Showing 78001 words to 81000 words out of 113443 words

Chapter 27 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7547

kuma sai gurin ƙarfe 12:20pm, kafin yayi mata sallama ya tashi ya tafi.










*************






Acan Kano kuwa ta ɓangaren su Fahad yanzu komai ya gama daidaita, domin zuwa yanzu hankalinsa a kwance yake tunda amaryarsa Basma ta tare, bai da wata sauran damuwa kuma.
Gabaki ɗaya hankalinsa yanzu kacokan ya tattarasa ne gurin shirye shiryen buɗe shagunan Ya Azeez da kammala shirin tafiyarsu China.
Wanda duk wani shiri da ya kamata suyi Abba ya riga da ya gama musu sai ɗan abinda ba'a rasa ba kuma wanda sune zasuyi da kansu, amma hatta da Visa da Epassport ɗin Ya Azeez ɗin gaba ɗaya suna hannu an riga an gama haɗawa, sai zaman jiran lokacin tafiyar tasu kawai suke.






************




A ɓangaren Shatu kuwa yau tunda wuri ta gama shiryawa domin tafiya makaranta, saboda yau ɗin ƙarfe 9am. Suke da text ɗin Sociology.
Bayan tayi breakfast ta gama ne kuma ta miƙe ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta yayinda take duba haɗaɗɗen agogon fatan dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, ƙarfe 8:30am.
A gaggauce ta sauko daga dinning area ɗin zuwa cikin falo inda Ummi da Zahra ke zaune ta ƙaraso inda suke, a hankali ta ɗan duƙa tare da faɗin "Ummi zan wuce saina dawo..." Ta faɗa tare da nufar ƙofa zata fice, ganin haka yasa Zahra miƙewa da sauri bayan ta ɗauki laptop ɗinta da jakarta tana cewa "Aunty Shatu jirani dan Allah tare yau zamu tafi...."


Ta faɗa tare da nufar ƙofar da sauri itama tana faɗin "Ummina bari muje sai mun dawo ayi mana addu'a..." Ta ƙare maganar tana bin bayan Shatu da tuni ta fice daga falon.


Kai Ummin ta jinjina, tare da ɗan ɗaga murya ta yanda zasu iya jiyota tace "Allah ya tsare ya dawo min daku lafiya, agaishe da ƴan makarantan..."


Da "Ameen Ameen..." Zahran ta amsa kana tasa kai ta ƙarasa ficewa daga cikin falon.
Suna fitowa harabar gidan nasu kuwa suka iske Ribadu direbansu tsaye a jikin mota yana jiran fitowarsu.
Ganinsu ne kuma yasa da sauri ya buɗe musu gidan baya, suka shiga suka zauna, sai da ya rufe kana shima ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna, a hankali kuma ya tada motar maigadi ya wangale musu gate yaja suka fice daga cikin gidan, kai tsaye suka nufi BUK, kasancewar acan ne dama dukkansu suke karatu sai dai kowanne da ɓarayinsa, inda Shatu ke 400 level dan tana matakin ƙarshe ne na kammala B.Sc ɗinta.
Yayinda ita kuma Zahra take 100 level, wanda ita sai yanzu ne ma ta fara.






**********




Fadwa ce zaune a tsakar ɗakin Mamansu, inda ta tasa robar soyayyar awara da yaji a gabanta tana ci sai kwalban coke mai sanyi dake aje a gefe guda, ci take a hankali yayinda kuma take korawa da sassanyan coke ɗin jifa jifa kuma suna ɗan taɓa hira sama sama da Maman, ɗago kai tayi a hankali tana kallon Maman dake zaune a ƙofar ɗaki tana jajjagen kayan miya a turmi, ganin kuma ta ɗauki daddawa ne zata saka a turmin yasa Fadwan ta wani kwaɓe fuska kafin cikin nuna ƙyankyami tace "Haba Mama me kuma za'ayi da wannan abun mai warin tsiya da naga kina ƙoƙarin sakawa a turmin...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana toshe hanci tare kuma da yi mata nuni da daddawar.


