Showing 87001 words to 90000 words out of 90241 words

Chapter 30 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9830

da gaskiyar Anna datake cewa Afnan
" kinatsu ki saurareni yau zaki koma wurin mijinki
Inaso kisaki jikinki ki nunawa mijiki soyayya domin zakijiki kinshiga cikin wata sabuwar rayuwa mai cike da jin dad'i."


Sai yanzun ta tabbatar da abunda Anna take nufi,
Rungume prince tayi tasanya bakinta a cikin nashi,
Anan suka shiga bawa junansu dad'i. Ko wannensu sai nishin dad'i yakeyi suna zubarda hawayen k'auna."
[3/6, 11:21 AM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*70*








Wata biyu kenan ba hajiya zainab ba labarinta,


Sarki ya yanke shawarar d'ora Afnan a kan kujerarta a matsayin sarauniya."


Inda Fulani da hajiya Amina suka farajin haushi domin a tsamma ninsu d'aya daga cikinsu za'a d'ora akan kujerar."


Bassam yaji dad'i sosai ya nuna farin cikinsa a fili."


Da murnansa ya nufi wurin Afnan, ya tarar da ita akan gado tana sanyawa Amir da Amira Pampas."


Rungumeta yayi ta bayanta ya sakar mata kiss a kunci had'ida d'aukar Amira da aka shirya mata yana wasa da ita tana dariya."

Itama murmushin takeyi ta k'ure da ido da alamar yana cike da farin ciki."


Tace "my Prince sannu da shigowa, amma daga ganin fuskarka akwai magana a bakinka."


Murmushin fuskarshi ya kuma yawaita, yace Albishirinki Angel."


"Goro fari." Ta fad'a itama tana murmushi."


"Sarki ya yanke shawarar d'oraki a matsayin sarauniya."


Zaro ido tayi waje, cike da mmki, tace "Anya my prince zan iya shugabancin nan kuwa?"


Dibo da yanda hajiya zainab take juya gidan nan tana fafatawa da kuyangu,
Sannan duk wani shige da ficen abincin gidan nan d'anye ko dafaffe a k'ark'ashinta yake."


My Prince bansan ko maiba a kan mulki, tayaya zan shugabanci mutanan gidan nan?"


Ido yabita dasu yana kallon d'an k'aramin bakinta dake magana cikin natsuwa da girmamawa,


Ya matso daf da ita yanda suke iyajin saukar numfashin junansu,
Ya rungumota cikin murya k'asa k'asa yace "Angel zaki iya mulkin gidan nan, karki manta da Anna na kusa dake anna zata nuna maki yanda zaki tafiyar da mulkinki cikin amana da gaskiya."


Tunawa tayi da Anna na kusa, yasa hankalinta ya kwanta ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya tayani rik'o."


"Amin Angel, yace had'ida shafa cikinta,
Anya Angel ba ajiyata a cikin nan domin na fara ganin alamu."


Turo baki tayi alamar shagwab'a "A'a nidai ba yanzunba ya zanyi dasu Amira?"


Murmushi ya kuma saki '"su Amira basuda Matsala, nifa nafison naga anata cika mun gida da 'ya'ya, kasan cewar in kad'aine a wurin maimartaba."


Batayi maganaba illah tashi da tayi tabar mashi wurin tashiga sauya kayan jikinta."


"Yawwa kiyi saurin ki shirya mutafi fada sarki nason ganinki."




Hakan ta shirya tsaf tasanya lesi ruwan madara, ta d'ora Alkyabbar ta,
itama ruwan madara, ta d'auki Amira ta sab'ata a kafad'a,
Shima ya d'auki Amir suka jera suka fita suna tafiya suna hira gwanin ban sha'awa, suka nufi fada."


A gaban maimartaba suka runsuna suna gaisuwa."


