Showing 36001 words to 39000 words out of 90241 words
Chapter 13 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
  
Yaja ya tsaya cak yana sauraren Anna."
Taci gaba da cewa, tace "kayi hak'uri bata lura bane, amma duk da hak'urin da take baka sai ka daketa?"
   Sannan kuma meye naka a ciki da tafiyar da takeyi tana girgiza, haka Allah ya hallice ta."
 
Yarima yaushe kazama haka ne?" yanzun kwata kwata baka tausayin macce, musamman Afnan?"
   Meta tare maka a gidan nan ne?"
shin Kasan baka son kabud'e ido ka ganta meyasa ka aureta?"
A zuciyarsa yake cewa "domin d'aukar fansa na aureta, yanxun kuma bana son na bud'e idona na dinga ganinta domin yanzun  ta zamar min fitina, duk inda naci garo da ita saita tayi min tabo a zuciya, saita b'ak'anta min rayuwa."
Anna ta katse masa tunani, tace "zoka fita, na sallame ka,
   In har kasan domin kadinga takurawa Afnan ko dukan ta zai dinga kawo ka sashin nan to kadinga yin zamanka a sashinka, gaisuwar ma na gode, idon na buk'aci ganinka ni da kaina zanzo, yana d'aya daga cikin aikina."
Had'e fuska yayi cikin jin haushi yace "yanzun Anna akan wannan Abar kike korata?"
yanuna Afnan da hannu da ta b'oye a bayan Anna sai zarar ido takeyi."
Anna tace "niba korarka nayiba, ta nuna masa k'ofa tace "Yarima Allah yabamu Alheri, 
     Bai kuma yin magana ba,
 yasanya kai yafita, a zuciyarsa ya yana fad'in " ai zan kamata ne a wani wurin sai na koya mata hankali."
Anna na ganin Bassam yafita, taja hannun Afnan suka zauna a kan kujera cike da mamaki tace "ya akayi kika gyara wannan agogon?"
     Kinsan ko shekararsa nawa a jiye an rasa wadda zai iya gyarashi?"
Tabbas Afnan ke 'yar baiwa ce, akwai dalilin da yasa kika shigo rayuwar masarautar nan, amma abunda nakeso dake ki ajiye hikimarki da basirarki akwai lokacin da zaki banyanar dasu, dasu mana amfani." domin yanzun a kwai k'alu bale gabanmu."
Ta mik'a mata  agogon tace ungo tafi ki b'oyeshi inda babu Wanda zai ganshi lokaci na zuwa da zamu fito dashi."
______________________________
Sarki ya Tara matan sa gaba d'ayansu,
Tare  da manya shedu a kusa dashi, yasa aka kira masa Yarima."
Ya d'auko wasu takardu ya mik'awa Yarima,  wasu manya  Gonakinsa ne  Wanda ko wace gona tayi girman rabin gari."
yace ya mallakawa Bassam ita kyauta." sakamakon yafito da rusult mai kyau."
Godiya aka shiga yiwa sarki, Hajiya zainab dake  zaune sai dariyar dole takeyi Wanda tafi kuka cowo."
Bassam tashi yayi daga inda yake yaje gaban Sarki ya durk'usa yashiga jero masa godiya."
Fadawa sai cewa sukeyi sarki ya Amsa Yarima magajin sarki."
       Yarima mai jiran gado."
Daga nan kowa ya tashi yatafi akabar yarima da sarki suna tattaunawa."
______________________________
Hajiya zainab harda kukan bak'in ciki, bata iya b'oye damuwar taba, sai cizon yatsa takeyi tana kai komo a tsakar d'akinta."
Sarkin gida na durk'ushe gefe sai ban hak'uri yake yi yana lallashinta domin yanzun ta saye shi da kud'i yazama na hannun damarta."
Cewa takeyi " ni maimartaba zai wulak'anta?"
Har da cewa ya ba Bassam gonakinsa guda biyu, hala mutuwa yayi da zai raba gado tun yanzun?"
Sarkin gida ya zanyi in wulak'anta Bassam ya zamto ya mutu ko baida amfani?"
Sarki gida yayi k'asa da murya yace "ranki ya dad'e a kwai wani mutum da ya fito yanzun aikinsa kamar yankan wuk'a."
