Showing 39001 words to 42000 words out of 90241 words
Chapter 14 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 wutar dafa kansa."
     Saratu yake son aure?"
Tun jiya da labari ya sameta ta kasa barci,
  tasanya saratu a gaba,
Tana tambayarta abunda tajeyi wurin Yarima har da ya ganta yace yana sonta."
Taga ita kanta da am macce bata son had'a ido da saratu idan tana mata gyaran farce, da wankin k'afa saboda tsananin muninta bare Yarima."
     
"Idan Saratu ta burge Yarima to kenan ita hauka kawai takeyi  na k'ok'arin  samo masa macce first class kenan."
Jakadiya kuma ta sanya aka warewa saratu sashi guda, inda za'a gyarata, an kuma sanya lokacin aure nan da wata uku masu zuwa."
Sarki kuma abun ya  girgiza shi dajin wannan labari, daga baya kuma yashiga jin dad'in d'ansa yayi abunda ba'a tab'a yiba, kuyanga ta zama sarauniya?"
    Lallai Yarima yazo da nashi tsarin mulkin."
Saratu har yanzun gani takeyi kamar mafarki takeyi, domin a mafarki take ganin komai ke faruwa,
     Har a lokacin da aka wanke ta daga daud'ar da take ciki bata yarda Yarima zai aureta ba."
        
Yau kusan sati d'aya kenan ana koyar da ita yadda zata yi kwalliya da irin shigar tufafin da zata rik'a sanyawa."
A can fada kuma sun kasa yadda da zab'in da Yarima yayi,
    Sarki ya d'aurewa Yarima gindi yace " tunda abunda yakeso ne to kada wanda yasake juya zancen a kyaleshi yayi abunda yake so lokacinsa ne."
Ba'a bari kowa yashiga wurin saratu sai jakadiya, A lokacin saratu tasha wanka da kayan k'amshi ana ta cud'ata da dilka."
Komai yasamu gyara dole ya canza komai muninsa kuwa, saratu tayi fes fes da ita gwanin sha'awa duk da fuskarta ta d'an canza, fatarta tayi sumul sumul, kusan wata d'aya ana ta gyaranta."
Akazo wurin koyar da ita cin abinci, saratu, sannan aka kuyar da ita yanda zata tarbi mijinta, a matsayinta na matar d'an sarki
  Mamaki tashiga yi kodai barci takeyi?"
Kusan watan nin biyu ana Abu d'aya."      Da d'an sauyin abinci da take samu da sauyin yanayi yasa saratu tak'arayin kyau har da 'yar k'ibarta tayi."
A cikin wata na uku aka d'aura auren Bassam da saratu anyi taron sosai, a gari kowa magana yakeyi, d'an sarki ya aure baiwa, masu kushewa nayi masu yabawa sun yaba, dama ai haka rayuwa take babu abunda zakayi ya zama kayi gwaninta ga mutane."
Sashin Yarima aka kawo saratu,
    An gyara wurin tsaf tsaf, Saratu bata iya runtsu idonta, saboda kada ta farka daga barcin da takeyi."
Ga kuyangi irinta sai kai da komo suke mata, suna faman CE mata ranki ya dad'e."
Ango Bassam yana tare da mahaifinsa suna hira a can fada kamar yadda suka saba,
    Maimartaba sai tsokanarsa yakeyi yana fad'in "ango kasha k'amshi saika tashi kaje gun amaryarka na tabbata tana can tana jiranka."
Mik'ewa Bassam yayi had'ida yiwa Sarki sai da safe."
Bassam ya isa  d'aki ya iske Amaryanshi saratu, ko ina a d'akin sai k'amshi yakeyi.'
Tanajin ya shigo ta koma k'asa ta zauna takasa ai watar da abunda aka koyar da ita idan mijinta ya shigo."
Bassam bai damuba yaje yayi wanka yazo ya zauna a gabanta sai zazzare ido takeyi."
Ya kalleta yace "tashi kije kiyi arwala muyi sallah."
Bayan sunyi nafila, ya rik'o hannunta zuwa kan gado ya d'ora hannunsa saman kanta yayi addu'a,
       Sannan yace "kisaki jikinki muyi soyayya ki daina jin tsorona."
