Showing 57001 words to 60000 words out of 90241 words
Chapter 20 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 wannan  matar taka k'atuwa tayi min duka."
Yaso yayi dariya sai kuma ya kuma had'e rai."
Yace "wai ke ba'a gaya maki bane?"
Tace "me za'a gaya min?"
Bakisan sharud'un  aure bane?" Ko bakisan matsayina a wurinki ba?"
Ke yadace ki kawo kanki gareni ki nemeni, bani ya dace na nemeki ba."
Ta kalle shi tace "Dan kana Yarima d'an sarki?"
    To Nan ba wurin kiwon dabbobi bane."
Ya sassauta murya yace " Pls Afnan ki manta da abunda ya faru daga baya,
    Nima idan na tuna da irin abubuwan da nayita maki duk sai inji banajin dad'i a raina, kiyafe min."
     Ya kafeta da ido yana kallon bakinta."
Tayi shuru batayi mgnaba yace "tashi mutafi sashina."
Ta tuna da darensu na farko irin wahalar da yabata,
    A ranta tace "kai wannan Abu da ciyo fa, ta ya mutsa fuska."
Ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar fita d'akin."
Yayi saurin tare gabanta cike da jin haushi, da takaici yanda take wani kad'ashi kamar kwallo, shi kamar shi Yarima.
 yace "ina zaki tafi?"
       Kina nufin tafiyarki zakiyi kenan, to idan bakiyi hankaliba zan d'auki mataki a kanki."
Ta kalleshi tace "zaka rabu da nine?" Alhmdulillah Allah nagode maka."
"Babu  rabuwa tsaka nina dake akwai mataki da yawa da zan d'auka akanki."
Tak'ura masa ido tana kallonshi batayi magana ba, itama ita yake kallo, ganin bata da niyar magana."
Yace "wuce mutafi d'akina umurnine daga yarima, ko hukunci ya hau kanki."
Ta sunkuyar da kai tace " tuba nake yarima mutafi."
    Ya wuce gaba tana bayanshi yana fita ta maida k'ofa ta rufe had'e da sanya sakata."
Yana ganin hakan bai kuma bin takanta ba yayi tafiyarshi cike dajin haushi yana cizon leb'e."
Yana zuwa d'akinshi ya iske Saratu kwance a kan gadonshi ta sanya wasu kayan barci Wanda duk jikinta a waje yake  kamar wqni k'ato."
Tsayawa yayi cak a bakin k'ofa, saka makon warin jikinta daya gauraye d'akin."
Yashiga kiran sunanta  da sauri ta mik'e zaune yace "zoki tafi d'akinki zankiraki idan na shirya."
Ta taso tana rangwad'a,
Ta wurinshi ta rab'a ta wuce. Yayi saurin rufe hancin sa, sakamakon wani kalar wari wadda yafi nada ya doki hancinsa."
Yayi saurin shigewa toilet yana kakarin amai."
Idonta yashiga zubar da hawaye, ta fita,
     A ranar tashiga tashin hankali marar misaltuwa domin talura tanaji tana gani Yarima yana gudunta."
Kuyangunta ta tayar daga barci,  tace "gaba d'ayanku kuzo ku sinsina."
Sukayi tsaye tsuro suna kallonta suna zarar ido. 
    Tsawa ta daka masu tace "cewa nayi kuzo Ku sinsina k'asana koji ko zakuji wari."
Suka had'a baki sukace "ranki ya dad'e wari kuma?"
A tsawace tace "ku sinsina nace bawai Ku tsaya kuna tambaya taba."
Sukayi saurin zubewa k'asa suka shiga sinainarta, sukace  "ranki ya dade babu wari sai dai k'amshin turaren wuta mai dad'i nan."
Tace "to Ku tashi."
 tashiga tunanin to meyasa Yarima yake toshe hancinsa da bakinsa yana b'ata fuskarsa yana irin yanayin nan da mutum yaji warin Abu."
   Idan kuma yana kanta sai yayi ta fama da b'acin rai kamar dole aka sashi."
Kwana biyu Saratu ta shiga damuwa,  k'aura cewar da Yarima yake mata."
Dole macce ta shiga wani hali idan mijinta ya k'aura ce mata."
 Jakadiya ta lura da Saratu tana cikin damuwa,
    Ta tuna da Sarki ya turo ta domin ta kula da matar Yarima."
Gashi kuma hajiya zainab ta sanyata a gaba, ta hanata sakat kullum saita kirata ta dinga tambayar ta, tana bugun cikinta tana tambayarta abunda ke faruwa tsakanin Yarima da saratu, tun tana nok'e nok'e har ta fara sakin jikinta, tana gaya mata  saboda zinare  da taba mai girman sosai."
