Showing 69001 words to 72000 words out of 90241 words
Chapter 24 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
     amma kuma ya dake, cikin k'arfin hali ya d'agota ya zaunar da ita."
Yace "saratu ki daina sanyawa rayuwarki damuwa, kisani kema matata ce
saboda ina sonki  na aureki."
Ki kwantar da hankinki ki daina kuka. Karkije ki janyowa kanki wani ciwo,
 kisani dake da Afnan duk d'aya na d'aukeko dukanku mata nane."
Sai a lokacin ta d'ago jajayen idonta ta kalleshi."
Cikin muryar kuka tace "duk d'aya ka d'aukemu kace dani da ita?"
Amma bakatab'a Shiga yanayin da naji kashiga a daren jiyaba idan muna tare da kai."
Ranka ya dad'e kuwa fa naji kanayi kana wasu irin magagganu,
   Ta kuma fashewa da kuka mai sauti."
Taci gaba dacewa Baka tab'a d'aukata ba da sunan ka kaini toilet tunda ka aureni."
Wannan shine kake kira da duk d'aya ka d'aukemu?"
Mamaki yashigayi yana tambayar kansa " to wane sabon yanayi ne yashiga?"
   Har da kuwa yakeyi?"
    Shi dai yasan kwata kwata baya cikin hankalinsa a wannan lokacin, bai baima san ko a wace duniya yakeba." Kai Afnan ta dabance ta haihu."
Amma sai ya shiga Lallashinta yana bata hak'uri,
 yace "ki daina shiga d'akina
 in har bani na  nemekiba, 
Bana son kinayi min lab'e idan ina tare da iyalina,
Kamar yadda idan ina tare dake bana son wani yazo yadinga yi mana lab'e."
Ya mik'a mata hannu yace tashi ki d'auko min extra key d'ina dake hannunki."
Ba musu ta tashi ta d'auko masa ta mik'a masa,
    Ya karb'a yasanya a aljihu yafito d'akin."
 yanufi d'akin Anna."
******************
Afnan na farkawa da salati a bakinta, kuyangu tagani, zagaye da ita shi ya tabbatar mata da safiya ta waye, kunya duk ta isheta, tace masu "Ina Anna?"
"Suka had'a baki sukace "tana falo ranki ya dad'e ita ta turomu Dan mu taimaka maki."
Babu b'ata lokaci komai an kimtsashi tsam tamkar babu abunda ya faru."
Tashi tayi, tashiga toilet tayi wanka ta kuma gyara jikinta sannan ta nufi d'akin Anna."
Tana Shiga da sallamarta a hankali, Anna ta amsa mata, sai wani sunkuyar da kai takeyi tana jin kunyar Anna."
Anna ta lura da hakan saita shareta Dan ta lura nauyinta takeji."
Yunwa ke damunta kai tsaye ta wuce wurin abincin gasu anjerasu kala kala."
Tana kaiwa wurin taga yarima zaune gefe yana cin abincin shima, yana ganinta ya sakar mata murmushi yace Angel antashi lafiya?"
Juyawa tayi taga Anna na cikin d'akin, tayi saurin juyawa zata komawa,
  Yakira sunanta yace "Afnan!!"
Ta tsaya cak, yace "ina zakije bayan nasan abinci zakici kina tare da jin yunwa."
Ta turo bakinta,cikin shagwab'a
   D'aya daga cikin d'abi'un Afnan kenan."
Tasowa yayi daga inda yake yanufota, da gudu tabar wurin, abun dariya ya bashi, yanda Kasan taga zaki."
Dama yasanta batajin wuyar gudu.'
Wurin Anna ta isa sai faman b'ata fuska takeyi.
Anna tace "lafiya d'iyata?"
 Ta turo baki tace "Yunwa nakeji."
Anna tace "naga daga d'akin cin abinci kika fito."
Tace "yana ciki."
