Showing 75001 words to 78000 words out of 113443 words

Chapter 26 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7557

faɗin "Na fahimceka AbdulAzeez kuma bazan taɓa ganin laifinka akan duk irin hukuncin daka yanke akan Fadwa ba, domin ina sane da duk irin zaman ƙuncin da kayi da ita na tsawon watannin nan har zuwa yanzu, saboda haka bazan sake tauyeka akanta ba. Kuma bazan taɓa ƙullatarka da wani mugun nufi akanta ba, amma tabbas banji daɗin rabuwar aurenku da Fadwa ba, domin zamanta a gidanka shine kwanciyar hankalina da farin cikina, amma babu yadda zanyi tunda aikin gama ya riga daya gama, kuma ni bazan taɓa matsa maka lallai dole saika maida Fadwa ɗakinta ba, sai dai in tayaka da addu'ar Allah ya zaɓa maka duk abinda yafi zama alkhairi a rayuwarka..."


Da sauri Ya Azeez yace "Abba dan Allah kayi haƙuri, wallahi sharrin shaiɗan ne, amma tun jiyan na maida ita ɗakinta, yanzu ma nazo ne in ɗauketa mu koma, sannan kuma in ƙara bada haƙuri..."


Girgiza kai Abba yayi cikin takaici kafin yace "Uhmm AbdulAzeez kenan, koda ka maida Fadwa zaman nan naku bazai taɓa yin dai-dai ba, domin tun farko abinda ta saba yi maka shi zata cigaba da yi, bazata taɓa sauyawa ba.
Kuma komai da kake ganin take yi daga tushe ne domin da haka ta taso, shiyasa take ganin kamar duk abinda take aikatawa mai kyau ne, kuma daga ita har me zugatan bazasu taɓa ganewa ba sai lokaci ya ƙure musu.
Saboda haka a matsayina na mahaifin Fadwa ina mai baka umarni daka janye maidata da kayi ɗakinta ka barta har zuwa ranar da tayi hankali ta gane abinda take yi sannan ta banbance idan mai kyau ta aikata ko akasinsa, sannan idan tana da wata dama ta gyarawa a lokacin sai ka maida ita ɗakinta, idan kuma babu dama sai ka ƙyaleta da abinda take ganin shine dai-dai da ita..."




A wulaƙance Mama ta kallesa dan ta gane maganganun nan duk da yake kawai tsabar cin fuska ne da neman zubarwa ƴarta da mutunci a gaban Ya Azeez ɗin, kauda kai tayi kafin tace "Ai bama zata taɓa komawa gidansa ba itama, ta barosa kenan bari na har abada, sai dai kuma abi wani sarkin, amma Fadwa kam yadda tabar nonon uwarta haka tabar auren wannan mara mutuncin wanda bai san abinda ya kamata ba..."
Ta faɗa a ƙufule tana harararsa.


Wani mugun takaicin Mama ne ya ƙara kama Abba, shiko Ya Azeez sake duƙar da kansa yayi da sauri yana ƙara jinjina halin rashin mutuncin Mama a zuciyarsa.


Haka shima Abba bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye, ya kamo hannun Ya Azeez da shima ya miƙe suka juya atare suka fice daga ɗakin.


Suna fita Mama ta bisu da wani ƙaton tsaki tana faɗin "Aikin banza kawai aikin wofi, wai sharrin shaiɗan ne..yo akwai wani babban shaiɗani ne bayan kai shege almuri, mai ƙirar samudawan zamanin daa, wai yanzu ma nazo ne in ɗauketa mu koma sannan kuma in ƙara bada haƙuri...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana kwaikwayon maganar Ya Azeez ɗin, kafin ta miƙe tana cigaba da mita tana faɗar maganganu, ta zare hijabin sallar dake jikinta ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakinsu Ilham.
Tana shiga ta samu Fadwa har lokacin tana ƙudundune a saman ƴar yaloluwar katifarsu Ilham ɗin tana ta sharar bacci abinta hankali kwance, wanda da ganin alamu ko sallah bata tashi tayi ba.


Ganin haka ne yasa Mama ta juya ta fice daga ɗakin, ta nufi kichin inda ta iske Amatullah har ta gama dama kokon ta wanke tukunyar tana ƙoƙarin ɗora musu ɗumamen tuwon jiya.