Hajiya zainab ta tsaya tana kallonshi   sannan tace "a ina yake?"
Sarkin gida yace "wanzami ne ranki ya dad'e, kinsan suma akwai su akwai lak'ani...."
Hajiya zainab tace "ka tabbata ya iya aiki?"
"Ranki ya dad'e a gabana sukayi wasa irin Nasu na wanzamai, jaka ce d'auke da kayan aikinsu,
   Wanzamin ya ajiye yace duk Wanda yakeji da k'arfi yazo ya d'auki jakar."
Ranki ya dad'e maza hud'u suka taru amma suka kasa d'aga jakar."
Murmushi tasaki na mugunta, tace "me zai iyayi a kan Bassam kasan yana da taurin ran tsiya."
Sarkin gida yace Abu mai sauk'i idai zaki iya zube kud'i masu yawa, 
    A dunk'ufar da shi wuri d'aya bai iya tashi inda yake daga nan sai barzahu......."
Dariya hajiya Zainab ta kyalkyale da ita,
Ta kalli sarkin gida tace "shiyasa duk a cikin dogaraina nakeji da kai."
"Sarkin gida inaso ka kasa kunne duk abunda Bassam yake ciki ka tabbatar da kazo kafad'a min."
"An gama ranki ya dad'e wadda ta gaji sarauta, babanki sarki kakanki sarki sarauniya maimartaba Ahmad moh'd Allah yaja zamaninki."
Ta zaro dumin kud'i ta mik'a masa shi ko sai kirari yake yi yana godiya." 
_______________________________
Labari ya zowa hajiya zainab cewa Bassam yana so yayi aure."
Cikin kinsa da makirci ta nufi sashin maimartaba, anan take cewa Sarki a bata dama ta samowa Bassam matar Aure."
Sarki bai hana taba illah ma yanuna jin dad'insa da k'arfafa mata gwaiwa, domin ganinta yakeyi kamar ta fara son Bassam a yanzun."
____________________________
Yarima na zaune a sashinsa cikin lambu yana hutawa."
Hajiya zainab tashigo cikin lambun."
   Yarima na kishingid'e yana shan isa, ga d'awaisu nata shawagi gabansa da bayansa."  
Ganin hajiya zainab tanufo shi, yasa yayi saurin d'aure fuska, yana cewa me ya kawo ta kuma?."
   Metake keso?"
Kafin ta iso har kuyangunta sun je cikin sauri sun yi mata shin find'a a gefen Bassam."
Tana isowa d'auke da d'anta Yazeed, bata b'a lokaci ba ta zauna tana ta fara'a a fuskarta."
      A ranta kuma ta kaici ne ke damunta irin yanda taga Bassam ya d'aure fuska kamar baitab'a yin dariya ba."
    Da ita da babu duk d'aya."
Ta kuma k'ak'aro murmushin dole tace "Yarima ga k'aninka na kawo maka tunda na lura baka damu da ka ganshi."
"Sai nake ganin har yanzun baka ga farta min abunda ya faru a can baya ba?"
D'auke kansa yayi, idonsa ya sauka a kan wata barewa dake wasa da 'd'anta."
Ajiyar zuciya yayi har har a lokacin bai kalle ta ba."
Dogaransa keta mata sannu da zuwa."
     Sai a lokacin ya d'an saki murmushi ya dube ta da kyau."
      Duk da manyanta ta shigeta tana da kyau, kyan nata bai dusheba,
     Ransa kuma yace "dama macce mai kyau had'ari ce dan haka na tsani  naga macce kyakkyawa, saboda nasan had'arin da ke tare dasu."
Daga sama yaji tace "Yarima naji ance sarki ya baka manyan gonakinsa guda biyu kayi masa godiya kuwa?"
Murmushin sa yayi na gefen baki,
   Sannan ya kalle ta yace "ranki ya dad'e ai ina ganin a gabanki akayi komai ko kin manta ne?"
  Da alama abun ya tsaya maki a rai."
Shuru tayi tana kallon gefenta, saboda jitayi bata iya k'ara kallonsa, domin yana da wani irin Abu a cikin idanunsa dake sashi yin wani irin girma idan ka had'a ido dashi karon farko baka son kasake na biyu."
