Showing 87001 words to 90000 words out of 113443 words
idanunsa daga kanta yana sauke numfashi.
Ita kuwa Zahra sai murmushin jin daɗi take yi wanda ke bayyana tsantsar farin ciki da jin daɗin da take ciki.
Abbie ne ya kallesu yace "Ku saki jikinku sosai dan Allah nan ma gidan ku ne kunji..? Ke Zahra maza zuba musu lemun su sha..." Abbie ya fada cikin kulawa yana duban Zahran.
Da sauri Zahra kuwa ta matsa gabansu ta buɗe robar juice ɗin ta soma zuba musu cikin wasu kyawawan kofunan tangara kana ta ajiyewa kowa agabansa kafin ta ɗago tana murmushi tace "Na gode Allah ashe da rabon zamu ƙara ganinka Ya Abdul, wallahi na ɗauka shikenan baza mu sake haɗuwa ba tunda kana Kaduna mu muna Kano, ashe kai ɗan uwan mu ne ma bamu sani ba..ko Abbie...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallon Abbie dake murmushi yana faɗin "Ɗan uwanku ne mana, dama kun sanshi ne dan naji ɗazu kin ambaci sunansa kai tsaye da alamu kun daɗe da saninsa ma..."
Baki ta washe cike da fara'a tana faɗin "Sosai ma Abbie, ai shine mai keke napep ɗin nan ɗaya taimaka mana a Kaduna, kuma da muka dawo har kukayi waya dashi...?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Abbien.
Wani irin mamaki ne ya lulluɓe Abbie, yayinda Ummi kanta sai da ta kallesa ta dubi yanayin shigar dake jikinsa kafin tace "Allah mai girma ashe kice ma ɗan gida ne shi baku sani ba...?" Ummi ta ƙarashe maganar tana ƙara kallon Ya Azeez da ya duƙar da kai yana murmushi.
Abbie kuwa gaba ɗaya farin ciki ya gama cika masa zuciya, ashe kunnuwansa basuyi masa ƙarya ba ranar daya fara ganinsa a gidan Alhaji Sale Musawa yaji muryarsa yake jin kamar ya taɓa jinta a wani guri, ashe dai da gaske ne ya taɓa jin muryar tasa.
Lallai Allah da iko yake ashe yaron da tunda ya gansa yake jin wani al'amari mai girma a kansa shine ya taɓa taimakon ƴaƴansa wanda har yake burin duk ranar daya haɗu dashi sai yayi masa kyakkyawan alkhairi domin ya nuna masa tsantsar jin daɗinsa akan irin taimakon da ya yiwa ƴaƴansa.
Ɗagowa Abbie yayi cikin tsananin farin ciki da jin daɗi yake kallon Ya Azeez ɗin kafin yace "Naji daɗin ganinka sosai AbdulAzeez, dama ina ta ƙoƙarin son inga na haɗu da kai, ashe ban sani ba ma kai ɗana ne. Lallai kai mutumin arziki ne babu abinda zan ce da kai kuma sai godiya da fatan alkhairi, Allah ya gafartawa mahaifinka yasa kuma ka rabu da mahaifiyarka lafiya..."
Da Ameen duk suka amsa, kana daga haka kuma Abbie ya hau bawa Ummi labarin Alhaji Naseer Arabi mahaifin Ya Azeez, da irin taimakon da yayi musu lokacin da yana raye.
Nan take kuwa Ummi ta shiga kwararo masa addu'a da fatan alkhairi tana faɗin "Ashe ma kai ɗan gida ne, lallai Allah da hikima yake. Aiko mun gode ƙwarai da gaske Allah ya saka maka da alkhairi yasa ka gama lafiya..."
Amsawa sukayi da Ameen dukkansu, kana kuma daga haka Ummi ta miƙe ta koma kichin dan sauke miyar stew ɗin da take yi, wanda kuma dai-dai lokacin aka soma kiraye kirayen magriba a masallatan dake cikin unguwar.
Shatu kuwa tunda ta baro falon take jin zuciyarta na tsananta bugawa, wanda duk taku ɗaya idan tayi sai gabanta ya faɗi.
Hakan ne kuma yasa tana shiga cikin ɗakin kai tsaye ta faɗa saman lafiyayyen gadonsu daya sha shimfiɗa da wani uban sun haɗaɗɗen zanin gado na alfarma, ta kwanta ruf da ciki lokaci ɗaya tana mai dafe saitin zuciyarta da take jin tana ƙara tsananta bugawa tamkar zata faso ƙirjinta da fito waje.
