Showing 33001 words to 36000 words out of 90241 words
Chapter 12 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 a ganinsa duk inda mace mai kyau take to algunguma ce da iya shirya shirri."
Ya tsani Mace mai kyau don ya sansu mayaudara ne, shi yasa da Afnan tayi mashi laifi yaji baya iya yafe mata, sai ya aure ta don ya nuna mata kyanta na banza ne shi mace ba ta isa ta wulak'anta shiba ko ta juya shiba."
Kallon Hajiya zainab yaci gaba dayi tana bashi hak'uri yana kuma karantar wani sabon makirci Wanda tazo dashi."
Sarki ya katse masa tunani da yaji ya dafa shi,
          Yace "Haba Yarima kazama mai yafiya mana, kayafe mata tunda ta gane kuskurenta tayi nadamar abunda ta aikata maka ko dan darajar k'aninka ko k'auna dake cikinta."
Murmushin dole Bassam yayi domin ya fahimci mahaifin nashi yayi amanna da tubanta
 yace "Abba na yafe mata, Allah ya yafe mana baki d'ayanmu."
Ya mik'e ya fita, Hajiya zainab tabishi da kallo tana fad'i  a zuciyarta Ashe wannan yaron yana nan da taurin halinshi, lallai aiki ne ke gaba na babba."
Kai tsaye sashin sa ya nufa, da tunani kala kala a zuciyar shi, 
     Domin yasan Hajiya Zainab farin sani, bazata fasa abunda dakeyiba
    Keb'eta da sarki yasa akayi tak'aro wani sabon salon mugunta da sharri, tambas dolene na kiyaye kaina da kuma masu kula dani, domin ta kowa ce hanya tana iya bi domin ta cutar dani."
 bawansa ya kira, mai mashi hidima Audu ya aike shi chilly ya sawo mashi giya domin Audu shi kad'ai yasan yana shan giya kuma yanzun shike zuwa sayo masa."
____________________________
Hajiya Zainab na ganin yarima yafita, ta d'an zauna a kusa da sarki ta d'an russuna, ta matso hawayen k'arya  tace "ranka ya dad'e ina ganin kamar Yarima bai yarda dani ba bai yafe min ba."
Sarki yayi saurin kallon ta yace "Haba Hajiya zainab daina kuka hakan karki wahalar da abunda ke cikinki, 
     Yarima ya yafe maki, ganewa ne, bakiyi ba, kin san halin yarima wani lokacin ba'a sanin gaban shi bare bayan shi."
Sai a lokacin ta d'anyi murmushi suka 
d'an tab'a hira domin yanzun sarki ji yake da ita sanadiyar cikin dake tare da ita, sannan daga k'arshe tayi mashi sallama ta tashi,  ta fita."
Tana komawa sashinta ta sanya a nemo mata Sarkin gida."
Shine masanin duk abunda ya kai kawo a cikin gidan."
Sarkin gida ya tsugunna yana jero gaisuwa."
Ta dakatar dashi da cewa ya isa!!
      Sarkin gida ba gaisuwa na kiraka kayi minba, 
   Kiranka nayi domin na tambayeka abunda ke tafiya a gidan nan tun lokacin da bana  cikin sa har zuwa yanzun."
Wane ci gaba Bassam yasamu bayan bana nan."
Sarkin gida ya sunkuyar da kai, domin shi kansa tsoron tuggunta yakeyi, lokacin da bata nan sunji dad'i sosai har Addu'a sukeyi Allah yasa daga can karta dawo  sai mutuwa."
"Yace Ai ranki ya dad'e Maimartaba yaso yaba Yarima kujerar mulkin ya zama Sarki."
Dajin hakan ta d'auki ta kalamin da ke kusa da ita ta jefa masa sai a goshinsa tana huci tana fad'in "kada ka kuma fad'in hakan a gabana domin muddun INA motsi babu Wanda ya isa ya zama sarki, sai Yazeed."
Abunda ke cikinta take nufi, domin bokayenta sun shaida mata cewa namiji zata haifa  anan take ta sanya mashi suna Yazeed."
