Showing 12001 words to 15000 words out of 90241 words
Chapter 5 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 naganki a gida, daga ranar baZai kuma ganinkiba, suka kalli juna sukayi murmushi."
Motarshi yanufa daniyar  yatafi, amma yakasa sai tunanin kalaman malam Nura yakeyi, da yace masa Azzalumi,  
       Waibasu San koshi wayebane?" sukeson suci zarafinshi,  ya girgiza kai had'ida dukan sitiyari yace "karya ne wlh duk Wanda ya kalleni tun daga shigar kayana zai gane ni jinin saurata ne, musamman idan yayi tozali da *tambarin sarautar* dake gaban hulata."
To suwai basu lura da hakan bane,
     Wata zuciyar tace masa "sun san kai d'an sarkine tsoronka kawai ne basayi."
Ya girgiza kai yace zan ganar dasu, inma basu ganeba, yaja motarshi yayi gida."
_______________________________
Malam Iro ya dawo daga tafiya, 
     Kai tsaye malam Nura ya tunkareshi da maganar auren *Afnan* malam Iro, ya amince ya kuma yi farin ciki sosai domin batun yanzun ba ya yayaba ta da tarbiyar malam Nura."
Bayan kwana biyu  malam Nura yaturo magaba tanshi, aka yanka mashi sadaki ya biya, had'ida sanya masu ranar aure, wata hud'u masu Zuwa."
Murna a wurin masoyan nan biyu abun ba'a magana."
*muje zuwa*π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
          *11*
Gida *Bassam* yadawo, yashiga sak'e sak'e a zuciyarshi, anan take ya yanke shawarar raba *Afnan* da Malam *Nura*."
      Domin idan ya rabasu yasan sai sunfi jin ciyon hakan akan a wani hukunci da zaimasu, 
sannan kuma daga k'arshe zaiyi  amfani da wannan damar ya wulak'anta *Afnan* da duk wasu magoya bayanta."
Yashiga tunanin to ta wace  hanya zaibi domin ganin ya rabasu, rabuwa ta har abada."
A can yatuna da maganar *Maryam* mahaukaciya  datace "ka aureta idan karama marinka saika saketa."
Girgiza kai yayi ya furta a fili  yace "tabbas aurenta zanyi na wucin gadi hakan shi zaisanya narabata da farin cikinta  masoyinta daga k'arshe na  wulak'antata na kuresu gaba d'aya a garin da ita da mahaifanta."
,
Zunbur ya mik'e tsaye, da saurinshi Kai tsaye fada yanufa  wurin *Maimartaba* da sallama yashiga, ya durk'usa k'asa ya gaida Maimartaba,
Cike da walwala Sarki ya amsa gaisuwar *Bassam* had'ida k'ure shi da ido yana kallonshi."
*Bassam* ya mik'e tsaye  yasamu kujera ya zauna had'ida sunkuyar da Kansa k'asa, yana jiran *maimartaba* yai mashi magana sannan yafad'i muk'atarshi."
Kallonshi Sarki yayi cike da kulawa  sannan yayi murmushi, dan ya fahimci akwai muhimmiyar maganar da yazo da ita, idan kuma be fara yimashi maganaba hakan zai koma da ita bazai furtataba sai dai tayita damunshi a rayuwarshi."
Sarki ya kalli *Bassam* cike da kulawa da kuma k'aunar d'an nashi, yace "Allah ya taimakeka  sarki maijiran gado meke tafe dakai?"
*Bassam* yayi k'asa da kai, sannan yayi gyaran murya yace "Ranka ya dade, game da maganar auren da kace ya kamata nayi,
   In har baka riga kazab'a min matar da zan  auraba, ranka ya dad'e zuwa nayi domin na shaida maka da cewa nasamu matar aure."
Murmushin jin dad'i Sarki yayi, yace "Alhamdulillah." *Bassam* naji dad'i sosai da wannan Albishir naka,
    domin yanzun nakeso natura waziri zuwa masarautar Zamfara wurin sarki Anas, ya kaimashi sakon cewa in har beyiwa 'yarshi Fareeda  mijiba nayi maka kamenta domin na yaba da hankalinta da tarbiyarta."
To Alhamdulillah tunda kazo da Wanda kakeso naji dad'i matuk'a Allah ya shi maka albarka *Bassam*."
'Yar wane gida ce? Wace unguwa suke?" 
    Kuma waye ubanta?"