Anna bata kuma yin maganaba, Dan tasan kwanan zan cen.
 sai dai tayi tab'i da hannunta kuyanga ta matso ta zube k'asa."
Anna tace "lissafo duk abunda ke cikin kicin d'in Wanda kuka dafa."
Babu b'ata lokaci tashiga lissafowa."
Anna ta kalli Afnan tace "mezaki ci?"
A dai dai lokacin yarima yashigo falon.'
Anna ta kuma cewa, "kifad'i abunda kikeso kici da kaina zanshiga kicin d'in."
Ganin yarima  tsaye gabansu,
 yasanya hannayensa a Aljihu yak'ureta da ido yana kallo,
 yana wani murmushi wadda ita kad'ai tasan manufarsa,
 duk sai taji bata iya magana,
  Ta mik'e tsaye tabar wurin."
Anna tayi murmushi tace "Afnan ho! Duk halinta a Tara 
Yake bai cika goma ba."
Yarima yabita da kallo. Yace "Anna Niko nasan da hakan."
 abani break d'inta na kai mata. Nasan yunwa takeji sosai zan ciyar da ita da kaina."
Anna ta kalleshi batayi magana ba. Tace ranta "'ya'yan zamani basa da kunya,
 Ta tashi tashiga kicin ta had'o masa breakfast ta mik'a masa ya amsa yace "mungode Anna Allah ya bar manake." 
Sukayi dariya gaba d'ayansu,."
***************
Hajiya zainab abun duniya duk ya dameta, 
   Komai ya jakule mata."
Aikinma da sarkin gida ke amso mata akan yarima da duk wani masoyinsa zasu bar duniya
 Aikin kwata kwata bayaci 
kashin kud'i kawai takeyi."
D'anta Yazeed kuma  wadda takeji dashi kamar k'urjin tsakar kai, a yanzun shekararsa hud'u, a duniya,
    Daren jiya da suka tashi daga barci suntsinci Kansu cikin wani Sabon yanayi na tashin hankali, domin Yazeed ya tashi cikin mawuyacin hali,
      Kamar wadda Aljanu suka shafa, Kansa ya karkace idonshi ya juye, babu abunda ke fita a bakinsa sai miyau."
Da gudu tafito d'akin maimartaba ta nufa a lokacin yana tareda Fulani, cikin tashin hankali take fad'a masa halinda yazeed yake ciki yanxun."
Da sauri maimartaba ya mik'e tsaye, suka nufi wurin Yazeed, d'in
       Gashi kwance amma baya iya aikata komai,
    Likita maimartaba yakira a waya, cikin minti goma sai ga likita ya iso da saurinsa, aka shiga diba yazeed likita bai fahimci abunda ke damunsa ba sai dai ya yak'ara  masa ruwa, had'ida yi masa allurar barci."
     Yace "insha Allah da zarar ya farka daga barcin komai zai zama normal."
Anan take labari ya zagaye  gidan sarauta cewa "Yazeed baida lafiya ciwon hauka yakamashi"
Saratu na zaune a falonta gefenta kuyangunta ne, na hannun damarta, wad'anda take shiri dasu, da inno da ladidi,
Ladidi take Cewa "ranki ya dad'e kina da labarin abunda yasamu Yazeed a Daren jiya kuwa?"
Saratu tayi murmushi abunda take jira taji kenan."
Tace meya sami yazeed d'in?"
Ladidi tace "ance a daren jiya ciwon hauka yatashi dashi baya iya komai."
Saratu tayi saurin kallon inno sukayi dariya, 
  Tace "inno aje azomin da jibo, domin nayi mata babbar kyauta dan yau burina ya cika akan hajiya zainab, tasanyani a k'uncin rashin haihuwa, 
nayi Alk'awari tunda ta hanani na haifi d'ana jinina a gidan nan, itama baxata tab'a moruwar d'antaba, baxai tab'a yi mata amfaniba, kuma daga k'arshe nasanya a kasheshi, kowa ya rasa."