Yana murmushi yana kallonsu cike da burgewa,
Yake Amsa gaisuwarsu, ya tara hannu ya karb'i jikokinsa da sukafi soyuwa a ransa. Yana masu wasa suna dariya kasancewar sunsaba dashi kullum a wurinshi suke yini idan ya fito daga fada."


Ya dubi Afnan yace "Afnan yarima ya fad'a maki matsayinda zaki hau a gidan nan, na yarda dake na yarda da tarbiyarki wannan dalilin yasa nazab'eki a matsayin sarauniyar masarautar nan."
Allah yatayaki rik'o yabaki ikon rik'e gaskiya da Amana."


Suka Amsa da Amin gaba d'ayansu."


Afnan ta tsurawa *Tambarin sarautar* ido data Ganshi a jiye wuri d'aya anzagayeshi da kyale kyale gwanin burgewa da alama yana da mahimmaci a masarautar saka makon yanda take ganin bayi da kuyanku da duk wasu masu dangataka a masarautar take ganinshi lik'e a jikinsu."


Bata mantaba ta tab'a tambayar Sadi da cewa wai meye amfanin mannawa mutane wannan tambarin a bayan rigarsu ko a saman hularsu."


Idon kuma motar masarautar ce zata ganta lik'e da tambarin."


Sadi yace Tab Aminiya akwai tambaya kamar 'yar jarida,
To Nima dai yanda kike ganin tambarin nan haka nake ganinsa, bansan dalilin dayasa masarautar nan suke girmama tambarin nan ba


Amma kuma ina ganin shine k'undin tarihin sarautar nan sannu a hankali zamu san komai."


To sai yanzun gata kusa da tambarin, kuma tana Neman sanin ko meye shi."


Ta kalli maimartaba da shima ita yake kallo tace "Abba inada tambaya."


Yarima ya d'ago kai ya dubeta, ta dubishi ta sakar mashi murmushi,


"Abba na dad'e ina tambaya akan wannan tambarin narasa Wanda zaibani amsa,
Abba Dan Allah wannan tambarin nameye?"
Me akeyi dashi?"
Meyasa duk wani mutum wanda ke rayuwa a gidan nan ko wanda keda dangartaka a masarautar nan sai na gashin lik'e da wannan tambarin?"


Sarki yayi murmushi yace 'yata kinyi tambaya mai kyau, wadda koda baki tambayaba nayi Alk'awarin zankiraku tareda yarima nabaku labarin *tambarin* nan."


Wannan shine *Tambarin sarautar* masarautar nan, duk wani k'undun tarihi na masarautar nan yana cikinsa, da iya adadin dokiyar da masarautar nan ta mallaka."


Sarki na d'aya yabar wasiya da cewa bazai tab'a amfanuwaba har sai sarki mai adalci ya hau kujerar mulkin garin nan


Bayan mutuwar sarki na d'aya sarki bakwai ya hau kujerar mulkin garin nan nine na takwas amma abun mmki maimakon ya gyaro sai dai ya kuma lalacewa saboda ba gaskiya a cikin zuciyoyin wasu sarakunan, har zuwa yanzun a kaina munkasa gyarashi,


Wanda ni bashine a gabanaba domin bantab'a dogaro da dukiyar sarautaba, wannan dalilin yasa tunda na hau kujerar mulki bantab'a kiran wani mai kyara dasunan ya gyarashi ba,


Sab'anin sauran sarakunan da suka gabata burinsu d'aya ne da zarar sun hau kujerar mulkin su gyara wannan tambarin domin su san adadin abunda masarauta takeda shi, su kwashi dukiya suyi abunda sukesu da ita."


K'asa k'asa jahohi jahohi, sunta kiran wanda zai gyara, masu shi."
Amma abun mmki da zarar antab'ashi da sunan gyara sai wani Abu a cikin fadar nan ya kuma d'aukewa ya daina aiki."


Wannan dalilin yasa bandamu dashiba, mulkina nasanya a gaba, babban burina a rayuwarta talaka yaji dad'i,
Babban burina shine in kyautatawa talakawa in faranta masu in yaye masu damuwa da kuncin rayuwarsu."


