Showing 48001 words to 51000 words out of 113443 words
ma numbern wani garjejen ƙaton ce ya karanto min ni kuma na kwashe, amma ai in da numbernsa ce da yanzu dana kira ya ɗauka ko....?" Cikin mamaki Shatu ke kallonta kafin tace "Wai numbern waye kike ta kira da yaƙi ɗauka ne haka duk kika damu...?" Ta faɗa tare da tsareta da ido tana kallonta.
Ɗan taɓe baki Zahra tayi kafin tace "Numbern mai keke napep ɗin mu na jiya mana...." Ta faɗa kai tsaye tana wani ɗauke kai. Wani sabon mamakin ne ya ƙara kama Shatu tace "Ban gane mai keke napep ɗin mu na jiya ba...kina nufin kice wanda ya kawo mu nan kika karɓi numbensa...oh daman da gaske kike karɓar numbern tasa kikayi Zahra....?"
Cikin ɓacin rai Tace "Eh mana dama ai nace miki zan karɓi numbernsa in kirasa yau yazo ya kaimu tasha mu shiga mota ko kin manta ne....?"
Wani kallon banza Shatun ta watsa mata tana faɗin "Amma shine dan iskanci da wulaƙanci ki rasa wayar da zaki karɓi numbernsa a ciki sai tawa...to ke ina taki wayar take da baki ƙarba a ciki kin kirasa ba....?" Ta faɗa cike da jin haushin kiransa da tayi da wayarta tana harararta.
Tura baki Zahra tayi ta ɗauke kai gefe kafin tace "Ai tawa tana can a kashe ne ta ɗauke shine na barota a mota...." A fusace ta miƙe tsaye ta fizge wayarta a hannunta tana faɗin "To bani tawa don ubanki sai kije ki nemo wacce zaki kira mai keke napep ɗin naki da ita..." Ta faɗa tana ƙoƙarin zura wayar a cikin jaka, da sauri Zahra ta miƙe ta riƙo hannunta tana marairaice fuska kamar zatayi kuka take faɗin "Please dan Allah Aunty Shatu ki bani in ƙara kiransa yazo ya kaimu tashan kinji...wallahi mutumin yana da kirki sosai kiga fa irin taimakon da yay mana jiya amma yaƙi karɓan ko sisin mu...?"
Harara ta watsa mata tana faɗin "Amma ai kina gani dai bani na hanasa karɓan kuɗin ba ko...? Shine yaga dama kawai yaƙi ƙarba don kansa ba nice na roƙesa ba...." Ta faɗa tana komawa ta zauna a bakin gadon, da sauri itama Zahran ta zauna a kusa da ita tana faɗin "Dan darajar iyayenki nidai ki kawo in sake kiransa kinji Aunty Shatuna...?"
Sake ɗaure fuska Shatu tayi kafin tace "Wai dan Allah ke wace irin yarinya ce mai shegen mita da rawar kan tsiya ne...Nace ni bazan bada wayata ba..bazan bada ba ko dole ne...?" Ta faɗa cikin ƙosawa tana watsa mata harara, zaro idanu waje Zahra tayi tana cewa "A'a ba dole bane Aunty Shatu riƙe wayarki Allah ya baki haƙuri..."
Ta faɗa tana matsawa can ƙarshen gadon ta zuba tagumi, da mamaki Shatu ta juyo ta kalleta kafin ta girgiza kai lokaci ɗaya tana buɗe jakarta ta zaro wayar ta wurga mata tana faɗin "Gashi nan sai kije ki ta kiransa mai shegen naci da rawar kan tsiya...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana jan tsaki kafin ta miƙe ta koma kan sofar dake ɗakin ta zauna ta zubo mata ido tana kallonta.
Cikin sauri Zahra ta ɗauki wayar ta lalubo numbern Ya Azeez ta sake danna masa kira a karo na shida.
Dai-dai lokacin shi kuma Ya Azeez fitowarsa daga ɗaki kenan cikin shirin fita, yau ɗin shigar ƙananan kaya ce yayi dan kusan duk ƴan kayan sawan nasa sunyi datti kuma gashi bai samu zama ba ballantana ya haɗa har da na Fadwa da yaga itama natan sun taru ya wanke musu, yana daga tsaye a ƙofar ɗakin ya gama ɓalle boturan gaban rigarsa lokaci ɗaya yana ƙoƙarin zura takalmansa wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ta ɗauki ƙara da sauri ya zarota yana duba mai kiran dan a tunaninsa ko Ummansa ce saboda kullum da sassafe idan ya tashi sai ya kirata sun gaisa yaji ya suka tashi kafin yake fita, amma yau saboda ya makara kuma gashi bai da kati ko na flashing a wayar shiyasa bai samu ya kiratan ba ya bari idan ya fita ya saka katin sai ya kirata.