***********
Malam Nura kuma soyayya tayi k'arfi tsakaninsa da Maryam, har anyi baiko ansanya ranar aurensu wata biyu masu zuwa.'
A yanxun ya hak'ura da Afnan yasanyawa zuciyarsa da rayuwarshi dangana, yako yawa zuciyarsa son maryam."
Wadda a yanzun soyayya sukeyi kamar su canye junansu."
Kaka itace uwar Amarya kuma itace uwar Ango, shirye shirye biki kawai akeyi."
[3/6, 9:31 AM] Ummu Safwan WS P1: π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄         π
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
           *59*
Bayan sallar isha'i Bassam yana zaune a kusa da maimartaba, suna hira, 
Yana shaidawa maimartaba cewa "yanaso yatafi England wurin bikin  abokinsa kuma tare da Afnan yake son zuwa."
Sarki yayi murmushi yace "kayi tunani mai kyau kuwa, 
Allah ya nuna mana lokacin  sai Ku fara shiri tun yanzun."
Bassam yace "to Abba nagode Allah yak'ara girma, sukayi sallama yafito, hankalinshi gaba d'aya yana wurin Afnan, yasan tana wurin Anna yanzun."
Dan haka kai tsaye yanufi d'akin Anna, ya tarar dasu a zaune a falo Afnan sai fira take zubawa Anna tana shagwab'a Anna na biye mata."
Afnan na ganinshi taja bakinta tayi shuru tak'asa iyar da maganar da takeyi."
   Ta sunkuyar da kai cike da jin kunyarsa."
Wuri yasamu ya zauna a kan kujera, had'ida gaida Anna."
    Idonsa akan Afnan, a kullum ganinta yakeyi tafi jiya kyau, 
      Wata irin sha'awarta yaji ta fisgeshi yayi saurin runtse idonsa, had'ida sakin ajiyar zuciya."
Yayi shuru yarasa abunyi, duk abunsa baya iya cewa Afnan ta tashi sutafi d'aki, a gaban Anna."
Anna ta katse masa tunani tace "Yarima akwai abunda kake so ne?"
Idonsa a kan Afnan yace A'a dama nazone ayi firar dani, amma naga shagwab'ab'iyar 'yar nan taki, ta hana ki kulani."
Anna tace "ni ko sai naga kamar a gajiye kake, hala yau kunsha aiki?"
A gajiye ko dai sha'awar 'yarki?"
   Ya fad'a a zuciyarshi, dama zaki sallameta muwuce d'aki yanzun."
A fili kuma yace " bari intashi inje in d'an huta, ya fad'a gad'ida mik'ewa tsaye a wahalce."
Anna ta kalli Afnan tace "tashi kije ki ciyar da mijinki kiji mai yake buk'ata daga k'arshe kuma ki tayashi hira, sai da safe."
Tayi rau rau da ido ya cika da hawaye, ta tuna wahalar da tasha a daren jiya."
Gaba d'aya jikinta duk ciwo yake mata, tana k'ok'arin shareware ne saboda kar a samata ido da yawa."
Hawaye suka cika idonta,
   Anna tabita da kallo tasan sai anyi fama da Afnan, saboda jikinta baya son wahala."
Ta lura da shaidar hannun Bassam a damtsenta, wata k'ila yanuna mata k'arfi, baiyi mata a sannu ba."
Bata son nuna mata tasan abunda ke faruwa tsakaninsu, ta Shiga lallashinta cike da Jan hankali irin nasu na manya."
A sanyaye ta mik'e zuwa gurin k'ofar fita sai kuma ta tsaya tace "Anna."
"Naam d'iyata."
      "idan zai takura min nadawo wurinki?"
Murmushi Anna tayi tace "Eh mana kizo."
Itama murmushin tayi tafita a d'akin gaba d'aya."