*ikon Allah oh ni 🤔 ummu safwan zanga yanda jariri Wanda baizo duniya ba zai mulki*🤔🤔🤔
[3/5, 4:35 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
           *29*
Sarkin gida ya rik'e .goshinsa da ya kumbura, a ransa kuma cewa yake "Yazeed?"  Waye kuma Yazeed?" Kai wannan matar akwai hatsabibiya."
Sai jin muryanta yayi tana fad'in Neman sani kakeyi kowaye Yazeed?"
     To bara na fad'a maka d'an da zan haifawa Sarki yau ko gobe nake nufi."
Tuk'ashi!! Abunda bazai tab'a faruwa ba kenan ko a mafarki."
 
A fili kuma yace "Allah ya huci zuciyarki ranki ya dad'e, kin gaji mulki mahaifinki Sarki Kakanki Sarki........"
Kai yimin shuru Sarkin gida, kab'ata min jin dad'in yau tashi kabani wuri kanajina."
     A fad'ace take magana."
          Mik'ewa yayi yafita yana fad'in Allah ya huce zuciyarki."
Jakadiyarta tamatso fuskarta na nuna tsoro,
       "Ranki ya dad'e kiyi hak'uri Allah ya huci zuciyarki, kowa yasan abunda sarkin gida ya fad'i k'arya ne. Ko labari bai zama bare ya faru."
Tsawa ta daka masu, kufita kubani guri, bana son ganin kowa yanzun."
Babu b'ata lokaci kowa ya fice daga makeken falonta, Wanda yaji kaya har babu gurin ajiye wani abun."
Zuciyarta zafi take yi mata, "sarki sarki shirin da yake yi kenan?" 
     Wato Bassam yakeso ya d'ora a kan mulki, ina Sam bazai yuyuba sai dai kowa ya rasa."
Ranta idan yayi dubu ya b'aci, "zan shiga tsakaninka da wannan yaron wata k'ila ajalinsa ne ya dawo dani, yafad'a a fili zan zama sanadinsa kota halin k'ak'ane."
______________________________
Bassam na zaune cikin d'akin shi  yasanya  Audu yaronshi,  mai yi mashi hidima kuma ya mik'a wuya bak'i d'aya gareshi, 
      Shi ne kad'ai yasan Yarima  na shan barasa, dan shine ma ajinta tunda ya gane Afnan shigowa take tana kwashewa tana zubarwa."
Yana zaune a gefensa yana tsiyaya masa yana sha, shuru babu hira tsakanin su,
           Audu dama bai damu da surutu ba, saboda tun fil'azal yana da nauyin baki, dan haka rashin maganar ba ta tab'a damunsaba."
Ya kwashe komai ya Adana ya shiryawa Bassam ruwan wanka har yayi ya fito, ya zauna bakin gado,  Audu zai kashe wuta sai Bassam ya kira sunan,
Da sauri ya matso ta tsugunna kansa a k'asa yana sauraron sa."
Bassam ya tsura mashi ido sosai, domin yanzun yanayin tsarin tsaro zai canza tunda Hajiya Zainab ta dawo tana iya saye makwad'aici da kud'i masu yawa domin tasamu cikar burinta."
Ya kuma kiran sunan shi a karo na biyu, yace "Audu."
Ya Amsa cike da girmamawa."
Bassam yace  "ya ka d'aukeni?"
Mene ne matsayina a wurinka?"
"Ranka ya dad'e ni a matsayina na mai yi maka hidima, ban wuce bawa mai kawar da lalurorin ubangidansa ba."
Yarima ya girgiza kai yace "kasan Amana?"
"Eh Ranka ya dad'e."
"Kada kaci Amanata domin ganin kud'i ko wani abun duniya."
"Zan rik'eka zuciya d'aya kaima ka rik'eni da zuciya d'aya,
 duk abunda kasani ka barshi tsakanina da kai,
       Idan kasan bazaka iyaba ka fad'a min tun yanzun karna saki jiki da kai a had'a baki da kai a cutar dani."
