Showing 21001 words to 24000 words out of 90241 words
Chapter 8 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 da ban aureshiba wata k'ila da yanzun kina lahira".
Maryam ta kuma kallonta tace "kinsan dai wannan alatun ba'a banzaba."
Afnan ta mik'e tayi shigewarta b'an d'aki, Wanda da shigarta tasaki baki tana kallo, a rayuwarta bata tab'a tunanin zataga had'ad'd'an ban d'aki irin wannan ba girmanshi ya kusan girman d'aki,
   Tasan tunda tashigo wannan gidan k'arshenta mutuwa ce, takirata datuna da kalaman Bassam da yace "zan aureki domin in wulak'antaki zaki shiga k'angin bauta Wanda hatta bayina sai sun tausaya maki."
Ta fashe da wani Sabon kuka mai sauti, ta dur k'ushe k'asa a nan tsakar ban d'akin tana k'ara tausayin kanta,
    Da kuma halin da masoyinta yake cikinsa a yanzun, 
    Kuka takeyi sosai kamar numfashinta zai d'auke."
Kwankwasar k'ofar band'akin shi yasa ta daina kukan da takeyi ta mik'e da sauri tana goge hawayenta."
Saiji tayi ana fad'in kifito muyi sallama zamu wuce."
Da saurinta ta bud'e  k'ofa tafito ta rungume Matan malam iro tana kuka tasakesu ta rungume Maryam tasaki wani kuka mai k'arfi, domin ta sadak'ar wata k'ila wannan shine k'arshen ganinsu da tayi, ta kumayi alk'awalin zata dake ta d'auki duk wata wahala da za'a gana mata domin ta ceci rayunka masoyanta da 'yan uwanta."
Maryam ta tab'e baki tace "kaji iyayi kukan me kikeyi hakan?"
    Bayan ke kikasa kanki,
    Kai duniya akwai abun kallo kala kala dibi yanda take kuka sai kace Wanda aka kawota dan dole, to munsan komai nidai sakeni, muyi tafiyarmu inda mukafi wayo."
Haka ta rakasu har bakin k'ofa, tana zubar da hawaye, domin tana ganin kamar ganin k'arshe take yimasu,
    Ta dafa d'aya daga cikin matan malam Iro, tace "inna kuyafemin, kuma kucewa Kaka ta yafemin iya zaman da mukayi da ita, idan na tab'a b'ata mata rai tayafemin dan Allah."
Suna gam da fita falon taji dantijuwar nan mai mutum ci wato jakadiya, tace "ranki ya dad'e ki tsaya daga nan,
   Ta nuna wata kuyanga tace "ke jibo kiyi masu rakiya zuwa wurin mota."
    Ta amsa da "to ranki ya dad'e."
Haka Afnan ta koma tana kuka tashiga d'akinta, ta zauna a kan makeken gadonta, jikinta duk yayi sanyi,
Saiji tayi anturo k'ofa anshigo, jakadiya ce, da masu aiki d'auke da kaya nik'i nik'i kayanta ne da  tazo dasu, nan da nan suka fara shiryasu cikin d'akin da ake sanya kayan sawa."
Jakadiya ta zauna d'aya daga cikin kujerun d'akin tana duban Afnan tana fara'a."
Tace "yarinya meye sunanki?"
Afnan tayi gyaran murya ta sauko daga zaman datayi  k'asan  gado ta zauna kan kafet mai taushi gaske tana magana cikin natsuwa,
 Sunana Afnan."
Masha Allah Jakadiya ta fad'a cikin murya mai walwala."
Taci gaba da cewa "nice Jakadiyar Mijinki wato Bassam kuma nice mari kiyarshi tun yana k'arami nake d'awainiya dashi da kula dashi har zuwa yanzun, Allah yasa ke.a zaki tayani tsakaninki da Allah mukula da marayan Allah."
Suna cikin magana sai gani sukayi anturo k'ofa anshigo,
    Fulani ce fuskarta d'auke da farin ciki, tace 'yata sannu da shiguwa sabuwar rayuwa.
   Idan bazaki damuba inaso insan tarihinki."
Anan Afnan tashiga fad'awa Fulani ko ita wacece da sunan mahaifinta da sanadiyar da yasa suka dawo Gombe da zama."
Suka  tausaya mata gaba d'aya najin cewa marainiya ce gaba da baya."