Anna abun yabata dariya ya za'ayi ya barta tafito daya sameta ai shikenan,  Allah ya amsa masu addu'a tasamu ciki shine burinsu."
Kai tsaye ta bud'e k'ofar d'akin, yana zaune akan kujera da jallabiya sanye a jikinsa, da alama bai dad'e da fitowa daga wanka ba."
Ya d'aga idonsa ya dubeta, ajiyar zuciya yasaki, ya bud'e hannunsa alamar tazo gareshi, yana fad'in oyoyo Angel."
Murmushi tayi taje kusa dashi ta zauna ya rungumeta had'ida sauke ajiyar zuciya, ya kai bakinsa a kunnenta yace Angel luv u."
       Sonki zai kasheni."
Ta turo baki tace Anna cewa tayi Nazo natayaka hira, karkayi mun komai."
Yayi dariya yace "OK to muyi hira bani labarin."
Ta tafa hannunra ta fara, yana kallonta, tana k'ok'arin kauda idonta."
Da tagama tace _your turn_",kaima kabani labarinka, ya mik'e tsaye kamar wadda aka mitsala mashi allura."
Itama ta mik'e tsaye da sauri ko kafin ya waigo, har ta kai bakin k'ofa,
   Yace tsaya mana Angel ina zaki?"
"Ba mungama hiraba."
Ai kince inbaki labari nima ko?"
       Tace "Eh."
shine na mik'e tsaye in gyara."
Toni ta bud'e k'ofa ta fita da gudu sai d'akin Anna."
Anna na kwance har tafa bacci taji shigowarta,
  Kuyangu suna cewa "lafiya ranki ya dad'e?"
Tayi banza dasu. Ta isa kan gadon Anna tana k'ok'arin hawa bisa."
Anna tayi saurin tashi zaune tace "ke meye haka?"
"Anna kikace in gudo idan yari.... 
   Ta katseta da tashi ki koma wurin mijinki." Ni bazan kwana dakeba."
"Ke wai bada ke nake ba?"
Ta turo baki tace "wlh ni yana bani wahala."
"Kash!!"π€¦ββ Anna ta fad'a, "fita ki koma nace Afnan kina so inyi fushi dake ko?"
A'ah."
Ta fad'a tana girgiza kanta."
"To tashi kitafi wurin mijinki, bakisan mala'ikun rahama  na tsine makiba, ko malam bai fad'a maki ba?"
   Idan baki zuwa shinfid'ar mijinki Allah zaiyi fushi dake."
Idonta ya cika da hawaye tace "nidai Anna kice mashi yayi hak'uri...."
"Wai baxaki wuce ba."
  Ta kira kuyangu tace "kurakata."
Ta fara zubar da hawaye tare da kama hanya duk hankalinta a tashe yake,
Sosai Anna ta tausaya mata, dole sai tayi hak'uri tasan Bassam ba sauk'i ne dashi ba, shima dai ya rik'a yimata a hankali mana."
Yana tsakar d'aki sai yawo yake shidai Afnan so take takasheshi da sonta da kuma sha'awarta ta huta."
Shin meye laifinsa dan ya nuna yana sonta yana kuma son kasancewa da ita?"
Yanaji ana kwankwasa k'ofa, ya isa ya bud'e da sauri yana addu'ar Allah yasa itace."
Ai kuwa ita d'ince ya isa ya ruk'o hannunta, yanajin yanda jikinta yayi sanyi, ya karanci tsoro daga fuskarta."
     
A bakin gadonsa yajata suka zauna, ya kalleta yace "me Anna tace maki?"
Shuru tayi bata bashi amsa ba."
Bai jira amsartaba ya fara aikin nashi dama a buk'ace yake, bata iya hanashi ba tasan bata iyawa tunda ya Riga da yasameta."
Ita abunda yake  damunta dashi sai yayi ta yimata da k'arfi, sai tayi tagani kamar baya a hayyacinsa, ko yaya ne sai yaji mata rauni, shin hakan zasu cigaba?"
