Showing 84001 words to 87000 words out of 90241 words

Chapter 29 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9845

Bassam da yashigo a fusace, duk abunda ake fad'i a kan kunnensa."


Wani huci yakeyi kamar wani zaki. Yasanya hannu ya damk'o gashin baiwar yajashi da k'arfi,
tasaki wata irin k'arar wahala harda sakin fitsari."


Idonshi ya rik'ed'e zuwa launinja ya koma damisa,


Hajiya zainab datayi ido biyu dashi Sai da gabanta ya fad'i jikinta yasoma rawa."


Yace "duk abunda kuke k'ullawa naji kuma nagani."


Yanuna hajiya zainab da hannu yace
"wallahi tallahi muddun Afnan ko abunda ke cikinta ya suka rasa rayuwarsu, narantse da Allah kema saikin bar duniyar nan, ni zan kasheki da hannuna." In kuma gashe wannan d'an naki."


In kashe duk wata zuri'a taku wadda kike Alfahari da ita."
Dan haka ki kwana da shirin barin duniya kema."


Yajawo gashin kan baiwar yafito da ita yana janta a k'asa sai kuwa takeyi tana bashi hak'uri."


Yakira sarkin hukunci yace "ayi mata horo mai tsanani kafin yadawo asibity ya zartar mata da hukunci da kansa,


Yashiga mota yajata da k'arfi yanufi asibity."


Hankalin hajiya zainab ya kai k'ololuwa wurin tashi bata zaune bata tsaye ta aika akira mata sarkin gida, yacewa d'an aikin yace baya nan."


Tabbas tasan duk abunda Bassam yafad'i saiya aikatashi, ta d'ora hannu akai tace "wayyo Allah nashiga uku. Allah ka kawomin d'auki banaso na mutu yanzun, kuma bana son yazeed ya mutu shine farin cikina a nan duniya."
[3/6, 10:39 AM] Ummu Safwan WS P1: πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*68*












A guje ya nufi asibity, baya kallon gabansa, kai tsaye d'akin haihuwar ya nufa yana k'ok'arin shiga."


Anna da Waziri suka rik'oshi suka zaunar dashi, suna lallashinsa da ban hakuri."


Wanda yayi dai dai da zuwan kaka wurin itama fuskarta cikin tashin hankali, ganin Bassam yafita shiga tashin hankalin yasa ta koma bashi hak'uri tana kwantar mashi da zuciya."


Likita ne ya bud'e k'ofa ya fito yana fad'in ina mutanen Afnan?"


Da Sauri suka mik'e suka nufeshi, Bassam ya rik'e likita yana girgizashi yana fad'in "gani nine mijinta meyasa meta?" Ta haihu ne?"


Likita yace "kwantar da hankalinka Yarima sakeni na fad'a maka."


Anna ta jayeshi daga jikin likita tace ka natsu mana yarima, kabar likita yayi bayaninsa musan halin da take ciki a yanzun Afnan Addu'a kawai take buk'ata. Likita muna saurarenka."


Likita ya d'an ja baya d'an ya had'iye miyau. Ya kalli Yarima yasaki murnushi yace "ina tayaka murna matarka ta haihu ta haifi 'yan biyu, duk suna cikin k'oshin lafiya, sai dai ita, a yanzun tana cikin mawuyacin hali domin tana buk'atar jini sakamakon tayi zubar jini da yawa."


Alhmdulillah kaka da Anna suka ce, yarima kuma yace likita mutafi a d'ebi jini na asaka mata."


Haka akayi aka d'ebi jinin sa aka sanyawa Afnan wanda take kwance bata san Inda kanta yakeba."


Addu'a kawai yarima yake mata yana tufa mata, kotakan 'ya'yan baibiba, d'aya yana rungume da kaka d'aya kuma yana rungume da Anna."
Suna zaune a waje dukansu sai addu'ar samun lafiya sukeyiwa Afnan."


Ko wannensu da carbi a hannushi yana salati."
Likita ya turo k'ofa yashigo ya dubi yarima yace "kayi hak'uri nan da awa biyu zata farfad'o kafita daga waje kabata wuri zuwa anjima kad'an sai ka dawo. A lokacin ta farka."


Ko kallon likitan baiyi ba, yaci gaba da Addu'ar da yakeyi yana tofa mata."


Likita naganin hakan bai kuma yi mashi maganaba yaja k'afarshi ya fita."


Awa biyu na bugawa Afnan ta bud'e idonta sai a kan yarima, murmushi ya sakar mata itama ta mayar mashi,
Da sauri ya fita yanufi wurin kiran likita."