Cikin mamaki yake kallon fuskar wayar tasa ganin ba Ummansa bace ke kira still dai special numbern da ake ta kiransa da ita ce tun ɗazu ya sake gani tana yawo akan wayar dan haka ya danna ya ɗauka ya kai kunnensa cikin sanyin muryarsa yana faɗin "Assalamu alaikum dawa nake magana pls...?" Ya faɗa tare da ɗan saurarawa cikin son ya gano muryar mai kiran nasa.
Daga can ɓangaren kuwa Zahra dake riƙe da wayar a hannunta ta danna handsfree da sauri ta ajiye wayar akan cinyarta tana faɗin "Waalaikums salamu..ina kwana an tashi lafiya...?" Jin yay shiru bai amsa ba, yasa ta juya ta kalli Shatu dake zaune har lokacin ta zubo mata ido ƙirr tana kallonta, cikin basarwa ta harareta a fakaice ta ɗauke kai tana cewa "Ka ganeni kuwa Malam...Zahra ce wacce motarsu ta lalace jiya da daddare ka taimaka musu ita da yayarta...?" Ta ƙarashe faɗa tana wani washe baki kamar tana ganinsa.
Daga ɗaya ɓangaren Ya Azeez ya buɗe idanuwansa sosai yana sakin ƙaramin murmushi kafin yace "Oh Allah sarki na ganeki ƴan mata, ya gajiyan tafiya ya kuma kwanan Kaduna...?" Ya faɗa gefe guda na zuciyarsa yana mamakin kansa da biye ma shirmenta da yake so yayi.
Ƴar dariya ta saki kafin tace "Ai dama nasan zaka ganeni da nayi magana saboda muryata bata taɓa ɓoyuwa..." Ta faɗa tare da juyawa ta saci kallon Shatu wacce ta kauda kai daga kallonta tana sakin tsakin takaici lokaci ɗaya tana ji kamar ta tashi taje ta rufeta da mugun duka dan baƙin ciki.
Ɗan yatsina fuskarta tayi tana taɓe baki kafin tace "Ga Auntyna ma tana gaisheka...tace ayi maka ban gajiya...mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana hararar gefen Shatun, a zabure Shatu ta miƙe tsaye tana zaro manyan idanuwanta waje tare da dafe ƙirjinta, kafin cikin sanyin muryarta tace "A gidan ubanki nace kiyi masa ban gajiya Zahra don uwarki...?" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana zafga mata harara, ko ajikinta bata damu ba ta ci gaba da faɗin "Yanzu ma ita tace in kiraka in gaya maka mun gama shiryawa kazo ka kaimu tasha dan Allah kar muyi dare a hanya..." Ta faɗa kai tsaye tana kallonta.
Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa wani irin mugun sanyi yaji a zuciyarsa lokacin da Zahra take cewa Auntynta tace a gaishesa ayi masa ban gajiya, take yaji wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarsa lokaci ɗaya ya samu kansa da sake maƙala wayar sosai a kunnensa kafin ya buɗe baki cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da daɗin saurare yana faɗin "Ok gani nan zuwa Zahra ku jirani yanzun nan zan ƙaraso insha Allahu...."
Ya faɗa daga haka ya yanke kiran yana kallon wayar kafin ya saki murmushi ya maida wayar cikin aljihun dake gaban rigarsa ya juya ya koma cikin ɗakin ya ajiyewa Fadwa dake ta sharar bacci ɗari biyar a kusa da ita, kana ya fito yasa kai ya fice daga gidan da sauri hannunsa riƙe da makullin keke napep ɗinsa.
