Showing 105001 words to 108000 words out of 113443 words
hankali cikin murya ƙasa ƙasa sosai ya fara karanto addu'ar saduwa da iyali, kafin tayi wani yunƙurin ceton kanta tuni taji har ya ɗauki hanyarsa cikin hikima da tausasawa, kana kuma a hankali ya ƙara saka bakinsa cikin kunnenta a sanyaye ya soma hura mata iskar bakinsa a kunnenta dan ƙara son ɗauke hankalinta.
A hankali ya ƙara gyarawa ya buɗe ƙafafuwanta da kyau, kafin ya sake yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa ya cigaba da neman hanyarsa.
Ɗiff tayi tana saurarensa, kafin ta ware idanuwanta da suke a lumshe ta sauke a kansa a hankali tace "Wayyooo Allahna zafiii..."
Ko bakinta bata gama rufewa ba ya ƙara ƙanƙameta ya mata riƙo irin na ƙam ƙam ɗin nan, wanda bazaka iya ƙwatar kanka ba, kafin ya ƙara daidaitawa da ƙarfinsa cikin dabara ya samu da ƙyar ya shiga.
Ihuuu ta saki da ƙarfi tana faɗin "Dan Allah Ya Abdul na tuba wallahi zafi kasheni zakayi..."
Bakinsu ya haɗe yaci gaba da neman hanyarsa har yayi nasarar shiga gaba ɗaya da ƙyar yana haɗa zufa.
Duk zantuka da ihun da take bai jinta balle ya tausaya mata, abunka kuma da an daɗe ba'a haɗu ba, ga kuma gyaran da tasha.
Cikin natsuwa da wata irin gigitar da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba tunda yake, sosai yake jin wata irin natsuwa da tasha bambam da irin wacce ya saba ji a lokutan baya, tabbas yaji bambanci sosai wanda bai taɓa jin irinsa ba.
Ita kuwa Shatu kuka kawai take tana jin tamkar yana yanka mata naman jikinta ne.
Shi kuwa ko kaɗan baya jinta banda sambatu da kwasar gara ba abinda yake lokaci mai tsayi ya ɗauka yana juyata yadda ransa yake so kafin ya samu natsuwa ya dawo hayyacinsa.
Zuwa lokacin kuwa Shatu tuni ko motsin kirki bata iya yi, hawaye kawai yake tsiyaya a idanunta.
Mirginawa yay gefe yana sauke numfarfashi a jere a jere, kafin ya lumshe idanunsa yana faɗin "Allah ya miki albarka na yafe miki duk wani laifi da zakiyi min a duniya, da wanda na sani da wanda ban sani ba daga nan har mu koma ga Allah..na gode na gode Allah yayi miki kyakkyawan sakamako da gidan aljanna fiddausi..."
Ya ƙarashe maganar yana buɗe lumsassun idanuwansa ya rungumeta sosai a jikinsa, ganin hawaye suna gangarowa ta gefe da gefen idanunta ne yasa ya ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta wanda sukayi jajir saboda tsabar kukan azabar da tasha.
Cikin rawar murya yace "Wayyo nine ko...?"
Kai Shatu ta ɗaga cikin shasheƙar kuka kafin tace "Ya Abdul ruwa zansha ƙishi nake ji..." Ta faɗa cikin wata iriyar murya mai cike da rauni.
Jikinsa na rawa yace "Ina zuwa..."
Ya miƙe da sauri ya sauko daga saman gadon ya ɗauki gajeren wandonsa da sauri ya saka, sannan ya shiga toilet ya haɗa ruwa mai zafi, kana yazo ya ɗauketa cak yaje ya sakata acikin ruwan.
Kuka ta Saki tana rirriƙe hannunsa.
"Kiyi haƙuri bari na kawo miki ruwan kisha..."
Kai ta jinjina tana ciza laɓɓanta.
Cikin rawar jiki ya fito, sai a lokacin ne kuma idanunsa suka sauka a saman zanin gadon wanda yake fari tass amma yanzu ya ɗan ɓaci da jini kaɗan.
Cikin sauri ya ciresa ya ɗauko wani ya shimfiɗa musu, kana ya naɗe wannan ya koma cikin toilet ɗin ya saka a kwandon wanki, kana ya fito ya sake ficewa daga bedroom ɗin ya sauka ƙasa.
Robar ruwan da ya siyo jiya ya ɗauko ya dawo ya tsugunna a gabanta lokaci ɗaya ya tallafo kanta ya manna mata robar ruwan a bakinta.
Cikin rawar jiki kuwa ta buɗe bakin ta hau kwankwaɗa tana sauke ajiyar zuciya.
