Showing 45001 words to 48000 words out of 90241 words
Chapter 16 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt
 koda Allah zaisa ya ganta."
Bai ganta ba, yanufi wurin zaman sa yana sake sake a ransa."
Afnan na ganin tafiyar sa, ta fito a guje, da mangwaro  a hannuta, tanufi wurin dabbobinta ta rera wak'a har da 'yar rawarta."
Sallamar da akayi masa ne, ita ce ta katse masa dogon tunanin da yakeyi."
"Yasir?" Ya fad'a tare da mik'ewa tsaye."
"Daga ina haka?" Ya mik'a masa hannu suka gaisa."
Yasir d'an Anna ne ba'a k'asar nan yake da zama ba."
 suna matuk'ar shiri da Bassam sosai, suka samu wuri suka zauna."
Yasir ya kalli Bassam yace "Yarima kenan kana hutawarka kaga yadda kazama kuwa?"
Bassam da idonsa na wurin  Afnan ko Allah zaisa ya ganta tafito."
Bai kalli Yasir ba yace "haba dai ina wani can zawa a haka muna cikin Nigeria."
Yasir yayi dariya yace " eh mana sai kace kalar halfcase kalar fatar ka."
Bassam ya kauda maganar saboda bayason yawan surutu a wannan lokacin, yace "tun yaushe ka shigo garin?"
Yasir yace "tun shekaran jiya."
Bassam yace "OK ya iyalinka?"
Yasir yace "suna nan lafiya k'alau yana ka  iyalin?"
Murmushi Bassam yayi ya fad'a a tak'aice yace "kowa lafiya k'alau."
Adai dai lokacin da ya hango Afnan a guje tana wak'a tana karkad'a k'ugu tana kuma shan mangwaro, 
   Wani sanyi yajiya a ransa tare da sauke ajiyar zuciya, yana murmushi wadda bai San yana yinsa ba, yana kallon wurin."
Sadi d'an daudu Wanda a yanzun shike dafa masa abinci,
   Ya iso yana rangwad'a kamar wata mace,
d'auke da tiren  abinci zai kawowa Yasir."
D'abi'oin da sadi yakeyi da maganar da yakeyi kamar mace shi yake bawa Yarima dariya, duk lokacin da yakawo masa abinci sai ya zaunar dashi a kusa gareshi yana tsokanar sa domin yayi dariya."
Sadi na ajiye tiren abincin a gaban Bassam yace "ranka ya dad'e ga abincin."
Bassam ko kallon Sadi baiyiba hankalinsa na wurin Afnan yace "Ajiye nan kayi tafiyarka."
Sadi ya ajiye yayi tafiyar sa cike da mamaki yau Yarima ko kallon sa baiyi ba, bare ya tsokane shi."
Yasir ya kalleshi yace "Yarima wani d'an daudu aka samu a gidan nan kuma?"
Yarima bai kalle shi ba saima murmushi da yaga yanayi a fuskarsa har da 'yar dariyarsa."
Yasir yakai idonsa a inda yaga Yarima na kallo yana murmushi."
Afnan ce ya hango tana yiwa doki wanka, sauran kuma dabbobi duk sun zagayeta, tana masu wak'a tana 'yar rawar ta mai d'aukar hankali."
Yasir ya k'ura mata ido yana kallonta , kyawon ta da yanayin ta ya matuk'ar burgeshi bai San lokacin da yace "wow beautifull girl."
     Yarima yarinyar can ta matuk'ar murgeni, naji inasonta a shirye nake zan aureta, banda mu da kasan cewarta a matsayin baiwa ba."
Wani razanen nen kallo Bassam ya wurga wa Yasir had'ida wata kalar harara,🙄 baiyi masa magana ba, shi kuma yasir bai San yanayiba, gaba d'aya  hankalishi ya tafi wurin kallon Afnan."
A dai dai lokacin da tayi wani irin juyi tana rawa, d'an kwalin kwanta yacire gashin kanta yazubo har gadon bayanta wani kuma ya rufe mata fuska."
Da sauri Yasir ya mik'e tsaye, baiko kalli Yarima ba, yace "Yarima bari natafi tun yanzun na gabatar da kai na tunkafin lokaci ya k'ore."
Yana k'ok'arin tafiya Yarima ya rik'o rigarshi ta baya, idon shi ya rik'id'e zuwa launin ja, cike da b'acin rai yace "karka kuskura kaje wlh mudun kayi kuskuren zuwa wurinta saina sanya fadawa sunyi maka bulala dubu." Sannan ya saki rigarsa."
