Showing 9001 words to 12000 words out of 90241 words

Chapter 4 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9825

rayuwarsu, ko ba komai kasanyasu cikin k'uncin da bak'in ciki rabuwa da masoyi."


Murmushin mugunta yayi yatashi ya fad'a toilet domin yin wanka."




Hajiya Zainab kai tsaye tanufi b'angaren *Bassam*
Fadawan dake gadin b'angaren nashi, suka bita da kallon tuhuma."


ganin da tayi suna mata kallon tuhuma ne, yasan yata, tayi saurin wayan cewa da cewa " *Bassam* ne yanemi tazo domin zasuyi wata magana ne."


Suka bata hanya tawuce, shigarta pollon taci karo da me kula da abincinshi d'auke da tiren abin da yabata umurni ta had'a mashi kafin yafito daga wanka."


Hajiya Zainab tasanya hannu ta k'arb'i abincin tace "bara nashigar mashi dashi, ina tunanin wanka yakeyi, tamik'a mata tiren abincin itama ba dan ranta yasoba."


Sand'a tashigayi ta bud'e k'ofar d'akinshi taji saukar ruwa natashi da alama har yanzun wanka yakeyi be kammala ba."


tayi murmushin mugunta, domin hakan yabata damar aiwatar da mugun nufinta gareshi."




*Bassam* kuma wanka yakeyi saiji yayi motsi yayi yawa a pallonshi,
Yayi saurin watsa ruwan a hankali, yasanya jallabiyarshi yanufi pallon dan ganin meke faruwa?"


Tura k'ofar pallon yayi yaci karo da Hajiya Zainab a kan abincinsa, tana kulle wani Abu a Leda a hannuta,


tana kuma neman tura ledar a zanenta, d'agowar da zatayi sukayi ido biyu dashi, tayi saurin wayan cewa had'ida fad'in "barka da fitowa Yarima mai jiran gado,
jiya kasanyamu a tashin hankalin rashin ganinka baka kwana a gida."


Murmushi yayi had'ida cije baki, yasamu kujera ya zauna yana kallonta, sannan yace "yauwa barka dai."


Ganin kamar be lura da abunda ta aikata masaba, yasanyata taja wani dogon ajiyar zuciya tace "ga abincinka nan kaci mana nasan kana da buk'atarshi."


Ya kuma kallonta yayi wani kalar murmushi na gefen baki,
Yace "nagode Hajiya amma da alamar kamar ke kika shiryamin wannan liyafa hakan ko?"


Tayi dariya jin dad'i tace " nice mana "Yarima d'an sarki kwaya d'aya tamkar da dubu, ai dole musoka mu kuma tarairayeka."


Yace "Nagode Hajiya."


Tace "ba damuwa, bara na zuba maka kaci,
Bayan ta zuba mashi a plete tace "kaci mana, had'ida tura mashi a gabanshi."


Ya kuma kallonta da kyau, yayi murmushi, yace "daina sauri Hajiya ci zanyi yanzun nan kuwa."


ya nuna mata kujera a kusa dashi yace "zauna anan idan na kammala cin abincin akwai maganar da nakeso muyi dake."


Cike da zak'uwa yayi yaci abincin ya mutu kowa ya huta, yasanya tayi saurin zama a kan kujerar da yanuna mata."


Ganin ta zauna ne, sai ya tura mata plete d'in abincin a gabanta, yace "faraci sai nima naci."


Cikin fad'uwar gaba tace "A'a Yarima ni a k'oshe nake kaci kawai kai kad'ai a shirya mashi, had'ida k'ara tura mashi plete d'in a gabanshi."


Ya canza fuska ya koma mata *Bassam* d'inda tasani Wanda babu wasa a fuskarshi komai yana iya aikata mata a yanzun."
Ya kuma tura mata da plete d'in gabanta yace "Hajiya saikin cinye abincin nan gabaki d'aya sannan zakifita a d'akin nan idan ba hakan ba to kasheki zanyi yanzun nan."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
_____________________________






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




*9*






Mik'ewa tsaye *Hajiya Zainab* tayi cike da tashin hankali a fuskarta,
Amma sai ta wayance, ta kalli *Bassam* tace "bud'e idonka da kyau *Bassam* ka diba ka fahimci Wanda ke gabanka, harkake cewa saina cinye abinci ko kuma ka kasheni,


Wato kana tunanin zan cutar dakai kenan ko?"
Tabbas yau kanuna min cewa banice na tsugunna na haifekaba."