A ɓangaren su Zahra kuwa Shatu na jin ya yanke wayar tayo kan Zahra dake ƙoƙarin aje wayar akan gado a fusace ta fizgota da ƙarfi ta miƙar da ita tsaye lokaci ɗaya tana watsa mata wani mugun kallo da idanuwanta wanda suka fara tara ƙwallar ɓacin rai take faɗin "Tsakaninki da Allah Zahra yaushe kikaji nace kiyi masa ban gajiya har da godiya...yanzu saboda Allah mutuncina kikeson ki zubar min a idanun wannan mutumin..meyasa kikeson haɗani dashi ne...Ke meyasa rawar kanki tayi yawa...? Wai haka kawai daga haɗuwa da mutum duk kinbi kin addabi kanki da rayuwarki sai wani shisshige masa kike kina neman zubarwa da kanki mutunci sannan hakan bai yi miki ba shine dole sai kin haɗa har dani nima kin zubar min da nawa mutuncin...? To wallahi ba kiji da kyau ba, dan ni ba ƴar iska bace da zaki dinga neman haukatani..." Ta ƙarashe maganar cikin fushi lokaci ɗaya tana tureta ta faɗa saman gadon.
Sakin baki kawai Zahra tayi daga kwancen tana kallonta kafin ta miƙe lokaci ɗaya tana gyara zaman gyalen dake kanta tana faɗin "Nidai ai ba wani abu nace akan ki ba gani nayi abun arziki yayi mana bana tsiya ba, kuma ni naga cancantar mu ƙara yi masa godiya ba shine zaiyi mana ba...amma tunda abun ya miki zafi to Allah ya baki haƙuri insha Allahu bazan sake ba...."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana matsar ƙwalla kamar gaske, dan tasan babu abinda Shatun ta tsana a rayuwarta irin ta ganta cikin damuwa balle har ta kaita ga zubar da hawaye, ballantana kuma idan itace ta ɓata mata rai yanzun nan zaka ga duk ta ruɗe ta hau lallashinta tana bata haƙuri. Saboda ita Allah ya yi ta da mugun son ƴar uwarta balle daya kasance Zahran ita kaɗai ce ƙanwarta dan su biyu ne kacal iyayensu suka haifa shiyasa gaba ɗaya ta ɗauki son duniya ta ɗaura mata.
Gaba ɗaya Shatu sai taji gwiwarta tayi mata sanyi cikin muryar lallashi tace "To me kuma nayi miki kawai daga miki faɗa sai ki hau kuka...to naji kiyi shiru na haƙura bari ya ƙaraso sai ya kaimu tashan kinji....?" Ta faɗa tana zama a kusa da ita ta kamota tana share mata hawayen fuskarta tana ƙara lallashinta da bata baki, itako Zahra sai ƙara narkewa take ajikinta tana ƙananun kuka duk ta gama ruɗata sai faman lallashinta take kamar wacce tayi mata wani ƙaton laifi.
*******
A ɓangaren Fadwa kuwa sai gurin ƙarfe 11am na safe sannan ta tashi daga bacci ta miƙe da sauri ta lalubo wayarta dake ajiye a gefen filo ta latsa, misscalls ta gani rututu daga ƙawayenta daban daban akan screen ɗin wayar da sauri ta miƙe bayan ta ajiye wayar ta sauka daga kan gadon ba tare data da tabi ko takan kuɗin da Ya Azeez ya ajiye mata a gefen gadon ba ta ja tsaki lokaci ɗaya tana sakin hamma alamar baccin bai isheta ba, ta hau cire kayan jikinta ta jawo zani ta ɗaura kana ta ɗebi ruwa a bokiti ta fice da sauri zuwa banɗaki.
Agurguje tayo wanka ta fito sannan ta ɗebi ruwa a buta ta ɗauro alwala, sai da tayi sallah kana ta hau shiryawa cikin wata irin shadda gezner mai ruwan toka ɗinkin riga da siket, sai ɗaurin Zahra Buhari data cokashi ta tsikarosa gaban goshi, fuskarta ba wata kwalliya sai hoda kaɗan data ɗan shafa ta saka kwalli da janbaki, ko gyalen bata tsaya yafawa ba ta sagalashi a gefen kafaɗarta ta ɗauki jakarta da wayarta ba tare da tunanin komai ba tasa kai ta fice daga ɗakin.
Yau ma bata tsaya kulle ɗakin ba ta jawo ƙofar kawai ta sakaya ta fice daga gidan tana taku ɗai ɗai kamar yadda ta saba, amma kallo ɗaya idan kayi mata zaka fahimci cewa bata da wata damuwa ko kaɗan a ranta.