"Ranka ya dad'e na mik'a wuyana gareka daga 
Allah sai kai, a hidimomina zanyi k'ok'arin rik'e amanar ka da yardar Allah."
Ajiyar zuciya Bassam yayi yace " Madallah sai da safe."
          "Allah bamu Alheri."
       Ya fice daga d'akin."
______________________________
Afnan na nan wurin zamanta wurin Anna shagwab'a sai abunda ya k'aru, ga shak'uwa da son junansu dama Afnan ta iya shiga ran mutum farat d'aya, sai wautar da dake sa duk Wanda yake tare da ita dariya."
Anna taji labarin dawowar Hajiya zainab ta kira Bassam tashiga shaida masa yayi taka tsantsan da ita  sannan kuma ya zama mai kula da duk wani Abu dake tafiya a gidan, kuma ya rik'e Addu'a domin Addu'a ita ce makamin muminice."
_____________________________
*Kaka* antare a babban gida Wanda Sarki yasaya mata."
Gida ne babban gida mai kayan more rayuwa a cikinsa,
 gidan b'angare biyu ne b'angare d'aya nata ba'angare d'aya kuma na malam Iro."
Sunyi farin ciki sosai kuma suyita sanyawa Auren Afnan Albarka dayi masu fatan zaman lafiya mai d'orewa."
Matsalar *Kaka* d'aya ce har yanzun bata sanya Afnan d'inta a idoba."
In tana cikin wannan tunanin sai ta tuna da sak'on da Sarki yake mata da cewa "tayi hak'uri Jikanyarta tana cikin k'oshin lafiya, zaisanya rana azo a d'auketa a kaita taganta."
Sai ranta yayi mata sanyi tasanyawa rayuwarta dangana."
*Malam Nura* kuma tun yana sanya ido Afnan zata dawo gareshi har ya dangana kuma duk ya kira number wayarta a kashe yake jinta."
Hakan yasanya wa rayuwar shi dangana, domin yanzun ya fitar da rai akan cewa Afnan zata dawo gareshi, yasan yanzun Afnan tayi masa nisa, 
sai dai Addu'a dayakeyi akan Allah yakawo masa wadda zata maye masa gurbin Afnan d'inshi."
_____________________________
4:30pm  Bassam ne kwance a kan makeken gadonshi sai juyi yakeyi domin  buk'ace yake da macce, sha'awa ta dameshi tun yana shan lipton da lomon tsami har ya kai yanzun idan yasha basa masa ganin komai."
[3/5, 4:35 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
        *30*
Haka ya dinga murk'ususu,
 hannu shi dafe akan marar shi sai nishi ya keyi saboda azabar ciyon da yakeji."
     Da kyar yasamu ciyon ya sake shi, ya d'an samu sassauci, sannan ya tashi ya shiga toilet yayi wanka had'ida d'auro Alwalar Sallar magariba sannan ya fito ya kyamtsa cikin wata da kankiyar shadda milk colour, hular kan shi ita ma Milk colour,
      Ya d'auko agogon shi mai d'auke da *Tambarin Sarauta* ya d'aura a hannunshi, yayi kyau matuk'a."
Kai tsaye b'an garen maimarta ya nufa, domin daga yau  hak'urin shi, ya  k'are  aure yake so ya k'ara."
Hajiya zainab na ganin giftawar Bassam yanufi sashin maimartaba, hankalinta ya tashi, domin ganin tayi yak'ara kyau da haiba da cika irinta jarumin maza,"    "tabbas dole ne, Sarki yace zai sauka a kan kujerar shi yaba Yarima domin ya cancaci ya zama sarki, amma kuma muddun ina raye hakan baza ta tab'a faruwa ba."
             Da sauri ta koma baya,  ta fad'a d'akinta ta d'auko mayafin ta, ta lullub'e jikinta  dama kuyanginta suna nan lab'e a guri d'aya  jiran umurninta kawai sukeyi."
Ta kallesu d'aya bayan d'aya cikin iko da mulki."
Tace "kuyi min rakiya sashen Maimartaba."