*Bassam* ya  sunkuyar da Kansa k'asa, a zuciyarshi yake cewa, "'yar matsiyatace zuri'ar aljanu, bakowa bane ubanta illah wani gantalanlan tsoho  mai yawo da riga d'aya a wuyanshi."
A bayyane kuma yace "ranka ya dad'e ba 'yar kowa bace, domin mahaifanta basuda wani k'arfi sosai talakawa ne."
Sarki yayi murmushi yace "inason halayenka yarima na taimakon talakan da kakeyi da rashin k'yamatarsu da bakayi."
Yimun kwatancin  gidansu yanzun nan zantura waziri yazomin da mahaifin yarinya sai  a tsaida maganar aurenku."
Murmushi *Bassam* yayi Wanda yafi kuka ciyo, yace nagode Abbah."
a nan *Bassam* yashiga yiwa *Maimartaba* kwatancen gidansu Afnan."
Malam Iro tareda Kaka a zaune a gidan kaka "yana mata bayanin lokacin da yaka mata ayi bikin su  Afnan da malam Nura."
Sai sallamar yaro sukaji a waje yana fad'in "wai ance idan malam Iro yana nan ana sallama dashi a waje." 
Da Sauri malam Iro yace "ganinan zuwa, ya tashi tsaye had'ida yiwa kaka sallama ya fita waje yana mamakin Wanda ke nemanshi a wannan lokacin."
Fitowar da yayi  yaci karo da fadawan sarki tsai tsaye a k'ofar gida,
ganin fitowarshi suka nufo inda yake,
Gaban malam Iro yashiga fad'uwa a nan yashiga tambayar kanshi meke faruwa?"
Tsintar muryansu yayi suna fad'in "Kaine malam iro?"
Malam Iro ya had'iye wasu yawo basu Zafi saboda tsoro. Sannan ya kallesu yayi k'arfin halin yin magana yace "Eh nine wani abun ke faruwa?"
Suka had'a baki gaba d'ayansu sukace "Sarki yace azo masa dakai."
Malam Iro ya razana had'ida zaro ido, yace "da laifin me? Menayi kuma?"
D'aya daga cikin fadawan yace "kabari idan katafi can saikayi wannan tambayar."
Haka malam Iro yashiga mota suka tafi dashi."
   Masu zame a ko inaba sai fada a gaban sarki."
Sarki yasa aka karrama malam Iro, danganen abinci da abun sha, sai a lokacin hankalin malam iro ya kwanta domin ya fahimci cewa bawani laifi yayiba."
Bayan ya kammala cin abincin, sarki ya kalleshi yayi gyaran murya yace "malam iro nasan zakayi mamakin ganinka a gabana, 
    To wannan ba abun mamaki bane, sai alkhairi dakeson shiga tsakanina da kai, da kuma wani taimako danakeso kayi min."
Malam iro ya kalleni maimartaba cikin girmamawa yace "ranka ya dad'e wani irin taimako ne wannan nake dashi Wanda har kake nema a wurina.?"
Marmartaba yayi murmushi, yace "d'ana yarima *Bassam* yaga 'yarka yanuna yana sonta, in har bakayi mata mijiba ina nemawa d'ana aurenta a wurinka."
Malam iro ya sunkuyar da Kansa k'asa yatuna da yanayin da yaga yarima cikin maye haryake tunanin ya aura mashi 'Yarshi Allah ya tsareshi domin 'yarshi mace d'ayace Maryam kuma ya riga da yayi mata miji, d'an uwansa zata aura."
Yace "ranka ya dad'e 'yata 'yarkace duk yanda kaso haka za'ayi, amma Allah ya taimakeka 'yata *Maryam* anriga da anyimata baiko da d'an uwanta zata aura."
Maimartaba ya kalli malam iro, yace "Maryam kuma?" *Bassam* ba. Maryam yake nufiba *Afnan* yace yanaso."
Malam iro ya kuma kallon maimarrtaba yace "Allah sarki *Afnan* yake nufi kenan,
     Ranka ya dad'e Afnan ba 'yata bace 'yar amanace awurina, domin kuwa marainiyace bata da uwa bata da uba, a hannun kakanta mace take itace gatanta sai kuma ni dake kula dasu, domin ina tausayawa rayuwar yarinyar,
              Sarki yace "Allah sarki tabbas marainiyace gaba da baya, Allah yabaka ladar taimako malam iro."