Tare sukazo tare dashi, yashiga dibata yana aunata, ya tabbatar da tasamu lafiya sai dai rashin k'arfin jiki saka makon wahalar da tasha."
Baza'a sallametaba yanzuba sai zuwa gobe a lokacin ta kuma samun sauki."


Sai a lokacin hankalin yarima ya kwanta, yashiga yiwa likita godiya."
Likita yayi murmushi ya fita."


Yana ganin fitar likitan ya tashi tsaye ya haye kan gadon ya jawota jikinshi yashiga sakar mata kiss ta ko ina, yana fad'in " Nagode Angel kinkawo farin ciki a rayuwata, da kuma rayuwar maimartaba, kin haifamana kyawawan 'ya'ya masu kama dake sak.
Sannu Angel ya kuma rungomota yasanya Bakinshi cikin bakinta yashiga tsotsa, jin k'arar bud'e k'ofar ne yasa yayi saurin durowa daga kan gadon yana d'an sosar kai."


Anna ce da kaka suka shigo, Anna ta kai mashi harara tace " nasan za'ayi hakan, wuce kafita kaje gida ka canza kayan jikinka, baka lura da yanda suka lalace bane?"


Sai a lokacin ya lura da jinin da ya b'ata masa kaya, ya juya ya kalli Afnan dake zaune a kan gado itama shi take kallo tana murmushi, yasakar mata murmushi had'ida kashe mata ido d'aya."


Maimartaba ne da kanshi ba aikeba ya turo k'ofa yashigo, fadawa na biye dashi."


Daka kalli fuskarsa Kasan yana cike da farin ciki,
Kai tsaye bakin gadon Afnan ya nufa yayi mata sannu da jiki, sannan aka d'ora mashi kujera ya zauna aka mik'a mashi jariran, ya karb'a farin cikinshi ya kasa b'oyuwa a fuskarshi sai murmushi yakeyi yana kallon yaran, wanda shima bassam dake tsaye kusa dashi ya tsurawa yaran ido cike da so da k'auna mussam 'yar macen daya lura tana kama da Afnan sak, shi kuma d'an namijin koba a fad'aba dashi yake kama."


Maimartaba yayi masu kiran sallah tare da hud'uba yasanya masu suna,
Yasanyawa namijin sunan babban Amininshi wato Alhaji Ibrahim mahaifin Afnan kenan, macen kuma yasanya mata Halimatun Sadiya, sunan mahaifiyar Afnan kenan."


Yafad'i sunan da yasan masu, kowa yashiga murna kaka harda kuka tayi haka itama Afnan."


Bassam yaja dogon numfashi yadubi jariran yace " Ubangiji Allah ya rayaku Amir da Amira yasanyawa rayuwarku Albarka,
Gaba d'aya d'akin suka amsa da Amin, kowa yaji dad'in sunan da aka sanyawa yaran har wanda Bassam yakirasu dashi Amir da Amira."


Sai a lokacin aka mik'awa Afnan su ta karb'rsu cike daso da k'auna take kallonsu idonta na tsiyayar da hawayen farin ciki."


***************


Labari ya game gidan sarautar Afnan ta haihu ta haifawa yarima 'yan biyu. Kuma dukansu suna cikin k'oshin lafiya."


Ajiyar zuciya hajiya zainab ta sauke,
Domin tasan ta kub'uta daga hukuncin da yarima yace zai d'auka a kanta idan d'aya daga cikisun ya rasa ransa."


Wani bak'in ciki da jin haushi taji yataso mata ya tokareta a wuya, jin Afnan ta haifi 'yan biyu,
Ta kai zaune, ta dubi d'anta yazeed kwance cikin mawuyacin hali. Washi wa babu duk d'aya,
idonta yana zubar da hawaye."


Ta mik'e tsaye kamar wata zautanciya, tace "na rantse da Allah indai ina numfashi a doron k'asa Bassam da zuri'arshi bazasu hau kujerar mulkiba."


Sai dai kowa ya rasa, domin zankasheshi in kashe zuri'arshi in kashe maimartaba, sannan daga k'arshe ni da kaina na haye kujerar mulkin, inyi yanda naga dama in juya kowa yanda nakeso, in kwashi dukiya in yi abunda nakeso da ita."


TaSaki wata irin dariya ta samun nasara."


**************


Alhmdulillah Afnan sauk'i yasamu, sundawo gida,


A b'angaren Anna aka ajiyeta, tana samun kula sosai tsakanin kaka da Anna wanda a yanzun kaka tadawo gidan da zama, idan Afnan tayi Arba'in zata koma gida a cewarta."