Sosai kuwa tasha ruwan fiye da rabi.
Cikin tsananin tausayawa da kulawa da kuma nuna tsantsar so da ƙaunarta yay mata wanka haɗe dana tsarki, kana ya naɗota a towel kamar wata ƴar baby yazo ya shiryata tsaf ya kwantar da ita, kana ya manna mata kiss a saman laɓɓanta yace "Ina matuƙar sonki da ƙaunarki Eishatuna, ina zuwa bari inyi wanka nazo kinji..."
Bata dai ce mai komai ba, sai turo baki gaba da tayi tana wani lumshe idanunta.
Murmushi yay kana ya juya ya koma cikin toilet ɗin, wankan tsarki yayi ya fito ya shafa mai a gurguje kana ya shirya cikin wasu sababbin kayan bacci farare masu taushi da kyau ya fesa turare, ya kashe wuta ya haye saman gadon ya kwanta lokaci ɗaya ya rungumota jikinsa yaja bargo ya lulluɓesu.
Lamoo tayi ajikinsa, tana ji yana mata wasu daɗaɗan zantukan soyayya, a haka har wani daddaɗan bacci ya dauketa.
Shima daga baya baccin yay cike da nutsuwa yana jin a ransa ba namijin da ya kaisa dace da samun macen data haɗa komai kota ko'ina irin Eishatunsa.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
3️⃣7️⃣
Dai-dai lokacin kuma Fadwa na kwance akan ƴar yaloluwar katifarta.
Sosai ta gaji tana son tai bacci amma gaba ɗaya tunanin duniya yayi mata rufdugu ya cunkushe mata zuciya, wanda hakan yasa ta rasa sukuni, sai juyi take tana sakin tsakin takaici, ga kukan sauro duk ya addabeta a ɗakin sai faman cizonta suke kota ko'ina, ta rasa inda zata tsoma ranta taji sanyi.
A zafafe ya turo ƙofar ɗakin ya shigo kamar an jefosa, direct inda take ya nufa kai tsaye ya haye saman katifar, kwanciya yayi ya rungumota jikinsa, bai yi wata wata ba kuwa ya hau shasshafata kamar wani mayunwacin zaki yana yi yana wani ƙara ƙanƙameta a jikinsa.
Cikin tsananin tashin hankali Fadwa ta zabura lokaci ɗaya tana janye jikinta tace "Dan Allah na roƙeƙa ka barni in huta na gaji wallahi na gaji, gaba ɗaya jikina ciwo yake min, bana jin daɗin komai, dan Allah ka barni inji da guda ɗaya..."
Cikin wata mayaudariyar murya yace "Kiyi haƙuri ɗan kaɗan zanyi kawai bazan takura ki ba..."
Da sauri tace "A'a nidai dan Allah Ya'u ka ƙyaleni, wallahi bazan iya ba idan kace zakayi mutuwa zanyi na roƙeƙa ka ƙyaleni ba dan halina ba..."
Ganin idan ya tsaya roƙonta ɓata masa lokaci zatayi, yasa ya jawota da ƙarfi a zafafe ya fara fizge kayan jikinta kamar mahaukaci.
Kokawa suka fara ganin da gaske take bata so ya kusanceta ne yasa ya ɗauketa da mari, kana ya matseta da ƙarfin tsiya bayan ya fizge kayan jikinta ya fara biyawa kansa buƙata cikin tsantsar rashin tausayi da imani, yana yi kuma yana zagin mahaifiyarta babu ko kunya balle tausayi.
Sosai Fadwa ke rizgar kuka kamar ranta zai fita wanda duk rashin tausayi da imaninka idan kaji yadda take kukan a wannan lokacin dole saika ji tausayinta, dan kuka ne da take yi da dukkanin zuciyarta, wanda kuma yake fitowa tun daga can ƙasan zuciyarta mai cike da rauni da tsantsar tausayin kanta.
Sosai ya ɗauki dogon lokaci a kanta yana aikin abu ɗaya, kafin ya sauka ya koma gefe yana sauke numfarfashi, Fadwa kuwa rakuɓewa tayi gefe guda tana kuka mai cike da rauni da tsantsar tausayin kanta da rayuwarta.
Bayan shuɗewar wasu mintuna a tsakani kuma ya sake wawurota cikin tsantsar rashin tausayi ya ƙara haike mata, wannan karon ba tayi masa musu ba ta buɗe masa ƙafafu.
Saboda tasan halinsa kota nuna bata so ɗin ba ƙyaleta zaiyi ba, ƙarshe ma sai dai yayi mata rashin mutunci sannan kuma yayi bata isa ta hanasa ba.