Fulani tace Allah sarki gashi Allah ya had'aki da wasu iyayen,
   Inaso kizama mai hak'uri da  kauda ido da zaman da zamuyi, kisani shi aure ibadane sannu a hankali zaki sanmu muma musanki 
   Banida burin tsangwama maki nima ki d'aukeni kamar uwar da ta haifeki, inaso ki saki jiki kema nan gidanku ne, kiyi yadda zaki yi gidanku kema 'yace a nan......
    
Ta kalli jakadiya tace "jakadiya cigaba da lurar da ita yanda ake zaman gidan nan, ta juya ta tatafi."
Anan jakadiya taci gaba da lurar da Afnan tana fad'amata k'a idodin zaman gidan sarauta."
Sannan ta gabatar mata da 'yan aikinta, masu yimata hidima."
Talatu 'yar aiki ta matso kusa da ita ta durk'usa  tace "ranki ya dad'e sunana Talatu tare da indo itama ta matso ta durk'usa, zamu dinga yimaki hidima duk abunda kikeso mune basu kula dashi, dan haka gamu munmik'a wuyanmu dan yimaki bautar aiki kowanne irine."
"Madallah." ta fad'a a ranta, tace kafin in mutu zan d'an samu canjin yanayi Dan haka zan saki raina inyi  abunda da raina keso kada in mutu da bak'in ciki biyu ko na b'ata raina ba tsira zanyiba, Dan haka zan sakata in wala in bararraje, aranta take maganar."
Indo tace ranki ya dad'e ruwan wanka anshirya."
Ta mik'e tsaye suma sukayi saurin mik'ewa, suka isa gareta zasu tab'ata, da saurin gaske ta matsa baya tace mezakuyi?"
Ta fad'a cike da tsoro."
"Ranki ya dad'e zamu tayaki cire kayan ne."
"A'a kubarni kuyi tafiyarku."
Tuni yanayin  fuskarsu ta sauya suka zube k'asa suna fad'in "ranki ya dad'e kiyi mana rai, Fulani zata b'ata mana."
Zaro ido tayi waje a zuciyarya tace "wata sabuwa."
    "To Ku zauna can inshiga infito."
A sanayye sukaje sukayi tsaye gefe guda, tashiga ban d'akin,
   Turarunkan wanka da bath liguid kala kala wad'anda bata tab'a ganiba, masu bala'in k'amshi,
   Dama ga Afnan ma abuciyar k'amshi wuri ya d'auke da k'amshi mai dad'i gaske."
Ta nutse cikin K'aton bith d'in ta runtse idonta, kai wannan dad'i da suka bani anya..... Anya na gaske ne? K'ila ma gobe zan bar duniya gara ind'anji dad'i ko kad'an ne."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRIT,ERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
            *19*
*Banda bakinda zan iya Baku hakuri friends a kan rashin ganin typing d'ina kwana biyu, abubuwa sunta faruwa amma komai ya koma dai dai zakujini yanzun akoda yaushe*
Hakan ta kammala yin wankan cikin tunani iri iri,
    Fitowa tayi daga toilet d'in sai  k'amshi take zubawa na turarun kan wanka."
Da sauri Talatu da indo sukayo kanta suka rirrik'ata suka nufi wurin da aka keb'eshi domin kwalliya, sai kirari suke zuba mata."
    Zaro ido Afnan tayi waje ganin sunshiga shafe mata jiki da wani kalar manshafawa Wanda bata tab'a ganin irin shiba, zuciyarta kuma tashiga fad'in "dama haka gidan sarauta yake?
    Ko ko dai ni akeyiwa hakan?" domin lokacin mutuwata ne yaxo?"
Haka sukaci gaba da shiryata kwalliya sukayi mata ta d'aukar hankali, nan take ta canza kama kamar ba Afnan bace, sai k'amshi take zubawa."
Alkibba suka Sanya mata suka zaunar da ita akan gado, had'ida jera mata kirari, daga k'arshe sukayi mata sallama da cewa yanzun Yarima zaishigo."
 Gabanta ne ya fad'i, idonta ya cika da hawaye, domin tasan kalar  zalunci irin na *Bassam* idon har yashigo tasan bazai bartaba wata kilama yasanya bindiga ya harbeta."
Kuka takeyi, da ta tuna da masoyinta Ya Sayyadi,
 ta kuma fashewa da kuka tana tuna ko a wani irin hali yake yanzun?"
