Showing 3001 words to 6000 words out of 113443 words

Chapter 2 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7580

safiya a gidana amma bana samu...." Ta karashe faɗa cikin takaicin tuna abun.


Rabi ta kwalawa kira tana zuwa tace ta kwashe komai ta gama jikin Rabi na rawa ta kwashe komai zuwa kitchen domin yadda Fadwa ke tafiyar dasu ko Hajiya Labiba da ta ɗauke su aikin albarka shiyasa dole suke kiyaye mata.


Fadwa tafi awa ɗaya da zuwa kana taji takun takalma faga sama ana saukowa ta ɗago idanunta ta sauke cikin na Hajiya Labiba da mijinta Alhaji Zayyanu Wakili suna riƙe da hannun juna Hajiya Labiba farar mace alkyabbar mata jikinta cikin kayan alfarma wuyanta da hannayenta cikin gwala gwalai, haka ma mijin nata cikin shigar gezner fara tas mai kyau da yarari.


Sai da suka sauko kana Hajiya Labiba ta lura da Fadwa cikin mamaki tace "Lah Habibi kalli Fadwa..yaushe kika zo ban sani ba...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta da mamaki.


Fadwa ta gyara zama tana faɗin "Sannun ku da fitowa..Alhaji barka da safiya..." Ya amsa cikin sakin fuska yana faɗin "Yauwa Hajiya Fadwa sannu da zuwa, shine kuma kika zo baki yi magana ba kike zaune ke kaɗai..." Kan Fadwa na ƙasa kamar wacce take gaban ubanta tace "Ahh ba komai Alhaji...ai da yake ba yanzu zan tafi ba..."
Hajiya Labiba tace "Haba ƙawata ai ko da haka da sai ki kirani a waya kice kin iso...."


Fadwa Tace "Ayi haƙuri ƙawa..." A tare suka saka dariya mijin Hajiya Labiba ya juya yana faɗin "Shikenan ni zan fita..Fadwa agaida gida...." Da sauri Fadwa tace "Adawo lafiya Allah ya tsare ya kiyaye hanya...." Cikin farin ciki yace "Ameen Allah yasa..." Hajiya Labiba ta kalli Fadwa tana faɗin "Ƙawata bari na raka Habibi na dawo Rabi kuwa ta kawo miki abun karyawa...?"


Fadwa tace "Eh..ta kawo min har naci..." Hajiya Labiba ta juya tana faɗin "Ok ina zuwa bari nayi rakiya in dawo...."


Fadwa ta bita da kallon sha'awa ji take dama ace itace Hajiya Labiba da tafi kowacce mace dacewa duniya da lahira.






















*Aisha Alto...*
[12/23, 10:15 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI..*


*Wattpad: Aishaalto09*


__________________________


*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*


*SADAUKARWAR SO!!!*


*Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!*


*Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!*




Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...?


Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku:


*Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*
*KO*
*Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488*


*Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574*


Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝


_____________________________






2️⃣




Hajiya Labiba bata daɗe ba sai gata ta dawo gefen Fadwa ta zauna tana faɗin "Ya akayi ne ƙawata yau na ganki wata iri dake kamar baki da lafiya...?"


Ajiyar zuciya Fadwa ta sauke tana ƙara bin Hajiya Labiban da kallo wacce ta tsargu da kallon da take binta dashi ta ƙara kallon kanta kafin tace "Ya dai Fadwa...? Da matsala ne...?"


Fadwa ta ƙada kai tana faɗin "Ke kam Labiba ta ina kika haɗa hanya da wata damuwa ballatana matsala..? Ai matsala da damuwa tana ga irin mu talakawa waɗanda suka taso cikin talauci kuma suka kare a cikinta Labiba..."


Hajiya Labiba tayi murmushi kawai domin indai ira iran waɗannan maganganun ne ta saba da jinsu a bakin Fadwa duk sanda tazo gidanta ko kuma suka haɗu a wani waje.
Kai ta kaɗa tana faɗin "Zaki fara ko ƙawata...? Ni banga wani talaucin da kike kira ma kanki ba Azeez ɗinki fa cikakken namijin duniya ne duk da bai dashi bai zauna ba yana neman na kansa kuma dai-dai gwargwado yana miki iya ƙoƙarinsa kece dai bakya gani kike kushewa Fadwa..."