Wannan dalilin yasa kike ganin kowa a cikin gidan nan da *tambarin sarauta* like a bayansa."


Afnan ta nisa tace "Abba zan iya gyarashi."


Yarima yayi saurin juyowa ya dubeta cikin mmki yace "tayaya?"


Bayan kinji Abba yace "babu k'asar da ba'a d'auko mai gyaraba da sunan ya gyarashi amma ya kasa." Saike?" Mekika sani?" A fannin gyara?"


Tayi murmushi tace "ni zan iya gyarashi, yarima yayi murmushi yace Angel ina ganin kamar baki fahimci bayanin da Abba yayi ba da kyau."


"Na fahimta sai dai idan Kaine baka fahimceni da kyauba."


Maimarba yayi gyaran murya yace "Ku saurara, "Afnan bazaki iya kyara tambarin sarautar nan ba, kibarshi kawai a yanda kika ganshi idan Allah yayi kafin nasauka a kan kujerar mulki zai gyaru Alhmdulillah idan kuma Allah yayi bazai gyaruba shikenan duk wanda ya hau ya gyaru a lokacinsa ina mashi Addu'ar Allah ya tayashi rik'o."


Suka amsa da "Amin gaba d'ayansu sukayi mashi sallama suka fito."


A Daren ranar Afnan kasa barci tayi sai tunanin *tambarin sarauta* takeyi, itafa zata iya gyarashi. Ta gyara abunda yafishi girma da had'arin gaske bare wancan tambarin."


Koda dai ance sai lokacin sarki mai adalci xai gyaru.


Amma ai Abba yana da adalci ga tausayin talakawanshi, tun kafin ta sanya rayuwar zata shigo gidan sarautar takejin labarin irin tausayi da karamcin irin na sarki Ahmad moh'd."


Juyawa tayi ta dubi yarima taga barcinsa yakeyi."


Agogo ta duba taga k'arfe uku na dare,
A hankali ta sauka daga kan gadon ta d'auko hijabin sallarta ta sanya a kan kayan barcinta kasan cewar riga da dogon wando ne masu yalwar fad'i,


Ta lallab'a a hankali cikin sand'a ta fita d'akin had'ida jan kofa."


Kai tsaye fada ta nufa, tayi sa'a da gaba d'aya masu gad'in fadar duk barci sukeyi,


Kai tsaye wurin tambarin sarauta ta nufa,
Ido ta tsora mashi tana tunanin ta ina zata fara."


Wuri tasamu ta zauna ta bud'eshi gaba d'aya tashiga gyarawa,
Tana cikin gyaran taga gaba d'aya wasu manyan kwaya kwai na kwala kwalai da suka bar aiki a masarautar sunkawo haske, tsoro abun yabata, amma hakan baisa ta daina gyaranba taci gaba."


Wasu kwaya kwayi tagani wad'anda ke ajiye wuri d'aya suma sunkawo haske sunfara aiki."
Sai wani jiniyar kuka da tambarin yake fitarwa wanda duk wanda ke rayuwa a cikin gidan saida yaji jiniyar."


Fadawa dake gadin wurin suka mik'e tsaye da takobi a hannunsu ganin hasken da basu tab'a ganin shiba yasa sukaja wuri d'aya suka toge suna zarar idanu.
Gaba d'aya haske ya haske masu fuska


Sarki a can cikin barcinsa yaga haske ya kashe masa ido, da sauri ya tashi zaune, yashiga mamaki ganin ba hasken NEPA bane wasu na"urori ne da tunda ya hau kujerar mulk yaga basa aiki sai yanxun."


Sautin jiniyar wani Abu yakeji yana tashi, a cikin gidan,
da sauri ya sanya jallabiyarsa ya fito waje cike da mamaki da tashin hankali."


Gaba d'aya gidan ya haskake da gaske kuma ba hasken wutar NEPA bane."