Fuskar Mama ba walwala tace "Zan jajjaga ne mana Fadwa, kinsan miyar kuka zamuyi kuma kuka ba daddawa ai bata shawuwa da daɗi, sai dai asha da haƙuri..."
Ɓata fuska Fadwa tayi tana faɗin "Miyar kuka kuma Mama, yau ma tuwon za'a ci kenan...?"
Kauda kai tayi da sauri tana yatsine fuska kafin tace "Haba Mama! Kullum tuwo kullum tuwo..tsakani da Allah ku ko gajiya bakuyi da cin tuwo, kullum kuci da daddare sannan ku ɗumama kuma da safe ku ci...? Nidai har ga Allah bazan iya ba na gaji da cin tuwo atoh..."
Ta faɗa kai tsaye ko a jikinta.


Galala Mama take kallonta kafin tace "Toh ya muka iya Fadwa..? Ya zamuyi da ranmu..? abinda muka samu ya kawo kenan kuma da babu ai gwara ba daɗi, amma wallahi ni karan kaina na gaji da cin tuwon nan kullum mu kenan cin ƙarza sai kace wasu ƴan iska, bamu da halin sauya girki kullum mu kenan girka abu guda, idan kinga mun samu canji to ya ɗan yi buga bugarsa ne ya samo wasu ƴan kuɗaɗen sai ya auno mana shinkafa ƴar Buhari mu dafa, amma in ba haka ba kuwa tuwon nan shi zamuyi ta ci kullum, ranar da ba'a samu na yin tuwon ba kuma kowa sai yasha ruwa ya kwanta..."


Wani irin kallo Fadwan ta aika mata tana faɗin "Wallahi yau bazamu ci tuwo ba Mama, dan ni na gaji tsakani da Allah, jiya kun bani tuwo da daddare an bani da safe, sannan yau kuma ace za'a ƙara min..? A'a bazan iya ba wallahi wannan ai sai ruwan jikin mutum duk ya tsotse idan yana cin irin wannan cimar..."


Dariya Mama tayi kafin tace "Toh ya muka iya mu kam Fadwa..? Haka nan muke daurewa mu ci, kafin zuwa lokacin da Allah zai haɗaki da babban rabo muma mu huta..."
Da sauri Fadwa tace "Aiko insha Allahu lokacin ya kusa tunda anyi mai wuyar na rabu da wannan mummunar ƙaddarar..." Ta faɗa tare da tashi taje ta ɗauko jakarta ta buɗe ta zaro dubu uku aciki, kana ta mayar da jakar ta rufe ta ajiye, ƙarasowa tayi gurin Mama ta miƙa mata kuɗin tana faɗin "Gashi ayo cefane a dafa mana shinkafa da miya da nama, yau muma mu samu canji..."


Da rawar jiki Mama ta saka hannu ta karɓe kuɗin tana washe baki cike da tsantsar farin ciki, kafin tace "Masha Allah lallai yau zamu ci daɗi a gidan nan, kai Allah yayi miki albarka ya rabamu da talauci, bari ki gani in tashi inje inyo mana cefanen da kaina dan ma kar in aika su Amatu suje suyo shirme..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana zare taɓarya a turmin ta jingine, kafin ta miƙe tsaye da sauri tana kakkaɓe jikinta, kana ta leƙa ɗaki ta ɗauko hijabinta dake sagale a ƙofa ta zura a gaggauce ta juya da sauri ta fice daga gidan.






********** **********






2:30pm.


Shatu ce zaune tare da ƙawayenta akan wasu fararen kujeru dake ƙarƙashin wata ƙatuwar bishiya a cikin makarantar tasu suna hira, wanda kuma fitowarsu daga Lecture Theatre ɗin kenan bayan sun kammala text ɗinsu.
Husna Baita ce a gefenta suna magana akan text ɗin da sukayi yau ɗin, yayinda Basma Jada kuma ke zaune daga gefe guda da waya manne a kunnenta tana magana ƙasa ƙasa wacce dukkansu babu mai jin abinda take cewa a wayar, sai faman wani narkewa take tana shagwaɓe fuska.
Juyawa sukai lokaci ɗaya suka ɗan kalli juna kana kuma suka sake juyawa a tare suka kalleta, kafin kuma suka saki tsaki lokaci guda a tare suna harararta, wanda ita ko kaɗan bata ma san sunayi ba, dan hankalinta kacokan yana kan wayar da take da mijinta, tana ta wani narke mai tana zuba mai shagwaɓa da sangarta.