Yasir ya kalleshi ido cikin ido yace "a kan me?" Dawani dalili zaka hanani zuwa wurinta bayan baiwa ce, kuma na ganta naji ina sonta, kuma aurenta zanyi, to ko kashe ni zakayi sai na isar da soyayya gare ta."
Ya rab'a Yarima  ya wuce zai nufi wurin Afnan,
Saiji yayi Bassam na kiran "Sarkin hukunci, Sarkin gishiri, sarkin kisa."
Da gudu suka zo suka durkusa gaban Bassam kowane sai zarar ido yakeyi fuskarsa babu imani."
Bassam ya kallesu cikin *K'unar Zuci* yanuna masu Yasir da yaja yayi tsaye wuri guda yakasa tafiya,
Yace mudun wancan ya kuma taka sahu biyu da sunan tafiya ni ninace Ku kamashi Ku kaishi gidan hukunci kuyi masa horo horo mai tsanani."
Yasir ya dawo baya yafasa tafiyar yana kallon yarima da yaga nan take ya canza kama kamar wani zaki, yasan halin Bassam sarai komai yana iya sanyawa ayi maka kuma babu Wanda ya isa ya rama ma."
Yasir ya rab'a Yarima yafita yayi hanyar waje."
Yarima yayi wa fadawa nuni da hannu a kan suyi tafiyarsu, sannan shima yanufi hanyar sashinsa da sak'esak'e a ransa."
[3/5, 4:54 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
         *40*
*Saratu* ta rasa gane kan mijinta kwata kwata ya juya mata baya."
Baya son kusantarta, yanzun gata kuma mai yawan buk'ata."
Har gara da yana zuwa ya d'an kwada kusantarta, yanzun kam abun ya lalace ko k'eyarshi bata gani, kuma ya hanata zuwa sashen sa, yace ta d'an dakata da zuwa turaka zai nemeta."
Shima Bassam ya rasa dalilin da yasa idan yana tare da Saratu baya jin gamsuwa da ita a ayanzun kuma bayajin dad'in ta kwata kwata  sai yaji kamar ya shiga ruwa, Sam baya gamsuwa a kwanciyarsu shima mamaki yakeyi yaushe ta zama haka bai sani ba?"
Tunanin yanda zai fara gaya mata halin da take ciki yakeyi
Mmki ykeyi ssai, koma abun daga gareshi ne shi baisani ba."
A Yau kam  ya shirya yana buk'atar matar shi, domin a tunanin sa shi ke da matsalar ba saratu ba, tunda ai ba hakan yasame taba tun farko,
       Shi dai yasani yana gamsuwa da ita, yanzun ne dai yafara jinta kamar ba komai ya shiga ba
, tamkar ya fad'a kwata ga wani irin wari dake fita a tsaka ninsu." Bai San ta inda zai fara gaya mataba, bayason ta gano yana cikin wani haline game da kwanciyarsu."
A yau kam ta b'aci yana kanta ya dawo gefe d'aya ya kwanta, yashiga tunanin mai yasa yakejin hakan ne?"
Shi dai yasan lafiya k'alau yake, ko dai ita ce bata da lafiya ne?"
Ya juya ya kalleta kuka takeyi, ya rik'o hannunta suka zauna suna fuskantar junansu, yashiga lallashinta,
Yace "ki daina kuka Saratu abunda ya shafeki nima ya shafeni."
Ta kuma fashewa da kuka tace " Rabuwa zakayi dani ranka ya dad'e? Bana son rabuwa da kai."
Yarima yace "ki yi shuru bazan rabu da keba, zamu nemi maganani tare domin muyi maganin matsalar."
Kintabbata baki sha magani da zai ja maki wannan matsalar ba?"
Kinsan fa Ku mata kuna shaye shaye magunguna Dan Ku samu ni'imar da zata gamsar da mazajenku."
Da sauri ta d'aga kai tace "eh munayi Allah munayi."
Murmushi yayi yace "kada kisha abunda zai b'ataki Dan yanzun kin samu matsala mai makon  in gamsu dake sai dai injiki salaf."
Ta matso ta rungume shi, warin dake fita a jikinta ya daki hancinsa, yayi saurin m'ik'ewa tsaye yana cewa "bari muyi wanka sai muyi maganar Saratu bazan rabu dakeba."