Karo yaci da Bassam shima ya nufo wurinshi
Gaba d'aya fada suka nufa domin sun fahimci a can komai ke faruwa."


Duk ilahirin jama'ar gidan gaba d'aya sun d'unguma suna bakin fada tsaitsaye anrasa Wadda zaishiga cikin fadar."


Zuwan sarki da Bassam wurin,
kallo ya koma kansu, kai tsaye suka tunkari fadar gadan gadan babu fargaba a tare dasu."


Shigarsu fadar yayi daidai da kammala gyaran *tambarin sarautar* da Afnan Takeyi
[3/6, 11:23 AM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑. 🤴 👑




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)












*71*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚










Wuri d'aya suka ja suka tsaya suna kallonta cike da mamaki,
Murnace a fuskar sarki ko farin ciki?"


Wani murmushi yake fitarwa yana kallon Afnan. Yana kuma kallon fada da nan take koma kamar ba itaba."


Da sauri Bassam yanufeta ya rungumeta,
Cikin da farin ciki da jin dad'i yarasa abunda zai cemata sai dariya' yake yana shafa bayanta,




A hankali ta janye jikinta ta nufi wurin maimartaba ta durk'usa k'asa tace "Abba kayi hak'uri, idan hakan da nayi nab'ata maka."


Kallon ya bita dashi ya kasa yin magana saboda farin ciki dake tare dashi."


Nuni yayi mata da ta mik'e tsaye, yace "nagode maki Afnan hak'ik'a ke Alheri ce a rayuwarmu.

Ya juya ya kalli yarima da yaje wurin tambarin sarautar yanason yatab'a yanajin tsoro kuma."


Mutanen dake waje ganin sarki da yarima sunshiga basu fitoba. Yasa sukayi ayari gaba d'ayansu suka shigo cikin fadar."


Abunda kowa ya ganewa idonsa yasa suka shiga mmki, tambarin sarauta ne ya gyaru.?"


Murna sukeyi suna kuwa,
Suna jin dad'i."


Sarki ya dakatar dasu yace "kowa yaje ya kwanta sai da safe za'ayi magana."


Ya dubi yarima dake rungume da Afnan yace "kutafi sashinku sai gobe zamuyi magana, ku kwanta da shirin gobe za'a gabatar da Afnan a matsayin sarauniya a gaban kowa ya shaidata."


Hakan kowa ya kwanta cike da farin ciki a ransa."


Anna tayi murna sosai taji dad'i ta kumajin ta k'ara son Afnan a ranta,
Hakan itama kaka taji dad'i sosai
Anan tashiga bawa Anna labarin irin baiwar da Allah yayiwa Afnan tun tana k'ara marta."


B'angaren Bassam shima hakan domin rungume yake da ita jiyakeyi kamar ya maida ta cikinsa, saboda murnar dafarin ciki."


Bakinsa ya Sanya a kunnenta yashiga yi mata rad'a yana fad'in?
Tabbas Afnan ke Alherice ga rayuwar Bassam, kuma farin ciki ce a cikin wannan masarautar."
Soyayyar Afnan ta kuma lunkuwa a cikin zuciyar Bassam."


Angel kinbani mamaki, Ashe ke 'yar baiwace, kece jin dad'inmu da annashawarmu."


Nayi maki Alk'awarin yanda kika wanzar da farin ciki a rayuwarmu, data mahaifina da kuma masarautar nan gaba d'aya baxaki tab'a kokawa."


Nayi Alk'awarin zanjiyar dake dad'i in kuna sanyaki farin ciki, mai d'orewa tare dake da duk wata zuri'a taku."


Kuma matseta yayi a jikinsa, ya shiga aika Mata da sak'onninsa masu wuyar misaltuwa."


*9:am*
Sun shirya tsam sunyi kwalliyarsu irin ta 'ya'yan sarauta, manyan Alkyabba ne s suka Sanya wad'anda sun karb'esu gaba d'aya sunyi kyau wanda baya misaltuwa."