Kusan sati suka samu tare da yarima, baya d'aga mata k'afa, kuma baya binta da sauk'i."
Abun mamaki Afnan duk tafara ramewa saboda Sam batada sukuni, yarima yana matsa mata sosai, ko motsi taji saita firgita saboda jarabar yarima nadamunta."
Anna na lura da hakan, suna zaune da yamma ta kalli Afnan tace "naga kin rage kuzari kuma kid'an fad'a."
Babu numfasawa Afnan tace "yarima ne."
Anna tace "hak'uri xakiyi aure kenan."
Idonta yacika da hawaye tace "kullum sai ya tab'ani wlh akwai wahala, baya sona, ta fashe da kuka."
Anna tace "waya gaya maki?"
"Ni nasani baya sona saratu kawai yakeso, ita yana yimata a hankali."
Anna tayi shuru tana naxarinta ta gano kishi ne k'arara a tare da ita, Ashe dama tana sonshi haka?"
Suna cikin maganar sai gashi ya shigo, tana ganinshi ta tashi sum sum tabar wurin, ya bita da kallo yasan hakan na iya faruwa amma shi meye nashi take gudunsa, ita matarshi abar sonshi dole tayi hak'uri da shi."
Anna ta fara sa ido sosai a kan irin abincin da Afnan ke ciki, saboda k'azabar yarima gareta idan bata kula ba zata lalace da yawa."
Tunda duk ta Dami kanta tsoro da rashin sabo da ta d'orawa kanta shi ke sata rama."
Dama idan namiji mai yawan buk'ata ne  ya had'u da maccen da bata damu da jima'i ba, farko dole ta fuskanci wannan matsalar."
Ya dace macce ta dinga laka'ari da ire iren abincin da zata rik'a ci Dan samun kuzari da wadataccen lafiya."
Idan ba haka ba saita fita hayyacinta. Duk ta lalace saboda tunani da damuwar da zata d'orawa kanta."
Akwai hanyoyi daban daban da zata rik'a kwantarwa da mijinta hankali,
Dole tayi tunani tasan yanda zata gamsar da mijinta kobata jima'i ba,
   Sannan tayi hak'uri da jajircewa Dan bashi kanta idan ba haka ba akwai matsala kuwa."
Bassam ya zama abun gudu ga Afnan, ta gaji da fitinarshi ita tarasa dalilin da yasa har yanxun bata sababa,
   Shin ita kad'ai keda wannan matsar?"
Ta lura da ma aurata suna tsananin son sukasance tare da junansu amma ita dai kam ba hakaba ne."
Ta tsani yashigo da rana ko yamma ko dare ya nemeta, ita kam tagaji idan dare yayi ko barcin kwarai bata samu, ba dole ta lalace ba."
Snn wuni idan yashigo sai yace sai ya nace sai yayi shin su kad'ai ne a gidan?"
Baya laka'ari da mutanen dake xagaye da su?"
Kullum tana cikin wanka gashinta yana da tsowo sosai ga cika gata bata son kitso.
Kullum a jik'e yake tana zama ana gyara mata shi, kenan ita bata da aiki sai wanka kowa sai yasan abunda suke ciki.
Dama gashi bayajin kunyar uban kowa a yanzun duk inda take sai ya nemota tun a can zai shiga kissing dinta har suzo d'aki,
   Ba wai bata son yarima bane A'a tana son abunta jarabarce tashi a kanta tayi mata yawa."
Shima yarima yasan a kullum yana canzawa bai San haka yakeba sai da ya auri saratu yayi dace da itama irinsa ce harma tafishi shiyasa bai gano yana da yawan sha'awa ba sosai."
A kan Afanan ya gano shi mabuk'a cine, to ya yake danne sha'awarsa a da?"
   Duk da dai yasan barasa na mantar dashi abubuwa da yawa."