Tace "to."
A ranar Bassam ya karantar da saratu ilimin kwanciya,
    Saratu har ihu takeyi na dad'i."
Bassam ya rufe mata baki saboda kada kuyangi sujita."
Itama ba bayaba a wurin kwanciyar su ta farko, Sam Bassam baidamu da rashin samunta da baiyi ba a matsayin budurwaba,
 saboda yasan kuyanga ce,.   Kuma kuyanga komai na iya samunta, don haka bai kyamace taba."
Saratu tasha dad'i sai murna takeyi da godewa Allah tasamu miji kamar Bassam."
Tanaji ana cewa akwai maza masu iya harka, akan Bassam ta shaida domin duk abunda yakeyi cikin sauk'i da hankali yake yinsa,
sai da ya sumar da ita akan dad'i."
Tun daga lokacin idan zai shige wurinta,
 saiba kuyangi da dogarai umurnin suyi nesa dasu, domin yagano Saratu bata iya control d'in jin dad'inta sai tayi ihu da surutai."
Amarci sosai suke kurzawa ba k'arya."
Hajiya zainab ta fara tunanin abunda ya dace tayi da Saratu,
   Ta lura da alama yarinyar zasu goga da ita kenan,
   Tun jiya tatura akira ta amma tak'i zuwa, ya dace ace tana zuwa kullum ta gaidasu a matsayinsu na iyayen Yarima mijinta."
    Har zuwa yau da tayi sati biyu bata zoba."
_____________________________
Jakadiya tashigo da saurinta ta fad'i k'asa a gaban Hajiya zainab tana gaisuwa, tana fad'in "ranki ya dad'e Allah ya ja zamaninki matar Yarima  ta iso dan gaidaki."
Bata amsa ba, sai dai tayi nuni da hannunta alamar ta shigo."
.
Saratu ta shigo cikin k'asaita da isa, ta zauna a kan kujera mai kallon ta hajiya zainab."
Hajiya zainab ta bita da kallon mamaki tace " Ke! Mekike nufi?"
       Munzama d'aya kenan?"
   To k'asa zaki zauna tunda har yanzun ke ak'asa na kike,
 ke matar yarima ce ba matar sarki ba."
Saratu tayi mata wani irin kallon raini tace "Ashe kinsan da haka?"
      Ta fad'a a gadarance."
Sannan saratu ta d'an durk'usa k'asa tayi gaisuwa,
     Kuyangu sukayi saurin  amsa mata, tare da jera mata kirari, suna fad'in " matar Yarima guda d'aya matarsa  da ido bay......
"Kai kuyi min shuru dan ubanku, hajiya zainab ta fad'a cikin jin zafi."
 
Saratu ta kalleta cike da mulki, tace "idan baki bari suka k'arasaba bazan sake zuwa gaisheki ba, tunda yana d'aya daga cikin aikinsu."
Hajiya zainab tasaki baki tana kallonta, 
    Nan fa kuyangu suka zube suna bawa Saratu hak'uri."
Da ka kalli idon hajiya Zainab kasan tashin hankali ya bayyana a tare da ita."
   Amma sai tayi k'ok'arin kame kanta kar saratu ta fahimci wani abun."
Har saratu ta fita kuyangu basu daina ban hak'uri gareta ba."
Hajiya zainab na ganin saratu ta fita, ta aika aka kira mata sarkin gida."
Sarkin gida jiki na rawa yazo, ya zube a gaban hajiya zainab."
Tace "kasan abunda ke faruwa?"
Sarkin gida yace " A'a ranki ya dad'e."
Hajiya zainab tace "inaso ka b'atawa saratu matsayinta a gidan nan."
Sarkin gida yace "ranki ya dad'e metayi?"
"Zagina tayi yanzun nan."
"Iye ranki ya dad'e, meya dace ayi mata?"
"Ina da labarin Yarima jarumine sosai don haka ya dace a sallace ta ya daina jin dad'inta."
Kaga tunda naga irin Matan da yakeso, sai mu had'a shi da wata irinta, har wadda tafita lalacewa."
 Sarkin  gida  Ya jinjina Kansa."
Sarkin gida yace "ranki ya dad'e magana ta kud'ice kinshirya?"
