Showing 33001 words to 36000 words out of 113443 words
alwala bayan ya gama ya miƙe riƙe da butar a hannunsa ya ƙarasa gabanta ya ajiye kana ya juya yana warware hannun rigarsa daya nannaɗe gurin alwala yana faɗin "Ni zanje masallaci sai na dawo..." Yana gama faɗin haka yasa kai ya fice yana kallonta tana aikin curin ƙuli ƙulinta ko ɗagowa ba tayi ba ballantana ya saka ran zata amsa masa, kawai ya kaɗa kai ya fice abunsa.
Fadwa kuwa haka tai ta tafiya a ƙasa kasancewar tafiyar akwai ƴar tazara sosai tsakanin gidansu da bakin titin unguwarsu, gashi rana ta ƙwallare zufa sai tsattsafo mata take, a haka har ta kai bakin titi sannan ta samu keke napep ta hau ta gaya masa ya kaita unguwarsu Hayin Rigasa dan bata jin zata iya zuwa Gwamna Road gidan Hajiya Labiba kamar yadda ta ƙudurta a ranta, dan yadda ta kwashi ranan nan gaba ɗaya duk ta haɗa uwar zufa fuskarta tayi jajir zaifi idan ta koma gida ta sake sabon wanka da sabon shiri kafin ta tafi gidan.
Koda ta isa gidan sai da tayi wanka kana ta gabatar da sallar Azahar sannan ta shirya ta cancaɗa kwalliyarta dai dai gwargwado kamar yadda ta saba, kana ta zura haɗaɗɗiyar baƙar abayarta wacce ta karɓi jikinta sosai ta sake fito da hasken farar fatarta.
Sai data feshe ilahirin jikinta da Arabian Oud ɗinta masu daɗin ƙamshi kana ta ɗauki mayafin rigar tayi rolling ɗinsa a kanta ya fito da farar fuskarta sosai sai tayi kamar wata balarabiyar ƙasar Oman.
A gurguje ta ɗauki wata baƙar jakar handbag ɗinta mai kyau ta zira wayarta a ciki kana ta sagala a tsintsiyar hannunta ta fice daga ɗakin, haka ta fito tsakar gidan tana wani irin yauƙi da taku ɗai ɗai ta jawo ƙofar ɗakin ta saka kwaɗo ta rufe babu ko ɗar a ranta tasa kai ta fice daga gidan kamar wata tauraruwa.
**********
A ɓangaren Ya Azeez kuwa lokacin da ya fito daga gida direct cikin gari ya nufa da keke napep ɗinsa dan can yafi shiga da rana yayi sana'arsa hankalinsa kwance, amma yau sai ya kasance kwata kwata bashi da natsuwar zuciya da sukuni komai baya masa daɗi, zuciyarsa gaba ɗaya a cunkushe take sosai da baƙin cikin Fadwa da ɓacin ran da take ta ƙunsawa zuciyarsa, kwata kwata ya rasa me ke masa daɗi shi kam ya sani bai yi dacen matar aure ta ƙwarai ba. Amma koda wasa bai taɓa tunanin cewa al'amarin Fadwa har ya kai ƙwarin haka ba gaba ɗaya kansa ya gama ɗaurewa da mamakinta, gashi idanunsa da zuciyarsa sun kasa goge hoton tsadaddiyar wayar da ya gani a hannunta tana amfani da ita, babbar damuwarsa yanzu kawai itace a ina take samun kuɗin da har ta siyi wannan wayar dan ya sani kaf cikin danginsu babu wanda yake da kuɗin da zai iya cirewa a yanzu ya bata ta siyi wannan tsadaddiyar wayar, kowa ta kansa yake yi, ba kamar da da suka fi karfin komai ba yanzu komai ne yafi ƙarfin su.
A haka ya kusan wuni a cikin gari yana ta faman gararanba cikin takaici da ƙunar zuciya har lokacin sallar azahar ya wuce bai sani ba gashi ya kasa tsinanawa kansa komai tunda ya fito dan ko tsayar dashi mutane sukayi a bakin hanya baya iya tsayawa sai dai kawai ya wuce yace ba tafiya ba ne, haka har la'asar tayi bai sani ba sai da yazo wucewa ta Abakwa dai-dai bakin wani masallaci ya ga mutane suna ɗaura alwala nan ya tsaya ya faka keke napep ɗinsa a gefen masallacin, ya fito da sauri bayan ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe 3:50pm dai-dai. Sosai yaji baƙin cikin subuce masan da sallar azahar tayi da bai samu yin ta akan lokaci ba ya tokare masa zuciya, cikin sanyin jiki ya ɗauki buta yaje ya tari ruwa a famfon dake gurin ya ɗaura alwala kana ya shiga cikin masallacin.
