Showing 24001 words to 27000 words out of 113443 words
gaban madubi tana fesa turare ya tsaya a gabanta fuskarsa a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba.
Ganin yadda gaba ɗaya yanayinsa ya sauya ne lokaci guda yasa gaban Fadwa ya tsananta faɗuwa taja baya da sauri cikin dakiya tana galla masa harara, bai yi wata wata ba ya fizgota ya haɗata da jikin bango ya matseta da iya ƙarfinsa ya zare mata idanu cikin wata irin murya yace "Maimaita abinda kika faɗa ɗazu akan Ummata....ki maimaita nace....?" Ya faɗa a fusace yana shaƙe mata wuya.
Zaro idanuwanta waje tayi cike da tsoro tana faɗin "Ni ba wani abinda na faɗa akanta...ka sakar min wuyana...." Ta faɗa cike da ƙarfin hali tana ƙoƙarin cire hannunsa dake wuyanta.
Sake matse mata wuyan yayi da kyau yana huci yace "Ba dai ke kince baki da kunya ba kuma baki da mutunci...? To yau kuwa zan koya miki hankali har ki ɗauki darasi tunda kince bakyaji....." Ya ƙarashe maganar tare da saka ɗayan hannunsa ya kama bakinta cike da mugunta ya matse da ƙarfin bala'i yana huci.
Ƙarar azaba Fadwa ta saki sakamakon wani mugun raɗaɗin azaba da ya ziyarceta lokaci guda dan gabaki ɗaya ji tayi tamkar numfashinta zai ɗauke ya bar gangar jikinta saboda tsabar wuyar da yake gana mata.
Shiko babu ko ɗigon tausayinta a ransa ya sake matse mata baki haɗe da shaƙe mata wuya yana faɗin "Daga yau ko ba Ummata ba zakisan irin maganar data kamata ki faɗa akan babba ko wane iri ne....kuma wallahi kika sake gigi ko kuskuren sake faɗar wata mummunar kalmar rashin kunya ko wani raini akan mahaifiyata agabana wallahi kinji na rantse sai nayi miki abinda har ki mutu bazaki taɓa mantawa dani ba ƙarshe ma sai kinyi da kin sanin sanina a rayuwarki dan sai na canza miki kamanni...."
Cikin rawar jiki ta shiga gyaɗa mai kai cike da azaba dan babu bakin magana, maƙoshinta da bakinta gaba ɗaya azaba suke mata.
Ya Azeez kuwa ko kaɗan bai ji wani tausayinta ya ɗarsu a ransa ba, sai daya gama gana mata azaba ya wajigata iya son ransa, ya tabbatar data gama wajiguwa a hannunsa tukunna dan bakinta har ya tasa sannan ya wancakalar da ita ya watsar gefe guda ya juya ya fice daga ɗakin.
*Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
1️⃣0️⃣
*ASALIN TUSHE...*
Malam Abdullah Arabi da goggo Fatime sune asalin kakannin su AbdulAzeez da Fadwa waɗanda suka haifi iyayensu, wanda ya kasance su ɗin dukkaninsu haifaffun garin Babura ne dake a jihar Jigawa.
Sai dai kuma tun asali dukkansu sun fito ne daga tsatso ɗaya kuma dama auren zumunci ne tsakanin Malam Abdullah da goggo Fatime. Daga Malam Abdullah har goggo Fatime ɗin dukkaninsu marayu ne gaba da baya kasancewar duk sun rasa iyayensu tun bayan watanni da yin aurensu, bayan haka kuma dangin nasu da suka sani basu da yawa, gashi wasu duk sun mutu sai ƴan ƙalilan ne suka rage su ma kuma kowa ya kama kansa da yawa duk sun bar ƙauyen sun koma cikin gari wasu kuma sun lula kudu neman kuɗi, sai ya kasance su kaɗai ne suka rage a garin Babura basu da wani babba nasu a tare dasu.
Basu shekara biyu da yin aure ba Allah ya basu Naseer, sai da Naseer ya shekara huɗu a duniya kana goggo Fatime ta sake haihuwar wani mai suna Jabir bayan shekara ɗaya kuma tai mai bi masa Adama daga nan sai Hauwa'u sai Zainab itace auta, kasancewar tun daga kanta Allah bai sake basu haihuwa ba.