Wani ƙaton tsaki Fadwa taja tana ƙara gyara zama lokaci ɗaya tana faɗin "Haba ƙawata ya kike son koda yaushe ki dinga bin bayan Ya Azeez ne alhalin kinsan komai me yake min...? Me yake dashi..!? Kalle ki fa ƙawata kalli gidanki kalli mijinki..? Ki duba da kyau ki ga irin rayuwar da kike ciki zaki taɓa haɗani dake ni da nake auran faƙirin matsiyaci mai tuƙin keke napep wanda saiya fita ya gama gararambarsa akan titi sannan zai samo na sakawa a bakin salati, ta ina zaki haɗa kanki dani keda kike kwance komai sai ƴan aiki sun yi miki store ɗinki cike da kayan abinci nau'i nau'i kala kala sai, sai kiyi shekara ma baki san babu ba...."


Ta faɗa cikin bayyana tsantsar takaicin da take ciki, Hajiya Labiba tayi murmushi tana faɗin "Kina da damuwa Fadwa kada fa ki manta ko hannayenmu ba dai-dai suke ba Fadwa wani yafi wani ne kai kuma kafi wani... A kullum ina ƙara gaya miki ki daina faɗin haka, a hakan da kike raina Azeez ɗin naki mata nawa ki kafisu dace da jin daɗi Fadwa...! Wani irin bauta ne Azeez baya miki, nifa da kaina nasha zuwa gidanki naga ya dage yana miki aiki harda wankin kayan sawanki cangal bakya mai Fadwa ko ta wannan fannin bazaki godema Allahn daya baki miji mai haƙuri da kuma neman na kansa ba, uwa uba Wadatar Zucci, sai fa ya samu kuɗi keda kanki kike faɗa min bai ma kansa komai ba ya kwashe ya baki kayan nan kina dasu dai-dai gwargwado na shiga ƙawaye ni kaina na gaya miki in kina da wata mtsala ki sameni kai tsaye Fadwa wallahi zan taimaka miki indai bai fi ƙarfina ba amma don Allah kidaina faɗin irin waɗannan kalaman ga mijinki hakan ba dai-dai bane sam bana jin daɗin jin hakan...."


Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana dafa kafaɗar Fadwa wacce ta haɗe rai tana wani tsuke fuska Hajiya Labiba ta girgiza kai tana faɗin "Kinji dan Allah ƙawata...?"
Fadwa ta gyaɗa kai tana faɗin "Naji shikenan..Aike daman baki son laifin Ya Azeez bansan dalili ba...." Hajiya Labiba tace "Bai da wani aibun da zaki zauna kina zaginsa ne Fadwa..mutum ne nagari kinsani nasani Azeez ya kai duk inda ake neman namiji mai zati da kyawawan hallaya..." Fadwa ta saki ƙaramin tsaki tana faɗin "Amma kuma bai da ƙumbar susa ko...? Shi kaɗai yayi mai cikas nima ban ce yana da wata illah ba...."
Hajiya Labiba tace "Oh....ƙawata baza dai ki daina maganar ba ko...?" Fadwa tace "Ni me nace...? Gaskiya ce kawai na faɗa namiji in har ba shi da ƙumbar susa ai ni bana masa kallon cikakken namiji wallahi..."


Hajiya Labiba tace "Shikenan...Yanzu ki tashi mu shiga ciki na ɗauko miki ankon ƙanwar Lubna wanda na siya mana ni dake...." Fadwa ta washe baki tana faɗin "Da gaske ƙawata....? Kai Allah ya barni dake ta hannun damana, shiyasa duk cikin ƙawayen mu nafi sonki saboda baki manta zaman tare ba kullum cikin alheri kike ba irin su Lubna ba, suna da dukiyar amma ba hannun alherin...." Ita dai Hajiya Labiba dariya kawai take tana faɗin "Nidai tashi mu shiga ciki...."


