Showing 66001 words to 69000 words out of 113443 words

Chapter 23 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7559

tsabar baƙin cikin abinda yayi.


Shi kuwa Fahad ganin yadda Ya Azeez ɗin ke masa wani mugun kallo ne yasa yasha jinin jikinsa, duk ya wani dabarbarce kana kuma cikin sanyi jiki yace "Toh ai na gaya maka ne dan ka bani shawara amma naga ka wani tsaya kana ƙare min kallo, ko har yanzu dai baka fahimci abinda nake nufi bane, saboda naga kamar sai kallon tuhuma kake min kana ƙara sanyaya min jiki...?"


Ƙwaffa kawai Ya Azeez ɗin yayi ba tare kuma da ya ce masa komai ba, ya fara ƙoƙarin tada motar su wuce, a fusace Fahad ya riƙe hannunsa lokaci ɗaya yana harararsa yake faɗin "Wannan wane irin abu ne haka..ya na gaya maka magana kuma amma ba kace komai ba kuma kake ƙoƙarin shareni, ko nufinka maganata bata da wani amfani kenan...?"


Idanu Ya Azeez ɗin ya buɗe sosai a kansa yana faɗin "Ashe ka gane nufina kenan, danni kaf a maganarka banga abun kulawa ba, wanda har mutum zai damu kansa da sai ya baka wata shawara akan wannan shirmen naka na banza da wofi..."


Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da jan tsaki, kafin ya zura key da sauri ya tada motar, yayinda kuma yana ƙoƙarin ja, Fahad ɗin ya riƙe masa hannu da sauri yana girgiza masa kai lokaci ɗaya yana faɗin "Haba abokin, dan Allah karka yi min haka mana, kasan dai bani da wani abokin shawara duk faɗin garin nan sai kai, kuma bayan Ubangijina kai kaɗai nake dashi wanda zan iya faɗawa damuwata, dan girman Allah ka tsaya ka saurareni ka kuma nuna min inda kuskurena yake, wallahi zan gyara..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cikin sanyin jiki yana kallonsa.
























*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*








2️⃣6️⃣




A hankali kuwa Ya Azeez ɗin ya kallesa shima yana faɗin "Wallahi ka bani mamaki Fahad, ace kamar kai da tunaninka da komai amma har ka iya biyewa son zuciyarka ka aikata irin wannan wawancin, dan wannan ai babban wawanci ne da rashin lissafi, to wai kai mema ya shiga kanka ne da har ka biye musu aka aikata wannan ɗanyen aikin da kai...?"


Bai yi magana ba illa sunkuyar da kai kawai da yayi yana sauke ajiyar zuciya.


Ajiyar zuciyar Ya Azeez ɗin ya sauke yana ƙara runtse idanunsa cike da takaicin Fahad ɗin, kafin kuma ya jingina kansa da jikin kujerar motar yana ƙara haɗe fuskarsa yace "Wallahi kayi wauta Fahad, kayi rashin tunani, idan tsoron kada ka rasata ne kuma yasa ka aikata hakan, to kuwa na tabbata ita a gurinta ka gama zubarwa da kanka mutunci ne, dan wallahi anan gaba dole sai abinda take so kuma taga dama shi zatayi a cikin gidanka kuma kana kallo baka isa ka tsawatar mata ba, tunda tun farko kai ne ka nuna mata cewa duk abinda take so ko tayi shine dai-dai a gurinka.
Amma inaso ka sani indai mata ne wallahi nan gaba sai kayi bala'in dana sanin biye matan da kayi, saboda kai shaida ne ban taɓa ɗora Fadwa akan irin wannan hanyar ba, amma yau fa wane irin zama muke yi da ita, aya ta ɗauke ni..meta maidani..? Duk fa kasan waɗannan abubuwan saboda babu abinda nake ɓoye maka kasan komai, wanda kuma a yanzu haka maganar da nake maka Fadwa na Abuja da sunan ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta, kuma koda wasa ban san ta tafin ba, saboda bata gaya min ba sai da suka sauka sannan ta kirani take gaya min wai tana Abuja, wanda kai da kanka ka sani a duniya bani da wata damuwa sai Fadwa, Fadwa itace babbar matsalata kuma kasan wannan.
Amma ban san meya shiga kanka ba har ya kaika ga sha'awar aikata irin wannan, wanda na tabbata tun farko daka nuna musu cewa zaka iya rayuwa ko babu ita, da tuni sunbi yadda kakeso, amma saboda shaukin soyayyarta ya gama rufe maka idanu ya hanaka ji da ganin komai sai ita, shiyasa ka yanke wannan hukuncin ba tare da tunani ko wani lissafi ba, kuma nayi mamaki da har su Abba suka iya biyewa wannan shirmen naka, basu taka maka burki ba..."