Barka ake zuwa yiwa maimartaba da Bassam k'asa k'asa garigari."


Kowa a gidan cike yake da murna da farin ciki, amma banda hajiya zainab."


Ranar suna bikine na 'ya'yan gata jikoki a wurin Sarki Ahmad mohd,
Kuzo kukaga taron jama'a a cikin gidan sarautar."


Matan sarakuna da matan shuwagabannin k'asa, matan gwamnoni kai duk wasu masu fad'a aji sun hallara a wurin bikin Amir da Amira."


Duk wanda kagani fuskarshi cike take da murna da farin ciki,
Afnan da Bassam sunci ado na burgewa sunsan ya wata dakankiyar shadda ruwan zuma har wani mai take fitarwa tana shek'e, daka gansu ka dubi fuskarsu kasan suna cike da farin ciki, sai d'aukarsu hoto akeyi."


Yan jarida da yan gulma duk ba'a barsu a bayaba, kowa k'ok'arin yake ya d'aukesu photo yaji dad'in ya d'awa a duniya."


To nima dai ina gefe d'aya zaune, da birona da takardata a hannuna sai d'aukar rahoto nakeyi,


d'aya gefena kuma jama'ar groups dina ne
_Ummu safwan and tambarin sarauta_
sai kwasar gara sukeyi,
Matsalata d'aya dasu a nan sukafi maida hankali, wurin dannar gara, musamman su o'o da o'a nidai ban fad'i sunaba😜


A can na hango ta wakagar yan group din Aisha A moh'd, wai wai ba laifi sun d'auki wanka, amma abun mamaki kular shinkafa suke hange suna had'iyar miyau." Tare da lashe bakiπŸ˜‹


Karku damu bikin Amir da Amira ne 'ya'yan gata zakuci shinkafa har sai kunbarta😜


Nima dai nayi nan, saboda nikaina yunwar nakeji, mukwashi gara lafiyaπŸ˜œπŸ˜œπŸ˜œπŸ˜œπŸ˜œπŸ˜œπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
[3/6, 10:42 AM] Ummu Safwan WS P1: πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*69*






Sarkin gida gurgane a gaban hajiya zainab yana sauke numfashi da sauri da sauri kamar wanda yayi gudu."


"Ranki ya dad'e wannan karon kam da kyar nasha a wurin boka na hayi."


Ya ciro k'ullin magani ya mik'a mata
Yace wannan yace kitafasashi da ruwan zafi, kibawa Yazeed yasha da zarar yashanyeshi kiyi mashi turare yace tabbas zai warke,
domin ya gano sammu ne akayi mashi."


Wannan kuma yace idan dare yayi, misalin k'arfe biyu da rabi na dare, idan kika tabbatar da kowa ya kwanta, zakiyi ziddir kicire kayan jikinki gaba d'aya, ki zuba maganin a kaskon wuta, kifito waje tsakar fili. Ki kikira sunan yarima sau uku da Afnan da maimartaba, da duk wanda kikeso kiga baya motsi a doron k'asa ki kira sunanshi sau uku."


Amma da sharad'i yace "kada kijuya, kada kiyi magana bayan kin ambaci sunan su."
Idan kika sab'awa umurninshi yace daga ni harke muna cikin matsala da tashin hankali."


Allah ya taimakeki Allah yabaki kujerar mulkin nan a ranar komai namune, muyi yanda mukeso dashi."


Wata dariya tasaki mai sauti, ta buga k'afarta k'asa tace "lallai ashe kwanan yarima da duk wani magoya bayanshi ya k'are."


"Sarkin gida kasanyawa rayuwarka cewa da zarar na hau kujerar sarauta,
nayi maka Alk'awarin zinari dubu, gwala gwalai dubu,
duk wata zuri'a taka nayi maka Alk'awarin sai na kaisu aikin hajjin bana,
Sannan kuma zan baka kujerar waziri na."


Sarki gida yace " godiya nake ranki ya dad'e Allah ya tayaki rik'o,
Aini yanzun hakan na hangoki a kan kujerar sarautar."


"Amma ranki ya dad'e ki kula da kyau da yanda zakiyi aiki da maganin dan gudun samun matsala daga ni harke."


"Kar kadamu sarkin gida aina fahimce ka, insha Allahu baza'a samu matsalaba."


Ta mik'a mashi rafar kud'i "ga wannan tukuicinka ne kafara rik'awa."


Yasanya hannu biyu ya amsa tare da bud'e baki yana dariya cike da jindad'i yatashi ya fita."