Fadwa ta miƙe tana ɗaukan jakanta da mayafinta tabi bayan Hajiya Labiba kichin suka fara shiga ta bama Rabi umarnin tayi musu ferfesun kayan ciki ta kawo musu suna sama, Rabi ta amsa cikin ladabi kana daga nan suka haura sama bedroom ɗin Hajiya Labiba mai kama da aljannar duniya kan lafiyayyen gadonta suka baje Hajiya Labiba ta buɗe ƙaton wardrobe ɗinta ta ɗauko wata babbar jaka ta ajiye ta gaban Fadwa dake kan gado tana faɗin "Gashinan harda jaka da takalmin da zamu saka wajen Dinner, less ɗin Dinner ɗin na ba wani telan Hajiya Lubna ya ɗinka mana. Less ɗin yinin biki kuma gashinan sai ki kaima telanki na baki kuɗin ɗinkin...." Ta faɗa tana zama kusa da ita.


Fadwa baki yaƙi rufuwa, tana buɗe kayan tana jinjina kai ganin tsadan kayan da haɗuwarsu yasa ta sakin wani ƙayataccen murmushi cikin fara'a ta ɗago kanta tana faɗin "Kai ƙawata...Na gode ƙwarai....Bansan da wace kalma zan gode miki ba wallahi...." Hajiya Labiba na buɗe ƙaramar jakarta dake gefen gadon tana faɗin "Haba ƙawata..Mun wuce wannan stage ɗin faa...." Fadwa dai sai santi take Hajiya Labiba ta miƙa mata rafar ƴan dubu dubu sababbi fil tana faɗin "Ga 20k nasan zai isheki kuɗin ɗinkin...."


Fadwa ta wangame baki tana kallon Hajiya Labiba duk da ba yau ta saba mata kyautan kuɗaɗe ba amma abun akwai jin Kunya kullum kai sai dai ka zauna abaka ba dai kai kabama wani ba, nan da nan yanayin fuskarta ya sauya ta kasa saka hannu ta karɓi kuɗin ganin haka yasa ta kama hannunta ta damƙa mata tana faɗin "Bana son wata magana...."


Fadwa ta kaɗa kai tana faɗin "Dole zanyi magana Labiba kifa duba wannan rayuwar tare fa muka taso tun muna yara mukayi makaranta tare amma yau kalli rayuwarki kullum ke ke bani badai ni na baki ba haka zan dauwama Labiba ba wani cigaba...?"


Hajiya Labiba tace "Fadwa dan girman Allah ki daina faɗin haka kinsan me Allah zai yi agaba ne...? Ƙilama wata rana ke matar gwamna ce fa Fadwa babu abinda Allah ba yayi da bayinsa..." Taɓe baki Fadwa tayi tana faɗin "Uhmm..Daman wannan mafarkin naki zai tabbata fa...? Sai dai nasan bazai taɓa zama gaskiya ba in ba auran Ya Azeez dake kaina ya saukemin ba ban ƙaryataki ba domin wallahi ko matar gwamman garin nan da nake gani a poster bata fini kyau da cika ba kema kanki kin sani Ya Azeez matar manya ya samu a sama ya aura...." Dariya Hajiya Labiba ta sheƙe dashi kafin ta dakata tana faɗin "Hakane ƙawata...amma shima kansa Azeez ɗin ai ba baya ba..kema kinsani dan ko kyan banza ya fiki..."


Yamutsa fuska kawai Fadwa tayi bata ƙara magana ba, sanin gaskiya Labiban ta faɗa kawai sai ta bangarar da zancen suka ci gaba da hirar bikin ƙanwar Hajiya Lubna da zai gudana nan da sati biyu. Suna nan zaune suna hira Rabi ta shigo musu da farfesun nan suka sauko suka ci suka ƙoshi suka ƙara komawa suka ci gaba da hirar su sai da aka kira sallah suka tashi sukayi kana suka sauko ƙasa lokacin su Rabi sun gama lunch nan suka ci farar shinkafa da miyar kaji Fadwa yadda kasan gidanta haka ta saki jiki ta baje tama manta da wani wai miji ko gidanta.


Sai bayan la'asar kana suka fita da Hajiya Labiba zuwa kasuwa ta rakata ta siya kayan kwalliyanta sun ƙare nan itama Hajiya Labiban ta siya mata daga nan ta rakata saloon dukkansu aka wanke musu kai suna fitowa ana kiran sallar magriba da motan Hajiya Labiba ta ɗauketa zuwa gida suna tafe suna hira cikin tsantsar shaƙuwa da ƙawancen su mai cike da yarda da juna.


