Showing 108001 words to 111000 words out of 113443 words

Chapter 37 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7582

hankali yana faɗin "Ina ne yake zafin to, nuna min...?"
Hannunsa ta kama ta kai dai-dai kan mararta ta ɗora tana ɗan shafawa a hankali a hankali.
"Nan ne...?"
Ya faɗa tare da saka yatsunsa biyu ya danna gurin da ɗan ƙarfi.
Wata irin zabuwa tayi ta ƙara ƙanƙamesa kafin a shagwaɓe tace "Wayyo Habiby nan ne..."
Yace "Ayya sorry..." Ya faɗa yana sake danna cikin a hankali, kafin kuma ya ɗago kai ya kalleta yace "Nan ma yana zafin...?"
Shagwaɓe fuskarta tayi ta gyaɗa mai kai, sai kuma ta rufe idanunta tana dariya.
Hannuwanta duka biyu ya kamo ya sumbacesu, kafin ya tashi ya miƙar da ita tsaye yaja hannunta suka nufi dinning table.
Da kansa yaja kujera ya zauna, kana ya zaunar da ita saman cinyarsa ta zauna ta zuba musu abincin, shi ya dinga bata da kansa tana ci, kana itama ta dinga bashi a baki yana ci, a haka dai suka ciyar da junansu har suka ƙoshi.
Koda suka gama kuwa kayan ta kwashe ta kai kichin, sai data wanke ta maida komai ma'ajiyarsa sannan kuma ta fara ƙoƙarin ɗora girkin dare.


A daren kuma sukaje wata babbar super market suka yowa Umma da Imaan siyayyan kaya masu yawa kala kala, kana ta haɗawa Imaan dasu chocolate da biscuits har dasu sweet da cingum kayan ƙwalama dai iri iri ta haɗa mata.
Sosai dai sukayi siyayya mai yawa kana suka dawo gida.


Washegari kuwa tunda sassafe ta gama haɗa musu breakfast, bayan sun ci ne kuma ta wanke kwanukan kafin suka haye sama suka shiga toilet suka sake sabon wanka.
Koda suka fito kuwa shiryawa sukayi cikin wasu tsadaddun kaya masu matuƙar kyau da tsada, inda Ya Azeez ɗin ke sanye da wata haɗaɗɗiyar shadda mai tsada ruwan sararin samaniya, yayinda kuma Shatu ke sanye da wani tsadadden leshi ja sai gyale da jaka da takalminta kuma suma duka kalar sararin samaniya ne.
Sosai shigar tayi mata masifar kyau ba kaɗan ba, kayan dake jikinta kaɗai sun isa su sakata tayi kyau balle kuma kwalliyar da tasha kamar wacce zata tafi gurin gasar sarauniyar kyau ta Nigeria.
Yana zaune a falon ƙasa yana waya da Fahad, ta soma saukowa a hankali yayinda kuma takalmin ƙafarta ke bada wani irin sautin ƙwaras ƙwas ƙwas, ɗagowa yayi da sauri yana kallonta, kafin ya miƙe da hanzari yana faɗin "Ina zuwa Fahad zan kiraka..." Ya faɗa tare da katse wayar lokaci ɗaya yana tsura mata idanu cike da zallar so da ƙaunarta, domin kusan kullum gani yake kamar ana ƙara mata kyau ne.


A hankali ya furta "Masha Allah Eishatunaaa kin ganki kuwa..? Gaskiya kinyi kyau sosai tubarakallah Masha Allah..."


Murmushi tayi kafin ta ƙarasa saukowa har ya ƙaraso gabanta ya riƙo hannuwanta duka biyu lokaci ɗaya ya jawota jikinsa ya ƙanƙameta yana juyawa da ita a tsakiyar falon.
"Zautani zakiyi da salonki ƴan matana, ina matuƙar ƙaunarki ina sonki..ina sonki..ina sonki..."
Ya ƙarashe maganar yana ƙara ƙanƙameta ajikinsa ƙam yana juyi da ita.
Itama ƙanƙamesan tayi tana faɗin "Nima ina sonka ina sonka ina sonka masoyina..."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana ɗago kai ta haɗe bakinsa da nata waje ɗaya ta shiga bashi wata irin salon tsotsa mai matuƙar ɗaukar hankali da gusar da tunani.
Sai data tsotsi bakinsa iya son ranta kafin ta janye ta sauka daga jikinsa ta rungumesa tana wani irin shafa gefen wuyansa.
"Muje Habiby wallahi duk na ƙosa mu isa inga Umma..."
Ta faɗa tare da sumbatar kumatunsa.
To yace, kana ya ɗauketa cak suka fice daga cikin falon.
Sai daya sakata a cikin mota ya rufe, kana ya dawo ya kashe wutar falon ya kukkulle ko'ina, sannan ya dawo ya shiga motar direbansa ya kunna bayan yayi horn maigadi ya wangale musu tangamemen ƙofar gate ɗin ya silala motar suka fice daga cikin gidan gaba ɗaya.
Koda suka isa airport ɗin kuwa direban ajiye su yayi ya dawo da motar gida.