Taga sunyi tsuru tsuru da ido basu da alamar tafiya."
Ta daka masu tsawa, tace  "me kuke jira?" Kuka kafeni da ido kuna kallona."
Gaba d'aya suka zube a gaban ta, suna fad'in "ranki ya dad'e ki gafar cemu maimartaba ya bada lokacin zuwa sashensa daga bayan la'asar zuwa Isha'i, kada Wanda yaje nemansa saboda yana tare da Yarima."
Da k'arfi, a fad'ace tace "kuyi min shuru magulmata kawai!"
Ta koma cikin palonta hankalinta a tashe, wato bayan bata nan  har wani lokaci Maimartaba ya ware na ganawa da Bassam."
"To me suke cewa?" wata k'ila shirye shirye sukeyi na yanda za'a d'orashi a kan kujerar sarauta."
da k'arfi tace "k'arya ne wallahi abun da bazai tab'a yuyuwa bane in dai ina da rai da lafiya Bassam ba zatab'a zama Sarki ba."
______________________________
Maimartaba da Bassam sunyi nisa wurin hirarsu."
Sarki ya fahimci akwai abunda ke damun d'an nashi daga ganin yanayinsa."
       Amma kuma  ya kyaleshi yaci gaba da jansa hira suna dariya."
Maimartaba ya kalli Bassam cikin barkwanci yace "waini Yarima sai yaushe zanfara ganin jikokina."
Anzo wurin Bassam ya fad'a a ranshi."
     Ya sunkuyar da kanshi cike da jin kunya sannan yace "Ranka ya dad'e Aure zan k'ara."
Sarki yace "iyee da gaske?"
Bassam ya kuma sunkuyar da Kansa, yace "Eh Abba ina son in k'ara Aure."
Sarki ya kalle shi yayi murmushi yace "lallai yaro kayi gado."
          Nima kasan a kwaini a kwai son macce."
Bassam murmushi yasaki amma baice komai ba."
Sarki yace "in kana so zan k'ara maka da kwarkwara biyar."
Bassam ya zaro ido😳 yace A'a Abba bari dai na fara auren tukunna."
Sarki ya kalli Bassam yace "Kai da Allah can rago halama Anna bata dafa ka ba?" Dan nasan Anna bata wasa da abunda tasan zakaji dad'i gareshi."
Kunya ce ta kama Bassam ya shiga sunkuyar da kai k'asa."
  
 sarki babu ruwan shi sauk'in kai gareshi da son barkwanci mussam idan suka keb'e da Bassam d'aukar shi yakeyi kamar abokinsa komai yana iya fad'a masa."
Sarki ya katse masa tunani yace "Yarima ina son kazama namiji jarumi a gaban kowa."
"Kada kazama Wanda zai sanyi a al'ummarsa."
         Kuma ka kula da irin mutanin da zaka rik'a huld'a dasu,
            Kasani ita sarauta baki d'ayan ta  siyasa ce ta gargajiya, dole kasamu masu adawarka kona tare da kaine."
 
Ka zama mai Sanya ido a ko Ina kake ciki da waje, kada kazama sakake, kuma ka zama mai rik'e sirrinka a cikinka, dan ciki ba anyi shi dan abinci ba,
      Ka kuma yi taka tsantsan da mutanen da kake hurd'a dasu duk yadda suke tunaninka  nuna masu  kawuce nan, idan zaka yanke mataki ka nemi shawarar ma'abota sani ba jahilaiba, ka kuma k'ara kula da hak'k'in mutanen da hak'insu ya rataya a wuyanka."
Hajiya zainab ta dawo, ba wai ta daina halinta ba ne," Kayi taka tsantsan da ita, da duk wani abu da zata baka kaci, ko menene shi."
A tak'aice ka zama mai kula don kuwa ba ita kad'ai bace,
Kaza mai kula da Wanda zai kawo maka abinci ko abin Sha,
 kowaye shi in dai ba yardanden ka ne."
  "kai ko yardanden kane, ka zama mai kula."
 domin kud'i suna iya can zawa mutum ra'ayi a nan take ka kiyaye."