Malam Abdullah Arabi wanda jama'a da dama su kafi kiransa da Baffa Arabi wasu kuma suce Malam Arabi sanannen malamin Addini ne mai tsantsar dattako da kiyaye dokar Allah, wanda a ɓangaren ilmin addini yayi gwagwarmaya da dama yayi koyarwa a manyan makarantun islamiyoyi da dama dake cikin garin Babura da ma sauran jihohin dake makwabtaka dasu, bayan shekarunsa sun ɗan fara ja ne sai ya daina zuwa ko'ina, ya buɗe shagon dake zauren gidansa dattijan unguwar suna zuwa kullum da daddare bayan sallar isha'i idan ya dawo daga kasuwa inda yake sana'ar saida kayan miya kamar su tumatur, albasa, tattasai, attarugu, latas, kabeji, doya da dankalin hausa, da dai sauransu.
Yana koyar dasu karatun Alkur'ani mai girma da sauran littattafan addini duk ƙarshen wata suna biyansa.
Malam Abdullah Arabi mutum ne mai kyakkyawar zuciya da jajircewa yaga ya nemi na kansa, uwa uba tsoron Allah da taqawa da son kiyaye dokokinsa, haka itama matarsa goggo Fatime mace ce mai tsananin kirki da hangen nesa gata da zumunci da son mutane.
Duk da sun kasance ba masu ƙarfi bane amma yayi ƙoƙari sosai gurin kyautata rayuwar ƴaƴansa, ya jajirce sosai gurin baiwa ƴaƴansa ingantaccen ilimin zamani duk tsadarsa tun daga kan Naseer da sauran ƙannensa babu wanda bai yi karatun boko ba, haka a fannin karatun addini duk sunyi saukar Alkur'ani mai girma da sauran litattafai wannan yasa suka samu ingantacciyar tarbiyya wanda yasa iyayensu suke matuƙar alfahari dasu.
Naseer tun yana da shekaru goma sha uku a duniya ya gama primary school ɗinsa yana kammalawa mahaifinsa yayi masa cuku cuku ya samu shiga SS1 yayinda shi kuma Jabir a lokacin yake da shekaru tara a duniya kuma yake aji huɗu a primary, haka sauran ƙannensu mata suma dukkansu a lokacin suka fara daga primary 1, ko kafin Jabir ya gama secondry tuni Sa'ad yana Federal University Dutse inda yake karantar Business Adminstration wanda gwamnati ta ɗauki nauyinsa, shi kuma Jabir a lokacin yana gama secondry dole karatunsa ya tsaya sakamakon rasuwar Baffa Arabi sai ya kasance shine ya cigaba da kula da ƴan harkokin kasuwancinsa na yau da kullum dashi suke ɗan samu suna rufawa kansu asiri da haka har suke samu suke cin abinci har yake iya biyan kuɗin makarantar sauran ƙannensu da sauran harkokin cikin gida.
A haka suka cigaba da manejin rayuwarsu har kawo lokacin da suka aurar da ƙannensu duka wanda lokacin Naseer na shekarar ƙarshe a haɗa digree ɗinsa na biyu a SLU goggo Fatime ta matsa masa tace dole dole sai yayi aure kafin ta mutu dan ta samu ganin kwansa a duniya, wannan dalilin yasa babu yadda ya iya haka yasa ta neman masa auren ƴar wani maƙwabcinsu Hafsatu, wanda cikin lokaci kaɗan akayi komai aka gama, sai bayan an gama komai ne Jabir ya tafi Zaria ta jihar Kaduna inda ya cigaba da zuwa yana saro kayan miya dasu kabeji da dankali acan yana kawowa nan ƙauyen na Babura, shi kuma Naseer yana zaune a gidansu ɓangaren da aka gyare masa kafin lokacin tafiyarsa service yayi ya tafi ya bar matarsa Hafsatu mai kunya da kawaici tare da goggo Fatime ya tafi Kano inda aka turasa can yaje yayi service ɗinsa.
Watansu goma da aure cif ta haifi kyakkyawan ɗanta mai tsananin kama da ubansa sak aka saka masa suna AbdulAzeez. Bayan shi sai bata sake haihuwa ba, lokacin ne kuma itama goggo Fatime Allah yayi mata rasuwa wanda kowa sai daya kokawa rashinta, sakamakon mutuwar Baffa Arabi data sake dawo musu sabuwa.