Fitowa sukayi suka nufi wurin taron gabatarda Afnan a matsayin Sarauniya."


Duk mutanen cikin gidan sun hallara har matan sarki Fulani da Hajiya Amina,
Da Anna da Kaka, suna gefe d'aya na musamman a zaune."


K'arasowar Afnan da yarima sukayi wurin
kowa ya hau kallonsu gwanin burgewa."


Wurinda aka tana darmasu domin su, zauna, a can suka nufa suka zauna."


Sarki da kansa, ya mik'e tsaye fuskarshi cike da annashawa yana murmushim farin ciki.
Sannan ya fara jawabi."


Yanuna Afnan yace "ayanzun itace sarauniyar gidan nan, duk wani Aiki da kukasan hajiya zainab na aiwayarwa a gidan nan, ya dawo a kan Afnan."


Kuyi mata biyayya kamar yanda kukeyiwa hajiya zainab biyayya."


Yin hakan shi zai sanya naji dad'i na kuma k'ara Alfahari daku a cikin masarautar nan."

Afnan takawo canji da d'aukaka a masarautar nan, na rantse da Allah da macce na hawa kujerar sarauta dana sauka na d'ora Afnan akai."


Bassam ya fara tab'awa sannan gaba d'aya kowa ya d'auki tab'awa."


Kaka da Anna Dan murna harda hawayen farin ciki suke fitarwa."


Anan aka shiga bikin nad'in Afnan a matsayin sarauniya, kid'e kid'e akeyi da bushe bushe, ana zuba mata kirari."


*A gurguje*
Gimbiya Afnan mulki takeyi cikin kwanciyar hankali da Adalci,
Wani lokacin gani takeyi kamar abun yanaso yafi k'arfinta, da taimakon bassam da Anna, komai ke tafiya dai dai yanda ya kamata.


Tafiya takeyi cike da k'asaita kuyangu na bayanta suna zuba mata kirari, gani tayi anwuce da kayan abinci b'angarin fulani."


Sashin su fulanin ta nufa, wurin da ake dafa masu abinci da kayan motsa baki taja ta tsaya."


Mamaki ya cikata ganin irin abincin da suke amfani dashi a rana d'aya."


Ya isa ya wadatar da mutum a shin a rana d'aya."
A dadin kud'insa a abincin talata mutum d'ari zai iya ciyar da gidansa da kud'in."


Ta dakatar da masu aiki a b'angaren, ta umurcesu da cikin kashi uku, a surage kashi biyu sudinga yimasu amfani da kashi d'aya."


Suka amsa da angama ranki ya dad'e."


Sashinsu ta koma ta tarar da yarima zaune cikin yaranshi yana wasa dasu suna dariya."


Kusa dashi taje ta zauna, yajawota a jikinsa, yana fad'in "sannu da aiki sarauniya."
Sarki da mutanen gidan nan suna Alfahari dake."


Murmushi tayi "ina godiya my prince.
Ta kuma nisawa. Yarima yace "meke faruwa sarauniya."


"Nasan Fulani zasuga laifina. ni kuma idan akan gaskiya ne bana shakkan hakan."


Tayaya abincin da suke amfani dashi rana d'aya ya isa ya wadatar talata d'ari tare da iyalinsa."


Tayaya zamu zab'i rayuwar jin dad'i talaka yana cikin k'unci na talauci."


Nayi Alk'awarin duk wanda naga zaishiga cikin dukiyar talakawa, domin jin dad'insa saina dakatar dashi."


Prince ya rungumeta yana aika mata da kiss ta ko ina."
"Allah ya tayaki rik'o sarauniya nima ina bayanki."


Sarki yace a fad'amaki kishirya gobe zamuje masarautar zamfara bikin sunan jikan da aka haifawa sarkin zamfara."