Ƙarfe 10am. Dai-dai kuwa jirginsu ya ɗaga zuwa Kaduna, suna sauka acan kuma direban Umma yazo ya ɗaukesu zuwa gidan Umman.
Zo kaga nuna ƙauna gurin Umma, kamar zata haɗiye Shatu saboda tsabar murna da farin cikin ganinsu.
Sai mamaki take yadda taga Ya Azeez ya canza cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙara wani kyau da haske na musamman.
Imaan ma tana ta murnar ganin yayanta da matarsa da take ji tamkar ta maida ita cikinta saboda son da take mata.
Sai yamma sannan suka sake yin wanka suka shirya cikin wasu tsadaddun kayan da har sukafi wanda suka zo dasu ajikinsu kyau da tsada, dan Ya Azeez kam duk wanda ya gansa indai ba kyakkyawan sani yayi masa ba da wuya zai ganesa lokaci guda, saboda tsantsar kyau da kwarjinin da kayan sukayi masa.
Har da Imaan direban Umma ya ɗaukesu zuwa unguwar Mu'azu gidansu Fadwa.


Dai-dai ƙofar gidan Abban Ya Azeez ya nunawa direban yace ya tsaya.
Sannan a hankali ya buɗe motar ya fito kana ya zagaya ɗaya ɓangaren ya buɗewa Shatu itama ta fito, Imaan ma dake kusa da direba ta buɗe itama ta fito.
Nan suka bar direban a cikin motar yana jiransu suka nufi hanyar da zata sada su da shiga cikin gidan, Imaan da Shatu na riƙe da ledojin tsarabar turaruka da manyan shaddojin da suka yowa Abban a hannayensu.
Cikin zauren gidan ya tsaya ya kira Abba yana sanar dashi cewa sun iso suna gidan, yayinda kuma Shatu da Imaan kai tsaye suka nufi cikin gidan bakunansu ɗauke da sallama suka shiga.


Fadwa da zuwanta kenan tana zaune a ƙofar ɗakin Mama tana cin wake da shinkafan da Maman ta dafa ta zubo mata, wanda kuma tunda aka ɗaura mata aure da Ya'u mai kifi, yau ce rana ta farko daya taɓa barinta fita har tazo gidan, shima kuma sai data haɗa masa da ƙaryar cewa Abbanta ne bashi da lafiya shine ya yarda tazo ta gaishesa, har da bata ɗari biyu yace ta siyan mai lemu da ayaba ta tafi mai dashi, wanda ɗari biyun ma da ita tai kuɗin mota tazo gidan.
A yunwace take cin abincin, domin rabon da taci abinci mai daɗi irin haka tun ranar bikinta da Ya'u mai kifi.
Ta ɗago da nufin kai kofin ruwa bakinta ne kuma idanuwanta suka sauka cikin na Shatu da Imaan da suke tsaye a tsakar gidan hannayensu riƙe da manyan ledoji suna kallonta.
Ganin kallon da suke mata ne yasa a kunyace ta dire kofin ruwan ta miƙe tana janye kwanon abincin gefe tace "A'a Imaan kune..? Sannunku da zuwa ku ƙaraso ciki mana..." Ta faɗa cikin rawar jiki tana tsallake abincin ta shiga ɗakin Mama ta ɗauko musu sabuwar darduma tazo ta shimfiɗa musu tace su zauna, kafin ta fice da hanzari ta nufi kichin ta kira Mama suka dawo cikin ɗakin atare.


"A'a Imam ashe dai ke ɗin ce da gaske..to sannunku da zuwa sannunku..ke Fadwa ungo ki siyo musu ruwa mai sanyi maza..."
Maman ta faɗa cikin rawar jiki tana miƙawa Fadwa hamsin ɗin dake hannunta, wanda kuma a dai-dai lokacin ne Ya Azeez da Abba suka shigo cikin gidan.
Miƙewa Fadwa tai zata fice da sauri Imaan ta dakatar da ita tana faɗin "A'a Aunty Fadwa ki barshi, wallahi Mama daga gida muke sai da muka ci abinci muka sha ruwa kafin mu fito..."