Tun bayan rasuwarta sai abubuwa suka fara canzawa wanda tun daga nan yanayin rayuwa yasa shima Jabir ya fara tunanin neman aure dan ji yayi gaba ɗaya gidan yayi masa girma kasancewar shi kaɗai ne yanzu yake rayuwa aciki dan tun bayan arba'in ɗin goggo Fatime da kowa ya watse shima Naseer ya ɗauke matarsa Hafsatu da ɗansa suka koma Kano da zama inda a yanzu yake gudanar da harkar kasuwancinsa acan, sai shi kaɗai ya rage yake rayuwa a cikin gidan.
Sai da AbdulAzeez ya shekara bakwai a duniya kana Jabir ya samu mata a garin Kaduna yayi aure inda yake da gida acan bayan Alhaji Naseer Arabi ya bashi kuɗi sosai ya kuma ɗorasa kan kasuwancinsa da yake dama motoci yake saidawa ƴan kwatano sannan yana shigo da kayan ginin kamfanoni da gidaje.
Matar Jabir Maryama itama ba ƴar kowa bace face ƴar talakawa ce futuk irinsa, dan mahaifinta asalinsa shima malamin zaure ne haka mahaifiyarta itama wankau take zuwa tana bin gidajen masu kuɗi tana yi ana biyanta, sai dai Maryama irin matan nan ne masu bala'in son abun duniya waɗanda basu da godiyar Ubangiji ko kaɗan, gata da mugun son jin daɗin rayuwa duk da kasancewarta ta fito daga tsatson talakawa futuk hakan bai saka ta rage wasu manyan burikan data ɗauka ta ɗorawa rayuwarta ba, shekararsu uku da rabi da aure ta haifi ƴarta mace wacce aka sakawa suna Fadwa, wanda ita da kanta ta zaɓi sunan kuma tace shi takeso a kasawa ƴarta dan tafi so komai nata ya kasance na ƴan gayu dan yazo daban a gurin mutune.
Sosai Fadwa taga gatan duniya a gurin mahaifiyarta Maryama dan tana tutiya da ita kaɗai ce Allah ya bata, shiyasa ta gama sangartata dan har ta cire rai da sake samun haihuwa saboda haka tun Fadwa na ƴar ƙarama Maryama ta ɓata ta da irin muguwar huɗubarta shiyasa bata ganin kowa da kwalli a idonsa ballantana tayi maka kallon mutunci, a haka rayuwarta ta taso da mugun buri a zuciyarta, gata dai jikar talakawa kuma mahaifinta bai da wani tarin dukiya amma kwata kwata a rayuwarta bata ƙaunar gamuwa da talaka ko a hulɗa ne bata son duk wani abu da zai haɗata da talaka tun tana ƴar ficiciyarta ta yiwa talaka mummunar tsana a rayuwarta.
AbdulAzeez nada shekara sha biyar a duniya lokacin har ya kammala makarantar primary ɗinsa, Hafsatu wacce take amsa Umma a yanzu ta haifi kyakkyawar ƴarta mace mai suna Khadija suna kiranta da Imaan, wacce AbdulAzeez yafi iyayensa murna da ɗokin haihuwar Imaan.
Tafi tafi sannu a hankali rayuwa na daɗa nisa har zuwa lokacin da AbdulAzeez ya kammala secondry school ɗinsa a wata tsadaddiyar makarantar secondry dake cikin birnin garin Kano.
Kuma a dai-dai wannan lokacin ne kwatsam sai ga Maryama da ciki a lokacin Fadwa tana ƴar shekara takwas cif a duniya wannan karon ma mace ta sake haifa aka saka mata sunan goggo Fatime sai suke mata alkunya da Ilham, bayan shekaru biyu da haihuwar Ilham ta sake haihuwar Amatullah.
AbdulAzeez tun yana ɗan ƙaraminsa yaro ne mai tsananin ƙwazo da son karatu dan haka koda ya kammala secondry school ɗinsa bayan ya karɓi takardunsa mahaifinsa bai wani sha wahala ba ya samar masa gurbin karatu a jami'ar BUK, kai tsaye ya nema masa admission bayan ya zaɓar masa irin course ɗin da yayi wato business Adminstration domin yana matuƙar sha'awar AbdulAzeez ɗin yayi karatu sosai ya zama wani abu kodan ya taimakesa akan harkan kasuwancinsa, wanda ta kai yanzu sosai yayi suna a duniya babu inda zaka zaga ka ambaci sunansa ba'a sanshi ba, gashi mutum mai taimako duk sai da ya taimaki ƴan uwansa especially ma mahaifin Fadwa, dan hatta da ita kanta Maryama a lokacin kusan koda yaushe tana kan hanyar zuwa Kano gidansu AbdulAzeez bata sati ba tare taje ta dangwali arziki taci mai kyau ta kwana a mai kyau sannan ta danƙaro abun arziki da kuɗaɗe ta dawo ba. Haka yasa itama Fadwan data ɗan fara zama budurwa a lokacin take matsawa Abbanta tace akaita gidansu AbdulAzeez itama taje tayi kwanakinta ta samo abun arziki ta dawo.