Tun daga nesa suka hangesa tsaye a ƙofar gidan ya jingina jikin ƙofar gidan ya harɗe duka hannuwansa a aljihu lokaci bayan lokaci yana duba agogon roban dake ɗaure a hannunsa yafi awa ɗaya da dawowa, sai da yaje ya kai kekensa gidan bulo ɗin da yake ajiyeta kana ya nufo gidan sai dai kamar kullum yau ma gidan yana kulle ne ganin zai yi zaman banza yasa ya gangara masallaci yayi sallar magriba ya sake dawowa yana zamam jiran Fadwa amma shiru bata dawo ba mutane sai wucewa suke suna binsa da kallo in da sabo sun saba ganinsa kullum yana tsaye zaman jiran Fadwa domin ba ranar da bazata fita ba yayi yayi ta bashi key ɗin ƙwadon amma Fadwa taƙi bashi tafi son kullum ya dinga zaman jiranta a ƙofar gidan kamar maigadi.


Sai da aka kira Isha'i kana ya ƙara komawa masallacin yayi sallar Isha'i ya sake dawowa ya iske har lokacin bata dawo ba, ransa ya ɓaci sosai yaji ya kamata Fadwa ta gane yana haƙuri da ita ne kawai saboda iyayensu amma ita tayi kaɗan ta zauna tanayi mai wannan cin kashin.


Hajiya Labiba ta waigo gefenta tana kallon Fadwa da tunda ta hango Azeez ta haɗe ranta ta ɗaure fuska cikin damuwa Hajiya Labiba tace "Kinga abunda nake ta gudun miki ko Fadwa...? Ga mijinki can ya dawo kuma daga gani ya daɗe da dawowa, Allah kaɗai yasan iya tsawon lokacin daya ɗauka yana zaman jiranki bakya gida ina amfaninsa....?"


Fadwa ta saki tsaki tana faɗin "Toh sai me Labiba..nace sai me...? Ko ina gidan me zan mai...? Kada ki damu daman ya saba zaman jiran...." Ta faɗa cikin halin ko in kula Labiba ta girgiza kai kawai bata ƙara magana ba har ta ƙarasa ƙofar gidan Fadwa inda Azeez yake tsaye yana kallonsu tun daga nesa ya shaida motar Hajiya Labiba ce ƙawar Fadwa kuma yana da tabbacin Fadwan na ciki.


Sai da suka ƙaraso gabansa ya ɗauke kansa kamar bai gansu ba har dukkansu suka buɗe motar suka fito Fadwa na riƙe da ƙatuwar ledarta tana saɓa jakarta a kafaɗa cikin dakiya ta kalli Hajiya Labiba tana faɗin "Na gode ƙawata sai munyi magana..." Hajiya Labiba ta kaɗa kai tana faɗin "Shikenan...Barka da dawowa Azeez..? Mun wuni Lafiya...?"


Ta fada tana kallon Azeez ɗin daya kalli can gefe guda kamar bai gansu ba jin Hajiya Labiba na gaishesa yasa ya waigo cikin ɗan sakin fuska yana amsa mata da cewa "Yauwa...sannu Labiba Alhamdulillah..." Ya faɗa yana sauke hannayensa daga ƙirjinsa kana lokaci ɗaya ya tashi daga jikin ƙofar ya matsa gefe.


Labiba taji tausayinsa ya kamata da takaicin ƙawarta Fadwa wacce ke tsaye tana wani ɓata fuska cikin sanyin jiki Hajiya Labiba tace "A ƙara haƙuri dan Allah ni na tsaidata tun ɗazu ta rakani kasuwa..." Cikin murmushinsa na koda yaushe yace "Ah haba ba komai fa...." Labiba ta kaɗa kai tana faɗin "Na gode..sai da safe ƙawata sai munyi waya..."