Zuba mata ido gaba ɗayansu sukayi suna ta kallonta, kafin Shatu ta saki tsakin takaici ta miƙe tsaye lokaci ɗaya tana ɗaukar jakarta da wayarta ta juya tana faɗin "Nidai nayi nan sai munyi waya Hussy..." Ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa, saurin miƙewa itama Husnan tayi tana faɗin "A'a jirani mana nima ai ba zaman zanyi ba..."
Ta faɗa tare da ɗaukar jakarta itama ta rataya, kafin ta kalli Basma data zubo musu ido tana so taga iya ƙarshen rashin mutuncin su, ganin da tayi da gasken sukeyi wucewar zasuji su barta ne yasa ta katse wayar da sauri tana kallonsu tace "Wai meye nufinku ne, naga duk kun ɗauki jaka kuna shirin tafiya ku barni anan ne, ban gane ba...?"


A karkace Shatu ta juyo ta kalleta kafin tace "Me kika gani halan...?"
Basma tace "Wucewa mana naga zakuyi baku min magana ba..."
Tsaki Husna taja kafin tace "Ai munga kina ta waya da angonki ne shiyasa, bama so mu takura miki ne dan karmu shiga hakkinku..." Ta faɗa kai tsaye tana harararta.


Tsaye Basma ta miƙe lokaci ɗaya kuma tana fashewa da wata irin dariya kana tace "Kutt lallai ma yaran nan, oh dama saboda ina waya da love shiyasa kuka haɗa kai zaku tafi ku barni..? To wai waya hanaku yin auren nan ne kuma kuje kuji yadda akeji...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa musu harara.


Ɗaure fuska Shatu tayi tana faɗin "Kisha kuruminki amaryar ƙarshen zamani muma mun kusa zuwa dai-dai gurin insha Allahu, me kike ci na baka na zuba ne..? Ai wallahi ko dan saboda gorin nan da kike mana kullum ya zama dole muma muyi zuciya mu fito da mazaje ayi mana aure, dan muje muji abinda kikeji da yasa duk kika wani susuce kika zama wata mara kunyar ƙarfi da yaji..."


Tsaye kawai Basma tayi tana kallonsu, dan ita fa Allah ya gani mantawa take da kowa da komai in tana tare da Fahad balle har ta tuna da wasu Shatu da Husna, dafe kai tayi kafin tace "Wai laifina kuke gani ne...?"


"Of course..ba dole muga laifinki ba, gabaki ɗaya tunda kikayi aure duk kin sauya sai kita wani shasshare mu irin ke kinsan abinda bamu sani ba ɗin nan, idan ana hira sai ki ƙi saka baki, ki koma gefe ki kira mijinki kuyita hira a waya mu ki barmu a gefe irin yanzu kin wuce da sanin mu ɗin nan, haka fa kike mana iskanci kala kala sai kace a kanki aka soma aure..." Husna ta faɗa tana watsa mata harara.
Basma tace "Toh kuyi haƙuri ƙawayena na daina, amma wallahi bazaku gane bane kuma sai kun shiga kunji yadda akeji tukunna..." Ta faɗa tare da yin dariya, kana ta miƙe ta ɗauki jakarta itama tace "Ku muje Cafeteria mu ɗan ci wani abun dan Allah, wallahi yunwa nake ji sosai...."
Shatu tace "Ni dai bana jin yunwa ruwa kawai zan sha...."
Haɗa baki Husna da Basma sukayi gurin faɗin "Ok muje to..."
Haka suka kama hanyar zuwa Cafeteria ɗin suna hira suna dariya, kamar basu ne yanzu suka gama balbale juna da faɗa ba.
































*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






3️⃣1️⃣








Ƙarfe 5pm. Dai-dai Shatu da Zahra suka dawo daga makaranta a gajiye tuɓus suka shigo gidan.
Suna shigowa cikin falon kuwa Shatu tai saurin zare gyalen abayar da tayi rolling akanta, tare da faɗawa saman kujera lokaci ɗaya tana dafe kanta da take jin yana sara mata kaɗan kaɗan.


Dai-dai lokacin kuma Ummi ta fito daga kichin, hannunta riƙe da jug wanda ta zubawa Abbie juice ɗin kankana data haɗa masa aciki.