Ya daɗe zaune a cikin masallacin bayan ya idar da sallolin, amma ya kasa tashi ya tafi yana kallo mutane suka dinga fita ɗaya bayan ɗaya amma shi ko motsi ya kasa yi, sai ma matsawa da yayi ya jingina da jikin bango ya lumshe idonsa yana ci gaba da tasbihi a zuciyarsa. Haka kowa ya gama ficewa aka barsa tsuru shi kaɗai ƙwal a zaune.
Yana nan zaune a cikin masallacin har gurin ƙarfe 5:40pm. Sannan ya tashi ya fito ya shiga kekensa ya zauna yana tunanin inda kuma ya kamata ya nufa.
*******
Fadwa kuwa lokacin data isa gidan Hajiya Labiba ta iske bata nan sai mai aikinta kaɗai dake ta aikace aikacen haɗa abincin rana a kichin, ita ke sanar mata cewa Hajiya Labiban bata nan taje gidan Hajiya Lubna amma ba zata daɗe ba yanzu zata dawo.
Ɗan sauke numfashi Fadwa tayi kafin tace "Ita tace miki bazata daɗe ɗin ba zata dawo, ko kuma wani iyayin ne da tsarinki kawai yasa kika faɗa...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta.
Saurin kaɗa kai tayi tana faɗin "Eh itace da kanta ta gaya min tace bazata daɗe ba saƙo kawai zata kai mata ta dawo, shiyasa kikaji nace yanzu zata dawo..."
Fadwa bata sake magana ba ta juya ta shiga cikin falo ta samu waje ta zauna akan kujera ta ajiye jakarta lokaci ɗaya ta kashingiɗa tana faɗin "Bari in jirata har ta dawo ɗin..." Ta faɗa a hankali tana lumshe idanunta.
Ita dai Rabi bata ƙara magana ba ta wuce ta koma kichin ta ci gaba da aikin girkinta.
**********
A natse ya ɗaga labulen buhun da ya kasance shine a matsayin ƙofar gidan ya shiga ciki bakinsa ɗauke da sallama, wata kyakkyawar dattijuwa ce fara sol sol da shekarunta a ƙalla zasu iya kaiwa hamsin da biyu zaune a ɗan madaidaicin filin tsakar gidan nasu wanda ya kasance ginin jar ƙasa ne mai kyau irin na da, sai dai duk ya gama jin jiki gefe gefen katangar duk ya zaizaye wani gurin ƙasan ma duk ta rufta sai buhu da aka kewaye wani gefe gurin yay kamar katanga gashi an share ko'ina har ɗan filin tsakar gidan nasu da yake ƙarami yay fes fes gwanin ban sha'awa.
Ita kaɗai ce zaune a tsakar gidan da faranti a gabanta tana tankaɗen garin tuwo, tana jin muryarsa ta ɗago kai fuskarta ɗauke da fara'a take faɗin "Masha Allah maraba da ɗan albarka...yanzu kake tafe da yammacin nan...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana ajiye rariyar hannunta ta miƙewa da sauri ta shiga cikin ɗaki ta ɗauko mai tabarma ta fito har lokacin fuskarta ɗauke da farin ciki tazo ta shimfiɗa masa a kusa da inda take tankaɗen kana ta wuce gurin randa tana faɗin "Zauna ina zuwa bari in kawo maka ruwa..." Ta faɗa cikin dattako tana ɗaukar kofin silba a kwando taje ta ciko masa shi da ruwan randa mai sanyi ta kawo ta ajiye a gabansa kana ta koma ta zauna ta ci gaba da tankaɗenta tana kallonsa.