A ɓangaren Ya Azeez da Abba kuwa koda suka fita sun daɗe tsaye a ƙofar gida suna tattaunawa akan abinda ya faru, inda Abba ke ta bawa Ya Azeez ɗin haƙuri akan abinda Mama tayi masa, da irin rashin mutuncin daya labarta masa Fadwan tai masa jiya, kana daga bisani sukayi sallama bayan Ya Azeez ɗin ya gaya masa cewa zai tafi Kano cikin satin nan domin cigaba da shirye shiryen tafiyarsu China, da kuma neman waɗanda zai wakilta acan ɗin domin su dinga kula mai da shagunan da Abban Kano ya bashi.


Sosai ran Abba yayi fari tas tas yaji gabaki ɗaya ɓacin ran da ya fito dashi ya kau, yay ta murna yana yi masa addu'a, kana daga haka kuma suka sake yin sallama ya shiga napep ɗinsa ya wuce, shi kuma Abban ya juya ya koma cikin gida, yayinda zuciyarsa ke cike da tsananin baƙin ciki da takaicin rasa nagartaccen miji irin Ya Azeez da ƴarsa Fadwa tayi, wanda kuma yake da tabbacin cewa nan bada jimawa ba ita da kanta sai tayi kukan rashinsa a rayuwarta.






Ya Azeez kuwa koda ya bar gidansu Fadwa direct gidan Ummansa ya wuce, sai dai kawai Umma ta gansa kwatsam, wanda koda Umma ta tambayesa lafiya ta ganshi da sassafe, bai ɓoye mata komai ba, ya kwashe komai da yake faruwa tun daga farko har ƙarshe ya gaya mata, sai dai ya ɓoye zagin da Fadwan tai ma iyayensa bai gaya mata ba.
Wanda kuma tunda take dashi yau ce rana ta farko data taɓa yarda har ta sauraresa ya kwashe duk abubuwan dake faruwa tsakaninsa da Fadwa ya labarta mata, dan a baya koda yazo mata da maganar tausarsa take tai ta lallashinsa tace yayi haƙuri Fadwan yarinya ce, ya ƙyaleta yarinta ke damunta wata rana zata bari.


Mamaki ya kama Umma sosai, dan bata taɓa zaton cewa Ya Azeez ɗin yana da haƙurin da zai iya jure duk wani rashin mutuncin Fadwa ba, shiyasa abun yayi matuƙar ɗaure mata kai.
Amma kuma duk da haka sai bata ji daɗin sakin da ya yiwa Fadwan ba, ko dan saboda mahaifinta, dan haka ta yanke shawarar anjima da yamma da kanta zataje gidan tayi bikonta ta dawo da ita ɗakinta.
Shi dai Ya Azeez jinta kawai yake, amma bai hanata ba, dan yasan koda ya hanata ɗin ma sai taje. Shiyasa kawai ya bita da Allah ya tsare, amma yasan kam da kamar wuya Maman Fadwa ta saurareta a yadda ta ɗauki zafin nan, ballantana har ta bar Fadwan ta dawo.










3:10pm


Mai napep ɗin daya ɗauko Umma daga gidanta ya ajiyeta a ƙofar gidansu Fadwa ta sauka, ta buɗe jakarta ta ɗauko kuɗinsa ta bashi, ya ƙarba ya bata canji, sannan ta juya kai tsaye tasa kai ta shige cikin gidan.


Dai-dai lokacin kuma Fadwa da Mama na zaune a tsakar gida kan tabarma, yayinda Mama ke bawa Fadwan labarin zuwan Ya Azeez da maganganun data gaggaya musu shida Abba, bata rage komai ba sai data kwashe tsaf ta gaya mata.
Dariya ta kama Fadwa tana cikin yi ne kuma Umma tayi sallama fuskarta ɗauke da murmushi ta shigo cikin gidan.


Cak Fadwa ta tsaida dariyar tata tana kwaɓe fuska lokaci ɗaya tana bin Umman da wani mugun kallo a wulaƙance kamar taga kashi.


Mama kuwa itama watsa mata wani ƙasƙantaccen kallon sama da ƙasa tayi a wulaƙance tana faɗin "Baiwar Allah lafiya kuwa zaki faɗowa mutane cikin gida haka kai tsaye, ba tare da neman izini ba..ko akwai wanda kike bi bashi ne a gidan da zaki diro mana haka kwatsam sai kace dirar yesu..?" Ta faɗa a wulaƙance tana mata wani ƙasƙantaccen kallon sama da ƙasa.