Tsawa ya daka mata Wanda batasan lokacin da ta Kai zaune ba,
Kallon fuskarshi tayi taga ya canza mata kamannin kamar ba *Bassam* d'in da tasaniba."


Yace " *Hajiya Zainab* kinsan bana son yawan surutu, bare gardama, karki kuskura ki kuma bud'e baki kiyumin magana,
batare da kincinye abincin da ke gabankiba."


Idan ba hakan ba yanzun nan zan kasheki, in kuma kashe banza."


Mikewa tsaye yayi ya jawo wata durowa, ya d'auko bindiga, ya saita mata ita saitin fuskarta yace zakici abinci ko sai na aikaki lafira yanzun."


Jikin *Hajiya Zainab* ya soma rawa kamar mazari, sai zufa take fitarwa kamar ruwa,
Ta shiga yimashi magiya tana fad'in "natuba *Bassam* kayafemin, ka d'auki ko wane irin mataki a kaina, batare da naci abincin nan ba, wlh mudun naci abincin nan mutuwa zanyi, domin guba ce a cikinshi."


A razane ya kalleta, yace "guba ce a ciki?" amma kikeso ni naci?" Wato burinki a duniya kiganni na mutu ko?


Me natare maki a rayuwa da kikeson ganin bayana tun ina k'aramina?"


to yau wasa ta kai k'arshe tsakanina dake, domin idan baki kasheniba ni yanzun ni zankasheki, da kuma abunda kikayi niyar kasheni dashi.'


Ya kuma saita bindigar a goshinta yace "zakici abincin ko saina k'arasa dake lafira."


Fitsari tasaki,
jikinta na rawa, tarik'e mashi k'afa tana kuka tana magiya."


D'aga bindigar yayi ya harbi sama, k'arar kukan bindingar ya gauraye gidan sarautar gaba d'aya, *Hajiya Zainab* kuma tayi mutuwar zaune, domin ta d'auka sakar mata ita kayi akai, gaba d'aya tajik'a zanenta da zawo da fitsari sai mulmula takeyi a tsakar d'aki."


Tsawa ya daka mata Wanda yasanyata tadawo hankalinta, sai a lokacin ta fahimci cewa ba mutuwa ce tayiba,
Yanuna mata kujerar da abincin yake kanta, yace "dawo nan ki zauna, magana ta k'arshe zanyimaki wadda daga gareta bazan kuma yimaki maganaba sai dai ki tsinci kanki a lafira,


Tasowa tayi ta zauna a kan kujeran, ya tura mata plete d'in abincin gabanta yace "canyeshi duka, ya koma kan kujera da ke kallonta ya zauna rik'e da bindiga yana kallonta."


K'arar bindigar da maimartaba yaji, hankalinshi yatashi yashiga mamaki ina ake harbi a cikin gidanshi,
Waye aka kashe a gidanshi."


Be gama rufe bakiba sai ganin fadawan yayi wad'anda ke gadin b'angaren yarima sun iso a gid'eme, suka zube a gaban shi,
hankalinsu a tashe, suka had'a baki gaba d'aya suka ce, "ranka ya dad'e a kwai matsala a b'angaren *Yarima* domin tun d'azun *Hajiya Zainab* tashiga bata fitoba daga k'arshe sai k'arar tashin bindiga mukaji yana fitowa daga ciki."


Hankalin sarki yashi be tsaya suka iyar da maganarba ya mik'e tsaye fadawa suka rufa mashi baya da saurinsu suka nufi b'angaren *Yariman*."


Suna gabda shiga sukaci karo da *Fulani* tare da Hajiya Amina suna sauri zasu nufi b'angaren yariman domin sun fahimci k'arar bindigar da sukaji a can yafito, *Fulani* kuma tasan halin yarima da zuciya komai zai iya aikatawa idan ranshi ya b'aci."


Babu Wanda yayiwa wani magana gaba d'ayansu suka d'unguma suka shiga b'angaren nashi."


*Hajiya Zainab* kuma rik'e da cokalin abinci a hannunta sai cakud'ar abinci takeyi, hannunta sai rawa yakeyi, tanayi tana kallon *Bassam*,
Wata hararace ya wurgomata had'ida kuma saita mata bakin bindiga a fuskarta, yasanyata tayi saurin d'ibar abincin zatakai baki kenan sarki yaturo k'ofa tareda mak'arraba sa."