Sannu a hankali ya fara karatunsa cikin nasara da jin daɗi cikin ƙudurar Ubangiji har ya kai matakin haɗa Masters ɗinsa, dai-dai lokacin da yake gaɓan da zai ci amfanin karatunsa kwatsam wata ranar litinin suka wayi gari cikin wani mummunan tashin hankali sakamakon ƙullawa mahaifinsa Alhaji Naseer Arabi sharri aka saka mai hodar ibilis a kaya aka kamasa dalilin da yayi sanadiyyar da komai nasa ya ƙare baƙin cikin hakan yasa ya samu paralays bai shekara yana ciwo ba Allah yayi masa rasuwa bayan duka kadarorinsa sun ƙare ga jinya ga abubuwa komai yabi ya runcaɓe musu, a dalilin haka ne mahaifin Fadwa wanda shima ya koma bai da komai sai sana'ar faci da yake a bakin titin layinsu ya ɗauko AbdulAzeez ɗin ya dawo dashi gidansa yana zaune har ya nema mai aikin tuƙin keke napep.
Ita kuma Fadwa zuwan AbdulAzeez gidan sai bai yi mata daɗi ba ko kaɗan sai ya kasance duk lokacin da AbdulAzeez yake guri bazaka taɓa iske Fadwa a gurin ba, duk da a lokacin tana ƴar shekara ashirin ne abun ya faru shi kuma a dai-dai lokacin AbdulAzeez yana da shekara talatin cif, amma idan Fadwa tayi maka wani abun sai ka zata ƴar shekara ashirin da biyar ce ita, sai ya kasance duk wata taɓara da sangarta da take yi a gidan shine ke taka mata burki kafin kace me tuni wata muguwar tsanar AbdulAzeez ta shiga zuciyar Fadwa, wannan yasa Maryama wacce suke kira da Mama nuna tsanar AbdulAzeez ɗin ƙarara itama domin bata da abar farin ciki irin Fadwa dan har yau ji take tamkar ita kaɗai ce ƴarta guda ɗaya tal data haifa a duniya, shiyasa ta gama sangartata komai sai tayi mata bata taɓa la'akari da cewa ita macece dole wata rana gidan wani zata, wannan abun na baƙanta ran AbdulAzeez sosai yadda Fadwa babu mai gaya mata taji tun tana ƙaramarta yarinya ce mai yawace yawacen bala'i da tara tarkacen ƙawaye gata da mugun kwaɗayi da son abun duniya, ga shegen son tara ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi ita dai ace wannan ƴar wane ce kuma ƙawarta ce tun tana ƙaramarta jikinta har rawa yake in taji ance gidansu wane ana biki, dan ko ba biki bane idan ta saka ƙafa ta fita daga gida tun safe sai yamma liƙis sannan take dawowa, dan sai taje ta gama yawon bin gidajen ƙawayenta inda take zuwa kwaɗayi kullum sannan, mahaifiyarta kuma ita ke ƙara bata dama wani lokacin ma Abbanta ke taka mata burki ya hanata fita kuma ta haƙura da yake tana tsoronsa.
Ana cikin haka ne AbdulAzeez yaje Kano ya ɗauko Ummansa da Imaan ƙanwarsa ya dawo dasu inda suka samu wani tsohon gida a unguwar K/Mashi bayan ta siyar da sauran ƴan kunnenta da awarwarayen da suka rage masu daraja a lokacin suka biya kuɗin gidan suka shiga.
Shiko mahaifin Fadwa zuwa lokacin tuni ya gama gajiya da halayenta saboda maganar da take ja masa a unguwar bata zama a gida kullum yawo shine ya yanke shawarar yace zai haɗata aure da AbdulAzeez, shi kuma AbdulAzeez a nashi ɓangaren bai taɓa jin son Fadwa ba ko kaɗan, amma kawai saboda yadda mahaifinta ya riƙesa tsakani da Allah yasa yaji bazai taɓa iya watsa mai ƙasa a ido ba ya amince yace zai auri Fadwa.