Sauke numfashi Ya Azeez yayi a hankali kafin ya ɗan ɗago kai ya kalleta, sai ya ga ta kafesa da idanuwanta ƙirr bai ce komai ba ya ɗauki ruwan data ajiye masa ya kafa kai, bai sauke ba sai da ya shanye tas kana ya sauke kofin ya ajiye lokaci ɗaya yana sauke numfashi kafin yace "Na gode Ummana Allah ya biyaki da mafificin gidan aljanna fiddausi..." Ya faɗa cike da tsantsar jin daɗi lokaci ɗaya yana gyara zamansa, tare da ɗan waigawa ya leƙa ɗakin dake kusa dashi yana faɗin "Wai ina Imaan ne taje data barki ke kaɗai a gidan kike yin aikin da kanki...?"
Murmushin daya ƙara fito da tsantsar haiba da kwarjininta ta saki kafin tace "Tana nan maƙota gidan Malam Sabo na aiketa siyan kayan miya yanzun nan zaka ganta ta dawo..." Ta faɗa tare da ɗan tsura masa idanu cike da nazari da son gano yanayinsa da yake ciki.
Kaɗa kai kawai yayi a hankali ba tare daya ce mata komai ba, ya juya ya ci gaba da kallon wani guri can daban.
Fahimtar da tayi kamar yana da damuwa ne a ransa yasa ta ajiye rariyar tankaɗen ta miƙe daga inda take ta dawo kusa dashi kan tabarman ta zauna tana fuskantarsa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi da sauri cikin ƙoƙarin danne abinda yake ji a ransa yana taso masa yace "Ummana har kin gama tankaɗen..ko kin gaji ne in ƙarasa miki...?"
Girgiza masa kai kawai tayi tana faɗin "Kayi haƙuri kaji..nasan akwai abinda yake damunka amma bana buƙatar ka gaya min, ka gayawa Allah ko mene ne sannan ka bar masa ikonsa, kuma duk abinda yake damunka kayi ƙoƙari ka danne ka jure ka barwa zuciyarka daga Allah sai kai karka sake duniya ta hango gazawarka har ta saka ido a kanka, ka zamo jarumi akoda yaushe kuma a kowanne irin hali karka sare, komai yayi tsanani maganinsa Allah..kuma komai yana da farko haka yana da ƙarshe wata rana sai labari..."
Take faɗa cikin taushin murya da nuna tsantsar kulawa da tawakali. A hankali Ya Azeez ya ɗago ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa yake faɗin "Umma ina cikin tsananin damuwa komai bai min daɗi, Fadwa ta hana zuciyata sakat bani da natsuwa da sukuni ballantana in samu kwanciyar hankali..gaba ɗaya a tsorace nake bana so Allah ya kamani da hakkin Fadwa Ummana na rasa inda zan saka kaina da rayuwata inji daɗi..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana share ƙwallar data soma zubo masa.
Wani irin sanyi Umma taji lokaci ɗaya jikinta ya ɗauka, a hankali ta juyo ta kallesa kafin ta ɗan saki murmushin yaƙe tana faɗin "Insha Allahu Allah ba zai taɓa kamaka da laifin komai ba a kanta, kayi haƙuri ka ci gaba da yi mata nasiha kuma ka dage da addu'a, duk abinda yafi zama alkhairi tsakanin kai da ita Allah ya zaɓa muku. Amma ban so kake nuna damuwa akan duk abinda zata yi maka ko kaji haushinta, saboda kar ka manta Fadwa dai jininka ce ƙanwarka ce kuma har yanzu akwai yarinya a tattare da ita, dan haka ka dinga haƙuri da ita wata rana da kanta zata gyara kaji...?"
Sosai Ya Azeez ya ƙara haɗe fuskarsa yana faɗin "Umma wace irin yarinta kuma, yanzu kamar Fadwan ce za'a ce akwai yarinta a tattare da ita har yanzu tana ƴar shekaru talatin da wani abu a duniya...?"
Kallonsa kawai Umma ke yi tana ɗan murmusawa kafin tace "Eh mana a kanka ai ita yarinya ce ko...?"