Ganin da tayi sarki yashigo yasanyata sakin cokalin abincin tanufi bayan sarki da gudunta ta b'oye, tana fad'in "Ranka ya dad'e ka taimakeni *Bassam* zai kasheni."


Gaba d'ayansu toshe hancinsu sukayi sakamakon wani kalar warin zawo da sukaji *Hajiya Zainab* nafitarwa,


Sarki yashiga salati yana fad'in lafiya Hajiya Zainab meke faruwa meya kawoki b'angaren *Bassam*?"
Wai yaushe ya dawo, a ina ya kwana Daren jiya?"


Haka sarki yadinga jefo tambayoyi, amma besamu amsar ko d'ayaba."


*Fulani* da saurinta tanufi *Bassam* ta dafa kanshi tace "yarona ina fatan babu abunda yasameka?"


Ya girgiza kai alamar babu." domin saboda b'acin rai ko magana baya iyayi."

*Hajiya Zainab* dake b'oye a bayan sarki, sai magiya take mashi, sarki ya doka mata tsawa, yace "ya isa *Hajiya Zainab* kiyi min shuru naji magana daga bakin *Bassam* tunda na tambayeki kinkasa fad'amin abunda ke faruwa."


*Bassam* zaune a kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana girgiza k'afa rayuwarshi idan tayi dubu to ta b'aci."


Sarki na ganinshi cikin wannan yanayin yasan lallai ba k'aramin Abu akayi mashiba,
Ya nufeshi had'ida dafa kafad'arshi yace "yi hak'uri *Yarima* kwantar da hankalinka kafad'a min abunda ke faruwa."


D'ago kanshi yayi daga sunkuyen dayake, ya kalli maimartaba, idon nan nashi sunyi jajir,
Dakyar yabud'e baki yace " babu abunda yafaru Ranka ya dade, illah abun farin ciki da yasamu a gidan nan.


Sarki yace "abun farin ciki kuma yarima kamar Yaya?"


*Bassam* yace bayan nadawo daga wurin walimar abokina wadda yayi tabud'a wani babban store na kayan masarufi, sai dare yayi mun, a can, kasan cewar kabani umurnin cewa na daina yawo idan dare yayi, shine na yanke shawarar kwana a can da safe idan nadawo nayi maka bayani."


Bayan nadawo ne, sainaci karo da Hajiya Zainab tashiryomin kwarya kwayar liyafa ta tarbona domin tace nasanyata a tashin hankalin rashin kwanan da banyi a gidaba."


Naji dad'i sosai ranka ya dad'e a tayani godiya a wurin Hajiya Zainab."


Fadawa suka dinga cewa "Allah yabiyaki gimbiya Yarima na godiya."


Hajiya Zainab ta kumayin tsoru tsoru da ido."


*Bassam* yayi murmushin mugunta na gefen Baki, yaci gaba da cewa, "Ranka ya dad'e idan ban mantaba kasha yimin umurni da cewa duk Wanda yabani kyautar abinci ko wanne irine nace yafaraci idan yaci sannan nima sainaci."


Sarki yace "tabbas hakane yarima."


Yarima ya girgiza kai yace "Ranka ya dad'e kabawa matar ka umurni da tafaracin abincin da takawomin sannan nima sai naci domin yunwa nakeji sosai.'


Sarki ya juya ya kalli *Hajiya Zainab* yace " *Hajiya Zainab* zokici abincin nan kiyi ko cokali biyu ne, sannan sai yarima yaci domin yace yunwa yakeji."


Kuka tafashe dashi kamar wata k'aramar yarinya tace dan "Allah maimartaba ka rufamin asiri wlh da zarar naci abincin nan mutuwa zanyi saboda akwai guba a cikinsa."


Salati kowa yashigayi suka had'a baki gaba d'ayansu sukace guba." kallonta, sarki yayi yace "amma dai Hajiya Zainab kinbani mamaki, ashe dama kina nan da mugun nufinki na sai kinga bayan *Bassam*


Yace "todaga yanzun nacireki a cikin jerin matana daga yau
Ya juya ya kalli fadawan dake tare dashi yace "ku kamata Ku kaita gidan hukunci a hukunta dai dai da lafinda tayi,
idan angama hukun tata, a kaita wancan b'angaren inda ba mutane a cikinshi taci gaba da rayuwarta a can."


Ya dafa kan Bassam yace Allah yayi maka albarka insha Allahu Allah zaici gaba da tsaremin kai a duk inda kake."
👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
_____________________________






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






*10*




"Sunkuyar da kansa k'asa yayi yace "Amin *Abba*."