Rausayar da kai Mama tayi tana faɗin "Ko dai anan ɗin ne baki son kusha ɗin ko...?"
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon suturar jikinta tana mamakin sauyawar da Imaan ɗin tayi cikin lokaci ƙanƙani da bata ganta ba.


Imaan ta buɗe baki kenan zatayi magana Abba da Ya Azeez suka sako kansu cikin ɗakin yayinda Abba ke gaba Ya Azeez kuma na biye dashi a baya.


Wani mummunan faɗuwa gaban Fadwa yayi jin daddaɗar muryar Ya Azeez ɗinta ne ke sallama, Mama kuwa daɓas ta koma ta zauna a tsakar ɗakin tana kallon Abba da bakinsa ya kasa rufuwa saboda tsabar murna da farin cikin ganinsu Ya Azeez ɗin.


Cikin rawar murya data jiki kuwa Mama ta hau inda inda tana nuna Ya Azeez cikin tsantsar mamaki tana faɗin "Wane..ne wann..an nake gani kamar AbdulAzeez, kai anya kuwa shine ko dai ɗan wanda ka kewa tsaron shago ne kasuwa Abban Fadwa...?"
Ta faɗa cikin tsananin mamaki da al'ajabi tana kallon Abba daya kamo hannun Ya Azeez ɗin ya zaunar dashi kusa da Shatu da tunda ya shigo ta ɗago kai tana kallonsa suna aikawa juna da wani sihirtaccen kallon tsantsar ƙauna da soyayya kana suna sakarwa junansu kyakkyawan murmushi mai tsayawa a zuciya.


Kallonta Abba yayi, kana ya juya ya kalli Ya Azeez daya ɗan jingina da jikin Shatu kaɗan yana yi mata raɗa a kunne, kafin yace "Ɗana ne AbdulAzeez dai kike gani..."


Wani irin zaro idanuwa Mama da Fadwa sukayi a tare suka kalli Abban kafin kuma suka juya suna kallon Ya Azeez wanda gaba ɗaya hankalinsa baya kansu, yana can duniyar shaƙar daddaɗan ƙamshi matarsa yana wani lumshe idanu cike da tsantsar ƙaunarta.


Tsura masa idanu Fadwa tayi tana ƙare masa kallo, kafin kuma ta ware ido sosai tana faɗin "Wallahi Mama Ya Azeez ɗina ne, shine wallahi..."


"Shine fa kikace Fadwa...?"
Mama ta tambaya tana wani zaro idanuwa waje, kamar wacce taga wani abun tsoro.


Jinjina mata kai Fadwa tayi tana faɗin "Wallahi tallahi Mama Ya Azeez ne ya dawo, kiyi addu'a Allah yasa maidani ya dawo yayi ɗakina wallahi Mama komawa zanyi bazan koma gidan Ya'u ba..."
Fadwa ta faɗa cikin fitar hayyaci tana kallon Mama data wani tsaya ƙam ta saki baki galala tana faman kallon Ya Azeez kamar mai son gano wani abu a cikin jikinsa.


Ganin irin kallon da Maman ke masa ne yasa ya ɗago kai ya kalleta, kafin kuma cikin sanyin muryarsa yace "Mama ina wuni mun sameku lafiya...?"


Da sauri Fadwa ta fito da idanu waje tana kallonsa, dan ita da kanta sai yanzu ne take ƙara tabbatar da cewa Ya Azeez ɗinta ne dai data sani, tabbas shine zaune a gabanta ba ƙarya ba, kuma ba gizo idanuwanta suke mata ba.


























*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






3️⃣8️⃣






"AbdulAzeez kai ne dai da gaske, Fadwa duba dai da kyau ki gani, anya kuwa ba idanuwanku bane suke yi muku gizo...?"


Mama ta faɗa lokaci ɗaya tana nunashi jikinta na tsuma, ji take abun kamar a mafarki wai AbdulAzeez ne haka a gabanta cikin kyakkyawar shiga wacce kana gani kuma kasan kuɗi sun gama zauna masa, ga jikinsa yay wani irin lukwi lukwi tamkar na jinjirai, gaba ɗayansa ya koma wani hamshaƙi na musamman.
Yunƙurawa tai zata tashi amma tsantsar kaɗuwa da mamakin abinda take gani ya hanata samun karshashin hakan, kawai sai ta koma daɓas ta zauna a ƙasa tana zare ido.


Abba dai guri ya samu ya zauna shima yana ta kallon Mama dake ta kaɗa kai tana faɗin "Ikon Allah ni kaga Imaan kaɗai na gane tsaf, amma kai ko kaɗan ban ganeka ba, dan wannan ma ni ban taɓa ganinta ba, ko ƴar uwar Ummanku ce...?"
Girgiza mata kai Ya Azeez yayi yana murmushi kafin yace "A'a matata ce sunanta Aisha..."