[3/5, 4:44 PM] Ummu Safwan WS P1: π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
          *33*
Bata kuma had'a ido dashiba,
   Kuma bata kuma yin magana ba."
Mik'ewa tsayi tayi cikin natsuwa, 
Tana k'ara kallon tsarin ginin sashin Yarima Bassam,
       Tasan nashi yafi nasu nesa ba kusa ba."
Tsarin ginin sa, yafi nasu kyau nesa ba kusa ba."
Mts!!
      Tayi tsaki a zuciyarta tace Yazeed ya ka mata yayi rayuwa a wannan gidan ba kaiba."
A zahiri kuma ta k'ak'aro murmushin dole tace "ina maka murnar zama cikakken mutum." zata wuce kenan,
Bassam ya kalleta yace "bakinzo muyi maganar aure naba ne?"
Ta wangale baki ta dawo ta zauna "tace har naso in mance abunda ya kawoni."
Zan turo maka 'yan mata sai ka zab'a, wacce tayi maka."
Murmushi yayi na gefen baki yace "A'a kitara min su a can b'angarenki in zab'a a can, ko kin manta me uwa ce."
Ta had'iye wani irin miyau da ya zamto mai d'aci a mak'oshinta,
    Sannnan ta kuma mik'ewa tsaye tana tafiya tana cewa "ba damuwa in dai wannan ne kana iya shigowa gobe da k'arfe hud'u da rabi na yamma."
Bai amsa mata ba sai kallon su yakeyi ita da 'yan hidimar ta.
    A ransa ya ce munafuka Allah ka d'aura ni a kanki."
*kuyi hak'uri da wannan*
[3/5, 4:45 PM] Ummu Safwan WS P1: π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
           *34*
*Washe gari* Hajiya zainab ta shirya k'ayataccen biki na musamman.  Ta Tara 'yan mata masu kyau da aji."
Anyi masu kwalliya anshirya su Yarima kawai ake jira yashigo ya zab'a."
  
Shuru ba Yarima ba labarin sa,
    Har kusan magariba bai zoba,  hajiya zainab tashiga bak'in ciki da jin haushi wulak'anci  kunya tata da Yarima yayi mata a idon jama'a, sai cizon d'an yatsanta takeyi, tana safa da marwa a cikin falonta."
Wato ita Bassam zaiyiwa haka?" Ta tara mutane amma ya kunyatata yak'i zuwa."
Tana cikin tunanin ne sai ga d'an aike daga Yarima,
   Cewa a shaidawa Hajiya zainab ba zai samu damar zuwa ba yana wurin wasa da doki."
Tsawa ta dakawa d'an aiken cike da jin haushi, tace "yi min shuru, tashi kabani wuri kar yanzun na Sanya ayi maka bulala d'ari."
Da sauri d'an Aiken yarima yaja 'yan takalminsa yayi fice"
Ta kuma Shiga bakin ciki, tana cizon hannun, ta juya ta kalli sarkin gida dake gefenta zaune tace "Bassam har ya isa ya kunya tani?"
Sarkin gida yace "ina ya isa kuwa?  Tunda a k'ark'ashin ki yake ranki ya dad'e."
"Sarkin gida yaza muyi da abunda ka amso wurin boka?"
   Tunda ko taron baizo ba." Wannan yaro Allah yayi tsinanne wallahi."
Sarikin gida ya kuma runsunar da kai k'asa  yace "karki damu ranki ya dad'e."
A fad'ace tace "ya za'ayi kace karna damu, kasan irin mak'udan kud'in da na kashe wurin amso wannan maganin kuwa?"
To kasani kai ne sarkin gida, kai Kasan yanda za'ayi da hanyar da za'abi a b'ata rayuwar Yarima, idan bakiyi k'ok'arin aiwatar da hakan ba, zan d'auki mataki a kanka, zan  Sa a fille maka kai."
"Tuba nakeyi ranki ya dad'e a gafarce ni, zakiga aikin da zanyi a kansa, kai koda ya bar garin nan sai dai kiji labarin ya mutu mushe ranki ya dad'e a d'an k'ara mana lokaci."
"Shi kenan tashi katafi."
