'u kenan, Afnan ta rasa gane abunda ke damunta."


Meyasa ta dainajin zafin abunda yarima yake mata,
Kuma abun mmki ita ke nemanshi da kanta?"


Bata mance duk abunda yake shiga a tsakaninsu mai yameta ne?"


Ta tsinci kanta da jin kunyarsa saboda irin abubuwan da take yi mashi da kanta."


Shima ya lura da hakan, amma
Bai damu ba saboda yasan da a hayyacinta take da bazai sameta hakan ba."


Baya gajiya da kasancewa da ita akoda yaushi saboda komai nata mai kyau ne da d'and'ano,


Wuri d'aya yake tausaya mata saboda bata barcin dare, ko kad'an shiyasa yake kyaleta da rana."


Idan suka Shiga bayan sallar isha'i babu wani Abu da sukeyi sai ba Kansu dad'i,
Lallai yanzun suke amarci mai dad'i."


Cikin kwana goma Afnan ta fara tunanin ko akwai abunda ake mata nabawa yarima kanta a sauk'ak'e?"


A Daren yau kam cewa tayi bazataci komaiba
A can wurin Anna taci abincinta ta k'oshi.


Yarima ya gano yau akwai rigima kenan tunda tak'icin komai,
Amma kuma sai ya shareta."


Sukaita kallo har tafara hamma,
taji batajin yanayin da takeji,tayi mmki
Mik'ewa tsaye tayi ta wuce d'akin barcinsu, ta kwanta."


Yarima yabi bayanta, yasan yau zaisha jinini kenan da raki, kuma bazai hak'uraba Dan ya shiryama yau."


Haka ya bita yayita lallab'ata, har yasamu ya biya buk'atarsa cikin kwanciyar hankali, dajin dad'i."
ba laifi, tafara sabawa Dan har tafara zomasa da wani sabon karatu wanda ya dad'e yana mamakinta."


Zaman lafiya da kwanciyar hankali yaci gaba da wanxuwa a tsakaninsu suna son junansu suna tarairayar junansu,
a gaban kowa suna iya nunawa junansu kulawa Da so da k'auna."


Cikin Afnan Kuma sai girma yakeyi,
Yayi mata kyau ta kuma cika tayi k'iba masha Allah."
yanzun tashiga watan haihuwarta Wanda ake sanya mata haihuwa ko yau ko gobe,
Tattali a wurin yarima da maimartaba da Anna abun ba'a magana."


*****************
Da yamma yana kishingid'e a gadina,
Anna tabata _juice_ tace ki tabbatar da yarima ya shashi akwai abunda nasaka mashi a ciki."


"Na minene Anna?" Yasoni ni kad'ai?"


"Jeki ki kaimashi Dan Allah na tsarine,
Ta kama hanya tana tafiya, duk inda ta gifta kuyangu sai sannu ake mata saboda girman cikinta."


Fuskarshi cike da fara'a ya hangota ya mik'e ya tarota ya rungumeta yasanyata a jikinshi yana mata sannu."


Murmushi tayi tace " barka da hutawa my Prince."
Cikinta ya shafa, "barka da zuwa my son, had'ida kaiwa cikin kiss, gaba d'aya sukayi dariya."


Ta tsiyaya mashi _juice_ d'in a cup, ya tsaya yana kallonta yana kallon _juice_ d'in."


Yace " _juice_ ne haka?"


Tasaki fuska sosai ta k'ara matsowa kusa dashi, ta d'auki _cup_ d'in zuwa bakinsa, ya amshi kofin ya rik'e."


Rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita duk ta sukurkurce,
Batun yauba ta lura idan ta kawo mashi _juice_ haka yakeyi sai ya dad'e yana kallon kofin kafin sai ya d'auka ya sha."


Ya maida kofin ya ajiye, ya dubeta "Angel!!!
Ya kira sunanta da murya mai taushi, "me kika saka a cikin _juice_ d'in nan?"


Ta d'an zaro idonta daka kalleta zaka gano a tsorace take, idonsa a kanta ya rik'o hannunta, sai rawa yakeyi."


"Ina saurarenki, ba wannan ne na farko ba,
Waya baki shawarar sa min Abu a cikin _juice_ ?"


"Uhm ban San komaiba."