Bai ce mata komai ba dan tsabar takaici, ya ɗauke kansa lokaci ɗaya yana ƙara jinjina kalaman Umman tasa akan Fadwa wai akwai yarinta a tattare da ita, sai kace wata ƴar jaririya. Fadwan ce take da yarinta..? Lallai kuwa Umma har yau har gobe ba tasan wacece Fadwa ba ganinta kawai take amma bata san ita ɗin wacece ba.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
1️⃣4️⃣
Umma kuwa a zuciyarta tana sane ta gaya masa hakan, saboda tasan dalilin abinda da yasa yake ta wannan kumburin yana ƙara jin haushin Fadwan a ransa, ba zai wuce ƙin amsar waya da batayi bane jiya ta gaisheta, ita kuma ko kaɗan hakan bai dameta ba, domin indai Fadwa ce tasanta farin sani ita da uwarta dama ba wani shiri sosai sukeyi da ita ba saboda yanayinsu kwata kwata ba ɗaya ba ne da nata, rashin kunyar Fadwa kuma ta daɗe da saninta iri iri tunda ko jiyan ma duk maganganun data gaggaya masa a kanta tana jiyota ta cikin wayar duk taji komai amma ko a jikinta hakan bai dameta ba.
Umma ta ƙara gyara zama sosai tana fuskantarsa tace "Nidai ina ƙara tunasar da kai muhimmancin haƙuri a rayuwa AbdulAzeez, kuma ina roƙonka akan kome Fadwa zatayi ka kasance mai yi mata uzuri a matsayinta na ƙanwarka, sannan ka dinga nusar da ita akoda yaushe kana yi mata nasiha a matsayinta na ƴar uwarka kuma matarka, ka daina ɗaukar zafi da ita har kayi fushi kaji..."
Ƙara sunkuyar da kai yayi a hankali yana faɗin "Insha Allahu Umma..."
Suna cikin haka wata matashiyar budurwa wacce a ƙalla shekarunta ba zasu wuce sha tara ba ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama tana riƙe da ledar kayan miya a hannunta, tana ganinsa kuwa ta washe baki cike da fara'a tana faɗin "Laaah Ya Azeez kaine..yaushe kazo...?"
Take faɗa tana ƙarasowa gabansa ta duƙa ta ajiye ledar dake hannunta kana tace "Sannu da zuwa Ya Azeez, ya Aunty Fadwa ya aiki...?" Ta faɗa tana sakin murmushi wanda kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsar kamanninsu sosai da Ya Azeez ɗin, tun daga kan dogon hancinsu zuwa ɗan madaidaicin ƙaramin bakinsu, da kalar fatarsu duk iri ɗaya sai dai da yake ita ɗin mace ce sai ta ɗan fishi hasken fata kaɗan, amma hatta da yanayin yatsun hannayenta dana ƙafarta duk irin nasa ne.
Ɗago kai yayi yana kallonta da murmushi akan fuskarsa yace "Alhamdulillahi Aunty Imaan sarkin surutu, ya makaranta..ana dai maida hankali gurin karatun ba'a wasa ko...?"
Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Eh ina yi sosai Ya Azeez, jiya ma muka kammala zana jarabawar Ssce ɗin mu..."
Cikin farin ciki Ya Azeez ya dafa kanta yana faɗin "Masha Allah lallai autar Umma an kusan zama ƴan matan jami'a kenan..ko kuma aure zakiyi idan kin kammala secondary school ɗin...?"
Ya faɗa cike da tsokana fuskarsa ɗauke da murmushi.
Imaan a kunyace ta rufe fuskarta tana girgiza kai take faɗin "A'a Ya Azeez nidai karatu zan ci gaba da yi abuna, ko Ummana...?"
Ta faɗa tana duban Umma dake sauraran diramar tasu tana ta murmusawa, jin ba tace komai ba ne yasa Imaan ta shagwaɓe fuska tana faɗin "Kai Umma kice eh mana..."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kwaɓe baki kamar zatayi kuka.
Umma tace "Toh nace eh autar Umma sai ta gama jami'a sannan zatayi aure shikenan...?" Ta faɗa tana kallon Ya Azeez daya kaɗa kai yana ta dariya.
Itama Imaan ɗin dariyar tayi kana ta miƙe ta ɗauki ledar kayan miyan data siyo ta ɗauko roba mai faɗi ta juye a ciki kana ta zuba ruwa ta wanke, ta shiga ɗakinsu ta fito da ƙaramin turmin su na jajjagen kayan miya tazo ta jajjaga ta kwashe ta ajiye.
Umma da Ya Azeez na zaune suna ta hira, har tayi talge ta tuƙa tuwon ta kwashe sannan ta ɗauko tukunya ta ɗora miya.