Ta faɗa tana buɗe murfin mota ta shiga Fadwa ta ɗaga mata hannu dukkansu suna tsaye ba wanda ya motsa har motar Hajiya Labiba ta ɓace daga layin, kana Azeez ya maida kallonsa kan Fadwa wacce take wani cika tana batsewa kamar wacce akayi ma wani laifi bai ce mata komai ba illah haɓa daya riƙe yana binta da kallon mamaki ita kuma tana ganinsa yana mata wannan kallon yasa taƙi yarda su haɗa ido ta fara laluban jakarta domin ɗauko makulli tana ɗaukowa ta matsa jikin ƙofar tana faɗin "Bani waje na buɗe ƙofar mana...."


Azeez bai ce komai ba ya ƙara matsawa yana ƙara binta da kallo, domin in dai halin Fadwa ne ko Abba ba zai gaya mai wacece ita ba. Yafi kowa saninta in bata da gaskiya haka take wannan borin kunyan bai mata magana ba har ta buɗe gidan ta tura ƙofar ta shiga bata ji takunsa ya biyo ta, sai ta tsaya lokaci ɗaya ta juyo tana kallonsa yana tsaye ya ƙurawa wani waje ido cikin ɗan tausayinsa daya shigeta tace "Bazaka shiga gidan bane...?"


Bai kalleta ba ya sauke numfashinsa ya raɓa ta gefenta ya shige gidan ya barta nan tsaye, da kallo ta rakasa kafin taja ledarta ta mara mai baya, ɗakin ma sai da ya jirata ta buɗe kana ya shiga ko ta kanta bai ƙara bi ba ya cire kayansa ya fita ruwa ya ɗiba ya shiga ya watsa ya fito yana shiga ɗakin ya sameta tana ɗaga jaka da takalmin da Hajiya Labiba ta siyamata ganin ya shigo ne yasa ta kallesa tana nuna mai kayan lokaci ɗaya tana faɗin "Kaga abun arzikin da Hajiya Labiba ta min ko...? Less biyu ta ɗinka min ɗaya na can wajen ɗinki ta bada a ɗinka mana ga ɗaya nan kuma zan kaiwa Idris telana, na bikin ƙanwar ƙawarmu ne Hajiya Lubna...."


Yana daga gaban jakar kayansa yace "Kin gode...." Daga haka bai ƙara cewa komai ba ya zaro wata baƙar jallabiyarsa ya zura, tura baki Fadwa tayi tana maida kayanta cikin ledar tana faɗin "Uhmm koma mutum yace an gode koma kar yace ban damu ba...Komai dai baƙin cikin tanda sai munci waina ni ƙashin arziki gareni ko ana so ko ba'a so ehe....!


Duk yana jinta amma bai ƙara cewa komai ba ya zura silifas ɗinsa bayan ya laluba aljihun wandon daya cire ya ɗauki kuɗi ya fice ta rakashi da taɓe baki har ta gama maida kayanta cikin leda ta diɓi ruwa taje tayo wanka dayake ma garin da ɗan zafi zafi tana fitowa ta saka kayan barcinta tabi lafiyan gado domin cikinta acike yake dam da daɗin dataci daga gidan Hajiya Labiba ta kwanta ba daɗewa taji dawowarsa da rufe gidan da yayi tana jinsa ya shigo ɗakin ya kulle ƙofa daga kwancen take kallonsa ta hasken fitilar wayarsa domin ta kashe fitilan da zata kwanta, ledar daya shigo da ita guda biyu ya tura ɗaya can gefe ɗayan kuma ya jata ya buɗe daga kwancen ta hango tsire a cikin takarda da hanzari ta miƙe lokaci ɗaya ta dirko daga kan gadon sai gata gabansa cikin washe baki tace "Shine ko ka tadani kasan fa ina jin yunwa...."


Cikin mamaki yake kallonta ta janye ledar gabansa har ta fara tura tsiran bakinta cikin sanyin muryarsa ya tsame hannunta yana faɗin "Na zata kin ci kin ƙoshi daga inda kika fito...?" Tana cika bakinta da naman tace "Eh naci na ƙoshi amma kasan bana bama nama kunya...." Bai ƙara mata magana ba ya miƙe bayan ya tura mata ɗayan ledar Youghrt ɗin dake ciki kaɗai ya ɗauka ya miƙe yana faɗin "Gashi nan na bar miki duka in zai isheki ki cinye...."


Ba kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login