A ransa kuwa, ransa a b'ace yake yana cewa a zuciyarsa waya gaya maki ina  iya hak'iri da macce a wannan lokacin dana kejin k'arfi kamar doki, ga kuma maganin tsari da lafiya da nake sha, yanzun ma nake cikin ganiyar sha'awar macce." Ya fad'a toilet
Wanka yayi ya fito ya tarar da ita a zaune sai kuka takeyi saboda matsananciyar sha'awa dake damunta, Yarima ya fara lasa mata zuma a baki kuma ya kyaleta."
Lallashinta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali shiyasa tamu damar da barci ya d'auketa." 
Ya tsura  mata ido yana  kallon  fuskarta, yace
     "kai gaskiya Saratu a kwai muni na bak'in kare."
Shi dai yasan yana zaune da itane, saboda yasan bazata tab'a zama mai bak'in haliba irin na kyakyawan mata ba,
   Yana ganin muninta zai hanata mugunta da jin kai, domin ya lura masu kyau akwaisu da jin kai." Me suke tak'ama dashi kyansu?"
Shi dai kyan 'ya mace a wurinshi shine k'irjinta da d'uwawu sai kuma tsawo,
   Tsawon ma d'in ba dole bane, ko guntuwa CE yana sonta in dai a kwai wannan qualities d'in."
Sannan kuma yana son mace mai laushin fata, mai laushin jiki,
   Saratu kan jikinta k'irk'ir kamar na maza,
Sannan kuma hannuta nada girma, k'afafunta ma haka sunada girma sai kace nasa.
Yana ganin ma tafishi girman k'afa, gasu sambal kamar guduma."
Komai girman k'afar da hannun macce kada ta wuce ta namijin da zata aura."
Kuma tasamu man hulba ta rik'a shafawa yana maganin fata, idan tana sha a cikin jikinta zata kuma samun lafiya."
Dogon tsaki yaja ya kawar da kansa domin shima yashiga cikin yanayin buk'atar mace."
Afnan ta had'o masa a rai a yanda ya ganta d'azun tana juya k'ugunta tana rawa."
Kai yarinyar ta kai yarinya halitta kamar ita ta halicci kanta, k'irjinta a cike yake fam,
  Sannan ga diri irin wanda kowane namiji yana iya wasoso a kanta."
Tuna wa yayi da yanda yaga Yasir na kallonta, yaji anan take ransa ya b'aci, ya fad'i a fili yace "dole ne nasanya ayi mashi katanga da shigowa gidan nan."
Mirginawa yayi daga kwanciyar da yake, domin jinsa yake baya iya barci saboda a buk'ace yake,
  Wata zuciyar tace kaje kanemi yariyar can mana ai matar kace."
     "Ina "ina ai saita rainani, kuma saita gane kurenta."
    A haka dai har barci b'arawo yayi awon gaba dashi."
Ko da saratu ta farka daga barci taga babu Yarima babu alamarshi."
Hankalinta yayi matuk'ar tashi ta kasa hak'uri tanufi sashin hajiya zainab,
  Ta shiga fad'a mata abunda ke faruwa."
Dariya hajiya zainab tayi irin wannan tasa mun nasara,  tace "ai Yarima sai ya gane kurensa bai San ni bace."
Sannan ta d'auko wani k'ullin magani ta mik'awa saratu, tana gaya mata yadda zatayi amfani dashi, sai nanata mata takeyi."
Tana ce mata "kikula da kanki da kyau Dan yarina akwai shi akwai son mata."
Saratu tace "haba?"
Hajiya zainab tace "kwarai kuwa aishi yasa nakeson ki mallake shi, tashi kije kisha kamin yashigo gurinki."
Saratu tafita tana godiya, hajiya zainab ta ci gaba da dariyarta da tafara yi d'azun, tace "sakarya mahaifarki ta lalace babuke babu yin  ciki a gidan nan."
_____________________________
Afnan yau ta ari rediyon sadi d'an daudu,
 da yake suna shiri sosai ahaka zasu zauna suyita hira sai kace k'awaye, Sadi yasha gaya mata tana da kyau."
Har shi yake koya mata wasu aikin girki a kicin d'in, sai kuma abinci mai kyau da take samu tana ci daga wurinshi."
Yawanci duk abunda Yarima keci shi itama take ci, shiyasa take k'ara yin kyau."
