Showing 15001 words to 18000 words out of 90241 words
Chapter 6 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 mata."
Dariya yayi "yacewa fadawa wai mekuke jira dashi ne."
D'aukarshi sukayi kamar jariri ko motsi baya iyayi, bare yayi yunk'urin kwacewa, yanaji yana gani yabar *Afnan*  aka sanyashi a mota aka tafi dashi."
Kuka *Afnan* takeyi sosai saboda b'acin rai,da bak'in ciki gata bata iya yin doguwar magana, sai kallo tabi *Bassam*  dashi cike da tsana."
      
Gani yayi tanayi mashi wani kallon rashin kunya  ya taso daga inda yake zaune yanufota ya sunkuyar da fuskarshi saiti fuskarta har suna iyajin saukar numfashin junan,
     Yayi murmushi cikin magana k'asa k'asa yace mata "wannan kallon na meye?" marar kunya."
Kinrabu da masoyinki yatafi yabarki ko?, haka zan aureki in rabaku rabuwa ta har Abada."
Yawu ta tufa mashi a fuska har cikin bakinshi."
Tace "Allah ya tsareni dana aureka."
 "dana aureka k'ara Allah ya amshi rayuwatah."👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
           *14*
Idonshi ya rikid'e zl yakoma launin ja, jijiyoyin kanshi suka tashi alamar b'acin rai ya dunkuli hannun shi👊🏻 da niyar ya kaimata duka,
Komai ya tuna oho, ya yasauke hannunshi had'ida cije Baki, ya dank'o gashin kansa, sannan yafita d'akin da saurinshin."
Fadawa yabawa umurni "duk Wanda yakuskura ya bari tafito to saiya d'aukar mashi mummunan mataki."
Suka amsa da "angama ranka ya dad'e Allah ya tsare mana kai."
Yashiga motarshi rai a b'ace yajata da k'arfi kamar yatashi sama,
   Bezame a ko inaba sai Club."
________________________________
Bayan an sauke malam Nura gida, yi yayi kamar yayi hauka idan yatuna Afnan d'inshi nacan  a hannun azzumi."
Kai tsaye wurin malam Iro ya nufa, cikin tashin hankali ya shaida mashi duk abunda ke faruwa."
Hankalin malam Iro yatashi matuk'a dayaji labarin Afnan na can hannun yarima d'an sarki."
Wayarshi ya d'auka yakira babban d'anshi Sanusi dake zaune a garin Abuja yafad'a mashi duk abunda yakeyi yazo yanzun yana nemanshi,
    Sanusi ya amsa da "to Baba gani nan zuwa."
Ajiye wayar malam Iro yayi yashiga gidan Kaka yasheda mata abunda Nura yafad'a mashi ya kuma kwantar mata da hankali insha Allahu *Afnan* bazata kwana a hannun Azzalumiba, da zarar Sanusi ya duru garin yau."
11:pm Sanusi ya duro garin gombe baizame ko inaba sai gaban mahaifinshi, a nan malam Iro yashiga zaiyana mashi duk abunda ke faruwa, ya kuma kwatanta mashi fuskar *Yarima*
 murmushi Sanusi yayi yace "Abbah nagane *Bassam* d'an sarki Ahmad moh'd,
 wani mashayin giya,
    Nasanshi kuma tsakanina dashi musan juna farin sani"
Sanusi ya mik'e tsaye yace "Baba bari natafi na amso Afnan tunkamin ya cutar da ita domin nasan halin *Bassam* farin sani."
Malan Iro yace "kabi a hankali Sanusi domin shiga gidan sarauta akwai had'arin gaske."
Kaka dake gefe d'aya babu abunda takeyi sai matsar hawaye, tana tausayawa Afnan da yanzun batasan halin da take cikin saba."
Ta kalli Sanusi tace "Allah ya taimakeka yabaka sa'a a kan azzalumi irin *Yarima*."
Sanusi yace "Amin Kaka sannan ya fita."
Yaransa yayiwa waya, a nan take suka hallara a gabanshi yabasu umurnin "duk inda Bassam yake su binciko masa shi."
Anan take suka amsa da "to Oga."
Cikin minti talatin sukayo mashi waya da cewa "sunsamu labarin cewa yana Club, anan sukayi mashi kwatancen Club d'in da yake."