Duk tazo bata labarin saratu sai tabata dumin  kud'i masu yawa taba jakadiya."
Saratu kuma in banda hantara da wulak'anci babu abunda ta iya, ga wulak'anta na k'asa da ita, shekararsu biyu da aurensu da yarima, ta canza kuyangi sunfi d'ari biyu, 
    Ita ta aure yarima dole ta juya duk Wanda takeso, ta wulak'anta Wanda taga dama."
Shi yasa komai arzikinka, Da ajinka  kace zaka wulak'anta d'an Adam kana tare da asara saboda mutum rahama ne, ka kore kowa kowa na gudunka."
Gata da muni sai kace biri ya haifeta, abun nata yayi yawa kenan, ga bak'in hali ga muni."
Har gara sarauniya akwai kyan gaske sai dai halin ne itama sai ta saya a kasuwa."
****************
Sadi ya maida gidan Anna wurin zuwansa 
    Kullum suna tare da Afnan suna hira suna dariya wadda hakan yana k'ara d'ebewa Afnan kewa."
Satin Yarima d'aya baizo gidan Anna ba, ya d'auki zafi da Afnan sosai."
Anna takira Afnan take tambayarta lafiya ta daina ganin Yarima kwana biyu ko wani Abu ke faruwa?"
Afnan tace itama bata San abunda ke faruwa ba."
Anna tashiga CE mata "ki kula da kanki domin nasan halin yarima sarai,
   Kuma nagane take takensa, kizama macce mai aji sai ki kuma samun matsayi a zuciyar mijinki."
Abunda Yarima yayi maki idan na tuna imajin zafinsa, 
    Ki kula da kanki har zuwa lokacin da zai soki soyayya ta gaskiya."
Lokacin da zanga nadama a  idonsa."
[3/5, 8:29 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
           *50*
Sati biyu kenan Bassam bai sanya ido ga Afnan ba hak'uri kawai yakeyi yana danne zuciyar shi,
  Amma ko wanne bugun zuciyarshi Afnan yake tunani."
Yau juma'a ya kasa hak'ura,
    Misalin k'arfe hud'u da rabi, da yamma lik'is, Sadi da Afnan suna cikin lambu a nan b'angaren Anna suna tsintar bangwaro suna dariya."
Yarima har zai wuce ya shiga ciki, sai yajiyo hayaniyarsu, ya nufo wurin, cikin sand'a."
Sadi ya fara ganinsa yayi masa alama da hannu da yatafi."
Sadi ya kama barin hanyar, 
  Afnan tace "Amini ina kuma zaka?"
Yace "ina zuwa Aminiya, bari in d'auko miki wani Abu da zamu hau mu tsinko mangwaron."
Matsawa tayi wurin iccen mangwaron tashiga tsalle alamar so take ta tsinko."
Saiji tayi and'agata sama, sai da ta tsunko d'aya, jin jikin mutum da tayi yasa tafara wutsil wutsil, gaba d'aya sukayi baya suka fad'i k'asa, ta fad'a kansa."
A dai dai lokacin kuma ruwan sama ya sauko masu k'arfin gaske. Nan da nan suka fara jik'ewa, ta mik'e da sauri, zata gudu wazata gani Yarima ne a gabanta yana ta mata fara'a."
Kasa yin komai tayi, ganin yana gabanta, tana tunanin abunda zatayi."
Rik'a hannunta yayi yajata zuwa wani iccen, yana da tsawo sannan a kwai reshe da yawa zai tare masu ruwan "
Ya jinginata da iccen yayi mata zube da hannunshi, yanda bata iya matsawa daga gurin."
Ido ya kafeta dasu yana kallonta ita kuma duk yanayinta ya canza, duk sai tajita wani iri ga tsikar jikinta dake tashi, saboda hannunshi dake shafar jikinta."
Ya furta a hankali yace "sanyi kikeji?"
Batayi maganaba sanadiyar matsowa da yayi tanajin iskar numfashinsa a kan fuskarta."
Idonta har a lokacin a k'asa suke, shi kuma yana k'ok'arin ya kai bakinshi a kan nata."
Ta gano hakan Dan haka saita kame bakinta."
Yace "baki son in sumbace ki?"
Yayi maganar a cikin kunnenta kamar rad'a."
Yin shurunta yabashi damar sanya bakinshi cikin bakinta yana tsotsar lab'b'anta a hankali."