Doki take yiwa wanka ta kunna rediyo, tasanya wak'ar Umar m Sharif, sai ta b'uge da yin rawa."
A hankali take yin rawar, dai dai da kid'an,
   Yarima na gefe yana kallonta rawar yau tafi ta kullum burgeshi jiyayi kamar yaje ya rungumeta ya stotse d'an k'aramin bakinsa yakeji."
"Sai cewa yakeyi kai wannan yarinyar ta iya komai na rud'a namiji, shi kanshi ya yaba da rawar yau, tun yana kauda ido har yakai yakasa zama ya jingina da bangon dake gurin, yaci gaba da kallonta."
Can sai yaga sadi shima yashiga ya jera da ita, yana rankwad'a kamar macce shima yana rawa, suna dariya suna rausayawa a tare."
Haushi ya kamashi ta yanda sadi yake jerawa da ita yana rawa, itama ko a jikinta rawarsu sukeyi suna dariya."
Tunawa yayi da malam Nura a yanda yake ganin su a tare a koda yaushe sun jera suna tafiya suna firar masoya."
Wani Abu yaji yana taso masa Wanda baisan ko meyeba, yashiga fad'i a zuciyar shi, 
"dama tasaba yawo da maza, tasaba ma'amalarta da maza tun a gidansu, yaja wani dogon tsaki cike da jin haushi ya bar wurin."
Kai tsaye fada ya nufa wurin maimartaba, 
Suka fara fira Bassam yace "ranka ya dad'e "inaso ka gaya min likita macce Wanda ka yarda da ita."
Maimartaba yace "matarka nada ciki ne?
Bassam yace "bansaniba ranka ya dad"e."
Sarki yace "kana nufin har yanzun bata da ciki, to mekake jira?"
[3/5, 4:54 PM] Ummu Safwan WS P1: 👑 *TAMBARIN SARAUTA*🤴
👑.             🤴         👑
             *NA*
     *UMMU SAFWAN*
    ( Farida Bashir)
         *41*
Bassam ya sunkuyar da kansa k'asa yace "shi nakeso a duba mata ranka ya dade."
Sarki yace "OK ba damuwa akwai likita macce Dana sani ta iya aikinta sosai zan turo maka ita gobe da safe  sai ta dubata."
Da safe likita tashigo ta shiga duba saratu,
Dr tace lafiya lau take babu abunda ke damunta, yarima yashiga mamaki sosai."
A daren yace bari ya gwada ya gani ko tamu lafiya, amma sai a hankali Dan abun yafi lalace wa, warin ya k'aru har yafi nada, 
    Sauka yayi a kanta ya shiga tunanin ko an samata hannu ne a gidan nan?"
Ya juyo ya kalleta yace "kin tabbata babu Wanda yatab'a wani  Abu kikaci ko kika sha?"
      
Ta girgiza kai tace "A'a babu."
Bassam yace "ikon Allah kina cikin babban lalura Saratu sai antashi tsaye an nema maki magani."
      Ya tashi tsam yafita ya barta a nan kwance tana kuka."
_____________________________
Afnan ce d'auke da tray na kayan abinci,
   Wanda Sadi ya kwaso wurin Yarima, hakan Sadi yake mata duk abincin da Yarima yaci ya rage, da zarar ya kwaso kayan to ita yake kawomawa, wani lokacin kuma tun kafin ya kai masa yake d'ebo mata, dan haka kullum sai k'ara cika takeyi tana kuma yin kyau."
 
tafiya takeyi zata nufi wurin abokanenta  dabbobi, sam bata san Bassam yazo wurin ba,
    Karo sukayi gaba d'aya Abincin ya zube masa a jikinsa."
Zaro ido yayi yana kallonta, cike da tashin hankali,da takaici duk ya rufeshi, ga shi fararen kaya ne ya saka, duk sunyi manja."
Kallonta yayi cikin masifa yace 
"KE!! 
    ina wasa dake?"
Tsaye tayi ta sunkuyar da kanta  k'asa cike da tashin hankali, taka sa furta kalma d'aya, jiran hukunci kawai takeyi."
Saratu ta iso wurin tana fad'in "Ashe kana nan ranka ya dad'e?"
Naje sashinka aka cemin kana nan wurin doki."
Bai kalli Saratu ba, Afnan yake kallo data sunkuyar da kanta k'asa, sai zazzaga masifa yakeyi."