Ta daɗe kwance a tsakiyar gadon tana dafe da saitin zuciyarta wanda har lokacin bai daina bugawar da yake mata ba, yayinda daga gefe guda kuwa ƙwaƙwalwarta ke ta tariyo mata kamannin Ya Azeez da irin tsantsar kyau da kwarjinin da taga ya ƙara, da sauri sauri zuciyarta ta hau bugawa, musamman a yanzu da take ƙara hasaso tsananin kyau da wani annuri da ta hango a saman kyakkyawar fuskarsa.
Haka tai ta tunane tunane haɗe da lissafa siffofin Ya Azeez wanda gaba ɗaya kamanninsa da zatinsa suka kasa gogewa a idanuwanta.
Juyawa tayi wanda kuma dai-dai lokacin ta soma jiyo kiran sallar magriba da akeyi a masallacin dake jikin gidansu, miƙewa tayi a hankali ta wuce toilet dan ɗauro alwala, wanka ta fara yi agurguje sannan ta ɗauro alwala ta fito.
Acan ɓangaren su Ya Azeez kuwa har akayi sallar Isha'i suna tare da Abbie, wanda kusan a tare ma sukaje masallacin sukayi sallar magriba da Isha'in.
Yanzu ɗin ma zaune suke a falon inda Abbie ya matsa musu dole yace sai sunyi dinner kafin su wuce.
Haka nan babu yadda suka iya Ummi ta zubo musu abincin ta kawo musu har nan cikin falon inda suke suka ci tare da Abbien.
Bayan sun gama ne kuma Abbie ya ɗauki wayarsa ya danna numbern Shatu wacce dai-dai lokacin ta idar da sallar isha'i kenan tana zaune a gaban madubi tana shafa mai a jikinta kiran Abbie ya shigo wayarta dake ajiye a gaban madubin.
Da sauri ta ajiye robar man dake hannunta ta ɗauki wayar bayan ta ɗaga kiran ne kuma ta ƙara wayar a kunnenta.
"Ki sauko ku gaisa da baƙi zasu wuce..."
Abinda Abbien ya faɗa mata kenan ba tare kuma daya jira cewarta ba ya katse wayar.
Ba tare data tsaya ƙarasa shafa man ba kuwa ta ajiye wayar ta miƙe da sauri ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinta ta buɗe ta zaro wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar material wanda tasha ɗinkin fited gown mai kyau da tsari, saka rigar tayi a jikinta wacce ba ƙaramin kyau tayi mata ba, gaba ɗaya ta fitar da kyakkyawan dirin jikinta mai kyau da burgewa, wanda kuma haka kawai ta tsinci kanta da son yin kwalliyar da tasan zata burge Ya Azeez ɗin.
Ko ɗan kunne bata tsaya sakawa ba ta ɗauki wani siririn gyale mara nauyi ta yafa akanta, kana ta zura wani flat shoe mai kyau a ƙafarta ta ɗan fesa turare a gurguje ta fice daga ɗakin.
A hankali ta fara saukowa ƙasa tana kallon cikin falon, inda gabaki ɗaya Ya Azeez ya karkata hankali da natsuwarsa kacokan a kanta.
Tsumammun idanunsa ya lumshe a kanta a hankali yana sauke wata irin sassanyan ajiyar zuciya.
Tabbas da kafin yanzu yana jin zuciyarsa na matuƙar tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinsa, sai dai kuma yanzu lokaci ɗaya yaji zuciyar tasa nayi masa wani irin sanyi, yayinda a hankali a hankali yake jin duk wani duhu daya mamaye zuciyarsa yana yayewa ya koma haske.
Ƙarasowarta cikin falon kuwa yayi dai-dai da miƙewar Abbie da Ummi a tare suka wuce falon Abbie ɗin kai tsaye.
Ganin haka ne kuma yasa Shatu zama a kujerar dake kallon wacce Fahad da Ya Azeez ɗin ke zaune akai ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa da zoben azurfan dake maƙale a yatsanta, da sauri Zahra ta kalleta kana ta juya ta kalli Ya Azeez da har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa akanta tace "Kai Masha Allah gaskiya fa kun dace sosai Ya Abdul ina matuƙar tayaku murna..." Ta faɗa kai tsaye tana kallon Shatu data ɗago kai da sauri tana watsa mata harara.