Ya mik'e ya fita gumi sai zubo masa yakeyi, saboda tsabar tsoro ance za'a cire masa kai."
    Yace "kai wannan matar hatsabibiyace idan baka ganta a wuta ba ranar lahira to hayak'i ne ya kareta."
Bassam kuma ya kishingid'e a sashinsa cike da farin ciki, domin yau yasan ya bak'antawa hajiya zainab kuma kad'an ma tagani, domin duk abunda take shiryawa yana sane dashi kuma Allah ba zai bartaba."
Bayan sati biyu da hakan,
   'Yan mata ne su biyar hajiya zainab ta zab'o masu kyau ga aji ta shiryasu da kanta, ga abinci kala kala ta shirya, kowacce tayi shiga ta gani ta yabawa, da ka gansu ka San suna da wani matsayi."
 'ya'yan ciroma ne da waziri har da d'an iya, hajiya zainab ta kirasu tace "yarima ne yake son yayi aure zai zab'i matar aure daga cikinsu."
Kowa nason 'yar sa tazama sarauniya idan Yarima ya amshi mulki."
     Don haka babu b'ata lokaci aka turosu, yau kwanansu uku sai gyara su akeyi."
Da yamma kamar kullum Yarima na kishingid'e cikin garden inda yake shak'a tawa cike da nishad'i d'auke a fuskarsa, iska na kad'awa, can ya hango shigowar 'yan mata,
   Ya juya ya kalli Audu dake zaune a gefensa, yace "Audu  su waye wad'an nan kuma?"
Audu yace "ranka ya dad'e sune bak'in dana gaya maka zakayi."
Bassam yace "amma baka fad'a min yanzun zasu zoba."
Audu yace "haka ne ranka ya dad'e 'ya'yan waziri ne da ciroma da d'an iya suka Zo gaisheka."
Murmushi yayi da ya tuna da hajiya zainab ya riga da yasan duk shirinta ne, yana ganin har yanzun bata san halin shiba."
Sallama da kirarin da dogarai keyi masa yasa ya daina tunanin da yakeyi,
     Yana kallon takon ko wacce a cikinsu babu wanda ba tada kyau, ko wacce tasha ado na alfarma ga tsari."
Sai da suka ajiye abun da suka kawo inda aka shirya kayan ciye ciye sannan suka zauna a kan kafet  mai laushin gaske da aka shinfid'a don zama."
Bassam yasaki fuska yace "ina godiya da tsarabarku gareni."
    Dogarai suka had'a baki sukace Yarima ya amsa gaisuwar 'yan mata adon gari."
D'aya bayan d'aya suka fad'i sunayensu da na mahaifinsu."
     Fuskarsa cike da fara'a yace "nagode da zumunci."
Kowacce a cikinsu ta tsura masa ido ta gid'eme domin Yarima ya kai namijin da dole a soshi ga kyau ga kud'i."
Minti biyar suka d'auka bayan maganarsa, sannan Yusra d'iyar waziri tace "ran Yarima ya dad'e ance zakayi aure kana Neman mata?"
"Haka ne ya fad'a a tak'aice."
"Ko zaka zab'a d'aya a cikinmu domin biyan buk'atarka ta aure?"
Ya k'ura mata ido fuskarta mai tsawo CE, amma bata da muni."
      Murmushin da yakeyi a fuskarsa ya kashe mata jiki, taji  jitake kamar yace ya zab'eta."
Katse mata tunani yayi daya ce " Ku gayawa hajiya zainab ina godiya da tayinta, sai mun had'u zamuyi magana da ita."
Suka mik'e rai a b'ace domin ba hakan suka soba, sun so  yace "yana son dukansu ko a kwarkwara yana iya ajiyesu."
     *ikon Allah 'yan mata adon gari kenanπ€*
Yace "Audu ka d'auko kud'i kaba ko waccensu, "an gama ranka ya dad'e, Allah ya k'ara taimakawa."
Suna wucewa ya tashi ya shiga bedromm d'inshi yacewa Audu "yana so hutu."
Shiga yayi ya kwanta rufda ciki a kan gadonsa, yashiga tunin, mahaifiyarshi, yasan da tana da raye hajiya zainab bazata sanyashi a gaba hakan ba, domin ya lura duk a gidan shi kad'ai ta tsana, to meyayi mata?" Bata tausayinsa ko Dan ganin shi marayane baya da uwa."