Fahad ya saki ajiyar zuciya kafin yace "Wallahi duk na sani aboki, kuma ko Abba da kansa ma sai daya so nusar dani a lokacin ya nuna min rashin dacewar hakan, amma na dage na nuna masa ni na amince kuma babu komai, wallahi banyi tunani ba aboki ban yi lissafi ba.
Sai yanzu gaba ɗaya na ke ji a raina ban kyautawa kaina ba, kuma banyi abinda ya kamata ba, amma yanzu meye abun yi..ya zanyi in nuna ni jajirtaccen namiji ne wanda zai iya nuna isa a gidansa..? Dan Allah aboki ka gaya min taya zan gyara kuskurena...?"


Sai a lokacin ne Ya Azeez ɗin ya sake gyara zamansa da kyau yana fuskantarsa kafin yace "Uhmmm ai kamar yadda ka nuna musu cewa ka amince tun farko, to yanzu ɗin ma haka zaka koma ka sake nuna musu cewa baka amince ba, kawai tunda an ɗaura kana buƙatar matarka ta tare a gidanka, idan yaso ka yarda ta ci gaba da karatun acan gidanka, amma wannan tsarin nasu karka sake ka yarda yayi tasirin da komai sukace dole shi za'ayi, ka gyara tun kafin lokaci ya ƙure maka..."


Gyaɗa kai Fahad yayi kafin yace "Insha Allahu kuwa aboki hakan zanyi, kuma tun yau zan fara yiwa Abba magana idan muka koma gida, dan Allah ya sani bazan iya haƙurin har nan da sati ɗaya zuwa biyu ba nima, dole ne za'a san abin yi..."
Ya faɗa yana dafe kansa.


Ya Azeez bai yi magana ba illa sauke ajiyar zuciya da yayi, ya kunna motar lokaci ɗaya ya tada suka soma tafiya a hankali, yayinda kuma suke ci gaba da tattauna maganar a tsakaninsu.






★★★★★




Acan ɓangaren su Shatu kuwa bayan sun kammala girkin ne ta fito ta koma ɗakinsu, tana shiga ta wuce toilet direct ta ƙara watso ruwa ajikinta ta fito.
Kasancewar garin akwai ɗan zafi zafi ne yasa ko mai bata tsaya shafawa ba, ta buɗe wardrobe ɗinta ta zaro wata laloluwar doguwar riga kalar ruwan madara mai hannun shimi ta saka, kana kuma ta ɗan fesa turare kaɗan ajikinta.


Koda ta gama shiryawan kuwa gado ta haye tai kwanciyarta abunta tai luf da nufin ta ɗan huta, kafin kuma lokacin sallar Azhar yayi ta tashi tai sallah.






*********




A ɓangaren su Ya Azeez kuwa basu nufi gida direct ba, cikin gari kawai suka wuce gurin abokanansu, inda suka kusan wuni acan, dan sai gurin ƙarfe 4pm. Da wani abu sannan bayan sunyi sallar la'asar sukayi musu sallama, suka kamo hanyar gida.


Wanda kuma suna ƙarasowa gidan ne suka iske Abba da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai zaune a wata ƴar madaidaiciyar baranda mai kyau dake gefen koridon da zai sadaka da shiga cikin babban falon gidan, a hankali sukayi parking ɗin motarsu a farfajiyar gidan kana suka buɗe lokaci ɗaya suka fito atare suka nufi gurin su Abban, inda suna ƙarasawa dukkansu suka rusuna agabansu cike da girmamawa suna gaishesu.


Juyowa Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai yayi ya kalli Ya Azeez dake durƙushe a agabansa yana gaishesa, domin a yadda yaji muryar tasa, da yanayin yanda yake gaishesan, sai take yi masa kama da wata muryar daya taɓa ji amma ya rasa tuna ko a ina ne ya taɓa jinta, amma kam tabbas ya taɓa jin irin kwatankwacin wannan muryar sak sai dai ya kasa tuna a inda ya jitan.