Shiko Ya Azeez Fahad ya kalla tare da nuna masa Shatun da idanunsa, kafin kuma ya juya yana yiwa Zahra alama data ɗan basu guri, aiko da sauri ta miƙe zaraf kamar daman jira take ta buga wani uban tsalle, kafin kuma cikin karaɗi tace "Abu dai ya tabbata da ikon Allah, Ya Abdul ina tayaka murna wallahi, Aunty Shatu kinyi sa'ar miji..." Ta faɗa cike da tsantsar farin ciki tana haurawa sama da gudu.
Dariya Fahad yayi, kafin ya kalli Ya Azeez daya wani tsare Shatu da idanu yayi masa alama daya matsa gurinta mana.
Wanda ita kuwa Shatu gabaki ɗaya kunyar kalaman Zahran sun gama kasheta a zaunen da take, kota ina kunyar su ta gama lulluɓeta ji take kamar ta nutse dan tsabar kunya da takaicin Zahran.
Wai abu dai ya tabbata sai kace yace yana sonta ne, har da wani cewa Aunty Shatu kinyi sa'ar miji. Shegiya kawai cakwaikwaiwa mai baki sai kace reza.
Tana cikin tunanin ne kuma taji daddaɗan ƙamshin turarensa mai tsada ya cika mata hanci, gabanta ne ya yanke ya faɗi ras rass, wanda har sai data dafe saitin zuciyarta, motsin zamansa a kusa da ita ne kuma ya ƙara haddasawa zuciyarta tsananta bugawa, tsam yayi da idanunsa akanta yana ƙare mata kallo, itako ganinsa a kusa da ita ne yasa ta ƙara ruɗewa duk ta daburce bakinta na rawa ta furta "Bar...Bar..ka...da dare..."
Lumshe kyawawan idanunsa yayi sakamakon wani sassanyan daɗi da yaji ya ziyarci zuciyarsa, bai taɓa tunanin anan kusa zai iya riskar irin wannan farin cikin mai daɗi da tsayawa arai ba.
Sassanyan murmushi yayi kafin kuma cikin daddaɗar muryarsa yace "Barkan mu dai Eishatuna..."
Cak ta ɗauke numfashinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta ɗago still dai har yanzu idanunsa tsaye suke ƙyam akanta yana ƙare mata kallo, wani irin zirr zirr taji ƙarar saukar wani sassanyan sauti mai tafe da daddaɗan yanayi ya ziyarceta "Eishatuna..." Haka tai ta maimaita sunan a zuciyarta tana ƙara jin wani irin mugun daɗi a ranta, wanda tunda Ummi ta haifeta bata taɓa jin wanda ya kirata da irin sunan kai tsaye cikin daddaɗan lafazi mai sanyaya rai irin haka ba.
Buɗe idanunta tayi karaf ko suka ƙara haɗa ido, jikinta ne ya fara rawa ta damƙe hannunta lokaci ɗaya tare da runtse idonta, saurin matsawa yayi kusa da ita yana faɗin "Eishatuna pls buɗe idanunki da kyau ki kalleni kinji...?"
Sunkunyar da kai tayi ba tare data buɗe idon ba, kallonta yayi yana tunanin wani abu kafin kai tsaye ya sake cewa "Pls Eishatuna ki ɗago magana zamuyi a matsayin mu na masoyan juna, ba'a matsayin mai keke napep daya taɓa taimaka muku ba..."
Jin haka yasa ta ɗago da sauri tana kallonsa, gyaɗa mata kai yayi alamar tabbatarwa.
Lumshe kyawawan idanunta tayi kafin ta ɗan ƙara matsawa gefe tana kallonsa.
Ya daɗe yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo zuwa ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jajayen laɓɓa masu taushi da santsi, kafin kuma ya sauke idanunsa kan zara zaran yatsun hannunta farare tas tas masu kyau da ɗaukar hankali.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ƙare mata kallon tsaf kafin ya lumshe tsumammun idanunsa ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya mai haɗe da muradi yace "EISHATUNA..."
Amsawa tayi ba tare da ta ɗago kai ta kallesa ba, shi kuwa idanunsa ya buɗe sosai a kanta yana kallonta kafin yace "Sosai na yaba da zaɓin Abba, kuma insha Allahu kema ina fatan ki yaba dani sannan ki karɓe ni hannu bibbiyu a matsayin masoyinki wanda zaki yi rayuwar aure dashi ta har abada. Saboda haka nidai na amince dake a matsayin matar da zan aura, dan da nasan kece ma matar da Abba yace inzo in gani, da ba sai na bawa kaina wahalar zuwa ba kawai zan sanar dashi cewa kin yi min kawai a ɗaura, amma duk da haka yanzun ɗin ma bata ɓaci ba. Insha Allahu ina yiwa kaina kyakkyawan fata na samunki a matsayin matar aurena...."