A sanyaye Umma ke kallonta kafin kuma ta ƙaƙaro murmushin yaƙe tace "Ayi haƙuri, amma nayi sallama sai dai in bakuji bane..." Ta faɗa tana ƙoƙarin zama a kusa da Fadwa da tayi saurin matsawa gefe tana watsa mata harara.


Kauda kai Mama tayi itama kafin tace "Ayya Allah sarki, to sannunki da zuwa fa, Allah kuma yasa dai lafiya..? Saboda irinku ba kasafai mutum ke buƙatar ganinku a gidansa ba..."


Ta faɗa tare da juyawa ta kalli Fadwa data juyar da kai can gefe guda tana harare harare tace "Kuɗina wai baki ga sarakuwarki tazo biko bane.? Tashi ki ɗebo mata ruwa mana tasha, dan da ganin alamu tashawo rana, dan yadda ake ƙwalla ranar nan kam nasan maƙoshi ya bushe sai an kora ruwa mai ɗan sanyi sanyi za'a samu salama..."


Asakarce Fadwa ta juyo ta kalleta kafin tace "Ina sarakuwar tawa take kuma Mama, ko har kin manta da cewa ɗanta ya sakeni ne yanzu zaman idda nake da kike dangantata dani...?"


Girgiza kai Mama tayi taja tsaki kafin tace "Oh ai na ɗauka zakiyi mata irin ɗan na mutunci nan ne, saboda zaman da kikayi da ɗanta na wata da watanni..."


Dariya ta ƙara ƙwacewa Fadwa tace "Kai Mama, sai kace wata wadda tayi zaman jin daɗi a gidan ɗan nata, da zan dinga wani ɓare ɓare akanta...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallon Umma a wulaƙance ta wutsiyar ido.


Ita dai Umma tsit kawai tayi a zaune kamar ruwa ya cinyeta, dan gaba ɗaya ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda tsananin kunyar wulaƙancin da Mama da Fadwa suka tasata agaba suke mata.


Wanda dama tun kafin ta taho sai da Ya Azeez ya gaya mata kuma ya sake jaddada mata dan yaso ma ya hanata amma sanin bazata hanun masa bane yasa kawai ya ƙyaleta ba dan yaso ba ta taho.
Amma bata taɓa zaton ko Fadwa zata iya mata haka ba ballantana kuma Mama karan kanta da take ganin tafi ƙarfin wulaƙanci a gurinta.


Haka sukai ta faɗan maganganu Umma dai na zaune tana jinsu amma babu wanda ta tankawa a cikinsu, har sai da suka gaji dan kansu sukayi shiru sannan Umma ta samu ƙwarin gwiwar bayyana musu abinda ya kawota gidan, nason a bata bikon Fadwa ta maida ita ɗakinta tunda Ya Azeez ɗin yace tun a daren jiyan da yayi sakin ya maidata ɗakinta.


Zaburowa Mama tayi cike da bala'i tana faɗin "Allah ya kyauta ƴata ta koma gidan ɗanki wallahi, ai tunda ya yarda ya saketa kuma ta bar wannan ƙaddararren auren nasa kenan har abada, banga abinda zai kuma maida ita wannan ƙasƙantacciyar rayuwar mara ƴanci ba, gida ne dai ta barshi kuma bari na har abada da ikon Allah dan banga mai mata dole ba ya maida ita, dan haka ku daina wani damun mutane da maganar kome kuna cewa ya maida ita dan bata maidu ba, atoh na gaya mikk..."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana harararta.


Galala Umma tayi tana kallon Mama data rufe ido tana ta zazzaga mata masifa kamar bata santa ba, Fadwa kuwa ta gefen ido take ta kallon Umman yayinda a ranta kuma take ta jin daɗin rashin mutuncin da Maman ke yiwa Umman kamar ta kurma ihu saboda tsananin murna da farin ciki.


Ɗago kai Umma tayi a hankali ta kalli Mama data wani haɗe rai tana harararta tace "Yanzu Maryama dan nazo bikon Fadwa sai ya zama abun tsiya da son tada zaune tsaye..? Tsakani da Allah duk waɗannan maganganun da kike faɗi kina ganin sun cancanta da ki gaya min..? Me nayi miki da zafi..? Aiko ni nasa AbdulAzeez ɗin ya saki Fadwa iya abinda zakiyi min kenan, amma ban san hawa ba bansan sauka ba daga zuwa abun arziki sai ya zama na tsiya...?"
Kai tsaye Mama tace "Na tsiya tsiya ma ya zama ba tsiya ba, nace na tsiya tsiya ya zama ba tsiya ba..." Ta faɗa a zafafe tana watsa mata harara.