Ganin tak'i sakin jikinta yasa yasaki bakinta  yaja kunnanta yana kissing a hankali zuwa wuyanta."
Ya d'an d'ago ya dubi k'irjinta ta jik'e sharkab da ruwa,
   Gashi k'irjinta ya bayyana kana iya ganin komai na jikinta."
Yarasa abunda zaiyi ga baki d'aya yaji buk'atarta yakeyi, ya dubu dama ya dubi hago babu kowa sai su kad'ai."
Yayi mata magana a kunne yace "Afnan pls ki tausaya min yau kizo turaka."
Ya kai hannunshi a hankali ya shafa k'irjinta had'ida murza kan Brest d'inda da d'an matsasu,
   Sabon yanayi ya riski dukkan gab'ob'in jikinta jitayi kamar zatayi yaye ne."
    Bata tab'a jin hakan ba a tare da ita." 
Ya sanya harshinsa a kunnenta, yashiga wasa dashi a ciki,
    Rufe idonta tayi saka makon wani Abu da taji yana mata yawo a jiki."
Cikin da sanshiyar murya ya maimaita maganarshi yace "yau kizo turaka please."
"To ta fad'a da wata dasan shiyar murya."
Yayi murmushi yasan tarkonsa ya kamata."
    Yasan zataso abun da yayi mata yanzun."
Ruwan saman ya tsaya cak ya dubeta yace "kisa d'ankwalinki ki rufe jikinki saboda baki San Wanda zaki had'u dashiba a hanya."
Ya rik'a hannunta sai da yakaita a bakin k'ofar babban falo sannan yasaki hannunta."
Ai kuwa ta ruga a guje."
Tabashi dariya yashiga tunanin yau zasu kasance tare zaiji dad'in sosai,
   Yanayin jikinta abun sha'awa ne, ya k'ara hamdala da bai rabu da itaba kai da nayi sake......"
D'akinta ta fad'a tana maida numfashin gudun da tayi, tana tuna abunda Bassam yayi mata tana murmushi."
**************
Bassam yana d'akinsa yayi wanka sai k'amshi yakeyi ya lura Afnan ma'a buciyar son turare ce,
   Yau zaisha Amarci,
Ya dad'e yana muradin macce irin ta,
   Shagwab'ata ya tuna yayi murmushi  Ashe masu kyau suna da halin kwarai, a da ya zargesu amma yanzun ya gane ba duka a ka taru aka zama d'aya ba."
Kowa zuciyarshi da ban yanda kowa halittarshi daban."
Ajiyar zuciya yayi tare da kallon a gogo, k'arfe sha biyu saura,yaji ana kwankwasa k'ofarsa ta ciki,
Da gangan ya bar k'ofarsa a bud'e saboda Afnan ta shigo kai tsaye duk da akwai masu gadi wurin."
Da saurin shi ya tashi yanufi k'ofar harda tuntub'e yake yi da kafet d'in dake tsakar d'akin."
Bakin k'ofa yanufa jikinsa na rawa ya bud'e k'ofar, 
   Sai ganin fuskar saratu yayi tana wani bud'e baki,
Ya kauda idonsa daga gareta ya shiga kallon bayanta,
Itama ta juya tana tayashi kallon bayanta."
Yafita falon yana ci gaba da kalle kalle, tace "akwai abunda kake nema ranka
Ya dad'e?"
"Oh A'a ba komai ya b'ata fuskarsa yace "kije d'akinki zan nemeki, ina aiki......."
"Ranka ya dad'e kwananka goma sha biyar yau rabonka dani......"
"Nace kije d'akinki zan nemeki, ya fice a fusace zuwa d'akin barcinsa, ya rufe gub! Kakeji."
Ta gano akwai matsala babban ta tsaya tana kallon k'ofar tana hawaye, kusan minti ashirin tayi a tsaye tana kallon k'ofar ya zatayi can ta juya ta fita."
Yanajin fitarta daga falon shima ya fito, baiji dad'in yanda ta kasance tsakaninsu ba yana ganin bai kyauta mata ba."
To amma idan ma wata goma yayi saita jirashi ya nemeta meya kawota?"
Turare ya d'auko yana fesawa saboda warin da tabari."
Zaiyi magana da malam Sanusi a dubata k'ila jifa akayi mata."
Wasu mutane suna da sakaci basu Neman kariyar da zata karesu daga shairin muguntar d'an Adam."
Ance kana iya koyon shairin dan ka kare kanka amma kazama mai yin komai Dan Allah."