Haka har suka gama gaishesu duk suka miƙe suka nufi cikin gida, amma Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Ya Azeez, wanda kuma har zuwa lokacin bai iya tantance a inda ya taɓa jiyo ko da mai kama da irin muryar ta Ya Azeez ɗin ba ne kawai dai hasashe yake, haka yay ta binsu da kallo har sai da yaga shigewarsu cikin gidan kana ya iya ɗauke idanuwansa daga kansu yana mai ƙara nazarin abun a zuciyarsa.


Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke tare da kallon Abba fuskarsa ɗauke da tsananin mamaki yake faɗin "Ni kuwa Alhaji sai nake ganin wannan yaron kamar ɗan wajen amininka Alhaji Naseer Arabi, dan naga kamar tasu tayi yawa ne har ta ɓaci wallahi...?"


Murmushi Abba yayi ya kallesa kafin yace "Babban ɗansa ne mana AbdulAzeez, akwai kuma ƙanwarsa Imaan itama tana can Kaduna tare da mahaifiyarsu..."


Cikin tsananin mamaki ya juyo yana dubansa, kafin kuma cikin sanyin jiki yace "Allah sarki Alhaji Naseer mutumin kirki, Allah yayi mishi rahama ya yafe masa kurakuransa..wallahi har yau na kasa manta karamcin wannan bawan Allahn, Allah yasa halinsa na gari ya bishi..."


Da "Ameen..." Abba ya amsa masa, kana daga haka suka ci gaba da tattaunawa akan harkar kasuwancinsu.


Sai gab da magriba kana bayan sun gama tattaunawan, Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya miƙe tsaye sukayi musabaha da Abba wanda ya rakasa har gurin motarsa sukayi sallama, direbansa yaja suka fice daga gidan. Yayinda shi kuma Abba ya juya kai tsaye ya wuce cikin gidan ya nufi ɗakinsa, domin ɗauro alwala ya wuce masallaci, dan yaji har an fara kiran sallar magriba.


Wanda kuma a tare suka fito daga cikin gidan shi dasu Ya Azeez da Fahad har ma da Ibrahim dukkansu suka nufi masallacin, koda aka idar da sallar magriban kuma gaba ɗayansu basu fito daga cikin masallacin ba har sai da suka sallaci sallar isha'i kana suka fito a tare suka dawo gida.
Inda direct kuma suna shigowa cikin falon dukkansu kai tsaye suka wuce dinning area, inda Mami ta gama shirya musu lafiyayyen girkinta suka zazzauna, Mamin da kanta ta miƙe tayi sarving ɗinsu inda ta zuba musu haɗaɗɗiyar jalop ɗin da tayi musu wanda taji hanta da kayan haɗi sai pepper meat, ta turawa kowannen su filet ɗin abincin gabansa, kafin itama ta zuba nata ta koma ta zauna a gefen Abba.


Bayan sun kammala cin abincin ne kuma suka miƙe dukkansu suka yiwa Abba da Mami sai da safe, yayinda Ibrahim shima yayi musu ya wuce ya tafi ɗakinsa, kana su kuma suka haura sama zuwa ɗakin Fahad.




*******


Washegari kuwa tunda sassafe Ya Azeez ya gama shirinsa tsaf, cikin wasu riga da wando masu kyau a cikin kayan daya taho dasu, sosai kayan sukayi masa kyau dai-dai gwargwado dan basu wani sha jiki sosai ba, gashi sun ƙara fito da asalin kyau da kwarjininsa a fili, uwa uba wani haɗaɗɗen ƙamshi mai daɗi dake tashi a jikinsa.
Cikin natsuwa ya ƙarasa saukowa cikin falon yayinda kuma Fahad dake biye dashi a baya yake riƙe da jakarsa, kai tsaye suka ƙaraso gaban Abba da Mami dake zaune saman kujerun dake falon, yayinda Abba ya saki baki cike da mamaki yake kallonsu, kafin kuma ya juya ya kalli jakar dake hannun Fahad yana faɗin "Ba dai har ka fito ba kenan, tunda sanyin safiyar nan sai kace ana koranka...?"