Ganinta yasa Zahra ta miƙe ta rungumeta tana faɗin "Barka da gida Ummina, ya aiki...?" Ta faɗa tana sakinta tare kuma da ƙarban jug ɗin dake hannunta ta nufi dinning area ɗin taje ta ajiye kana ta dawo.
Koda ta dawo falon kuwa bata zauna ba direct kichin ta wuce dan ta ɗan samu abun taɓawa, dan ita bata taɓa iya zama shiru ba tare data ji bakinta na motsi tana cin wani abun ba.


Shatu kuwa miƙewa tayi a hankali ta ɗauki jakarta tana faɗin "Bari inje in ɗan watsa ruwa Ummi, yanzu zan sauko..." Ta faɗa a gajiye tana ɗan yatsine fuskarta.


Kai Ummin ta gyaɗa mata kafin tace "Ok sai kin fito, nima bari in ƙarasa aiki a kichin..." Ta faɗa tare da juyawa ta koma cikin kichin ɗin, yayinda Shatu kuma kai tsaye ta wuce ta haura sama zuwa ɗakinsu dan yin wanka.





*A TAƘAICE*




Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai mutumin kirki ne kamili mai kwarjini da son jama'a, Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai su biyu ne rak a gurin iyayensu, Alhaji Muhammad da Hajiya Aisha.
Shine babba sai ƙaninsa Alhaji Abubakar da ake kira da Baffa Buba, kuma shine auta kasancewar tun daga kansa Allah bai sake basu haihuwa ba.
Asalinsu ƴan garin Mubi ne ta jihar Adamawa wanda kusan gabaki ɗaya danginsu duka suna can, inda kuma iyayensu ba masu ƙarfi bane, amma kuma sun jajirce sosai gurin basu ingantaccen ilimin addini dana zamani.
Kasuwanci ne kawai ya kawosa garin Kano, inda kuma a yanzu haka yake da manyan manyan shaguna a kasuwannin dake cikin garin Kanon.


Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai matarsa ɗaya Hajiya Khadija, haifaffiyar ƴar ƙasar Chadi ce, marainiya ce iyayenta duk sun mutu tun suna ƙanana ita da ƙanwarta Salma wacce a yanzu take auren wani babban ɗan siyasa a garin Abuja ruƙonsu ya dawo hannun kakarsu Ata, sun haɗu ne kuma da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai a bikin wani babban abokinsa Alhaji Baballe da sukaje ƙasar Chadi.


Hajiya Khadija macece mai kyaun hali da mutunta mutane, gata kamila mai dattako da sanin ya kamata, bata da ƙyama ko hantara, ita kowa nata ne.
Ƴaƴan ta biyu Aisha wacce ake kira Shatu itace babba, sai kuma mai bi mata Zahra.


Wannan kenan.








************






Duk yadda Ya Azeez yayi ƙoƙarin sakin ransa ya yakice tunanin abunda Mama da Fadwa suka yiwa Ummansa abun yaci tura, koya ya tuna irin cin fuska da cin mutuncin da sukayi mata sai yaji gaba ɗaya ransa ya baci, yaji kamar ya ƙarashe cikashewa Fadwa sauran saki biyun da suka rage su zama saki ukun cif, saboda tsabar baƙin ciki da takaicin abunda sukayi.
Ko kaɗan a ranar bai samu baccin kirki ba, saboda tsabar tunani da saƙe saƙen daya wuni ya kwana yana yi.


A haka washegari da safe kuma ya tashi da shirin tafiya Kano, dan gaba ɗaya komai na tafiyarsu ya gama kammala yau da daddare jirginsu zai ɗaga zuwa ƙasar China.


Koda ya gama shiryawa bai samu biyawa gurin Abba ba saboda baya so lokaci ya ƙure masa, a waya kawai ya kirasa sukayi sallama yay masa fatan alkhairi.
Kana ya nufi gidan Ummansa yayi mata sallama itama, kana kuma daga can direban da Abba ya turo daga Kano ya ɗaukesa suka kama hanya.




7pm.


Dai-dai kuwa tayi musu ne a Mallam Aminu Kano International Airport, inda Abba da Mami har ma da Basma sukayo musu rakiya a motarsu har Airport ɗin, sai Ibrahim dake riƙe da ƙatuwar jakar sababbin kayan Ya Azeez ɗin wanda Abba ya saka Fahad ya siyan masa su masu matuƙar kyau da tsada.
Yayinda kuma suna isa airport ɗin ko cikakken minti talatin basu yi ba, jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar China.