Tana kammala aikin gaba ɗaya ana kiran sallar magriba, dan haka gaba ɗayansu suka miƙe domin yin alwala Ya Azeez ya fita zuwa masallaci, su kuma suna yin alwalar suka shiga ɗaki dan gabatar da tasu sallar.
Koda ya dawo daga masallacin sai daya zauna ya ci tuwon da ya tarar Umman ta saka masa ya ƙoshi yasha ruwa kana ya wanke hannunsa yayi musu sallama Umma ta tashi ta rakosa har bakin ƙofar gidan tana ta saka masa albarka ya shiga napep ɗinsa ya tada duk tana tsaye, sai da taga wucewarsa kana ta juya ta koma cikin gidan.
**********
A ɓangaren Fadwa kuwa tun ƙarfe 6pm. Suna can Ahmed Musa Garden cikin wani haɗaɗɗen Hall daya sha decorations kiɗa sai tashi yake ga manya manyan jiga jigan mata kota ko ina a zazzaune cikin shiga ta alfarma wannan na wane wannan, ga uban gwala-gwalai a wuya da hannuwansu kamar waɗanda suka zo wajen gasar nuna gwal da auna gram ɗinsu.
Fadwa kuwa itama tasha tata kwalliyar ta kece raini tana sanye da ankonsu na wani Maroon ɗin leshi mai tsada a jikinta wanda akayi mata ɗinkin riga da siket da ya zauna sosai a jikinta ya fito da kyakkyawar surarta, kanta kuwa wani irin ɗaurin zamani akayi mata da head kalar golding aka wani turosa gaban goshinta ya karkace sai aka ɗan jashi baya kaɗan hakan ya bawa baƙin gashin dake kwance luf luf a gaban goshinta damar fitowa.
Zaune tayi abunta ta kame tana ta wani yatsine yatsinen fuska tana kallon mutane ɗai ɗai ita a dole hamshaƙiya, wanda duk abunka idan ka kalli Fadwa kaga yadda tasha gwala gwalan da ƙawarta Hajiya Labiba ta ara mata a wuyanta da hannuwanta itama saika ɗauka cewa matar wani shahararren ɗan siyasan ce ko wani babban ɗan kasuwa dan ko kaɗan ba tayi kama da matar mai jan keke napep ba, gaba ɗaya ta saje dasu ga wani haɗaɗɗen make-up ɗin da akayi mata wanda ya ɓoye bakinta da har lokacin yake a ɗan kumbure bai gama saɓewa ba.
Sai kai kawo take tana ɗaga kai tana wani hura hanci dan jin kanta take yau wata daban, itace gata ga uwar gidan gwamnan jihar Kaduna da kanta da take gani a talabijin da fostoci a cikin gari yau gasu zaune a waje guda teburinta na kallon nata suna kallon juna har ana ta ɗaukarsu Video da hotuna a tare, kanta har wani girma taji ya ƙara.
Sosai idan ta kalleta take ƙara jin wani alfahari da nishaɗi haɗe da tsantsar farin ciki aranta, yau ɗin ta kasance babbar rana ce ta musamman a gareta, ganinta tsamo tsamo cikin taron manyan matan ƴan siyasa da ƴan kasuwa ga gogaggun ƴan boko ya fiye mata komai farin ciki da jin daɗi a rayuwarta, sai wani shisshige musu take tana naniƙe musu dan ita wannan babban ci gaba ne agareta a ganta tare da matan manya.
*******
A ɓangaren Ya Azeez kuwa lokacin da ya baro K/Mashin gidan Ummansa bai biya ko'ina ba direct gidansa ya nufa, yana shiga unguwar tasu kuwa ana kiran sallar isha'i dan haka sai daya tsaya yayi sallah a masallacin dake bakin layinsu kana ya fito ya ƙarasa shagon masu sayar da fura dake kusa da gurin yasa aka damawa Fadwa sannan ya fito ya siyan mata kankana dasu abarba da apple ya biya sannan yaja kekensa ya wuce ya nufi gida.
Yana isa ƙofar gidan nasu ya faka napep ɗinsa a gefe kana ya fito riƙe da leda mai layi layi da makullin napep ɗin a hannunsa, yana ƙarasawa ya iske ƙofar a sakaye yasa hannu ya tura ya ga ta buɗe cike da ƙwarin