         Kalmar da mahaifiyarshi ta jefeta da ita a lokacin da za'a d'aukeshi a sanyashi a mota tayita mata yawo a kai,
     Da take cewa "wlh muddun d'ana ya rasa rayuwarshi a kanki to kisani kema saikin bishi a inda yatafi."
Kuka ta kuma fashewa dashi mai sauti, 
Tana fad'in "kiyi hak'uri Mama, kice kika haifi Malam Nura amma nafiki sonshi, nafikison ya rayu karya mutu, domin shine farin cikina,
   Nasan mutanen duniya zasuyi min kallon na yaudari Malam Nura, 
ba hakan bane Allah yasan abunda ke zuciyata, kuka takeyi sosai tana sambatu."
Daga k'arshe ta mik'e  tsaye ta d'auko  wayarta a cikin Jakarta, ta lalubo number Malam Nura, tashiga kiran wayarshi,
 gata tashiga tana ringing amma ba'a d'aukaba, cigaba tayi da kira tana saraurare har lokacin da za'a d'auka burinta taji muryashi tasan halin da yake ciki koda zata samu sukuni a ranta."
________________________________
Malam Nura kuma tunda aka tallabeshi aka d'orashi a kan gadon asibity be kuma Sanin Inda kanshi yakeba, baci basha sai ruwa kawai ake sanya mashi,
   Mahaifiyarshi kuma inbanda aikin kuka babu abunda takeyi, tana tsinewa Afnan domin duk itace silar jefa  d'anta kwaya d'aya tilo a cikin wannan halin."
   Ringing d'in da yasanya mata a wayarshi  daban ne,
    Acan cikin kwakwalwarshi yaji sautin kiran wayar Afnan na shugowa, motsa k'afarshi yashigayi had'ida motsa hannunshi, a hankali yake bud'e idonshi, 
Mama na ganin hakan tayi saurin mik'ewa tsaye ta nufoshi tana hamdala,
Da sauri tafita   tanufi wurin likita tana shaida mashi ya farka."
Wayar taci gaba da ruri k'okarin mik'ewa yakeyi ya d'auki wayar dake a jiye agefen jakar Mama amma ya kasa."
Mama CE taturo k'ofa tareda likita  tana fad'in ya farka docter zoka dibamin shi wlh shikad'ai gareni a duniya."
Malam Nura sai zura hannu yakeyi yana nuni da wayarshi dake ta ringing alamar so yakeyi ya d'auki wayar,
kallo ya koma gaba d'aya a wurin wayar, mama tayi saurin zuwa wurin wayar da niyar ta d'auka ta mik'a mashi, sai ganin sunan *Preety* tagani a kan screen d'in wayar a nan take ta fahimci Afnan ce, ta mayar da wayar ta ajiye,
   Malam Nura na ganin hakan yafara kiran "Mama Afnan ce,
   Bani na d'auka naji damuwarta, nasan halin da take ciki, Mama Nasan *Bassam*  zai cutar da Afnan.
    Hawaye keta gangaro wa a gefen fuskarshi yana mik'a hannu ya karb'i wayar."
Tsawa ta daka masa wanda tasanyashi yaja bakinshi yayi shuru taci gaba da cewa, a hir d'inka Dana kuma jin ka ambashi sunan Afnan a bakinka, Afnan tayi maka Nisan da bazaka tab'a  samuntaba har abada,
 dan hka idan kana cireta a ranka ka cireta idan ba hakan ba zanyi mummunan  sab'a maka."
Likita duba minshi idan yaji sauk'i a kabamu sallama kai ko be warkeba abamu sallama mu koma gida can yayi jinyar domin na fahimci abunda ke damunshi."
Anan likita yashiga dibashi, ba laifi yaji sauk'i aka rubuta masu sallama, suka koma gida zuciyar malam Nura kullam cikin k'unci da tunanin Afnan d'inshi take"
________________________________
Ita kuma Afnan takira wayarshi yayi sau d'ari amma be d'aukaba hankalinta ya kuma tashi tashiga tunanin ko ya Sayyadi ya mutu ne?"
Jifa da wayar tayi sai a kan k'afar Bassam wanda shigowarshi kenan bata lura dashi ba,
Sai kuka takeyi tana fad'in 
"nashiga uku ya Sayyadi karka mutu kabarni Wlh inasonka banga amfanin rayuwata ba idan babuka a dorun k'asa."
Wani gigitancin mari taji an d'auke mata fuska dashi har sau biyu, dafe kuncinta tayi 
Had'ida d'a kanta sama tana kallon Wanda ya mareta koba'a fad'aba tasan Bassam ne."