Bassam ya durk'usa gaban Sarki cike da jin dad'i, yace "Abba nagode kwarai Allah ya k'ara yawancin rai."
Sarki ya shafa kansa yace " Amin  Allah yayi maka Albarka."
     Kak'i yarda ka amshi sarauta."
"Abba sarauta da da kai ta dace ban San komai ba a kan mulki, ina da saura tukun, ina son in fara koyon tsarin mulki daga gareka."
Sarki yaji dad'in kalaman Yarima yayi murmushi irin naso na manya, yace 
"To shi kenan nagode da tunanin da kayi,
      Ina so ka mai dani tamkar abokin ka, kada kadamu da abunda zaka fad'a min ko meye shi in har ya shafi rayuwar ka."
 Am ready to be a father and also a friend."
Sosai Bassam yaji dad'in firarsu ta yau da mahaifin nashi daga k'arshe, suka tashi suka nufi masallaci domin yin sallar magariba."
_______________________________
Labari ya iske Anna Bassam zaiyi aure, abun ya d'aure mata  kai sosai, 
    Ba tace komai ba, don tasan halin  sarki, bazai hanashi ba illah ma ya zuga shi zai k'arayi."
Don haka ta yanke shawarar ta zura masu ido taga iya gudun ruwansu."
_____________________________
2:20am na k'uda ta kama hajiya zainab sai kuwa takeyi ta hana bayi da kuyangi barci dama sauran mutanen gidan, 
      Fulani kuwa sai hawaye takeyi domin ganin yanda Sarki ya rud'e ya hana kanshi zama lafiya hankalin shi duk ya tashi, baya da lokacin ta, kuma gashi a d'akinta yake."
Hankalin mutanen gidan bai kwanta ba sai da hajiya Zainab ta haihu ta haifi d'anta namiji mai kama da ita sak,
    Murna a wurin sarki abun ba'a magana."
Safiya na wayewa sarki ya shiga fad'awa mutane k'asa k'asa shuwa gabanni da yan siyasa."
Bassam najin labari baiyi wani murnaba sai dai yace "Allah ya raya mata abunda ta haifa, ya kama gabansa."
Satin biki, biki ne akayi na kece raini, manya mutane sun halarta wurin bikin, domin Rabon da ayi taron bikin haihuwa a gidan tun haihuwa Bassam yanzun shekara talatin kenan."
Anci ansha an zubar da naira."
Tun ana gobe suna Bassam ya tsiri tafiya England dibo takardun sa, domin kaddama ya tsaya ayi bikin yana nan, domin a duniya babu abunda ya tsana sama da hajiya zainab da duk wata zuri'arta."
Anyi biki lfy an watse lafiya, hajiya zainab ansamu abun duniya wadda dama shitake nema."
Anna da Afnan suna gefe sun zama yan kallo, dama Afnan ba kowa yasanta a gidanba."
Fulani da Hajiya Amina, sun nuna farin cikinsu ba laifi, suka duk'ufa da add'a Allah yabasu nasu rabon suma, domin sun san yanzun sai sun danne zuciyarsu da kunnensu da kuma idonsu, domin yanzun hajiya zainab abunda taga dama shi zatayi a gidan tunda taga ta haifi d'a namiji."
[3/5, 4:44 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
        _we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_
  #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
        *32*
Jikinta ya soma rawa kamar mazari ta had'e hannuta wuri d'aya tana fad'in Dan Allah kayi hak'uri ban san kana wurin ba."
Anna ta zuba masu ido tana kallon su, batayi magana."
A fusace ya mik'e tsaye,
 yayo kanta yana wani huci zai daketa, yana fad'in ke mahaukaciyar ina ce?"
 da bakya ganin  gabanki, 
Ina ko zaki ganni kina tafiya kina girgije girgije."
to bari yanzun na saita maki tunaninki tunda baki da hankali."
Yayo kanta zai daketa, Anna tace "karka kuskura  ka daketa a gabana."