Jin kalmar daya faɗa ta ƙarshe ne yasa ta ɗago kanta lokaci ɗaya wani kyakkyawan murmushi na shirin suɓuce mata, amma nauyi da kunyarsa sun cika mata ido.
A hankali ta ɗan jinjina kai ba tare da tayi magana ba.
Ɗan murmusawa yayi kafin yace "Meye ra'ayinki...? Dan Allah karki ɓoye min ki gaya min duk abinda ke zuciyarki a game dani..." Ya faɗa cikin nuna alamar shirun nata ya damesa.
Ɗago kanta tayi ta kallesa kafin tace "Nima..." Sai kuma tayi shiru ba tare data ƙarasa ba.
"Kema me...?" Ya faɗa a tsorace yana jin wata mummunar faɗuwar gaba.
Girgiza masa kai tayi a hankali kafin tace "Yanzu dare yayi ka ɗan bani lokaci zamuyi magana insha Allahu..amma yanzu ya kamata ku tafi gida domin abokinka ya baro min ƙawata a gida ita kaɗai...."
Ɗan kwaɓe fuskarsa yayi yana faɗin "A'a Eishatuna ya tafi shi kam ga makullin mota, amma ni ina nan sai mun gama magana..." Ya faɗa kai tsaye yana jefawa Fahad da waya ke manne a kunnensa suna magana da Basma makullin motar yana faɗin "Gashi nan ka tashi ka tafi gurin matarka, nima ka barni da tawa matar zamu yi sirri..."
Kallonsa Fahad yayi a karkace kafin yace "Toh meye na wani korata, kaima ai dole ka taso mu tafi tunda ba'a riga an ɗaura auren ba. Sai ka bari idan an ɗaura an kai maka ita ne sai ka faɗi haka..."
Harararsa Ya Azeez yayi kafin yace "Aiko insha Allahu nan kusa za'a gama komai, sai dai ka mutu munafuki..."
A ɗage Fahad ke kallonsa kafin ya juya ya kalli Shatu data duƙar da kai tunda suka fara ja'injan tana dariyar diramar tasu yace "Ƙawarmu kiyi masa magana ya tashi mu tafi, gobe ya dawo shi kaɗai ku ƙarashe, dan ni kam na bar sake rakosa yau ne na farko kuma na ƙarshe..."
Wani kyakkyawan murmushi Shatu tayi kafin ta kalli Ya Azeez ɗin daya tsareta da ido kamar zai cinyeta, kana kuma cikin lalama tace "Ok Ya Abdul tashi to ku tafi zamuyi waya idan kuka isa gida kaji, pls kuje..."
Ta faɗa cikin taushin murya tana kallonsa.
Saurin kallonta yayi yana jin wani irin farin ciki lokaci ɗaya yana mamaye zuciyarsa, kafin ya miƙe tsaye yana mata wani sassanyan kallo kana cikin kwaɓe fuska yace "Nidai da kin ƙyaleni Eishatuna shi ya wuce, dan ni ban gaji da ganinki ba. Pls ki barni in ɗan ƙara ganinki anjima sai in tafi kinji...?" Ya faɗa yana tsareta da ido.
Hakan yasa ta gano nufinsa kwata kwata baya son tafiyar ne, kawai dai babu yadda ya iya ne saboda ita tai masa magana da kanta, amma da babu inda zaije sai sun gama daddale magana.
Ita kuwa Shatu ganin yaƙi tafiya ne ya tsaya yasa ta miƙe tana ƙara lallaɓasa kafin ya yarda ya juya tabi bayansa wanda kuma tuni Fahad shi har ya fice daga falon dan yaga take taken abokin nasa yau gabaki ɗaya sai a hankali, sai wani rawar ƙafa yake yana wani rawar jiki kamar wanda aka ce an ɗaura masa aure da Shatun ta zamo tasa.
Har wajen da motarsa ke fake ta rakosa inda nan ma da ƙyar Ya Azeez ya barta tayi musu sallama ta juya ta koma cikin gida, yayinda su kuma suka shiga motar wanda a wannan karon Fahad ne ke jan motar suka fice daga cikin gidan.