"Baxaki gaya minba?"
Akwai abunda nake maki Wanda bakiso?" Kike so in daina?"


A'a babu." Ta fad'a a sanyaye.


"Meyasa to?" Tarasa abunda zata ce masa, tayi shuru."
"Kiyi magana mana."


Ya d'auki kofin zai kai bakinsa tace "kada kasha akwai......tayi shuru kuma."


"Kina so ki mallakeni ne?"
Tasaki baki tana kallonshi."


"Bari insha ki mallakeni Angel."


Tayi shuru tasa kanta k'asa,
Ya shanye juice d'in ya ajiye kofin."


Kallonshi takeyi, tace "ya akayi kasani?"


Kema baki bani amsa ba, Dan haka nima bazan baki amsaba."


"Anna ta koya maki?"
Da sauri tace A'a ba ita bace."


"Ina kika samu?"


Ta matso kusa dashi sosai suna iya jin saukar numfashin juna, tace "inasonka baxan iya abunda zan zaluncekaba, ko kuma na cutar da kai. Ka yarda dani."


"Nasani ai bance baki sonaba."


To ka yarda banyi komaiba, yayi murmushin gefen baki yace "na yarda dake Angel bazaki cutar daniba."


A ranta tace "sai nagayama Anna kada ak'ara sawa."


A zahiri kuma hira sukeyi cike da nishad'i, al'amarin yarima yana bawa Afnan mamaki sai kace gaba nai akayi?"


Ko dai akwai mai zuwa yana gaya masa?"


Anna tana bata labarin Bassam tabbas ba k'aramin shiri akayi masaba sai yau ta tabbatar da hakan."


Hira sukeyi suna dariya yana bata labarin d'anta da zata haifa sai kace ya Ganshi da idonshi."


gajiya tayi da zaman ta mik'e tsaye had'ida shagwab'e fuska, ta kalleshi my Prince zanje na kwanta na huta."


Mik'ewa tsaye shima yayi "mutafi na kwantar dake."


Murmushi sukayi suka nufi hanyar sashinsa."


Afnan ce gaba yana biye da ita a baya yana kulata da gefenta da bayanta."


Tana kaiwa k'ofar d'akin tajita ta taka wani Abu mai sulb'i tana k'ok'arin karta fad'in ina sai jinta tayi ta fad'i,
Ta saki wata irin k'arar wahala."

Da gudu yayo kanta ya tallabeta jini kawai ke mata zuba.


Cikin tashin hankalin yashiga kiran sunanta yana girgizata amma ina bata motsi."


Ganin wurgawar mutum yayi da sauri,
bin wurin yayi da ido yana kallo tabbas akwai abunda aka zuba a wurin domin Afnan ta taka ta fad'i."


Haka yayi dai dai da zuwan maimartaba tare da Anna."


Cikin tashin hankali Sarki ya kira fadawa sukazo da mota aka d'auketa tare da Anna aka nufi asibity da ita domin ceto rayuwarta."


Gaba d'aya jikin bassam ya b'aci da jini. Amma bai damu da hakanba, hankalinshi a tashe yake."


Maimartaba yashiga kwantar mashi da hankali, yana tambayarshi ya akayi hakan ta faru?"


Murmushi Bassam ya k'ak'aro yace "munfito kenan ina ganin nakuda ce taka mata tafad'i"


Sarki yace "Allah ya sauketa lafiya, kaje ka can za kayan jikinka.
sai ka k'arasa asibitin ko dayake Anna na wurin tare da waziri da fadawa."


Yana ganin sarki ya tafi, yanufi inda yaga giftawar mutum a lokacin da Afnan ta fad'i."


Wata baiwa ya hango sai kugudu takeyi tanufi sashin hajiya zainab."


Kai tsaye yanufi sashin hajiya zainab d'in zuciyarshi tana ta farfasa."


Baiwar tsugunne a gaban hajiya zainab tana fad'in "ranki ya dad'e nagama komai, a gaban idona ta taka tafad'i yanzun hakan an nufi asibity da ita jini na bata zuba, ai ranki ya dad'e ina ganin da ita da abunda ke cikinta bazasu rayuba."


Dariya hajiya zainab tasaki mai sauti, tace kwananki ya k'are "yar Aljanar yarinya, waya gaya maki ana karawa dani."


Sai a kunnen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login