Domin sarakuna da matan sarakuna zasu hallara a wurin.
Za'a nunaki a cikin taron sakuna kece macce d'aya tamkar da dubu, kice kika samu nasarar gyara *tambarin sarauta*


a gaban sarakuna maimartaba zai baki kyautar ban girma da d'aukaka."


Tayi murna sosai wanda hakan yasa ta k'ank'ameshi tana godiya."


Tace my prince tashi mutafi karakani store na shirya duk wani Abu da za'ayi amfani dashi gobe."


Hakan suka shirya suna tafiya suna hira gwanin ban sha'awa da burgewa."


Suna gafda shiga store d'in, sukaci karo da bayi tsaitsaye a k'ofar wurin suna zarar ido."


Yarima ya fara tambayarsu "lfy meke faruwa?"


Dukansu suka zube k'asa "ranka ya dad'e motsi mukeji a saman sili,mun d'auka kusani, amma wannan motsin yafi k'arfin na kusa."


Kai tsaye Afnan tashiga yarima yayo saurin jawota yadawo da ita baya, ya wuce gaba bayi suka rufa mashi baya."


Wata k'ofa ce k'arama wadda zata sadaka har cikin silin.
ya d'ora tsani ya hau , yanufi cikin silin."


Wazai gani hajiya zainab,
Gaba d'aya tafita hayyacinta wannan kyawon nata ya dusashe. Gashin kanta ya gutsere, sai nishi takeyi sama sama alamar mura tayi mata muguwar kamu."


Saukowa yayi yaba bayi umurni su hau su fito da ita."


Bayan anfito da ita gata kwance tsirara, Afnan tabawa bayi mata umurni da sud'auko sutura su Sanya mata."


Bayan ansanya mata sutura, yarima ya d'aga waya ya kira maimartaba,
Da sauri maimartaba yazo."


Yana ganinta cikin wannan halin saida gabanshi ya fad'i ya tausaya mata matuk'a."


Gani sukayi ta mik'e zaune idonta yana zubar da hawaye, Anan tabud'e baki tashiga tonawa kanta asiri duk irin mugun abunda tayita shukawa."


Ta dubi yarima "yarima ka yafe min, Maimartaba ka gafarceni, Afnan kema ki yafe min."


Tana kaiwa nan tafara shakkuwa, ranta ya fita."


Duk wanda ke wurin sai da idonshi ya cika da hawayen tausayinta."


Anan take akayi mata wanka akayi mata sittura. Aka kaita gidanta na gaskiya."


*hajiya zainab Allah ya yafe maki*


**************


Zamfara,
Masarautar zamfara masarautace mai cike da Adalci da daraja d'an Adam."


Bikine akeyi na jikan sarkin zamfara jika na uku."


Kowa ya hallara sai wad'anda ba'a rasaba."


Afnan da Bassam sunk'araso cikin shiga ta Alfarma suna rik'e da 'ya'yansu gwanin burgewa."


Wanda shi maimartaba ya dad'e da zuwa tare da Fulani."


Tafiya sukeyi wanda zata sadasu da fadar masarautar."


Wasu bayi sukagani su biyu macce da namiji, and'ora masu manyan itace suna tafiya ana tsula masu bulala sai kuwa sukeyi saboda azaba."


Sautin Kuwaarsu yaja hankalin yarima da Afnan suka juya,
Wazasu gani saratu da Alhaji Aminu, duk sunfita hanyacinsu cikin k'angin bauta."


Saratu nayin ido biyu da yarima da Afnan da yaransu masu sunfar larabawa,
Kukanta ya tsanta tana kallonsu ba damar tayi masu magana."


Yarima yakuma kallonsu ya mere Baki,
Afnan kuma ta tausaya mata matuk'a amma ba yanda zatayi mata
Tana gani aka tasa k'eyarsu suna tafiya ana zafga masu bulala."


*karshen Azzalumi da maci Amana baikyau. Allah yasa mufi k'arfin zuciyarmu*


Alhmdulillah anyi biki lfy ank'are

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login