Malam iro yace "Amin."
    Amma ranka ya dad'e ita *Afnan* d'in ba'ayi wata d'aya da amsar sadakinta ba domin har ansanya ranar aurenta nanda wata uku basu zuwa."
Sarki ya girgiza kai alamar gamsuwa, yace "Allah yasanya Alkhairi yasa ayi damu, malam iro kana iya tafiyarka idan shi *Bassam* d'in yadawo sainayi mashi bayani, duk yanda mukayi dakai."
Ya runsunar da kanshi k'asa yace nagode sarki mai adalci ka huta lafiya."
________________________________
Koda malam iro yadawo gida bezame ko inaba sai gidan kaka ya tarar da kaka zaune tsakar gida tareda *Afnan* da malam Nura sai fira sukeyi suna dariya."
Anan malam iro yasamu wuri ya zauna yashiga fad'awa kaka wad'anda suka aiko kiranshi fadawane sarki yaturosu sutafi dashi,
Gaban Afnan da malam Nura yashiga fad'uwa domin sunsan sunfad'a tarkon yarima d'an sarki, kashe kunne sukayi domin su kuma ji me yasanya aka tafi da malam iro." 
Malama iro yaci gaba da cewa "wai wannan hatsabibin d'an nan nashi Wanda ya maida giya kamar ruwan pure water waishi yaga *Afnan* yaji yanasonta kuma aurenta zaiyi."
Kaka ta washe baki tace Allah sarki ai anriga da anyiwa " *Afnan* miji."
*Afnan* tayi saurin mik'ewa tsaya cike da tashin hankali tace "wlh kaka koda maza sunk'are a duniya nasarasa   mijin aure babu abunda zaisanyani na aure mashayin giya."
Malam Nura kuma dake gefe zaune, idonshi sunfara komawa launin ja, saboda tsanin kishi da jin haushi, mik'ewa tsaye yayi batareda yayiwa kowa maganaba ya fita."
Kaka tabishi da kallo had'ida rik'e baki tace ikon Allahπ€
_muje zuwa_
π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
            *12*
" *Maimartaba* ya aiki *Waziri* domin ya kira mashi Yarima."
Waziri Tare da *Yarima* suka nufo fadar *Maimartaba*
      Anan Sarki yabada umurnin da kowa ya watse a basu wuri zai gana da *Yarima*."
Bayan kowa ya fita, Sarki ya kalli *Bassam* da kyau, sannan yace "Yarima inaso ka natsu  ka saurareni magana zanyi da kai."
Bassam ya kuma gyara zama had'ida sunkuyar da kanshi k'asa."
Maimartaba yaci gaba da cewa "Yarinyar da kace mun kanaso zaka aureta,
   To Nayi magana da Mahaifinta yace mun anriga da anyi mata miji domin har sadakinta an karb'a."
   
"Daga nan yake shaida min cewa Marainiyace,
Na kuma tausayawa yarinyar domin marainiyace ba uwa ba uba, a hannun Kakarta mace take zaune
ita ke rik'onta."
   "Wanda kake tsammanin shine mahaifinta Ashe bashi ya haifetaba, mak'ocinsu ne, yana dai kula da itane saboda yana tausayawa rayuwar yarinyar."
"Dan haka kajanye maganar aurenta, dakace zakayi, kafita lamarinta gaba d'aya." domin kasani  cewa haramun ne, Neman Aure kan Aure."
*Bassam* ya d'an runsuna, yace " na fahimta Abbah, amma duk soyayyar da mukeyi da ita bata tab'a nunamin cewa an tsayar mata da mijiba."
 Abba tana sona nima inasonta sosai amma nayi mamakin jin wannan Maganar daga bakin mahaifinta."
"Amma ba komai na hak'ura da ita idan Allah yak'addari  rabona  ce zan aureta."
Maimartaba yace "yawwa Yarima Allah yashimaka Albarka,
 tashi katafi."
Haka Bassam yafito fada yana sak'e sak'e a ranshi,
     D'akinshi ya nufa yafad'a kan gadonshi yayi rubda ciki yana tunani,
Yanzun shi kenan wannan matsiyaciyar yarinya ta mari banza kenan?"