Da fitarshi takira kuyangunta ta mik'a masu maganin tace "ina bugatar a tafasa min wannan maganin da ruwa zafi a kawo min shi yanzun,
Dasauri suka karb'a suka nufi kicin domin ai watar da aikin da tasanyasu."


Cikin minti goma suka kawo mata tafasasshin maganin har wani kumfa yake fitarwa,


A hakan ta Tayar da Yazeed zaune tashiga d'ura mashi maganin yana sha, sai da ya shanyeshi tas sannan ta ajiye copin maganin tana murmushin samun nasara."


Minti biyar da kammala bawa yazeed magani ya fara wani kalar zawo tsanwa shar mai mugun wari."


Da gudu ta bar d'akin tana toshi hancinta saboda azabanbin wurin kashin,
D'aya d'akinta ta bud'e ta shiga,


ta shiga kiran masuyi mata hidima "tabasu umurnin su kula da Yazeed."


*2:30am* Hajiya zainab ziddir haihuwar uwarta tafito waje, tsakar fili, da kaskon wuta a hannunta hayaki na tashi, fuskarta ba tausayi ba imani.
Yarima shine mutum na farko da tafara kira har sau uku sannan ta fara kiran maimartaba."


Jitayi anrik'e mata k'afa tayi saurin juyawa domin ganin ko waye,
Yazeed tagani a gefenta tsaye rik'e da k'afarta yana fad'in "mama mekikeyi a nan ba kaya a jikinki?"


Murna da jin dad'i ya kamata tace "yazeed ka warke kai Allah nagode maka,
Wuce ka koma d'aki ganinan zuwa yanzun."


Tunawa tayi da sarkin gida yace "ba'a magana tayi saurin rufe bakinta tana fad'in "wai na manta ance ba'a magana to amma kuma ai murna ce nayi."


Taci gaba da turarenta takira sarki takira Afnan da yaranta, harda Anna, duk sunshiga a cikin matattu."


Tana kammalawa tasaki wata irin dariya da shewa gaba d'aya filin wurin sai da ya amsa,
Hakan yajawo hankalin bayi masu gadin wurin suka firfito da fitulu a hannunsu suna fad'in "waye ne?."


Keta kowa hajiya zainab tayi ta yanka da gudu tabi hanya tsirara tana fisgar gashin gabanta."


Dafa mata baya sukayi suna fad'in hajiya zainab ce fa."


Amma ina tab'ace masu,
Basu gantaba
kasancewar gidan babban gida ne, wanda baya misaltuwa."


Jin hayaniyar mutane gidan kowa ya farka, yasa maimartaba fitowa yana tambayar lafiya meke faruwa?"


Anan aka shiga fad'a mashi abunda ya faru,
Cikin tashin hankali ya dokawa bayi tsawa yace "me kuke jira da bazaku shiga lungu da Sak'o na gidan nan kunemotaba?"


Ai bairufe bakinsaba gaba d'aya kowa ya watse a wurin,
suka rarrabu ko wannensu da fitila a hannunshi suka Shiga nemanta."


Tashin hankali sarki ya shigeshi na haukacewa hajiya zainab, wanda damuwar tasanyashi zubar da hawayensa, barcin da bai kwantaba kenan yashiga jera salloli, yana Addu'ar Allah ya bayyanata."


Har safiya ta waye ba a gantaba, sai dai akaji labarin sarkin gida ya rasu, saka makon wasu k'uraje dasuka fito masa cikin dare kafin Safiya ta waye yarasu."


Hankalin Sarki ya kuma tashi ya d'aga waya yakira Bassam da baisan abunda ke faruwaba,
yana can b'angaren Anna yana wasa da 'yan biyunsa yana dariya."


Ganin kiran maimartaba yasa ya mik'awa Kaka su,


Ya d'aga wayar had'ida mik'ewa tsaye yanufi hanyar waje."


Sarki yace "yarima duk Inda kake kayi Sauri kazo ina kiranka domin gidan nan ba lafiya."


Da sauri Bassam ya fita yana fad'in "Abba lafiya meke faruwa?"


Sarki ya katse wayar,
Da sauri Bassam yanufi sashin maimartaba."


Sarki yashiga gaya masa abunda ke faruwa harda b'atan hajiya zainab a daren jiya harda mutuwar da sarkin gida yayi yanzun da safen nan."


Wannan labarin ya girgixa yarima sosai, duk da dai yasan mugun abunso ne ya koma masu."


Ya dubi sarki yace "Abba toshi yazeed awane hali yake yanxun?"