Hakan yasa ba'a ɗau wani dogon lokaci ba cikin wata biyu aka gudanar da bikinsu cikin kwanciyar hankali aka kaita gidan daya kama haya a unguwar Hayin Rigasa, wanda Fadwa da mahaifiyarta tamkar zasuyi hauka haka abun ya kasance musu, dan Fadwa har shirya guduwa tayi amma ta fasa dan sanin an riga da an ɗaura auren yanzu a matsayin matar aure take, dan haka koda ta gudun babu abinda guduwar zata ƙareta dashi, saboda haka ta ƙuduri aniyar ƙuntata masa tare da huɗubar mahaifiyarta da take ƙara zugata tana ingizata kan ta wulaƙantasa ta muzgunawa rayuwarsa, hakan yasa ta sake buɗe sabon shafin jin daɗin rayuwarta a gidansa domin koda akai auren bata fasa yawace yawacen bin gidajen ƙawayen da take yi ba sai ma abinda ya ƙaru, amma abun bai taɓa bashi mamaki ko ya ɓata mai rai ba, dan tuni ya riga da ya gama sanin halinta farin sani shiyasa kwata kwata bai ɗorawa kansa damuwa akan abubuwan da take mai ba, domin yana da tabbacin cewa dole wata rana ita da kanta koda an biyo mata ance ta tashi ta tafi yawon zatace baza taje ba, shiyasa ko kaɗan hakan bai damunsa dan yasan komai take wata rana zata daina.
Sai gashi ko sati uku basuyi da aure ba AbdulAzeez ya fara tantance halayen Fadwa ashe da can da shi ba sanin halinta yayi ba, kawai ganinta yake yi, saboda ko girki tunda sukayi aure Fadwa bata taɓa yi ba, sai dai shi idan ya dawo ya girka tana daga zaune ya gama ya bata taci ta ƙoshi, wannan yasa Fadwa ta sake sakankancewa ta miƙe ƙafa tana zuba iskancinta yadda taga dama a gidan, saboda ita a nata haukan ɗauka take soyayyarta ce tasa baya taɓa ganin laifinta shiyasa yake mata komai kamar jin tsoro saboda kar ranta ya ɓaci.
Watansu uku da aure al'amuran Fadwa suka ƙara taɓarɓarewa sakamakon idan ta saka ƙafa ta fita daga gida tun da sassafe bata dawowa sai dare, kuma kullum idan ta tashi fita sai ta kulle gidan ta tafi da makullin kuma bata taɓa sanar dashi ga inda zataje, haka zai dawo yazo ya zauna a ƙofar gida yana jiran dawowarta, haka zai ta zama har zuwa lokacin da taga dama ta dawo sannan ta buɗe mai ƙofa ya shiga.
AbdulAzeez da yake haƙuri garesa ko tayi wani abun bai cika mata magana ba saboda haƙuri da miskilacinsa, uwa uba kuma matsayin mahaifinta a garesa da irin taimakon da yayi masa a rayuwa yasa baya jin zai iya wulaƙanta ta, amma tabbas zamansa da Fadwa akwai cutarwa haƙuri kawai yake saboda babu yadda zaiyi.
A haka dai rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi ba daɗi har kawo yanzu da suke wata tara da aure babu abinda ya sauya.
*Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
1️⃣1️⃣
Wani tarin azaba ne ya sarƙe mata wuya babu ƙaƙƙautawa nan da nan idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir saboda tsabar raɗaɗi da zafin da maƙoshinta yake mata, a hankali taja jikinta ta matsa ta jingina da jikin bangon ɗakin lokaci ɗaya tana shafa wuyanta kana ta fashe da wani matsanancin kukan azaba da tsantsar baƙin cikin irin rashin mutunci wulaƙancin da Ya Azeez yayi mata.
Sosai ta zauna take rusa uban kuka kamar zata shiɗe sai sauke ajiyar zuciya take da numfashi lokaci ɗaya, gefe guda a ranta kuwa mamakin tsantsar rashin tausayi da imaninsa take yadda ya zage ya rufe idonsa ya karta mata rashin mutunci. Wai shine yau har da shaƙeta kawai dan tace baza ta gaisa da uwarsa ba..? Lallai idan kuwa ta barshi ya cigaba da mata irin wannan iskancin