"Matarka...?"


Fadwa da Mama suka haɗa baki gurin faɗa a tare suna kallon Shatu data sunkuyar da kai ƙasa tana murmushi.


Jinjina kai Imaan tayi kafin tace "Eh Mama matarsa ce yau suka zo daga Kano..."
Imaan ta faɗa tana kallon Ya Azeez ɗin da Shatu tana murmushi, girgiza kai Mama tayi tana kallonsu kafin ta gyaɗa kai tana faɗin "Ikon Allah! Lallai arzikin bawa na tare dashi, kuma hausawa sunyi gaskiya ɗan hakkin daka raina wata rana shi zai tsole maka idanu, wallahi yanzu kam na yarda da maganar nan gaskiya ce na yarda, yanzu AbdulAzeez kai ne haka kuma wannan matarka ce...?"
Ta faɗa cikin kuka tana kallon Abba da yay zaune ya zubo mata idanu yana kallonta.


Wata iriyar mummunar bugawa zuciyar Fadwa tai, yayinda lokaci ɗaya kuma taji wani abu mai tauri ya sarƙe mata maƙoshi yana barazana da numfashinta, zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar wacce ake hurawa wuta.
Idanu kawai ta zubawa Shatun tana kallonta tun daga kan kyakkyawar fuskarta kuwa har zuwa kan tsadaddiyar suturar dake jikinta da wayar dake hannunta, haka take binta da kallo har kan babban ɗan yatsar ƙafarta sosai take ƙare mata kallo.
Kafin kuma a hankali ta mayar da idanuwanta gam ta rufe tana jin taruwa wasu azababbun hawaye masu matuƙar raɗaɗi da ƙunar zuciya na tsiyayowa daga cikin idanunta.
Tabbas yanzu kam Ya Azeez yayi mata nisa, nisan da ko anyi kiransa ma bazai taɓa jiyowa ba ballantana ya amsa, kuma ganin Shatu a matsayin matarsa kaɗai ya isheta babban darasi, domin ita kanta ta sani ko da gami bazata haɗa kanta da ita ba, balle kuma tayi tunanin zata so haɗa matsayinta da nata.
Dan haka bazata taɓa raudarar kanta da zuciyarta ba dole tayi ƙoƙarin goge mafarkinta na son komawarta gidan Ya Azeez, domin ita kanta ta sani wutsiyar raƙumi ta riga da tayi nesa da ƙasa, dole tayi haƙuri ta fuskanci rayuwarta ta yanzu.


Wani irin bugawa Shatu taji zuciyarta tayi, saboda ita sai a yanzu ne ma take tunawa da labarin Fadwa da Mamanta da Ya Azeez ɗin ya taɓa bata.
Ganin kuma irin kallon da Fadwan ke mata ne yasa ta ɗago kai ta watsa mata harara kana ta saki tsaki ƙasa ƙasa, tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, yayinda a kuma gefe guda na zuciyarta take mitar Allah ya gani da tasan cewa idan suka zo zasu samu wannan abar a gidan da babu abinda zaisa ta yarda mijinta yazo, saboda ita in ba dole bama bata yadda za'ayi Fadwa ta ƙara ganin mijinta koda ko akan hanya ne sai dai ko a hoto, shima a hoton inda hali sai ta gogesa a inda tasan zata iya gani ɗin.