Ya kuma mirginawa daga runda cikin da yake zuwa kallon silin, yashiga tunanin, "tun lokacin da tasanya hannu ta mareshi, be kuma samun farin cikiba a rayuwarshi, kullum cikin tunani yake ta yaya, itama zata kasance cikin bak'in ciki da *k'unar Zuci* domin a rayuwarshi babu wanda yatab'a d'aga hannu ya mareshi sai ita, 
 ita d'inma matsiyaciya  marasa gata, rik'on tsohowa mai cin goro."
    
Ya girgiza kai yace "ina bazai yiyuba, dolene hukunci ya hau kanta."
Da sauri ya duro a kan gado, ya d'auki key d'in motarshi ya fito harabar gidan ya tsaya yana dibe dibe, da alama akwai abunda yake nema."
 fadawa na ganinshi sukayo kansa suna zubewa k'asa suna  kwasar gaisuwa,
D'aga masu hannu yayi alamar ya amsa." 
   Sannan ya kuma kallonsu yace "ina fadawan hukunci?"
Suka amsa da "gamu ranka ya dad'e Allah ya taimakeka ya tsare mana lafiyarka."
Yace "kubiyoni mutafi, akwai inda nakeda buk'atarku."
Da saurinsu suka had'a baki sukace "angama Yarima mai jiran gado."
Mota uku suka d'auka, gamida motar *Bassam* hud'u kenan."
Motar *Bassam* ce gaba sannan ta fadawa na bayanshi,
Kai tsaye unguwarsu *Afnan* suka nufa, sukayi sa'a tafito  sanye da uniform zata makaranta, malam *Nura* na gefenta d'auke da jakarta suna tafiya suna fira."
Burki *Bassam* yayi da k'arfi yaja ya  tsaya,  yana kallonsu yana murmushi gefen baki."
Da gudu fadawa suka fito gaba d'ayansu suka shiga tambayarshi "ko wani Abu ke faruwa?."
Murmushin mugunta ya kumayi Sannan ya kallesu, had'ida da nuna masu su *Afnan* yace "kuje Ku kamomin wad'ancan yaran yanunasu da hannu "ku sanyasu a mota ku tafi dasu gidan hukunci a jiyemin su kamin nazo."
Cikin girmamawa sukace "angama ranka ya dad'e."
*Afnan* da *Nura* dake tafiya basuma lura dasuba,
    Sai ganin fadawa sukayi tsaitsaye a gabansu sunzagayesu kowane hannunshi  d'auke da k'atuwar bulala."
     
D'aya daga cikin fadawan wani k'ato maigirman jiki, ya kalli *Nura* da *Afnan* yace " *Yarima* ne yace azo mashi daku, dan haka kuwuce mutafi."
*Afnan* ta kallesu a wulak'ance cikin muryanta mai sanyi tace "wanene *Yarima*?"  Wayeshi a garin nan?"
  " To Kutafi kuce masa bazamu zoba saboda bai isaba."
Wani bafade dayaji kalamanta sunyi tsauri dayawa ya hasala da kalaman *Afnan* ya zuciya ya d'aga bulala zai doka mata,
      *Nura* yashige gabanta ya kareta yana kallonsu d'aya bayan d'aya,
    yunkuri yayi domin bugawa *Nura* Bulalar saiji yayi a bayansa *Yarima* na magana yana fad'in "karka dakesu, 
        Cewa nayi kutafi dasu gidan hukunci idan  kuma suka sanya tsaurin  kai ku d'aukesu a kai kusanyasu a mota kutafi dasu."
Kallon tsana  *Afnan* tabi yarima dashi, zatayi magana kenan, taji malam *Nura* na fad'in karkice komai *Gimbiyata* mubisu mutafi muga iya gudun ruwanshi."
Kallo *Bassam* yabi *Nura* dashi yayi murmushin mugunta, 
    Amma kuma Kalmar *Gimbiyata* ta tsaya mashi a rai."
π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
         *13*
*DIDECATED TO AISHA A MOH'D*  
        ( _yayi sake_)
Gidan hukunci aka nufa dasu, 
    Aka ajiyesu a cikin wani  d'aki marar yalwa."
*Bassam* ne ya turo k'ofa yashigo cike da k'asaita, fadawa suntake mashi baya, sai kirari suke zuba mashi."
   Afanan da Nura Atare suka d'aga kai suka kalleshi, kallon tsana."
*Afnan*   tace "dan Allah bawan Allah kayi sauri kafad'i buk'atarka da kuma dalilinka na  yasanya  a  satomu aka kawomu wannan kucakin gidan." 