Bata sauke idonta daga kallonshi ba taji ya kuma sauke mata wani marin Wanda saida takai kwance."
Shi kuma sai huci yakeyi kamar wani zaki."
Dafe  kunci tayi tana kuka tana kallonshi tana fad'in Allah ya isa azzalumi kawai me namaka?."
Murmushin mugunta yayi yanufota da Sauri da niyar ya kaimata duka,
 tayi saurin mik'ewa tsaye tanufi hanyar fita,
   K'ok'arin bud'e k'ofa takeyi tajita a kulle  alamar ya sanyawa k'ofar key."
Tsaye tayi jikin k'ofar ganin yana tunkarota, rufe idonta tayi tana fad'in dan Girman Allah kayi hak'uri,Dan laifi nayi maka bazan sakeba."
Matseta yayi a jikin k'ofar har suna iya jin fitar numfashin juna ya sanya k'afarshi mai takalmi ya take mata k'afa ya murza,
      Wani irin k'ara tasaki dan azaba tana fad'in wayyo Allah na k'afata."
Kuma d'aga hannu yayi ya kai mata wani marin a fuska,  yace wakike yiwa Allah ya isa?
     Marar kunya marar tarbiya, duk maganganun da kikeyi a kan kunnena,
Bakisan rayuwarki bata da amfaniba sai kin wayi gari kinga nasanya fadawa sun gutsire maki k'afa da hannu, sannan zaki kuma tabbatarwa da cewa bakida amfani a doron k'asa."
Ya kuma kai mata mari had'ida kuma murza k'afarta."
K'ara tasaki had'ida rufe baki  tana kuka, shi kuma sai kallon tsana yake mata,
   
Can tasamu sa'arshi ta rik'a hannunshi ta gantsara mashi cizo, yayi saurin yin baya rik'e da hannu,
Tabi ta k'arshin k'afarshi ta fad'a toilet tasanya key, tana fad'in "nace Allah ya isa, Kuma Allah bazai barka ka cutar daniba, azzalumi kawai mashayin giya."
K'okari yakeyi ya bud'e k'ofar toilet d'in amma ya kasa, sai diba hannumshi yakeyi inda ta cijeshi wurin yayi jajir abunka da farar fata."
Ganin yakasa bud'e toilet d'in kan gado ya fad'a yayi rubda ciki ranshi idan yayi dubu ya b'aci,
   Mikewa yayi yabud'e prege d'inshi ya d'auko robar ruwan faro mai sanyi yakai bakinshi koda zaiji zuciyarshi zatayi mashi sanyi saboda ta farfasa,
Amma INA a banza domin babu abunda kesanyashi yaji yayi saurin mantawa da b'acin rai kamar giya, kuma gashi baya ajiye giya a gida saboda tsaro,
 gashi dare yayi da zarar yafita maimartaba zaiji tashin motarshi."
Hakan yaci gaba da zubawa cikinshi  ruwa mai sanyi har b'arci b'arawo yayi awon gaba da shi."
Itama Afnan a can cikin toilet d'in, takurewa tayi wuri d'aya tana kuka tana kiran Kaka, har barci ya d'auketa."
  
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
          *20*
Kiraye kirayen sallar asuba ne ya tayar dasu 
     Afnan dake makure a toilet,
 tayi saurin mik'ewa tsaye, had'ida furta  addu'ar tashi daga barci a zuciyarta
saida tasamu natsuwa sannan ta fahimci a toilet ta kwana jiya,  zare zare ido ta shigayi cike da tsoro ganin cewa tabbas a cikin toilet d'in ta kwana."
Shima *Bassam*  mik'ewa yayi da sauri yanufi toilet domin ya d'auro alwalla yatafi masallaci,
    Tura k'ofar yayi yajita a rufe, 
   Anan take ya tuna da abunda ya faru jiya,  yace "wato a toilet marar kunyar  yarinyar nan ta kwana kenan?"
Bugun k'ofar yashigayi da karfi, 
      Alwalla takeyi tanajinshi tak'i  bud'ewa."
 tazo wurin wanke k'afarta taji wani irin azabar rad'ad'i a k'afar tata, wurinda Bassam ya takata jiya ne, wurin ya sulb'e yayi ja, idonta ya cika da hawaye tace "Allah shi zaisaka min duk abunda kakeyi mun mugu kawai."