Sannan *Maimartaba* yabada umurni kowa yayi tafiyarshi yana buk'atar ganawa da *Yarima*


Hakan takasance kowa ya watse akabar *Maimartaba* tare da *Yarima*."


Sarki ya yatafi kan kujerar dake kallon ta *Bassam* ya zauna had'ida k'ura mashi ido yana kallonshi cike da tausayin d'an nashi."


*Bassam* da kanshi ke sunkuye a k'asa, hawayen da yakeso yafitar tun d'azun ganin fadawa yasa ya rik'eso, sai yanzun suke fita a idonshi."


Sarki yataso ya rungumeshi yabashi tausayi matuk'a domin rabon da yaga hawayen yarima na zuba,
tun lokacin yana k'araminshi. Ko a lokacin ba k'aramin Abu kesanyashi kukaba sai kuma yanzun,
tabbas yau anbak'antawa *Yarima* rai."


Kuma rungumeshi yayi gam a jikinshi kamar k'aramin yaro,
Yashiga cemasa "yi shuru *Yarima* daina kuka duk wani Wanda ke bibiyarka da shairi Allah zai saka maka, kuma Allah zaitoni asirinshi kowayeshi kamar yanda asirin *Hajiya Zainab* ya tuno a yau."


*Yarima* ya d'ogo kansa daga jikin maimartaba yace "Abba dama duk Wanda beda mahaifiya hakan rayuwarsa take kasancewa cikin had'ari?"

Na lura a gidan nan Abba idan akacire *Fulani* burin kowa shine yaga bayana, yaga bana motsi a doron k'asa, Abba mena taremasu, bani nayi kainaba Allah ya halliceni Pls Abba tunkamin suk'arasa dani lafira, kabani izini nabar garin nan natafiyata England naci gaba da zamana a can, duk lokaci da nabuk'aci ganinka zanzo naganka nakoma."


Maimartaba yace "daina fad'in hakan *Bassam* babu inda zakatafi kana kusani dani, bazan tab'a barin ka kuma yin nisadaniba


Mafita d'aya ce kayi aure,
kanemo yarinyar da kakeso na aura maka ita, zaman da kakeyi a hakan kai kad'ai batareda mataba yana kuma k'ara bawa azzalumai damar da zasu cutar dakai."
Ya dafa kafad'arshi yace " *Yarima* ka natsu ka kwantar da hankalinki kanemo matar aure ko 'yar gidan waye a garin nan zan aura maka ita,
Kasani kaikad'ai ne d'ana d'aya tilo a duniya, inaso na fara ganin jikokina, inaso nafara d'aukar jikokina tunkafin mutuwa ta d'aukeni na bar duniyar."


Idan kuma baka da zab'i nizan zab'a maka matar aure mai mutunci da tarbiya."


Shuru *Bassam* yayi yace *Abba* kaine gatana a duniya kuma kaine farin cikina, tunda hakan kake buk'ata na amince zanyi auren kazab'a min matar aure duk Wanda ka amince da ita a rayuwarka."


Maimartaba yayi murmushin jin dad'i domin a duniya bbu abunda yakeso sama da *Bassam* gashi da bibiya uwa uba tarbiya,


Yadafa kansa yace "nagode *Bassam* Allah yayi maka albarka."


*Bassam* yace "Amin *Abba*


Maimartaba yatashi yafita cike da farin ciki."


D'aki *Bassam* yashiga ya fad'a kan makeken gadonshi, idonshi sama yana kallon silin,
babu abunda yake tunani sai yanda rayuwarshi zata kasance idan akayi mashi aure, to wacece Abba zai aura mashi?


Haka yadinga tunani, can ya tuna da marin da Afnan tayi mashi,
Zumut yayi ya mik'e zaune yashiga shafar fuskarshi inda ta mareshin, ko meyatuna oho tashi yayi zaune da saurinshi ya duru kan gadon had'ida d'aukar key d'in motarshi ya fita da saurinshi."


_________________________________


Malam *Nura* tsugunne a gaban kaka yana rok'onta akan ta amince da buk'atarshi,
Da cewa "da zarar Afnan ta kammala ssce d'inta a d'aura masu aure, daga baya yayi alk'awari idan tana gidanshi zataci gaba da karatunta har saitace ta gaji."