Kaɗa kai kawai Umma tayi tana kallonta kafin tace "To shikenan Allah ya huci zuciyarku ya kuma baku haƙuri, amma ni bansan..."
Ɓata fuska Mama tayi kafin ta katseta da faɗin "Dan Allah nidai tashi ki tafi mun gode Allah ya saka da alkhairi, amma Fadwa dai bazata koma gidan wannan basamuden ɗan naki ba mara mutunci da bai san ciwon kansa ba..."


Da sauri Fadwa tace "Gaya mata dai Mama hanyar jirgi daban ta mota da daban wallahi, kowa kuma yaje yaji da kansa, amma ni kam bazan taɓa komawa gidan Ya Azeez ba, na barshi bari na har abada. Yaje can ya auri dai-dai shi ya cigaba da manejin rayuwarsa kamar yadda ya saba, amma ni ba komawa gidansa zanyi ba, dan daso samu ne ma daya ƙarashe tsige sauran igiyoyin sai kowa ya huta ko ya kikace Mama....?" Ta ƙarashe maganar hankali kwance tana kallon Mama.


Da sauri Maman ta gyaɗa mata kai tana faɗin "Sosai kuwa, dama kamar akan ƙaya muke duk mun ƙagara a samu masalaha, to yanzu kuma Allah ya kawo mana ai baza muyi wasa da damar mu ba...." Ta faɗa a wulaƙance lokaci ɗaya tana kallon Umman.


Umma bata mata magana ba illa kallon Fadwa da take yi kafin tace "Kiyi haƙuri da abinda yayan Imaan yayi miki kinji dan Allah, ba zai sake ba insha Allahu nayi masa faɗa...? Amma dan Allah na roƙeki ki koma ɗakin mijinki dan girman Allah..."
Jin haka yasa Mama sakin tsaki ta miƙe tsaye tana faɗin "Kinga dan Allah tashi tashi ki tafi, haba mata sai kace mayya, yarinya tace bazata koma gidan ɗanki ba bazata koma ba, amma kin wani ishisshire kin zauna kina neman matsa mata haka kawai sai kace ana kome dole..ina dalili..? Dan Allah tashi ki fitar mana a gida tun kafin raina ya ɓaci..." Ta ƙarashe maganar tare da nuna mata ƙofar fita.


Miƙewa Umma tayi a hankali ta ɗauki ƴar pos ɗinta ta riƙe a hannunta, kafin ta juya lokaci ɗaya tana faɗin "Toh Allah ya huci zuciyarku ya baku haƙuri na gode..." Ta faɗa tare dasa kai cikin sanyin jiki ta fice daga gidan.


Da ido Mama da Fadwa suka bita, kafin Maman ta rakata da ƙaton tsaki tana faɗin "Agayas dai Allah ya raka taki gona almunafunfun..."
































*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*








*Mum Khairy, Ummin Sauban, Aysher Umar Yaro, Maman Abba, Ummu Shuriem. Ina matuƙar jin daɗin sharhinku, kuna sakani nishaɗi sosai nagode matuƙa Allah ya saka muku da mafificin gidan aljanna fiddausi🤝*






3️⃣0️⃣




Koda Umma ta koma gida zaune tayi tana ta saƙe saƙe da tunanin abinda Fadwa da Mamanta sukai mata, sai a lokacin ne kuma take ƙara gasgata haƙuri da kawaicin da Ya Azeez yayi na zama da Fadwa har tsawon wannan lokacin, sai taji tsananin tausayin Ya Azeez ɗin ya ƙara kamata.
Sosai abun ya tsayan mata arai, sai dai ko Imaan bata sanarwa ba saboda bata son ta haddasa mata tsanarsu Maman da Fadwa aranta tazo ta dinga jin haushinsu.
Haka ta kwana da juyayin abun aranta, amma bata iya gayawa kowa ba.


Washegari da safe da suka tashi sai da ta bari Imaan ta gama shirin makaranta ta tafi, sannan ta samu zatafin kiran Ya Azeez ta sanar masa tana son ganinsa.
Ko cikakken awa ɗaya ba tayi ta kiransa ba kuwa, sai ga Ya Azeez ɗin ya iso gidan cikin gaggawa, koda ya shigo ya samu Umman zaune a tsakar gida ita kaɗai ta zafga uban tagumi da hannu bibbiyu tayi kasaƙe alamar tayi zurfi a cikin tunani.