A hankali Ya Azeez ɗin ya durƙusa a gabansa yana faɗin "Eh Abba inaso ne dama in isa gida da wuri dan in samu damar yin magana da Umma dan ban riga na gaya mata yadda mukayi da kai ba, so nake sai na isa gidan tukunna..."


Kai Abba ya jinjina cike da gamsuwa yana faɗin "Hakan yayi dai-dai kuwa, Allah ya tsare ya kiyaye hanya Allah kuma ya saukeku lafiya..."


Da "Ameen..." Duk suka amsa atare, kana kuma daga haka Ya Azeez ya sake gyara zamansa cikin girmamawa yana faɗin "Abba dan Allah muna ƙara roƙon arziki ayi haƙuri a dubi buƙatar mu, wallahi Abba abin bai yi tsari ba kwata kwata kuma su iyayen yarinyar sune suka yanke hukunci ba tare da sun yi tunani ba, amma t..."


"Amma me AbdulAzeez..? Abba ya faɗa a kausashe yana kallonsa, kafin ya ci gaba da faɗin "Kai a naka ganin kawai sune suka yanke hukunci ba tare da amincewarsa ba kome...?"


Ɗan ƙara duƙar da kansa Ya Azeez ɗin yayi yana faɗin "Amma ya kamata su duba abinda ya dace da wanda bai dace ba kafin su zartar da hukuncin, wannan ai yana nuni da cewa su ba manyan mutane bane sam, saboda babu ta yadda za'ayi babban mutum da yasan ciwon kansa yayi irin wannan shirmen..."


Da kallo kawai Abba ya bishi kafin ya ɗan saki murmushi a fili yace "Ka daina ganin laifinsu AbdulAzeez, ga ƙaton mai laifin nan tunda shine ya azalzala ya matsa yace dole sai an ɗaura auren kamar yadda yake so..dan haka laifinsa zaka gani ba nasu ba..."


Abba ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana nuna Fahad da yayi kasaƙe yana kallonsu.
Sai a lokacin ne kuma Mami tayi magana inda ta kalli Ya Azeez daya fututtuke ya dage wai dole sai an je an samu iyayen Basma amaryar Fahad an gaya musu cewa ya fasa jiran sai ta gama makaranta kafin ayi biki atare, kawai shi yanzu yake buƙatar matarsa, tunda an riga da an ɗaura auren kawai a kawo masa abarsa.


Baki Mami ta taɓe cikin ɓacin rai tace "Toh wai waye kuka maida ƙaramin mutum ɗin da zai je yayi muku wannan aikin, ko kun haifemu ne da zaku dinga juyamu kamar waina kuna abinda kukeso...?"
Ta faɗa a zafafe tana hararar Fahad ɗin daya duƙar da kai yana sauke numfashi.


Abba kuwa miƙewa tsaye yayi yana faɗin "Ki barsu dai Fiddausi, ai nace zamuje anjima nida Alhaji Bello muji yadda zamuyi da iyayen yarinyar, idan ma basu yarda ba sai mu barsu da abinsu, su ida ƙarasa abinda suka fara, tunda mun riga munyi mai wuyar an ɗaura, sai su san abin yi kuma..."
Ya faɗa tare da raɓewa ta gefensu ya wuce, miƙewa Mamin tayi tana faɗin "Aiko dai wallahi, tunda duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma duk abinda mutum ya zaɓa shi zai gani..." Ta faɗa cike da jin haushi tare da juyawa ta wuce tabi bayan Abba daya haura sama zuwa ɗakinsa.


A sanyaye duk suka bisu da kallo, har suka shige, kana suka miƙe cikin sanyin jiki suma suka fice daga falon, yayinda Ya Azeez ke ta ƙara kwantarwa da Fahad hankali, yace ya natsu kar ya damu insha Allahu komai zaiyi dai-dai.


A hankali suka fito farfajiyar gidan nasu, wanda ganin fitowarsu ne kuma yasa direban Abba tasowa da sauri ya ƙaraso gabansu, jakar dake hannun Fahad ya ƙarba ya saka a boot, kana ya buɗe masa gidan baya ya shiga ya zauna, kafin ya ɗan leƙo da kansa yana faɗin "Pls Dude ka kwantar da hankalinka, insha Allahu nan bada jimawa ba komai zaiyi dai-dai..kaji...?"