Da sauri Sanusi yashiga motarsa tare da Bodyguard d'insa suka nufi Club d'in,"
*Bassam* da ya iso Club d'in rai b'ace, wuri yasamu a kan wani tebur ya zaune, aka shiga jera mashi kwalabin giya irin tasu ta manya mai tsada  tare da kofi."
Ido rufe yashiga tsiyaya giyar a kofi yana shanyewa, ya d'ora kofi na biyu a kan bakinsa ke da wuya, yaji anzo kusa dashi an tsaya."
baiyi saurin d'aga idonshi ya kalli mai tsayuwar ba sai da aka zauna gefenshi, aka buga teburin dake gabansa saida kwalbar giyar da kofin suka girgiza, har a lokacin kansa a k'asa yake ko motsi baiyiba, balle ya nuna yaji tsoro,
Ya kuma d'aukar kwalbar giyar  ya tsiyaya a kofi, ai kuwa sai Sanusi ya d'auka ya shanye ya ajiye masa kofin."
Anan Bassam ya d'aga kai ya kalleshi fuskar nan tashi a b'ace,
    Duk da jarumta irinta Sanusi sai da ya razana da ganin fuskarsa, har yaso ya gid'eme amma kuma ya dake yayi k'okarin kama kansa, yace
"Kai yaro ina k'anwata take, tun safe da tafito zuwa makaranta angaya min lokacin da kazo tareda fadawa ka d'auketa, ina take?" Ina ka kaimin k'anwa?" Ya k'arasa maganarsa cikin d'aga murya."
Bassam yayi murmushin gefen baki ya kalleshi cikin rashin tsoro ko far gaba,
 yace "danine kai da karage d'aga muryarka, Dan bakasan dawa kake maganaba."
Sanusi yasha  tunkarar mutane daban _daban na kwarai da na tsiya amma bai tab'a had'uwa da mutum mai fuskar damisa irin ta *Bassam* ba."
Ai tuni yakira bodyguard d'insa da hannunsa, babu b'ata lokaci suka zagaye inda suke zaune ko wanne naji da bak'i kamar zunubi fuskarsu babu kyan gani."
*Bassam* yana ganinsu ya kallesu d'aya bayan d'aya, babu tsoro a tare dashi yayi murmushinsa na gefen Baki, ya d'auki kwalbar giyarsa ya tsiyaya a kofi,
Sanusi ya d'auka ya shanye ya ajiye kofin da k'arfi gaban *Bassam* yace "ina k'anwata idan baka fad'a min inda k'anwata takeba komai na iya samunka."
Mik'ewa tsaye Bassam yayi, ya kalleshi da jajayen idonshi yace "k'anwarka tana hannuna  kuma bazan saketaba yanzun har saina koya mata tarbiya wadda iyayenku basu  bata,
    Idan kuma kacika kai jarumine kazo kabiyoni ka amshi k'aunarka."
Bodyguard  din dake tsaye bayan Bassam suka dafa kafad'arshi suna fad'in "kai ka iya bakinka Oga ba tsaran wasanka bane."
Kamin ya rufe bakinshi Bassam ya rik'e hannun da yadafashi dashi, ya d'agashi ya nanashi da teburin wurin, tuni suka bazu suna k'ok'arin dukan Bassam Wanda jikinsa har rawa yakeyi, saboda dama yana jiran Wanda zai yidashi, haba nan fa suka fara duke duke aka b'ata wurin securities da dama suma jiran hakan sukeyi, aikinsu kenan rabon fad'a sunaji da k'arfi da kyar aka samu aka rabasu.
Bassam ya dokesu sosai shi kam be gaji da kokowarba fad'i yakeyi, 
     "Ku kyaleni in dokesu 'yan iska kawai."
Yanuna Sanusi yace "kai kasanni na sanka, idan ka isa kazo muje inda ba'a rabamu banza mai k'aton ciki kawai."
Sanusi dariya ya kyalkyale da ita, irin wannan bai ban haushi yace "nasan kana da zuciya d'an sarki kayi a hankali dani Kansan kowaye Sanusi gwaska."
Kallo Bassam yabishi dashi domin jiyake kamar ya shak'eshi ya mutu yakeji,
Shima Sanusi kallon Bassam yakeyi yana sak'e sak'e a ranshi, kome ya tuna oho, yayiwa bodyguard d'inshi alamar "sutafi."
Bassam ya koma ya zauna  cike da b'acin rai da bak'in ciki, bai tab'a shan sigariba, amma a take ya d'auki kara biyar ya zuk'a ya busar ya lumshi idanunsa, matakin  da zai d'aukarwa Afnan yakeyi, saida ya kusan samun awanni uku a zaune sannan yatashi yabar Club d'in."