Kaka tayi kyaran murya tace "Nura ba wai nak'i shawararka bane, ni a wurina bakada matsala domin ba tun yanzunba na yaba da hankalinka kuma nabaka Afnan."


Amma wani hanzari ba guduba, kajira malam Iro ya dawo daga tafiyar da yayi, saikayi masa maganar domin shine matsayin Mahaifin Afnan a yanxun, kaga daga nan zuwa wata biyar lokacin ta kammala karatun nata, sai ayi aurenku."


Gaba d'ayansu murna suka shigayi, sannan Afnan ta mik'e tanufi hanyar waje dama uniform ne a jikinta tanufi hanyar makaranta malm Nura ya rufa mata baya dama shi ke rakiyar ta harta samu abun hawaye sannan ya dawo gida."


Sauri ta keyi cike da farin ciki domin kunyar had'a ido takeyi da malam Nura,
Shima saurin yakeyi domin yacin mata, da kyar yasamu ya cinmata, yashiga ce mata "Afnan yau kojirana bakyayi nayi rakiyar?"


Rufe idonta tayi da hijabi taja wuri d'aya ta tsaya cike da jin kunya,
Murmushi yayi yace "Afnan sarkin kunya,
Irin wad'an nan halayen naki sune suke k'ara sanya min naji ina sonki,


*Afnan* "ina sonki ba zan gaji da furta maki hakan ba,
Fatana d'aya Allah yadawo da Baba Iro lafiya yasanya mana ranar aurenmu,

Jin kad'an yayi shuru yana kallonta,, idanshi ya cika da hawayen k'auna, yaci gaba da cewa, "Afnan sai nakeji a raina kamar zan rasaki, kuma rasaki a rayuwata kamar rabani da numfashina ne."


D'ago kanta tayi, suka had'a ido taji sonshi da k'aunarshi had'ida tausayinshi ya kamata tace "ya sayyadi ka daina furta hakan, zuciyarka ta daina yimaka sak'e sak'en cewa bazaka sameniba,
babu Wanda zai rabamu sai munyi aure mun haifi yaranmu kyawawa masu kama dakai."


Dariya suka sanya gaba d'ayansu, d'aga kan da zasuyi sukayi ido biyu da *Bassam* gefensu a tsaye duk abunda suke fad'a akan kunnenshi,
Sun tsunduma duniyar masoya basuma San yana wurinba."


Basu kuma kallonshiba suka jera sukatafi, har sunfara tafiya ya cinmasu ya shiga gabansu ya tsaya,


yana dariya had'ida Sosa gemunshi, malam Nura ne yayi k'arfin halin yimashi magana, yace "malam me kake nema damune kakeso kaga kashiga rayuwarmu, me muka tare maka a duniya ne?


Be tanka mashiba saima tsurawa *Afnan* ido yayi yana kallonta, da kyar ya bud'i baki yayi magana, yace "kin d'auka zaki mari yarima d'ansarki kuma kiyi tunanin zaki zauna lafiya?


Yayi murmushi yace "akwai hukuncin Dana tanadar maku keda duk wata zuri'arku, amma yanzun na rusheshi, ya kalli malam Nura yace zan d'aukar mku wani hukunci daidai daku, Wanda zan hanaku farin ciki da walwala injefa kunci a cikin zuciyoyinku, Ku biyu nan da kai da ita, saina sanyaku kuka da hawayenku."


Yana kaiwa nan ya juya yayi tafiyarshi, yabarsu nan cikin tunani daga k'arshe malam Nura yayi k'arfin halin yi mashi magana yace "Allah yafiKa Azzalumi kawai Allah bazai barkaba."


Karaf sai a kunnen *Bassam* ya juyo ya kalleshi yayi murmushinsa na gefen baki yayi tafiyarsa."


A zahirin gaskiya kalaman malam Nura sun bak'anta mashi rayuwa matuk'a, domin babu Wanda yatab'a jifarshi da zafafan kalamai kamarshi.".


Tafiya sukeyi *Afnan* ta kalli malam Nura tace "ya sayyadi niko narasa abunda wannan d'an sarkin yake nufi damu, ya ke kuma bibiyar rayuwarmu, ina ganin alamarshi soyakeyi ya ruguza mana farin cikin rayuwarmu"


Malam Nura yayi murmushi yace "kwantar da hankalinki *Afnan* babu abunda zai iya Allah yafishi,
Ni dai abinda nakeso dake kiyita addu'a da zarar Baba Iro yadawo nakai sadakinki a d'aura mana aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login