Tayi dariyar keta tace " kaje kasamu d'an jumma ku shirya ko nawa ne zai baka a fara aiki daga yau."
Yace "angama ranki ya dad'e."
Ta kyalkyale da wata kalar dariya, tace "Ni za ki yiwa wulak'anci?"
     Sainaga bayanki shaid'a niya kawai."
[3/5, 4:46 PM] Ummu Safwan WS P1: ๐ *TAMBARIN SARAUTA*๐คด
๐.             ๐คด         ๐
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *36*
A kwana atashi ba wuya ga mai yawancin rai,
     Saratu tasamu kwanciyar hankalin, tayi fes da ita an zama matar manya, babu abunda ke damunta a rayuwa."
Halinta d'aya ne dai sai a hankali na wulak'anta bayinta, domin irin wulak'aci da bautar da tasha a wurin hajiya zainab shi take cewa zata rama a wurin kuyanginta, kwata kwata kuyanginta basa jin dad'inta ko kad'an daga ta buge wannan sai ta naushi wancan."
Juye takeyi kam a  gidan wani wurin  hartafi hajiya zainab mulki."
Hajiya zainab ta zura mata ido cike da mamaki tana kallon ikon Allah."๐ค
     Dole taja da baya domin yanzun lokacin ne,
 Tana gudun kada tayi mata magana tasata jin kunya."
______________________________
Anna na sane da duk abunda ke faruwa a gidan, amma taja bakinta tayi shuru tana zuba ido taga iya gudun ruwansu,
Afnan da taji labarin Bassam  yayi aure, d'aki tashiga ta rufe kanta tashiga rusar kuka, babu abunda take tunawa sai Kaka da malam Nura."
Kwana biyu har da 'yan rama tayi saboda son ganin Kaka da takeyi, kullum duk ta kwanta barci sai tayi mafarkinta."
Kullum  tunanin ta "wai me Bassam yake nufi da ita ne? Meyasa ya tsaneta?" Meyasa baya maida ita a gaban iyayenta." Saboda kawai  mugunta, da tsanar da yayi mata,
ta kuma fashewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya."
Kwana biyu Anna ta lura da Afnan tashiga damuwa, tashiga k'ok'arin kwantar mata da hankali, tana lallashin ta."
 Afnan na kwance abun duniya duk ya dameta tun lokacin da taji labarin Bassam yayi aure, bata kuma samun natsuwa ba."
 Tarasa meyasa ta shiga damuwa."
Anna na bedroom d'inta Afnan ta diba taga bata nan, ta kira wani yaro maiyi masu aiki dake zaune a k'ark'ashin Anna, tace ya rakata wurin Yarima."
Da yamma ne lik'is  Yarima na lambu yana hutawa tare da Saratu, sai hira sukeyi suna dariya."
Afnan ce tafe tareda yaro d'an rakiya Sun nufo wurin Yarima."
     Sabbin fadawa da kuyangin da aka zubawa  Yarima basu tsaron lafiyar shi. Suna ganin Afnan ta nufo su,
Basu santaba don haka suka tsayar da da ita suka hanata shiga, sai sunje sun nemo  izinin shigarta sannan."
Kallo tabisu dashi cike da mamaki,
       Tace "idan kukaje kuce masa sak'o ne daga wurin Anna."
Dajin ta ambaci Anna sukayi saurin bata wuri ta wuce saboda sunsan darajar Anna a wurin Yarima."
  Daga sarki sai Anna sune kawai ke juya Yarima kuma yabi umurninsu a yanda sukeso."
A can ta hango Bassam tare da Saratu zauna da alama suna cikin farin ciki, ido ta tsurawa saratu tana kallonta sai da ta kusan tuntsirewa da dariya data hango k'aton bakin saratu ta wangale shi๐คฃ wai ita nan dariya ta keyiwa miji."
     
Tashiga fad'i a zuciyarta "dama wannan abarce  itace Amaryar da ake cewa ya aura?"
    Tafd'ijam lallai wannan mutumin  yayi dacen mata."
Hangota yayi tafe zata k'araso wurinsu cikin tafiyarta mai Jan hankali, yayi kamar bai gantaba ya shiga yi mata kallon gefen ido."