Kai tsaye gida ya nufa, inda yasanya aka ajiye Afnan, kasan cewa yaba da umurni a  canza mata d'akin zama 
D'aya  daga cikin d'akunanshi wanda yake hutawa a can aka kaita."
Dashigar shi d'akin yaci karo da ita tana sallah,
  Harara 🙄 ya kaimata cike da tsana, yace "Hmmm."
Ya kuma kallonta had'ida mere baki☹  yace "dubeta saikace ta kwarai kullum cikin sallah amma ta munafurci."
Ya wuceta yashiga ban d'aki yayi alwala yayi magariba da isha'i a  lokaci guda,
Ta kalleshi ta yatsine fuska tace a zuciyarta "ko sallah bai tsayawa yayi ya da kyau ga had'a sallah kai wannan mutumin baiyiba, akwai azzalumi wallahi."
Koda ya idar da sallah ya tsareta da ido yana kallonta, tanaji a jikinta cewa kallonta akeyi, saiji tayi yace mata, "yar gidan tsohuwa maicin goro, kalli nan photo nane yake nuna mata, photon Kakane da Malam Iro da kuma Yaya Sanusi da kuma photon Maryam."
Yace mata na gano cewa keba 'yar kowa bace ba kuma ko maibace bakida gata bakida kowa sai wannan tsohuwar sai Kuma wad'an nan mak'otan naku  dasuka taimakawa rayuwarki saboda suna tausayawa rayuwarki."
To gaba d'ayanku zan wulak'antaku sai kun gwammace bakuzo duniya ba, ita daga k'arshe nasanya bindiga na harbe kan tsuhuwa ta mutu, su kuma mak'atanku sai sunyi dana sanin saninki da sukayi,
"Shi kuma ustaz masoyinki Wanda kuke ikirarin baku iya rabuwa sai mutuwa, to nasa annemo min inda yake kwana, inada matasa da suka shiryu a kan kisa batare da an wahalaba zan basu adireshinsa zasuje su kashe shi a daren yau."
"Dan Allah kayi hak'uri ." Afnan tasaki kuka mai sauti had'ida matsowa kusa dashi."
"Dan girman Allah kayi hak'uri ka taimakeni kabar min Kakata, ita kad'ai ta ragemin a duniya, kafad'i duk abunda kakeso wallahi zanyi maka."
Murmushin mugunta yayi yace "shikenan yimin shuru kiji sharud'd'ana idan kikabi kikayi abunda nakeso to zaki ceci rayuwar kaka da masoyinki."
"Gayamin ko mene ne zanyi wallahi zanyi."👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
          *15*
"Yimun shuru!." Ya daka mata tsawa Wanda saida tayi saurin zabura, had'ida rik'e bakinta."
Sannan yace "ki saurareni da kyau inaso kije gida kifad'awa tsohuwa da Iro cewa aure kikeso nan da kwana uku, 
    Kuma ki shaida masu da cewa kinfasa auren malam Nura ni kikeso a aura maki kuma nan da kwana  uku."
Dafe k'irji tayi cikin tashin hankali tace "aure?" Kuma kai zan aura?"
Yace "eh hakan nake buk'ata, kuma idan kika kuskura kika fad'i nina tirsasaki bayin kanki bane, har kika bari kwana ukun suka wuce to a ranar Kakarki da masoyinki zasu bar duniya."
Kuka tafashe dashi tana fad'in "wayyo Allah wallahi banason su mutu, naji na Amince zan aikata abunda kace domin na cece rayuwarsu, amma kasani har abada bazan tab'a son kaba."
Dariya ya fashe da ita irin ta mugunta nan yace "babu soyayya a tsakaninmu sai dai azaba."
Ya mik'a mata dubu biyar yace "ki hau mota."
Watsa mashi kud'inshi tayi tace "bana buk'ata bana son kud'inka zanje nayi abunda kasanyani tayi fice warta."
Dariya yashigayi yana fad'in "yarinya sai fad'in rai tana magana sanyi_sanyi don tsabagen  yaudara."
________________________________
Bayan Malam Nura ya bar gidan malam Iro, kai tsaye gidansu ya nufa cikin tashin hankali,
Kai tsaye yafad'a a kan jikin mahaifiyarshi yana kuka, kamar wata mace,
 kasan cewar shikad'ai ne d'a d'aya tilo a wurin mahaifiyarshi."