******* *******
Koda ya isa hotel ɗin ya daɗe a harabar gurin amma ya kasa kiran layin da Zahran ta kirasa dashi, sai da yaga yana ɓatawa kansa lokaci ne kawai a banza, yasa yayi shahada ya zaro wayarsa ya danna numbern data kirasa da ita ɗazu, ba ɓata lokaci ta ɗaga haɗe da yin sallama, cikin sanyin muryarsa ya amsa mata kafin yace "Idan kun shirya ku fito ina jiran ku a waje...." Ya faɗa daga haka kawai ya yanke wayar.
Cikin murna Zahra ta miƙe tsaye ta kama hannun Shatu dake zaune har lokacin a kusa da ita tana faɗin "Tashi muje Aunty Shatu kinji ya ƙaraso yana waje...." Ta faɗa tana jan akwatinsu ta kama hanyar ficewa daga ɗakin tana ci gaba da faɗin "Dan Allah ki taso muje kar mu tsaidashi yay ta zaman jiranmu kinga ba daɗi...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarasa ficewa daga ɗakin.
A sanyaye Shatun itama ta miƙe tabi bayanta suka fice tare, suna fita tun daga nesa ya zuba mata ido, ganin yadda take tafiya cikin natsuwa dole ya ɗauki hankalinka, sosai ya shagala da kallonta har suka ƙaraso bakin napep ɗin bai sani ba, sai da suka shiga suka zauna sannan Zahra ta ɗan zuro da kanta ta gefensa ta kallesa da kyau kafin tace "Allah yasa dai ba tunanin budurwarka kake yi ba har muka ƙaraso baka sani ba...." Ta faɗa tana kallon gefen fuskarsa inda lallausan baƙin gashi ya kwanta yay luf luf gwanin sha'awa, ajiyar zuciya ya sauke cike da kunya kafin ya waigo ya ɗan saci kallon Shatu data duƙar da kanta tana latsa wayarta dake hannunta yace "Barkanku da ƙarasowa to Hajiya Zahra...." Ya faɗa yana kallon Shatu da har lokacin kanta ke duƙe taƙi ɗagowa ta kallesa.
Ƴar dariya Zahra tayi kafin tace "Yauwa Ya....uhmm Ya wama zance....?" Ta faɗa cike da tsokana tana kallon Shatu, banza da ita tayi bata tanka mata ba sai ma ci gaba da tayi da latsa wayarta tana harararta ta gefen ido.
Cikin wani irin yanayi ya kalleta kafin yace "Cikakken sunana AbdulAzeez Naseer Abdallah Arabi...amma matata da ƙanwata Imaan suna kirana da Ya Azeez....Ummana kuma tana kirana da Yayan Imaan...kinga kema sai ki zaɓi suna ɗaya da zaki dinga kirana dashi a ciki...." Ya faɗa a hankali yana ƙoƙarin tada napep ɗin, da sauri Zahra ta kallesa kafin ta juya ta kalli Shatu data wani haɗe rai tace "Kai amma gaskiya sunanka yayi daɗi sosai, amma ni daga yau Ya Abdul zanna dinga kiranka dashi...ko Aunty Shatu ai yafi daɗi....?"
A hankali ta ɗago ta saci kallonsa, karaf kuwa ƙwayar idanuwansu suka haɗu waje guda, rass gabanta ya buga ta juya da sauri cikin rashin abun yi ta hau gyara wuyan rigar abayar dake jikinta, kafin ta ɗago lokacin har sun fara tafiya ya fice daga cikin hotel ɗin ya ɗauki hanyar tashar Kawo, ta ɗan kamo gefen rigar Zahra ta jawota, da sauri Zahran ta kalleta ta ɗaga mata gira kafin ta saki wani ƙaramin murmushi tana harararta tace "Taɓ amma Aunty Shatu gas..." Da sauri ta katseta ta hanyar toshe mata baki tana zaro manyan fararen idanuwanta waje kamar zasu faɗo ƙasa.
Hakan yasa Zahran taja bakinta ta tsuke tayi tsit har suka ƙaraso babbar tashar Kawon bata sake magana ba, shi kuwa duk abinda sukeyi yana kallonsu ta madubin napep ɗin daya saita yana ta murmusawa abinsa amma bai tanka musu ba, haka har suka ƙarasa cikin tashar.