Lura yayi da inda take kallo Saratu ce ta tsurawa ido, fuskarta na nuna alamar dariya takeso tayi, ta kuma matseta."
         Yasan ba komai zata yiwa dariya ba illah fuskar saratu."
Kuma yasani sarai Afnan bata da kunya sakakkiya ce gata da wautar tsiya, yanzun zata iya kunyata shi a gaban bayinsa."
Had'e fuska yayi, yana jiranta ta k'araso yaji meke tafe da ita?" Meta zoyi nan?" Shi har ga Allah idan ba ganinta yayiba mantawa yakeyi da ita."
Tana k'ara sowa ta kai gwaiwarta k'asa tana gaida shi, bata kalli inda Saratu take ba."
Bassam bai amsa mata gaisuwarta ba, sai ma kallonta da yayi yaji a nan take gabansa ya fad'i da yayi tuzali da k'aramin bakinta, sai da ya lashe leb'onsa na k'asa."
Sannan ya saita kansa yace "meya kawoki wurina?"
     Ya zaki zomin gida batare da kin nemi izinin matar Yarima ba?"
Afnan taji wani Abu mai zafi  ya tab'ata a k'ok'on zuciyarta, 
    Ta juya ta kuma kallon saratu,
    Sannan  tace "kayi hak'uri na katse maka jin dad'i, kana tare da matarka abar sonka."
 sannan ta sunkuyar da kanta   k'asa tace
     "Nazo ne Neman izini a wurinka, inaso intafi gida inga iyayena kullum dasu nake kwana dasu nake tashi a raina."
Kallonta yayi yace "me kika ce?"
"Dan rainin wayyo wato ma baiji abunda nace ba, tafad'a a zuciyar ta."
    Amma kuma tunda ita ke nema dole ta maimata masa abunda take cewa."
Tace "tunda nazo garin nan wata na gama sha d'aya banga kowa nawa ba." Kuma banyi magana da kowa nawa ba,
 na kuma neme wayata bangan taba,
 wani b'arawo ya sace ta."
Dariya ma taso tabashi wato "shine b'arawo?"
      Ya dake ya kuma had'e fuska, yace " Baza kijeba."
 Ta yaya zaki sanya hannuki ki mare yarima d'an sarki sannan kuma kice zaki zauna lafiya?"
 Wato kinaso kice kin mare banza kenan?"
 tunda har yanzun banga na nadama akan fuskarki ba, illah koda yaushe da wata sabuwar rashin kunya kike k'ara yimin, domin ganin Anna tana tare maki, har ya kai yanzun Anna bata son ganina idan kina kusa da ita."
To yanzun ina Anna?"
     Kinkawo kanki zanyi maki abunda naga dama kuma babu Wanda ya isa ya hanani."
Ya kalli yaron da suke tare da ita, yace "kai tashi kayi tafiyarka, kuma muddun kaji Anna na nemanta ka kuskura kace Kasan inda take saina sanya anyi maka bulala dubu." 
 
Da sauri yaron ya tashi yana bawa Yarima hak'uri."
Idanun Afnan suka fara komawa launinja,
Saratu ta d'ago kanta tace "Ranka ya  dad'e wannan kuma wacece?"
"Yace "Baiwar ki ce daga yau."
Afnan ta d'ago idanunta da suka cika da hawaye, tana kallonsa,
      Shima d'in ita yake kallo yace
 "ki zama mai kula   da matata banbaki izinin barin harabar gidan nan ba."
Ya kira Audu." Audu yazo da saurinsa ya matso"
 Yace "wannan Yarinyar ta zama d'aya daga cikin kuyangun gidan nan, kada a bari ta bar gidan nan, kuma kar a bari ta zauna ko ina batare da inda Kunyangi ke zama ba, itama tayi bautar gida, irin yanda kuyangi keyi."
Ya kalli saratu yace gimbiya ko kina da wani aiki da zatayi maki?"
Saratu ta yamutsa fuska kamar kashi๐ tace "ni babu wani aiki da zatayi min sai dai in zata  kula min da wankan tumakina danake dasu."
Yarima yace "duk abunda kikeso tayi maki gaya mata."