Ya dace ko addu'ar safe da Allah ya tanadar yayi Alk'awarin kare bawansa mudage muyi Allah mai hikimane."
Babu abunda zakayi a duniyar nan da babu addu'arsa ko ta wane yare kayi Allah najinka kuma zai kareka, idan har kayi imani dashi, koda wani mugun abu zai sameka zai zo maka cikin sauk'i."
Shuru ba Afnan ba labarinta, Yarima ya kasa zama sai safa da marwa yake tsakanin falo zuwa d'aki, yarasa abunda keyi masa dad'i,
  
Ya tattara ya haye kan gado, yaso ya tafi sashin Anna sai kuma ya duba agogo k'arfe biyu da rabi, baya son a fara tunanin wani Abu a kansa, Dan haka yayi zaune kan kujera ya d'auko giyarshi yana sha yana kallon TV."
Da kyar yasamu safiya ta waye, masa."
Misalin k'arfe goma na safe yanufi fada wurin maimartaba da damuwa a fuskarsa."
Maimartaba nada bak'i dole ya sallamesu,
   Ganin yarima ya shigo kuma ya lura yana da damuwa a rayuwarsa baya son ganin Bassam cikin damuwa."
Ya matso ya zauna kusa dashi yace magajin sarki ya akayi ne?"
Ya d'anyi shuru sannan daga k'arshe yace "Anna ce ta rik'e min matata."
Sarki yace "bangane  matar da kake nufiba?"
Bassam yace "matata ta farko Afnan."
Sarki yace "yanzun kana buk'atar ta kenan?"
Yarima ya sunkuyar da kai,
  Sarki yace "ina ita d'aya matar taka?"
Yarima yace "ina ganin kamar ansamata hannu, kasanar da jakadiya a nema mata magani."
Yarima yace "ranka ya dad'e tashi muje Anna tabani matata."
Sarki yace "A'a bari muyi salla mana sai mutafi, zomuje muci abinci suka jera suka nufi wurin cin abinci ga kuyangu sai zagaye sukeyi."
Suka baje gaban abinci da aka shirya masu, maimartaba ya kalli Yarima yace "shiyasa nace ka had'a da kwarkwaraye."
Bassam yayi dariya sarki Ahmad Mohammad shima yayi dariya."
Sarki yace "shikenan tunda bakaso,
   Amma fa kabani mamaki da ka zab'o wannan abar a matsayin mata, bayan kana da tsaleliyar mace."
Ka koyi gadona kuwa Yarima? saboda ni akwaini a kwai son macce kyakkyawa."
[3/5, 8:32 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
*Pls Dan Allah basu biyata prv suna Neman natura masu novel daga farko Dan Allah su daina saboda na riga da nayi nisa*
           *51*
Bayan Sallar la'asar iskan yamma na bugawa a hankali, sarki da Yarima suka jera suna hira gwanin ban sha'awa suka nufi wurin Anna."
Fadawa suka ruga suka fad'awa Anna cewa ga sarki nan tafe da kansa ba aikeba."
Anna ta mik'e daga kan kujera ta shirya, dama kuma a shirye take, ta zauna a kan kafet."
Sarki ya shigo tare da fadawa sai kirari suke mata, yayi masu nuni da su dakata a waje,
   Sannan yashiga sashin Anna."
Kai tsaye kan kujera ya zauna, shima Yarima ya zauna a k'asa gefen Anna."
Anna tashiga gaida sarki had'ida jera masa kirari, sarki ya d'aga hannu yana murmushi a lamar ya amsa."
Sannan yayi gyaran murya yace "Anna meya had'aki da d'an naki?"
  Ayi hak'uri a bashi matarsa."
Anna ta dubi Bassam daya sunkuyar da kai,  a ranta tace "wato k'arata ya kai wurin maimartaba kenan."
Tace "ran sarki  dad'e ban hanashi matarsa ba, kasan yarinya ce k'arama idan za'a kaita gidan shi ya dace a gyara t....."
Sarki ya girgiza kai yace "gaskiya ne Anna."
Anna ta dubi Bassam daya kasa had'a ido da ita, tace "ina rok'on Yarima yabamu nan da watanni goma
 za'a kawo masa ita."
Bassam yayi saurin d'aga kansa ya kalli maimartaba. Sukayi ido biyu, sarki yasan manufar sa."
   Dan Bassam ji yake kamar yayi ihu."
Sarki yace "Anna ayi hak'uri a tausayawa d'an naki, wata goma sunyi yawa, a barshi a wata biyu."