Shiko Abba gyara zamansa yayi lokaci ɗaya yana bin kowa da kallo kafin kuma ya maida kallonsa kan Fadwa da har lokacin take ta kallon Shatu kamar zata haɗiyeta yace "Kunga dai hukuncin Ubangiji ko...?"
Ya faɗa tare da juyawa lokaci ɗaya ya kalli Mama data zafga uban tagumi ta tsurawa Ya Azeez da Shatu idanu tana tsiyayar hawaye, kafin ya ci gaba da cewa "Dama haka Allah ke ikonsa ya kuma wanzar da lamarinsa yanda yaga dama babu kuma mai ce masa a'a, shiyasa hausawa ke cewa duk abinda ya baka tausayi wata rana shi zai baka mamaki, haka kuma duk abinda ya baka mamaki wata rana zai baka tsoro.
To kunga dai yadda Allah ya juya lamarinsa akan AbdulAzeez a lokacin da baku taɓa zato ko tsammani ba, shiyasa akeso duk halin da kaga bawa a ciki walau daɗi ko akasinsa karka taɓa tunanin zai ɗore masa, domin shi daɗi baya taɓa ɗorewa haka wuya ma duk tsananin da zaka tsinci kanka a cikinta akwai lokacin da Allah zai kawo maka ɗauki ya yaye maka halin ƙunci da baƙin cikin da kake ciki..dan haka karka sake kaga wani a cikin wata matsala ko wani mummunan yanayi kayi zaton zai ɗore a cikinsa har abada, domin duk wanda kika gani a duniyar nan Allah yasan da zamansa, haka kuma duk a halin ƙunci da baƙin cikin da mutum zai tsinci kansa a ciki to akwai ranar da komai zai wuce har ya zamo kamar bai taɓa faruwa ba.
Kai dai ka riƙe Allah kawai ako wane irin hali zaka tsinci kanka aciki, ka kuma saka a ranka cewa shine yake badawa a duk lokacin da yaso ya kuma kwace a lokacin da yaga dama, kuma babu wanda ya isa ya tuhumesa don me...saboda haka idan har ka kaɗaita Allah ka kuma riƙe wannan to tabbas zaka zauna lafiya a duniya babu abinda zai dameka..."
Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana kallon Mama da Fadwa da tunda ya fara maganar hawaye ke faman zubo musu babu ƙaƙƙautawa.


Girgiza kai kawai yayi kafin ya ci gaba da faɗin "Tun lokacin da kuka dinga nuna ƙiyayarku ƙarara akan AbdulAzeez da halin daya tsinci kansa a ciki nake ta son nusar daku amma kuka nuna min kunyi nisa, bazaku taɓa jin kirana ba.
Wanda kuma a lokacin so nayi in tunasar daku sannan in tuna muku abinda kuka manta, amma kuka nuna min ni bansan komai ba, dan haka bazaku taɓa saurarata ba, shiyasa daga ƙarshe nima na ƙyaleku kawai na zuba muku idanu, gashi kuma yanzu wa gari ya waya...?"
Ya tambayesu fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonsu.
Bai kuma basu zarafin magana ya ci gaba da faɗin "Lokaci guda dukkanku kuka nuna kun manta taimakon da mahaifinsa yay muku lokacin da yake raye, sannan kuka rufe idanuwanka kuka nuna tamkar baku taɓa saninsa ba a rayuwarku, alhali ku kanku kun sani mahaifinsa yayi mana komai a rayuwa, amma daga baya da Allah ya jarrabesa sai kuka shafe komai kuka manta da duk abubuwan da suka faru a baya, sannan kuka rufe idanuwanku ku a dole kanku kawai kuka sani baku san kowa ba..."
Sai ya girgiza kai kana kuma ya cigaba da faɗin "Sai gashi da yake shi Allah ba azzalumin sarki bane sai dai kai ka zalunci kanka, cikin lokaci ƙanƙani ya juya duk wasu al'amura ta yadda baku taɓa zato ko tunanin zasu kasance ba..."


Nan ya fara basu labarin abubuwan da suka faru tun daga kan komawar Ya Azeez Kano da zama, da fara kasuwancinsa zuwa shagunan daya buɗe masa anan garin Kaduna da motar da ya siya masa, da farkon haɗuwarsa da Shatu har zuwa aurensu babu abinda ya ɓoye musu, sai gashi tun Mama na zaune har ta koma jikin bango ta jingina tana sauraren Abba.


Fadwa kuwa sai kuka take har da shassheƙa, Imaan ko ta rafka uban tagumi tana ta kallonta.
Ya Azeez da Shatu kuwa ido kawai suka tsura musu suna ta kallonsu.
Har ya kai ƙarshe Mama da Fadwa kuwa kuka suke tamkar ransu zai fita.


Abba kuwa share hawayen da suka cika masa idanu yayi, kana ya ci gaba da faɗin "Cikin hukunci da buyawar Ubangiji sai gashi Allah ya dubi zuciyarsa da maraicinsa, da kuma kyawawan halayensa na kirki ya buɗe masa kaɗan daga falalarsa da rahamarsa lokaci guda ya mayar dashi abun kwatance ta yadda wani daga cikin mu bai taɓa zato ba balle tsammani.
Shiyasa ko a baya lokacin da abubuwan suka dinga faruwa nayi ta ƙoƙarin inga na fahimtar daku kun gane amma ina sam kuka ƙi saurarata, shiyasa na ƙyaleku duniya ta fahimtar daku ta kuma bi daku ta yarda zaku fi ganewa, sai kuwa gashi cikin hukuncin Ubangiji duk abinda kuke zaton kuma bashi ɗin ne ya faru a kanku ba, sai wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login