A ranta kuma cewa take "can baya zan turaki, wannan kyan naki kamar Aljana ai sai ki amshe min mijina, tunda Nima a kuyanga ya ganni ya aure ni, kema haka na iya faruwa."
Audu ya matso kusa da Afnan yace "tashi mutafi."
Suka bar wurin, Yarima na kallonta yana dariya a can k'asan zuciyarsa yana fad'in bazan gyaleki ba har sainaga nadamar abunda kika aikata min a fuskarki."
Afnan tafiya kawai sukeyi da Audu amma k'afafunta basu da kwari,
     A can k'arshen gida aka kaita, aka nuna mata wani d'aki babu laifi sabon guri ne."
D'akin tabi da kallo gado ne na k'arfe hawa biyu sama da k'asa da alama akwai mutum a na k'asa, na sama ne nata kenan."
zaunawa tayi ta fashe da kuka meyasa Bassam ke son kullum yaga ya wulak'anta mata Rayuwa?"
In gaskiya ne ai itama matar sace."
      Meyasa yake son takura wa rayuwarta bayan ya rabota da iyayenta da masoyinta malam Nura."
     Kuka tafashe dashi mai sauti๐ญ
*Wayyo Allah Afnan๐*
[3/5, 4:48 PM] Ummu Safwan WS P1: ๐ *TAMBARIN SARAUTA*๐คด
๐.             ๐คด         ๐
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *37*
Anna ta diba Afnan sama da k'asa amma bata gantaba."
 ta tambayi su jummai " ko sunga lokacin da tafita suka ce basu gantaba."
Haka tabi kuyangi masu aiki a k'arshinta tana tambayarsu. Amma maganar d'aya ce masu ganta ba kuma  basuga lokacin da tafita ba."
Anna tayi bak'in cikin guduwar da Afnan tayi, tashiga cikin tashin hankali Wanda sai da ya bayyana a fuskarta."
Yaron da yaraketa gidan Yarima yanaji ana cigiyar ta amma yaja bakinsa yayi gum."
    Bare  idan ya tuna da bulalar da Yarima yace zai sanya ayi masa har dubu."
Kusan Sati uku kenan Anna ta hana kanta zama lafiya, tasanya cigiyar Afnan domin bata son Basssm _yasan_ abunda ke faruwa Dan haka tabawa kowa umurnin yayi shuru da bakinsa."
Afnan tashiga k'uncin rayuwa aiki takeyi ba k'afk'aftawa, daka ne kawai batayi ko shi saboda  akwai injinin nik'a a  wurin."
Kwata kwata Saratu ta sanya a  hanata zuwa Sashensu."
Haka ta hak'ura ta zauna a cikin kuyangi kullum sai tayiwa tumaki wanka tare da dokin Yarima sannan ta kuma basu abinci."
Akwai masu yin wannan aikin maza ne bayi, amma gaba d'aya Saratu ta daka tar dasu, tace "Afnan take so taci gaba da gudanar da aikin."
Gaba d'aya yanzun ta daina kwana a d'akin da aka basu sai dai tashiga store ta kwana  saboda wadda suke tare ta da ita ta kore ta, kuma ga mazan da take gani a d'akin."
Duk Wanda yaga Afnan a wannan lokacin sai tabashi tausayi, saboda bata saba da wahala ba, haka nan take tursasa kanta, tana k'ok'arin ganin tayi aikin da aka sanyata ko yin haka ne,
 Allah zai amshi  Addu'ar ta Bassam yaga tausayinta ya fitar da ita a wannan bak'in gidan, ya mai da ita gaban iyayenta."
Tunawa tayi da Kaka sai ta fashe da kuka, tana kallon jikinta da kayan dake sanye a jikinta, irin na kuyangi masu d'auke da  photon *Tambarin sarauta* lik'e a gaban rigar."
Ta tuna da kayan da tazo dasu a jikinta T.shirt ce da zane sai abaya  wadda ta rufe  jikinta da ita."
      Amma saboda zalunci  wannan mummunan mai kama da akwa kwa,
 tasanya aka kwace mata kaya aka bata na kuyangi ta sanya."
A kwana a tashi Afnan har tayi wata biyu a gidan, 
    Saratu bata