Bassam yayi sauri ya kalli mahaifinshi, shima kallonsa yake, sukayiwa junansu murmushi, yaji dad'in taimakon da sarki yayi masa, 
    Yafara godiya."
Sarki yace "za'ayi k'aya tancen taro ana gobe zata tare saboda mutane su shaida ta."
Dad'i yak'ara kama bassam sai murmushi yakeyi."
Anna tace "to ranka ya dad'e yanda kazartar haka za'ayi, sai a tara mutane kenan."
Sarki yayi murmushi yace "Anna nima baza bari naga Amaryar ba?"
Murmushi Anna tayi tace ranka ya dad'e Angama inkana buk'atar ganin d'iyar taka."
Sarki yace "ba damuwa a ci gaba da gyarata zamu had'u ranar biki."
***********
Labari ya 
Iske hajiya zainab cewa Yarima aure zaiyi, 
   Kuma matar sace a cikin gidan nan take zaune."
Hankalin hajiya zainab yatashi tace "ina bazai yiwoba, sai dai ta kashe Yarima da matar tasa ta huta, ita wannan bala'i ya isheta a kan Yarima ta hana kanta zama lafiya to anzo k'arshe kashe shi kawai yakamata ayi kowa ya huta."
Ta aika aka kira mata sarkin gida."
Sarkin gida yazo da gudunsa ya zube a gabanta sai huci takeyi tana burzar da iska mai zafi a bakinta."
Sarkin gida yashiga ce mata "Allah huci zuciyarki ranki ya dad'e, ki kwantar da hankalinki in dai inada rai da lafiya, bazaki tab'a zama cikin k'unciba."
Sannan ta d'an saki fuskarta, ta kalle shi tace "Sarkin gida ka kosan abunda naji kuwa dan gane da Yarima?"
Sarkin gida yace "ban katsi numfashinki ba ranki ya dad'e, nasan lbrin Aurensa kikaji  zaiyi 
To ba aure zaiyiba ya dad'e dayi  dan matarsa ce ta fari  ta dad'e a gidan nan, 
Hajiya zainab ta mik'e tsaye tace "yaushe hakan tafaru ban saniba?"
Tabbas saina d'auki mummunan mataki ga bassam, 
  Ni d'in nan saina ga bayan Bassam kamar yanda naga bayan uwarsa, inyi da uwarshi yace Zaiyi dani?"
Sarkin gidan ya jinjina kai yana cewa a ransa kin d'aukowa kanki babban aiki, saboda mungwada yi mashi sammu, amma abun ya gagaremu."
Saboda yayi nisa a  neman tsari, babu yanda banyi ba amma an kasa yin komai a kansa, shi yasa ko ido kuka had'a sai hanjin cikinka ya motsa Dan gani zakayi damusa kake kallo, Anya ba'a bashi naman zaki yaciba?"
A fili kuwa yace "ranki ya dad'e zamuyi k'ok'arin cimma burinmu, ki kwantar da hankalinki ki d'auka cewa Yarima da matarsa dukansu kamar sun bar duniya ne."
Ki natsu kisaki kud'i aiki kamar anyi angama ne idan har boka wanzam nada numfashi a doron k'asa,
    
Tace "sarkin gida sanin kanka ne, kud'i batsalata bane indai buk'atata zata biya musamman a kan tsinanan yaron can Bassam, mai taurin ran tsiya."
Yace ranki yadad'e zamuyi k'ok'arin cimma burinmu, Allah yaja zamaninki matar da babu irinta a gidan sarki kekad'ai kike juya gidan sarki yanda kikeso."
Da alama kirarin da sarkin gida yake mata yana ratsata, ga sanyin AC sai lumshi ido takeyi tana murmushi."
Kai jama'a mulki da dad'i da kuma b'ata, Allah yasa mu dace, Amin."
Saratu tafito domin tasha iska, saboda a kwanakin nan a cikin d'aki take yini bata fitowa Dan kar a zargi wani Abu tsakaninta da yarima."
Ta gifta ta wurin kuyangunta basu lura da itaba, sai gulmar ta sukeyi irin bak'in halinta d'aya daga cikinsu tace "ai ance ma wai aure zaiyi."
Tsayawa tayi daga tafiyar da takeyi, taji gabanta na fad'uwa, ta kallesu tace "wa zaiyi aure?"
Baki d'ayansu suka juyo, suna ganin itace suka fara inda inda,
  Tasaka hannayenta a k'ugunta tace "tambayarku nakeyi?"
Sukayi tsuru tsuru hankalinsu a tashe."
Ta kira d'aya daga cikinsu da alama