Ido ya kura mata cike da mamaki da kuma k'arfin hali irin nata naraahin tsoro."
  murmushi yayi yace "idan kika kuma yin magana saina sanya fadawa sunyi maki bulala goma  yanzun nan."
*Nura* ne yayi mata alama da tayi shuru karta kuma yin magana, domin yaga fuskar *Bassam* ba wasa a cikinta komai zai iya aikata mata tunda azzalumine."
Kujera fadawa suka d'ora mashi ya zauna yana fuskartarsu, sannan yayi murmushi had'ida gyaran murya, ya kuma kallonsu yace "masoyan juna."
      Kunsan dalilin da yasanya nace a kawo man kunan?"
Kallo suka bishi dashi babu Wanda ya tanka mashi."
 yaci gaba da cewa "saboda inyanke maku farin ciki rayuwarku, kamar yanda wannan mai kama da Aljanun ta yankemin nawa farin cikin lokacin da tasanya wannan mataccin hannun nata ta mareni."
Dan haka abunda nake so daku nake kuma baku umurni shine daga yau bakai ba wannan abar, yanuna *Afnan* ta wurga mashi hararaπ
"kema bake ba wannan ustazun dolene Ku rabu, domin na fahimci   rabukun da zanyi shine silar yankewar farin cikin rayuwarku gaba d'aya."
Be rufe bakiba *Nura* besan lokacin da yace  "baka isaba wallahi"babu Wanda ya isa ya rabani da Afnan sai mutuwa kai ko kasheni zakayi wallahi bazan rabu da itaba sai na aureta."
Kallo *Bassam* yabishi dashi yana girgiza kai, yace "hattara ustazu ba'a fad'a ina fad'a,
    Yace "sarkin hukunci."
Da gudu sarkin hukunci ya k'araso ya zube k'asa yana fad'in "gani ranka ya dad'e."
yanuna malam *Nura* yace afita dashi waje ayi mashi bulala goma, sannan adawo dashi."
Haka fadawa suka d'auki *Nura* akayi mashi bulala goma sannan aka dawo dashi."
Babu abunda Afnan takeyi sai zubar da hawaye tana ganin yanda  ake zalunci k'iri k'iri."
Kallo yabi *Afnan* dashi yaga yanda take kuka, yayi murmushi yace "bakiyi kukaba za dai kiyi kukan lokacin da aka d'aura min aure dake."
Tayi saurin d'aga kanta sama ta kalleshi cikin muryan kuka tace "Allah ya tsareni na aureka, Dana aureka k'ara Allah ya amshi rayuwata Azzalumi kawai."
Yace "aikuwa sai dai ki mutu domin kuwa mutuwarki tafi komai sauki gareki, da irin k'angin bautar da zaki Shiga bayan na aureki."
Ya juya ya kalli malam *Nura* yace ko kanada magana?"
*Nura* baima kalle inda yakeba bare ya tanka mashi, domin jiyake kamar ya shak'eshi ya mutu yakeji."
Dariya Yarima yashigayi yana kallon Nura da Afnan yana nunasu da hannu, yana fad'in "yau ina soyayyar da kukeyi take?"
Ya kuma kallon Nura yace karka damu da halin da ka tsinci kanka  a cikin   masoyiyarka *Gimbiyarka*ce ta daza maka."
Kallon *Afnan* Nura yayi da ta had'a kanta da gwaiwa sai faman kuka takeyi,
 tausayi tabashi matuk'a, shima idonshi ya rik'id'e zuwa launin ja, amma bashida halin lallashinta saboda wannan azzalumin yasanyasu gaba."
Kallonsu  *Bassam*  yakeyi d'aya bayan d'aya,
 yanayin da ya gansu a ciki yanzun yayi mashi dad'i sai murmushi yakeyi."
Fadawa yakira sukazo da sauri, "yanuna malam Nura yace "kud'aukeshi Ku maidashi inda kuka d'aukoshi, 
      Domin ina ganin nadama a fuskarshi,
    Ita kuma wannan ku barta nan har sai lokacin da naga tayi nadama."
Malam *Nura* najin hakan yace "wallahi bazan tafi na bar Afnan wurin Azzalumi irinkaba k'ara ni kacigaba da rik'eni a hannunka ita kasaketa ta koma gida,
"Amma bazan tab'a tafiya nabarta a wurinkaba saboda ba imani a zuciyarka komai kana iya aikata