Ohoπ€·ββ  yanzun lokacinsa ne gara ya amfana ma kansa farin ciki tunda Allah yabashi wadda yafiso a rayuwarshi."
**************
Anna a gaban maimartaba, tana gaya masa ya dace ya rage bawa yarima maganin da yake bashi na jaraba."
Abin dariya ya bashi  maimartaba yace "ni bana bashi maganin jaraba, halinsa ne, aishi magani yafi k'arfi da irin halin mutum, 
   Dan haka Anna karki shafa min wannan laifin."
Tace "ranka ya dad'e to wani irin magani kake bashi?"
"Wannan kuma ba ruwanki tsakanina dashi ne."
Anna tace "ranka ya dad'e kiransa zanyi nayi masa magana yarinya duk ta kod'e ta ya mutse saboda fitinarsa."
Jiya harda kukanta, Allah ya taimakeka mezai hana kayi dubara ka lurar dashi fitinarsa gareta tana hanashi sukuni."
"Bakince zakiyi masa ba?"
A'a ranka ya dad'e kai yakamata kayi masa tunda maganarku ce."
Naga a da ba haka yakeba,
   Maimartaba yayi dariya mai sauti yace "Anna karfa kitakura masa kibarshi yayi lokacinsa ne yanzun yakejin k'arfi."
Dole Anna ta samuma Afnan maganin k'arin lafiya da kuzari h
_honey telly capsole_ dan samun ingantacciyar lafiya."
Kuma tana cin abinci mai kyau kullum zata bata maganin d'aya tasha sannan hankin Anna ya kwanta."
**************
Maimartaba da yarima suna hira cike da nishad'i, sarki ya kalli Bassam yace "yarima ina maka sha'awar kwarkwara."
Murmushi Bassam yayi tare da sa idonsa k'asa yasan Anna ta gaya mashi halinsa ga Afnan."
    Shin meye ruwanta wai?
"Ranka ya dad'e zanyi kwarkwara amma ba yanzun ba."
Akwai kwarkwarori yan shekara goma sha uku wad'anda basu San namiji ba jiya aka kawosu idan kanaso kawo maka su."
Bassam yayi murmushi a ransa yace "a duniyar nan babu macce da takai min Afnan, 
    Afnan itace rayuwata Afnan ta dabance a cikin mata babu tamkarta kota ina."
A zahiri kuma yace Abbar abarsu kawai idan natashi buk'ata zanyi maka magana."
Sarki yayi murmushi yace har yanzun bakason tara mata, 
  Mata biyu sun isheka?"
 
A lokacin da nake kamarka matan da na ajiye sunyi ashirin."
Da Sauri ya dubeshi tare da sakin baki,
Sarki yayi dariya yace "naga ka kai salati Bassam, amma kana nok'e nok'e."
Kana da damar yin hakan akwai mata masu aji da suka shahara wurin kwanciya da namiji, musamman danjin dad'in namiji akayi."
Anshirya komai ko yanzun kake son ganinsu zaka gansu."
Bassam ya nisa yace "ranka ya dad'e a gaskiya nafi 'ya'ya daga matana kawai,
     Kasan 'ya'ya suna d'aukar hali na usulinsu.
   Nafi son 'ya'yana sufito daga uwa ta gari,
  Jin dad'in tara zuri'a da maccen da baka San asulintaba akwai matsala."
Tabbas maganarka gaskiya ce, amma kuma ana iya tsaida masu da haihuwa, shiyasa kagani banada 'ya'ya a kwarkwarori."
Bassam ya kuma nisawa yace "Abba a dai barsu zan naima zuwa nan gaba."
Hajiya zainab ta katse masu hira da shigo a gigice cikin tashin hankali."
[3/6, 9:33 AM] Ummu Safwan WS P1: π *TAMBARIN SARAUTA*π€΄
π.             π€΄       