Ganinta haka yasa jikinsa ƙara yin sanyi ya isa gabanta da sauri ya durƙusa cikin damuwa yana faɗin "Umma lafiya kuwa..meyake faruwa...?"
Murmushin yaƙe ta ƙaƙaro tana ƙara jin tausayin ɗan nata a ranta, kafin kuma ta ɗago tana nuna masa gurin zama akan tabarman dake shimfiɗe a tsakar gidan tace "Toh zauna mana ɗan gidan Umma..."
Da sauri ya zauna yana ƙara nazarinta kafin yace "Dan Allah Umma meyake faruwa ne, na ganki ba'a yadda na saba tarar dake ba, kuma tun kiran da kikayi min a waya yanayin muryarki kaɗai na gano akwai abinda yake faruwa, mene ne Umma...?" Ya faɗa cikin tsantsar tashin hankali yayinda kuma yake jin wani irin ɗaci aransa.


Nan Umma ta gyara zama ta zayyane masa komai ta kwashe tun daga farko har ƙarshe na abinda Fadwa da Mamanta sukayi mata ta gaya masa, bata rage komai ba, kuma bata ƙara musu komai ba.
Duk irin rashin mutuncin da sukayi mata sai data gaya masa, babu abinda ta ɓoye masa.


Aiko ba ƙaramin ɓaci ran Ya Azeez yay ba, jikinsa har wani irin tsuma ya ɗauka saboda tsabar baƙin ciki da ɓacin rai, mamaki ya kamasa ko kaɗan bai taɓa zaton Mama zata iya rufe ido ta yiwa Ummansa irin wannan wulaƙancin ba, dan har gwara Fadwa dama yasan zata aika har ma fiye da haka indai itace.


Sosai Ya Azeez ya jinjina al'amarin kuma ba domin komai ba, sai irin yadda suka iya kallon tsabar idanun Ummansa suka iya gaggaya mata maganganu masu zafi irin haka yaga ƙoƙarinsu sosai, amma bai ga laifin kowa ba, sai laifin kansa saboda shine yaja mata domin duk ta dalilinsa ne aka samu zarafin yi mata irin wannan cin mutuncin.
Ran Ya Azeez ya ɓaci ya dinga sauke numfashi, Umma tace "Dan Allah kar kasa abun a ranka yazo yana damunka, suma kuma nasan sharrin shaiɗan ne da ɓacin ran abinda akayi musu yasa suka aikata hakan, shiyasa banso ka saketa ba wallahi dan babu yadda zanyi da kai ne amma da ka ci gaba da haƙuri kamar yadda nake gaya maka da duk hakan bata faru ba..."


Cikin tsananin ɓacin rai Ya Azeez ya ɗago yana kallon Umma kafin yace "Amma nayi matuƙar mamakin Mama sosai wallahi, dan ni a uwa na ɗauketa ba matar ƙanin mahaifina ba, taya Mama zata iya rufe idanu su ci mutuncinki ita ƴarta wacce take a matsayin suruka agareki hakan bazai min zafi ba, wanda koda wasa ni bazan taɓa iya kwantanta yi mata hakan ba...?" Ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka, saboda baƙin ciki.


Ajiyar zuciya Umma ta sauke a hankali tana faɗin "Ka barsu kansu suka yiwa kuma insha Allahu sai sunji kunyar abinda suka aikata..."


Ƙasa yay da kai yana ƙara jin wani ɗaci a cikin ransa, Umma kuwa kawai runtse ido tayi tana girgiza kai, yayinda kuma take ƙara tausar Ya Azeez ɗin kan yayi haƙuri ya cire abun a zuciyarsa ya manta dashi.


Haka dai ya dinga ƙoƙarin yakice duk wani ɓacin ran da yake ji a zuciyarsa, ya nuna mata komai ya wuce, kafin ta tashi ta kawo masa abin karin kumallo, bayan ya gama karyawa ne kuma suka shiga hirar business ɗinta, wanda yanzu komai ya daɗa kankama dan babu abinda bata kawowa har su kayan kichin da sauran tarkacen kayan aikace aikacen gida, kome ka gaya mata kana so ko baka da kuɗi zata kawo maka ga kayanta da sauƙi, kuma bata zuwa ko'ina, duk mai so har gida ake biyota a siya.
Ya daɗe a gidan suna tattaunawa kana daga haka kuma suka gangaro kan zancen tafiyar Ya Azeez ɗin Kano jibi da zaiyi.
Bai bar gidan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login