Dukan k'ofar yakeyi amma tak'i bud'ewa,  ranshi ya b'aci, yace "duk kika kuskura na bud'e toilet d'in nan saina kankaryaki,
Ji yayi tace "wlh bazan bud'eba idan kabud'e  ka kasheni idan kana iyawa mugu kawai."
Girgiza kai yayi cike dajin haushi,
 ganin zairasa  sallah, yayi saurin bud'e k'ofar d'aki yafita da saurinshi yanufi massalaci da niyar idan yatafi can saiyayi arwala abunda betab'a yiba,  amma muddun ya dawo saiya kuya mata hankali domin ya fahimci batada tarbiya."
Jin alamar fitarshi da tayi yasanyata ta bud'e k'ofar ta lek'a kanta a hankali jikin k'ofar domin ta tabbatar yana nan ko ya fita?"
Ganin alamar baya nan yafita."
taja wata doguwar ajiyar zuciya,  tafito tasanyawa k'ofar key."
Sannan ta shimfid'a abar sallah ta tayar da sallah."
Bayan ta kammala sallah."
zaune take ta d'uko AlKur'ani tana karatu cikin muryarta mai taushi da dad'i."
Shi kuma Bassam bayan ya kammala sallah, kai tsaye b'angaren maimartaba ya nufa,  domin ya diba ko lafiya yake saboda  kullum a tare suke sallah asuba amma yau bai ganshi yafitoba."
Kwakwasa k'ofar d'akin maimartaba yashigayi had'ida sallama,
    Maimartaba najin muryan Bassam yaba shi umurni da yaturo k'ofar yashigo."
Kai tsaye ya shiga d'akin had'ida sallama, ya durkusa k'asa ya gaida mahaifin nashi,  cike da girmamawa maimartaba ya amsa gaisuwar tashi had'ida tsokanar d'an nashi yana fad'in "ango Mijin amarya kuntashi lafiya lafiya?"
Kuma sunkuyar da kanshi k'asa yayi yace "lafiya k'alau Abbah."
    Hankalina har yasoma tashi rashin ganinka da banyi a masallaciba, nashiga tunani da wasiwasi Alllah yasa dai lafiya kake?"
Maimartaba yayi murmushin jin dad'i kulawar da d'ansa yake bashi,
   Yace "da sauk'i  dai Bassam domin daren jiya bansamuyin barci ba sakamakon matsanancin ciyon kai da ya matsamani amma yanzun Alhmdulullah nasamu sauk'i, kammala Sallah ta kenan kashigo."
Cike da kulawa Bassam ya kalli Mahaifinshi yace "Sannu Abba bara nakira docter Ahmad yazo yadiba jikin naka."
Murmushi maimartaba yayi yace "a'a Bassam kabarshi kawai nasha magani, naji sauki sosai."
Hankalin Bassam bai kwantaba saida yaga maimartaba yatashi yayi wanka ya shirya, sannan sukayi breakfast a tare ya tabbatar da cewa babu abunda ke damunshi, sannan suka fito a tare, maimartaba yanufi fada, shi kuma Bassam yanufi nashi b'angarin, saida yakusan kaiwa b'angaren nashi ya tuna da Afnan, cikin ranshi yace ko ita wancan k'azamar ta fito a toilet d'in?" 
      
Tana kwance a kan makeken gadonta, barci ne mai dad'i ya figeta saiji tayi ana kwankwasa kofa, a hankali ta bud'e idonta cikin fad'uwar gaba domin 
   A tunaninta shine yadawo,
 shuru tayi batada alamar tashi ta bud'e k'ofar saida aka d'auki kusan minti goma ana kwankwasa k'ofar amma batada alamar tashi ta bud'e,
 saida taji murya a waje suna fad'in " wata k'ila Talatu Gimbiya bata tashi daga barciba domin k'ofar a rufe take."
Jin muryarsu Talatu ce, tayi saurin durowa daga kan kadon  tanufi k'ofar d'akin  ta bud'e masu."
   Ganin anbud'e k'ofar sukayi saurin   zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa had'ida  zuba mata kirari."
Kallo tabisu dashi had'ida nuna masu hannu alamar sutashi tsaye."
 Talatu tayi saurin yin magana tace "ranki ya dad'e anshirya komai akan Dinning table, munzone  mushiryaki, domin yau ne zakuyi zagayar gida tareda mai girma  Yarima."
Gabanta ne ya