Sai ƙarfe 10:20pm suka isa gida, wanda koda suka dawo su Abba tuni sun daɗe da rufe sashensu sun kwanta, suma ba su bi ta kansu ba, Ya Azeez ya shige ɓangarensa ya garƙame ƙofa, yayinda Fahad shima ya wuce nasa ɓangaren yana mai jin haushin Ya Azeez kan ɓata masa lokaci da yayi bai dawo gida da wuri gurin amaryarsa ba.
A ɓangaren Ya Azeez kuwa yana shiga bedroom ɗinsa kai tsaye ya wuce toilet bayan ya tuɓe kayan jikinsa ne kuma ya sakarwa kansa shower.
Inda ya ɗauki kusan mintuna sha biyar a cikin toilet ɗin yana wankan, bayan ya gama ne kuma ya ɗauraye jikinsa yayi brush ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa, sai wani ƙarami dake riƙe a hannunsa yana tsane ruwan dake kansa.
Sai daya gama goge jikinsa tsaf kana ya ɗan shafa mai sama sama ya fesa turare, kana ya saka wani tattausan riga da wando na wani yadi mai tsantsi da sheƙi.
Kafin ya ƙarasa gaban haɗaɗɗen gadonsa da yasha shimfiɗa da wani lafiyayyen zanin gado mai kalar ruwan ƙasa ya haye ya kwanta bakinsa ɗauke da addu'a, kana yaja lallausan bargonsa ya lulluɓe jikinsa.
Ɗan juyawa yayi ya ɗauki wayarsa dake aje a gefen gadon cikin lokaci kaɗan ya nemo numbern Shatu wacce Zahra ke kiransa da ita, wanda Allah ya taimakesa ya daɗe da yin saving ɗinta bai dai taɓa kira bane, sai yau da yake ta zumuɗin kiran.
SHATU
Sake rungume hannuwanta tayi a ƙirji tana ƙara ƙudundunewa a cikin lallausan bargonta.
Wanda a ƙalla ta kai kusan mintuna sha biyar zuwa ashirin tana so bacci ya ɗauketa amma ko kaɗan babu shi a idanunta.
Duk yadda ta kai da runtse idanunta kuwa hoton Ya Azeez kawai take gani ko ya ta ƙifta idanuwanta, yayinda a cikin jikinta kuwa gaba ɗaya wani baƙon al'amari take ji a ko wane lungu da saƙo na ilahirin gangar jikinta.
Haka nan ta samu kanta da sakin wani ƙayataccen murmushi.
Lumshe kyawawan idanuwanta tayi tana ƙara ƙanƙame jikinta waje ɗaya, wanda kuma tana cikin haka ne wayarta dake aje gefen Zahra dake ta sharar baccinta hankali kwance ta soma ƙara.
Da sauri ta tashi zaune tare da miƙa hannu a hankali ta ɗauko wayar, ganin sunan dake yawo akan screen ɗin wayar ne yasa ta sakin wani malalacin murmushi mai cike da tarin farin ciki kafin ta shiga maimaita sunan aranta kamar mai ƙoƙarin haddacewa.
"YA ABDUL..."
Ta sake maimaita sunan tana kallon screen ɗin wayar, haka wayar ta dingi ringing tana kallo amma har ta katse bata ɗauka ba, bai haƙura ba ya sake kira, nan ma har ta ƙarashi ringing ta katse bata ɗaga ba.
Bai daddara ba ya sake danna mata kira, haka har sai da yayi mata misscall biyar amma duk bata ɗauka ba, kuma duk tana kallo amma ita kanta ta rasa dalilinta na ƙin ɗaukan kiran nasa.
A ɓangaren Ya Azeez kuwa gaba ɗaya rashin ɗaukan wayar nata sai ya saka masa wani tunani da kokwanto a zuciyarsa, wanda nan take ya shiga fargaba da tsananin tashin hankali.
Ya ɗauki sama da mintuna kusan talatin yana tunane tunane da saƙe saƙe a zuciyarsa, kafin ya haƙura ya ajiye wayar ya sake gyara kwanciyarsa lokaci ɗaya yana ƙara jin matsananciyar fargaba a zuciyarsa.
Haka ya kwana juyi cike da fargabar kar Shatu ta juya masa baya ta canza shawara tace bata sonsa.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
3️⃣4️⃣
Washegari kuwa haka ya tashi sukuku dashi gaba ɗaya zuciyarsa ba tai masa daɗi.
Daga gefe guda kuwa duk da kasancewar ransa baya masa daɗin amma hakan bai hanasa jin wata irin masifaffiyar ƙaunar Shatu mai matuƙar ratsa zuciya da gangar jikinsa na