Ransa ya b'aci matuk'a ya mik'e tsaye ya bud'e fredge domin d'auko giyarsa yasha, tunawa yayi da ta k'are,
   Ya koma kan gadonsa ya kwanta, yashiga tunani, tunawa yayi da Jummai wadda tazamo kuyangarsa tun yana k'arami kamin yatafi England karatu."
Mik'ewa yayi tsaye yafito falo, ya shiga kwalawa Audu kira."
Da gudu Audu yashigo ya tsugunna gabanshi."
    Yace "gani ranka  ya dad'e."
Bassam ya kalli Audu Yace "ina jummai?"
Audu yace Allahu Akbar, Allah yayi mata rasuwa shekaru biyu da suka wuce."
Bassam ya dafe kaiπ€¦ββAyyah Allah ya jik'anta, ciwo tayi?"
Audu yace "Eh sanyi ne ya shigeta."
Bassam yace "Allah sarki nasan tanada 'ya ko?"
Audu yace "Eh tana da 'ya amma tayi aure."
    Amma akwai jikanyarta da yanzun tana aiki a nan gidan hajiya zainab."
Bassam yace "kaje ka kawo min ita." 
"To ranka ya dad'e."
Rok'on Allah yakeyi Allah yasa bata da kyau, domin yasan kakarta akwai rashin kyau ga kuma bak'i, yasha gaya mata a lokacin da yana yaro ta daina kallonshi, domin tana da manyan idanu kamar su fito waje, ga hancinta a bud'e yake sai a hankali daka ganta kaga irin bayin nan 'yan wahala."
Bayan isha'i yasanya Audu yasawo masa barasa, 
Ya ajiye gabansa,
yana sha yana kallon jikar  Jummai wadda ta kame jikinta wuri d'aya tana gaida Yarima."
Yarima yace wa fadawansa sufita waje,
   Ya maida kallonsa gareta, yayi sa'a kuwa bata da kyau akwai muni kam, gatanan dai, kamar dutse."
 a hankali, ya kai idonsa a kan k'irjinta ba laifi tanasu cikanku, sannan tana da haske, duk da dai bata kai kakarta da muniba amma kuma baka isa kace tana da kyauba."
Ya kuma kallonta yace "meye sunanki?"
 Jikinta na rawa tace "Saratu." Da muryarta kamar ganga. Ba yauk'i irin na 'yan mata da suka amsa sunansu irinsu Afnanπ
Yace " Saratu kinaso?"
Tambayar ta zama shock a gareta bata amsa masaba, don a ganinta ba taji da kyau ba, k'ila dai Aljanine yayi maganar ba Yarima ba."
Ya kuma maimaita maganar, "Saratu kina sona?"
   Zaki iya aure na."
Ajiyar zuciya tayi tana kallonsa, tace "ranka ya dad'e dani kake?"
"Basunanki Saratu ba?"
Bakinta a sake hancinta a bud'e ta rasa abunda zatace tayi shuru tana murzar hannunta."
Audu ya kira, yace "inaso kasame jakadiya ka gaya mata na zab'i Saratu a matsayin mata!"
Audu ya dubi Saratu da Sauri ya dubi Yarima yace "Ranka ya dad'e banji da kyau ba."
Bassam yace "nace ka gayawa jakadiya ta sanar da maimartaba da Fulani cewa nazab'i Saratu a matsayin matar da zan aura."
"Ikon Allah, Audu ya fad'a a bayyane, "ke k'arshen wahalarki tazo, haka Allah al'amarinsa."
Yasanya ta gaba yana ta surutunsa, Allah me yin abinda yake so."
[3/5, 4:45 PM] Ummu Safwan WS P1: π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *35*
Washe gari labari ya  zagaye gari Yarima ya fidda kuyanga a matsayin matar da zai aura."
Tabid'jam!
   A gurin hajiya zainab, guyangar ma  wadda tafi tsana a cikin kuyanginta  mai wanke mata k'afa."
Me Yarima yake son maida ita ne?"
Lallai ya d'aukowa kansa