Shatar sharon suka ɗauka tun daga nan har Kano daga ita sai ƙanwarta su biyu kaɗai ta biyasu kuɗin, yana nan sai da yaga tashinsu kana ya juya ya shiga keke napep ɗinsa shima yaja ya fice daga tashar.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣0️⃣
*KANO STATE*
Ƙarfe 2pm. Dai-dai suka shigo garin Kanon dabo, inda direct mai motar ya nufi tsararriyar unguwar ta Nasarawa GRA dasu, kamar Zahra dake zaune a bayan motar kusa da Shatu tai ta kwatanta masa.
Bakin wani tafkeken haɗaɗɗen gida na gani na faɗa, mai ɗauke da tangamemen gate na kece raini suka yada zango.
Inda direban yana yin parking suka buɗe ƙofofin motar suka fito, bayan sun sallami direban Zahra ta buɗe boot ɗin motar ta ɗauko akwatinsu, kana shi kuma direban yaja motar ya wuce.
A hankali su kuma suka ƙarasa bakin gate ɗin gidan suna isa Zahra ta ƙwanƙwasa ba jimawa sai ga wani farin dattijo ɗan kyakkyawa dashi wanda da gani kasan maigadi ne yazo ya buɗe musu ƙaramar ƙofar yana ganinsu ya washe baki cike da farin ciki yana yi musu maraba, cikin fara'a duk suka amsa masa kana suka shige ciki.
Wani lafiyayyen ginin gida ne na kece raini kamar a turai, harabar gidan shaƙe take da haɗaɗɗun motoci kala daban daban wasu duk suna rufe an lulluɓesu da tampol yayinda wasu kuma suke a buɗe sai ɗaukar ido suke suna sheƙin sabunta, ga wasu manyan manyan bishiyoyin ya'yan itatuwa dogaye masu kyau da tsari sun kewaye gidan, ga wasu fulawowi suma kala daban daban da aka ƙayata jikin ginin gidan dasu sai ɗaukar ido suke sunyi shar gwanin sha'awa.
Suna gab da shiga ɗan koridon da zai sadasu da babban falon gidan ne, Shatu taja ta tsaya tana kallon Zahra data wuce da sauri zata shige ta tari gabanta tana watsa mata harara tace "Naga kina ta wani rawar jiki kin ƙosa ki shiga kije ki kai rahoto ko...? To saura idan mun shiga ki cewa Ummi ni na matsa nace mu tafi Abuja jiya, dan nasan halinki wannan shegen bakin naki kamar na Parrot yake wallahi idan ki ka ƙulla min sharri sai kin san sauran..." Ta faɗa tana fizge wayarta dake hannun Zahran lokaci ɗaya tana ƙara haɗe fuskarta.
Kallonta Zahra tayi sama da ƙasa tana faɗin "Haba mana Aunty Shatu wai dan Allah me kika maidani ne...? Nifa babu abinda zan gayawa Ummi kuma mu shiga kiji idan zan gaya mata wata magana Allah kuwa...." Ta faɗa tare da kamo hannunta tana cewa "Muje Aunty Shatuna wallahi bazan ce komai ba, tsit zanyi da bakina..."
Ɗago kai Shatun tayi ta galla mata harara tana cewa "Ai nasan halinki ne indai kece tsaf zaki zame jikinki ki ɗora min laifin duka ki barni a ciki..." Ɗan murmushi Zahra tayi ta kalleta kafin tace "Babu abinda zance na rantse kuma muje kiji..."
Wucewa tayi ba tare data sake magana ba ta nufi ƙofar da zata sadata da makeken falon gidan Zahran na biye da ita a baya.
Makeken ƙaton falo ne haɗaɗɗe na gani a bada labari wanda aka tsarashi iya tsaruwa fiye da tunanin mai tunani, ga wasu manya manyan luntsuma luntsuman kujeru masu girma da taushi na alfarma da aka kewaye falon dasu, sai wani tattausan kafet mai tsananin laushi da nutse ƙafafu da aka malale falon dashi tun daga bakin ƙofar shigowa har zuwa cikin tsakiyar falon ya mamaye ko'ina. Gefe guda kuma ga wani sassanyan ƙamshin turaren wuta mai bala'in daɗi daya gauraya da sanyin Acn dake tashi a falon yana yi maka maraba, sai ya haɗu ya bada wani daddaɗan ƙamshi mai sanyaya rai da tsayawa a zuciya.
Cikin natsuwa dukkansu suka shigo falon bakinsu ɗauke da sallama, Babu kowa a falon sai wani tangamemen talabijin da yake maƙale a jikin bango yana ta