Tunawa yayi da yanda yake ganinta da Sadi, suna ma'amala kamar macce 'yar uwanta,
    Da kuma yanda yake ganinta da malam Nura sunjera suna tafiya suna fira, 
   Wani Abu yaji ya taso masa A cikin zuciyarsa
, bai san lokacin da yanuna ta da d'an yatsa yace " 👉🏻 ke karuwa kishiga hankalinki bazan d'auki iskanci daga garekiba, dibi yanda kika b'ata min jiki da Abinci, ko kin d'auka nima ina d'aya daga cikin 'yan iskan samarinki?"
Afnan ta waro idanunta cike da hawaye  ta kalleshi ido cikin ido tace " *NI BA KARUWA BACE*!!
     kuma duk Wanda ya kuma kirana da karuwa bazan tab'a yafe masa ba, sai Allah yayi mana hisabi a ranar gobe k'iyama."
Ya saki dariyar jin haushin kalamanta a gaban fadawansa, yace "ke karuwa ce."
Saratu tace eh ke karuwa ce, had'ida galla mata harara."
Saratu bata rufe bakinta ba, Afnan ta d'aga hannu  ta kwad'a mata lafiyayyen marinta har biyu, a kuncinta."
Idanunta yana zubar da hawaye, tace "idan ina magana da shugabanki Wanda ya ajiyeki, kidaina sanya min k'aton bakinki,
      Sannan ni ba karuwa bace sai dai inkece karuwa."
Saratu ta kalleta cike da mamaki da kuma tashin hankali. Tayi kukan kura zatayi cikinta ta doketa."
, Bassam ya  doka mata tsawa da k'arfi Wanda bata San yana da wannan muryarba yace "karki kuskura ki daketa."
Ta zaro ido waje cike da mamaki, batayi magana ba."
Bassam yace "ina ruwanki da ita?"
    Me yasanya bakinki a ciki?"
    Wato ina magana kinayi?"
     Ina zartar da hukunci ga bayina kina sanya Baki?"
    Meya kawoki nan?"
    Waye ya fad'a maki nazo nan?"
Da sauri ta zube k'asa tana bashi hak'uri, 
  Kuyangu sukayi tsaitsaye suna kallo."
Ganin haka bai kuma yin magana ba, yajuya yayi tafiyarsa."
 
Sashinsa yanufa Saratu na biye dashi, yana juyo
Wa, sukayi ido biyu dashi, ya tsaida ta, yace "koma sashinki ina buk'atar inzama ni kad'ai."
A san yaye ta juya ta  tafi, tasan hakan sai ya faru." Wai mai yake shirin faruwa da ita ne?" Meke shirin samunta, da har Yarima ya fara fifita baiwa a kanta?"
Ya dace taje taga Anna ko ba komai gari d'aya suka fito, kwad'ayine yasa ta sai da kanta gidan sarki"
Da jummai kakarta ta rasu, ita da kanta tazo tace tanason tayi aiki a gidan."
Hajiya zainab na ganinta tagane ita jinin jummai ce,
    Da jummai da Anna sune suka rik'e Bassam saboda Allah, suka shiga k'ok'arin tsiratar dashi daga shairin hajiya zainab."
Tun daga lokaci Hajiya zainab ta mayar da Saratu mai wanke mata k'afa da gyara mata farce, sai gashi ta zama matar Yarima abunda bata zataba."
Bassam sai safa da marwa yakeyi, shi kad'ai a d'aki, 
   Domin bai tab'a jin tausayin Afnan ba sai a yau,
   Hawaye ya gani kwance a fuskarta, ji yayi kamar yaje ya rungumeta ya lashe mata su."
Shima yasan kalmar da ya furta mata ta karuwa, tayi mata nauyi a kai, to amma shi bai san lokacin da ya furta kalmar ba, baisan lokacin da Kalmar ta fito a bakinsa ba."
Yashiga tunanin yanzun ko a wani hali take?"
Wata zuciyar tace "ai kaima tayi maka rashin kunya a gaban kuyanginka, har da Allah ya isa tayi maka."
    Kuma ta k'arya taka a gaban kuyangunka."
Wani zafi yaji yaji a k'irjinsa, yana fad'i a fili, wato ni zata karyata a gaban mutane,
   Lallai yarinyar can ta d'auko ruwan Dafa kanta zai nuna mata shiba mak'aryaci bane, ita har ta isa yayi mata k'arya akan menene?" Ita wacece ma da za'ayi mata k'arya."
Daren ranar har