Hakuri tashiga bashi tana tambayarsa abunda ke faruwa?"
Gaya mata yashigayi yana kuka bai k'arasa magana ba numfashinsa yashiga d'aukewa, hankalin mahaifiyarshi yatashi matuk'a da saurita takira mahaifinshi a ka  tallabeshi aka sanyashi a mota aka nufi asibiti dashi."
______________________________
Afnan ta isa gida kowa yana mamakin dawowarta domin gaba d'aya zuri'ar gidan malam Iro suna gidan Kaka suna lallashinta domin hankalinta yatashi matuk'a inbanda kuka babu abunda takeyi."
Kaka na ganinta ta taso da gudu ta rungumeta tana fad'in Alhmdulillah."
Afnan ina fatan baiyi maki illah ba, Kaka ta kuma fashewa da sabon kuka."
Afnan ta dafata tace "daina kuka Kaka babu abunda yayi Mani, lafiya galau muka rabu dashi."
Gaba d'aya suka had'a baki sukace "Alhmdulillah." Malam Iro yace "to ai bari na bugawa Sanusi waya nace gaki kindawo."
Afnan ta kalli malam Iro da Kaka tace "Baba da Kaka inada magana daku, Kaka tace "Afnan  bazaki bari kihutaba kici abinci," diba kigani yanda kika fad'a, kikayi dugun wuya,
 arzikinmu d'aya baiyi maki illah ba, mudai tsakaninmu da wannan yaro sai dai Allah ya isa."
Afnan Tayi murmushi tace "Kaka kenan aiba wani aikin wahala nayiba,
   Malam "Iro yace fad'i maganarki Afnan muna saurarenki."
Afnan ta sunkuyar da kanta k'asa idonta yacika da hawaye amma batabari kaka taganeba tace "Baba Kaka ina neman alfarma a wurinku inaso a d'aura min aure nanda kwana uku da yarima d'an sarki domin yanzun shi nakeso ba malam Nura."
      Tayi maganar cikin d'acin zuciya, amma a fuskartar murmushine da bai kai cikiba."
      Dole tayi hakan domin tasan Kaka da saurin fahimtar abu, bataso su zargi wani Abu."
Kaka tace "Afnan kina da hankali kuwa?" 
     Anya lafiyarki k'alau kuwa?" Keda ko maganar aure bakyaso anayi gabanki meya kawo kice aure kikeso cikin kwana uku?"
Malam Iro yace "wannan Abu ya d'aure min kai, to baza'ayi maki aure nan da kwana ukuba, ke ko aure zakiyi cikin kwana uku har abada bazamu had'a zuri'a da mashayin giyaba kuma azzalumini."
Kuka ta rushe dashi "wayyo nashiga uku kutaimaka min, Ku aura min shi."
Mamaki suka shigayi musammam kaka tunda take da Afnan bata tab'a ganin tashiga wannan halinba sai yau, meke shirin faruwa da ita ne?" Meya sameta?"
Afnan ta kalli malam Iro tace "Baba kajanye maganar cewa d'an giyane baza'a aura minshiba, ninaji nagani haka zan aureshi."
Kaka ta daka mata tsawa tace "bazai yiwu ba."
A za hannun tayi a kai tashiga kuka tana fad'in "wayyo Allah na! Nashiga uku! Kutaima keni Ku aura minshi."
Gaba d'aya rik'e baki sukayi suna kallonta cike da tashin hankali, musamman Kaka da tunda take bata tab'a ganin Afnan ta fad'a cikin wannan halinba sai yau, meke shirin faruwa da ita ne ?"
Tausayi tashiga bawa Kaka, da tuna da cewa marainiyace ba uba ba uba, ga wannan tashin hankalin da ya tunkarota,
Ta durk'usa kusa gareta  tashiga bata hak'uri, a kan ta natsu a bi komai a sannu,
b'are baki tayi gaba d'aya tana kuka wiwi, tana fad'in Kaka bakison in rayu kenan, kinfison in mutu ki huta."
Tun kaka na lallashinta har ta kai da rik'e kafad'arta tana jijjigata,
     Tana fad'in Afnan lafiya kike kuwa?"
    To kisani bazamu d'aura maki aure da mashayiba."