Wanda su Abba basu dawo ba, sai da suka ga tashin jirginsu, kana suka dawo gida tare dasu Basma wacce zuciyarta ke cike da tsananin kewa da muradin mijinta.




Su Ya Azeez kuwa sai gab da asuba jirgin ya saukesu a Shanghai Pudong International Airport.
Bayan sun sauka ne kuma suka tari taxi, Fahad ya gaya mai ya kaisu hotel mafi kusa, inda direct ya nufi wani tsadadden hotel A Marriott Hotel dasu.


Koda suka shiga cikin hotel ɗin kuwa booking ɗin ɗaki suka fara yi, kafin kuma sukayi wanka suka gabatar da sallar asuba, kasancewar kuma garin bai gama wayewa bane sosai yasa kawai kowannen su ya nemi gurin kwanciya suka kwanta bacci, saboda gaba ɗayansu a gajiye suke tuɓus.






**************




Shatu da Zahra ne zaune a babban falon gidan kowa na sha'anin gabansa, Shatu na daga gefe guda ta harɗe a saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana latsa wayarta, yayinda kuma Zahra ke kwance a ƙasan kafet ɗin dake falon da laptop a gabanta tana kallo.
Dai-dai lokacin ne kuma Abbie da Ummi ke saukowa daga saman bene inda kwannensu ke sanye da shiga ta alfarma sai zuba ƙamshi suke.
Cikin dattako suka ƙarasa saukowa cikin falon, inda da sauri Zahra ta rufe laptop ɗin da take kallon ta tashi zaune lokaci ɗaya tana ɗan sosa gefen wuyanta kafin kuma cikin yanayin rashin gaskiya tace "Barka da fitowa Abbie..."


Juyowa Ummi tayi ta kalleta, kana ta harareta tana cewa "Oh saboda baki da gaskiya shiyasa kikayi saurin rufe laptop ɗin dan kar aga abinda kike yi ko...?"
Kallonta Abbie yayi kana ya juya ya kalli laptop ɗin yana faɗin "Hala game takeyi ko...?" Ya faɗa yana kallon Ummi data wani haɗe rai tana hararar Zahran kafin tace "A'a ina wannan take da lokacin wani game, kallon films ai shi yafi shige mata zuciya yayi kane kane, dan indai zaka ganta da laptop a hannu to ba komai take yi da ita ba sai kallo, dan bana tunanin tunda aka siyan mata ita ta taɓa karatu ko wani assignment kullum cikin duba sabbin film ɗin India take da Korean Drama take, sai kace aikin da aka kawota yi kenan..." Ummi ta ƙarashe maganar cikin faɗa tana hararar Zahran.


Haɗe fuska Abbie yayi yana faɗin "Oh dama abinda kikeyi kenan..? Ashe kice asarar kuɗina kawai nake babu karatun da kikeyi...? Toh kodai aure kikeso ne ayi miki...?"


Sai lokacin ne Shatu ta ɗago kai da sauri ta kallesu, kafin kuma ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai ƙasa lokaci ɗaya tana jin faɗuwar gaba.


Zahra kuwa baki ta turo gaba a shagwaɓe tana faɗin "A'a Abbie nidai bana son aure, karatu zanyi a fara yiwa Aunty Shatu auren tukuna..." Ta faɗa tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka.


Wani mugun kallo Shatu ta watsa mata tana faɗin "Ni sa'arki ce da zaki dinga haɗa kaina dake, ko kuwa ni abokiyar wasanki ce da ana miki magana zaki kauce ki sako sunana...?"


Cike da mamaki Zahra ke kallonta, kafin ta taɓe baki tace "Ai dai dole kema zakiyi auren ko, tunda ba zamanki ba kenan a gida ba aure..."


Zaburowa Shatu tayi a zafafe tayo kanta tana faɗin "Dan ubanki ba sai ki kawo min mijin in aura ba, tunda ina wasa dake ne da zaki dinga cewa zanyi aure zanyi aure, ko kin taɓa ganina da wani saurayi ne da zaki damu mutane da maganar aure aure, sai kace a kanki nake...?"


Salati Ummi ta fara tana faɗin "Yau na banu ni Khadija, daga fatan arziki sai ya zama na tsiya..?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login