Sarki ya mik'e tsaye yace "mutafi munganshi musan halin da yake ciki."


Yazeed kwance cikin zawo mai wari, gaba d'aya jikinshi wasu manyan k'uraje sun fito mashi, shigowar maimartaba da yarima ransa na fita."


Runtse idonsa Sarki yayi yaja da baya yafita d'akin ya jingine da bango ya yana sauke numfashi a hankali."


Yana fad'in "meke faruwa a gidan nan ne bansaniba?"
Hajiya zainab ta haukace ba'a gantaba,
Sarkin gida ya mutu jiya,
Yanzun kuma d'ana yazeed shima ya mutu yau."
Yarima meke faruwa ne?" Ya fad'a cikin d'aga murya, alamar tashin hankalin!!!!!!!


Yarima ya matso kusa dashi ya dafashi, yace "Abba karka d'aga hankalinka, har wani ciwo yashigeka."


Ka natsu ka kwantar da hankalinka, ka fahimci ko wacece hajiya zainab da irin mugun halinta da yanda take gudanar da rayuwarta."


Abba nasan kafi kowa sanin ko wacece ita, tunda kai kake cewa muyi hattara da sharrinta,da muguntarta."


Idan kayi la'kari da hakan, zaka fahimci cewa Allah ne ya mayar mata da muguntarta da mugun nufinta ya koma a kanta."


Sarkin gida kuma dama na hannun damarta ne duk abunda take k'ullawa da kwancewa a gidan nan tare sukeyinsa."


Ka kwantar da hankalinka Abba karka sanyawa rayuwarka tunani. Gudun kar wani ciwo ya shigeka kasani kaine gatana, kai kad'ai nake dashi a duniyar nan."


Muyi Addu'a duk inda tashiga Allah ya bayyanar da ita."


Fadawa aka kira akayiwa sarkin gida sutura tare da yazeed aka kaisu ma kwancinsu."


Wasa wasa kusan sati biyu kenan ba labarin hajiya zainab gaba d'aya anduba cikin gidan ba'a gantaba,

Gaba d'aya gidan ba mai fad'ar mata alheri sai sharrinta, ma aikatanta bbu abunda suke furta mata sai tsinuwa suna fad'in Allah yasa kar a ganta."


Tun sarki yana damuwa, har ya kai ya hak'ura sai dai a duk lokacin da yayi sallah yana addu'a Allah ya bayyanata, koda gawarta ce a gani."


**************


Ayau Afnan take cika kwana arba'in da haihuwa."
Gyarane tashashi a wurin Anna da kaka, tayi kyau har ta gaji, Amir da Amira kuma suma sun girma sunyi k'iba idan ka gansu sai ka d'auka 'yan wata bakwai ne."


Shiryata akeyi sosai domin yaune zata koma turaka."


Inda shima yarima cike yake da murna da jin dad'i, yau zai kasance tare da abun sonshi Afnan."


Indai hak'uri yayi hak'uri, yau kwanansa arba'in batare da macce ba, sai dai idan dare yayi yayita matse matse akan gado mararshi tana yimashi ciwo."


Idan kuma ya tunkari wurin matarshi Anna ta koroshi tana cemasa baya da hak'uri to shi kuma meye rashin hak'urinshi a ciki, tunda dai matarshi ce."


Shiri yakeyi sosai ya shiga toilet yayi wanka ya feshi jikinshi da turare ya sanya kayan barci ya haye kan gado ya kwanta Afnan kawai yake jira."


Da sallama ta shogo tareda kuyangu d'auke da Amir da Amira da suka dad'e da yin barci."


Karb'arsu tayi ta kwantar dasu ko wanne a kan gadonsa,


tayi sallama da kuyangu suka tafi."


Juyawar da zatayi tashiga brdrom yarima taci karo dashi tsaye a bayanta."


Rugumeta yayi yashiga aika mata da kiss ta ko ina yana fad'in _missing you Angel_


A hankali yajata zuwa gado yashiga nuna mata yanda yayi _missing_ d'inta."


A yau ya kuma tabbatar da Angel d'inshi ta dabance ko a cikin mata,

Jinta yayi ta canza mashi dama haka macce take canzawa idan ta haihu?"


Sai yanzun ya kuma tabbatar da ni'imar da Allah yayiwa Afnan ta dabance, hannu ya d'aga sama yna godiya ga Allah da ya Azurtashi da macce kamar Afnan."


Itama A wurinta hakan ke faruwa, domin bata tab'ajin dad'in da tajiya irin na yauba."


Tabbas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login