Malam Iro tsaye yayi yakasa magana domin gaba d'aya abun ya d'aure mashi kai mamaki yakeyi sosai"
Mik'ewa tsaye  tayi tana kuka takama hanyar  barin gidan,
Kaka da malam Iro suka had'a baki sukace "Afnan ina zaki?"
     Kaka nabin bayanta tana kiran sunanta."
Ina harta kai tsakar gida, sai cewa takeyi Afnan karki fita, Iro zoka kamomin ita,
     Bata kai k'ofar gidaba taci karo da Sanusi zai shigo gidan,
Saiji yayi  kaka na fad'in a ruk'o mata ita."
Yasa hannunshi ya rik'e hannunta suka dawo gidan tare."
Kuka Afnan takeyi wiwi kukan da takeyi ba wai dan zata rabu da kaka bane, sai ganin tanayiwa Kaka da malam Nura kallon matantu, tana tuna ya zatayi da rayuwarta idan tarasa Kaka, itace gatanta itace bangon jingina warta,
 bata san kowa ba a danginta sai HKaka itace Wanda idan ta ganta take mantawa da cewa ita marainiyace,
   Ta gwammace ita ta fara mutuwa kamin ita ta mutu, ta k'ara sakin wani kuka mai sauti."
Kaka ta rik'a hannunta ta turata d'akinta ta maida k'ofa ta rufe tana fad'in "kina  haukane Afnan?"
Daga cikin d'akin Afnan take cewa "lafiya ta k'alau ni aure nakeso ayi min nan da kwana uku da Yarima ko nakashe kaina...."👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *16*
Dukan k'ofa takeyi sosai tana kuka, ita kad'ai tasan abunda take hangowa kanta."
hankalin Kaka ya tashi sosai, ta kai zaune tareda rafka tagumi, ta Shiga tunanin yanda Afnan ta taso marainiya gaba da baya,
    Taso ta auri yaro mai hankali da natsuwa, Wanda zai kula da ita, ya kuma tausaya mata, saboda maraicinta."
Sanusi dake tsaye ya sunkuyar da Kansa k'asa shima ranshi ya b'aci matuk'a domin ya fahimci duk abunda  ke faruwa."
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli mahaifinshi malam Iro yace "Baba ina zuwa bara nadawo."
Yafita da saurinshi ransa na tafasa."
Kai tsaye Club yanufa domin yasan babu inda Bassam ke zama a dai dai wannan lokacin sai can."
Yayi sa'a kuma ya tarar dashi a zaune a inda yasameshi d'azu,
   gabanshi yaje ya zauna, giyar dake gaban Bassam ita ya d'auka ya sha."
Bassam yadibeshi yace "malam kadaina shamin drink."
Sanusi ya kalleshi kallon gefen ido yace  "kai katurota?"
Bassam ya kallashi yace "wakenan?"
"Afnan mana."
"Wacece kuma hakan."
Sanusi ganin yayi yanaso ya raina mashi wayo, yakira waiter yace "kawo min irin tashi barasar."
Waiter ya kalleshi yace "Oga mai tsadace ba irin wadda kake saya bace."
Yadaka mashi tsawa yace "Kai!! Me ruwanka nace ka kawo min...."
Da saurinshi waiter yace "to Oga." Ya fice."
Sanusi yaci gaba da kallon Bassam yana mashi kallon tuhuma, yayi shuru yana tunanin wani abu game dashi da Afnan, amma kuma bega alamar wani abunba, sai ma firgitashi da Bassam yayi da mazan takarshi."
Haka ya gama shan barasar Shi,
saida ya shanye kwalba uku mai tsada, baitab'a sanin gard'in  giyaba sai ranar, ashe dai ba giya yake shaba burkutu ce aka gyara ake sayar masu, sai yanzun yasan yasha abu mai gard'i."
Ko kamin yagama tunaninshi, ya wai ba Bassam ba alamarsa,
 haka ya tashi, yanufi gida."
Koda yashiga gida maganar d'ayace a kan Afnan, ita fa sai an d'aura mata aure da Yarima d'an sarki nan da kwana uku."
Tsawa yada makata yace Ke! Yimana shuru kincika mana kunne da koke koke, shi wanda kikeyi domin shi, yanzun nafito wurinshi cemin yayi baima sankiba."
Cikin muryar Kuka Afnan tace "wallah k'arya akeyi yasanni kuma munason junanmu, ni adaina zuwa ana tsireshi kadda ranshi ya b'aci, ni kawai a aura minshi