Kai kawai Fahad ɗin ya ɗaga masa cikin sanyin jiki kafin yace "Insha Allahu aboki, Allah ya tsare ya saukeka lafiya ka gaida min dasu Umma. Sai mun yi waya..."
Ya faɗa cikin ƙaƙaro murmushi tare da ɗaga masa hannu.
Har motarsu ta fice daga cikin farfajiyar gidan Fahad na tsaye yana ɗaga musu hannu, har sai da maigadi ya mayar da ƙofar gate ɗin ya rufe sannan ya juya cike da kewa ya koma cikin gidan.






**********




A ɓangaren Shatu kuwa, yau ɗin wani irin sakayau take jin kanta, zuciyarta babu nauyin komai, dan haka tunda ta tashi da asuba tayi sallah, ta koma bacci, bata tashi ba sai gurin ƙarfe 10am. Tana tashi kuma ta faɗa toilet tayo wanka ta fito, a gurguje ta hau shiryawa cikin wani rantsatstsen leshinta mai tsananin tsada da kyau kalar ja da baƙi, wanda aka yiwa ɗinkin doguwar rigar fitted.


Koda ta gama shiryawa bata tsaya wata kwalliya ba, ta ɗan shafa hoda kawai a fuskarta, ta ɗan saka kwalli sannan ta shafa lipstick a laɓɓanta.
Ba tare kuma data sake shafa komai a fuskarta ba, ta ɗauki fashion ɗan kunne ta saka a kunnenta, kana ta yafa wani ɗan siririn gyale kalar ja a kanta, ta sanya tsadadden takalminta mai tsinin dunduniya shima ja, sannan ta ƙarasa gaban madubi a gurguje ta fesa turare, ta ɗauki wayarta dake aje agurin ta fice daga ɗakin.
Fuskarta ba wata kwalliya amma kuma duk abinka idan ka kalleta a lokacin saika so ka ƙara kallonta, saboda wani sihirtaccen kyau da shigar tayi mata, ta ƙara fito da zallar natsuwa da wayewarta.




Koda ta sauko ƙasan kuwa Ummi kaɗai ta iske zaune a falon tana kallo, ganin kuma irin kallon da Ummin take mata ne, yasa ta wani ɓata rai ta juya tana faɗin "Ummi nayi kyau kuwa...?"


Kaɗa kai Ummi tayi kafin tace "Ana ma magana ƴan matana..? Sosai kikayi kyau wallahi tubarakallah Masha Allah, sai ina kuma tunda safiyar nan akaci wannan uban gayun haka...?" Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo.


Ɗan kwaɓe fuskarta tayi kafin tace "Gidansu Basma Jada zani Ummi, ashe wai an ɗaura aurenta tun shekaran jiya, amma shine babu wanda ya gaya min sai jiya da daddare ne muna chat da Husna Baita take faɗa min, amma wai ɗaurawa kawai akayi ba'a yi bikin ba tukunna, sai nan da sati mai zuwa sannan za'a yi biki ta tare..."


Gyaɗa kai Ummi tayi tana faɗin "Masha Allah Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya, Allah kuma ya nuna mana na ƴan baya lafiya..."


"Ameen ya Allah..." Shatu ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa daga falon.


Da sauri Ummi tace "Wai kina nufin a haka zaki fita ba tare da kinyi breakfast ɗin ba, ga can kuma abincinki akan dinning fa tun ɗazu har muka gaji da jiranki muka karya baki fito ba..."


Fuska ta kwaɓe kafin tace "Ummi a ƙoshe fa nake, idan na dawo zanci..."


Harara Ummin ta galla mata tana faɗin "Aiko babu inda zakije sai kinyi breakfast..."


Ta faɗa cikin haɗe rai tana watsa mata harara, ganin babu yadda ta iya ne yasa ta juyo ta koma cikin falon kai tsaye ta nufi dinning area ɗin tana turo baki taja kujera ta zauna.
Tea kawai tasha sai farfesun kaza data haɗa dashi, tana kammalawa kuma ta miƙe tsaye tana goge bakinta da tissue, saurin kallonta Ummi tayi tana faɗin "Ba dai har kin gama ba..."


A hankali ta gyaɗa mata kai kafin tace "Na ƙoshi Ummi..."


Ta faɗa a shagwaɓe tana shafa cikinta, kafin ta wuce ta nufi ƙofar fita daga cikin falon tana faɗin "Ummi na tafi sai na dawo..." Ta faɗa tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login