Dan haka ta ƙyalesa ta zuba masa ido, ya gama bidirinsa ya sauka.
Tashi tayi da ƙyar tana dafa bango, zaninta daya yasar a ƙasa ta jawo ta ɗaura kana ta ɗauki buta tana tafiya da ƙyar tana buɗe ƙafafunta a haka ta samu ta fice daga cikin ɗakin ta nufin banɗaki.
Tana shiga banɗakin kuwa ta zame ƙasa a hankali ta jingina da jikin bango lokaci ɗaya tana sakin wani maraitaccen kuka mai cike da rauni da tsantsar nadama da tausayawa kai gwanin ban tausayi.
Kuka take sosai kamar zata siƙe gaba ɗaya duniyar tayi mata duhu, tunda take bata taɓa tunanin koda wasa zata iya tsintar kanta a irin wannan rayuwar da take ciki a yanzu ba.
Tabbas tasan ta aikata babban kuskure a baya, domin kuwa Allah yayi mata ni'imomi masu tarin yawa a rayuwarta amma bata gode masa ba, shiyasa duk iya tarin dukiyarka indai baka da wadatar zuciya bazaka taɓa ganin yawan arzikinka ba sai dai ka hangi na wani, a baya tana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali lokacin da take gidan Ya Azeez, amma saboda rashin wadatar zucci irin nata sai ta dinga hange waɗanda suka fita, a ƙarshe ga yadda rayuwa ta maida ita.
Yanzu ido rufe take fatan dama ace rayuwar ta baya ta dawo da ta gyara kuskurenta, amma ina tasan bakin alƙalami tuni ya riga daya bushe, amma duk da hakan zata gwada sa'arta saboda tasan Ya Azeez akwaisa da tausayi kila zai dubeta a karo na biyu idan ta nuna masa tayi nadama ya maida ita ɗakinta, dan ba zata iya zama a cikin wannan ƙasƙantacciyar rayuwar ba, insha Allahu sai tasan yadda tayi ta kashe wannan ƙaddararren masifaffen auren ta koma gidan mijinta na asali mai sonta da ƙaunarta tsakani da Allah, saboda yanzu ta gano kuskurenta kuma da ikon Allah zata gyara.
A haka tai wankan tsarki ta tsarkake jikinta, tana wannan tunanin bayan ta gama ta fito ta koma ɗaki.
Lokacin kuwa tuni Ya'u ya daɗe da yin bacci sai sakin munshari yake, dan haka itama tana shiga ɗakin kawai riga ta saka ta haye katifa ta kwanta tana ci gaba da tunanin neman mafita a ranta.
A haka itama baccin ya ɗauketa mai cike da mafarkin rayuwarta a gidan Ya Azeez.
**********
Acan ɓangaren su Eishatu da Habibyn ta kuwa.
Da asuba ma da ƙyar tai sallah, sai kukan sangarta take masa tana faɗin bayanta da cinyoyinta duk ciwo suke mata, gaba ɗaya ta addabesa da rigimarta, motsi kaɗan sai ta fashe masa da kuka tana zafi cinyoyinta ƙirjinta da bayanta kuma kamar zasu rabe gida biyu, duk ta gigitasa da koke kokenta kamar wata ƙaramar yarinya.
Shiko sai lallashinta yake yana lalaɓata, ganin ta kasa sakin jikinta ne yasa yaji tausayinta ya ƙara kamashi, ya jawota jikinsa ya rungumeta yana lallashinta da kalamai masu daɗi da sanyaya rai.
Abincin da Mami ta aiko musu ma bata wani ci na kirki ba, sai tea daya haɗa mata shima kaɗan tasha tace ta ƙoshi.
Haka ya lalace a gurinta yana ta lalaɓata bini bini kuma yace suje toilet ya gasata, tun tana nonnoƙewa kuwa har ta saki jikinta, shiko ya zage ya dinga gasa mata jiki yana ƙara tarairayarta yana lalaɓata tamkar kwai, ko kaɗan bai son ya matsa daga kusa da ita, duk inda take yana nan naniƙe da ita.
Kusan wunin ranar kuwa haka suka kusan cinyesa tana ta zuba mai shagwaɓa da sangarta kala kala.
Bai bar gidan ba sai gab da la'asar shima saboda mutanen dake zuwa ganin amarya ne, duk wanda ya ganta kuwa sai yasan tasha kuka domin gaba ɗaya fuskarta da idanuwanta sun nuna, dan ma baƙin duk ƴan uwanta ne, sai Imaan da ƙannen Abban Ya Azeez ɗin ƴan Babura, sai yamma liƙis sannan suka tafi, aka barta dasu Basma da Husna.
Kamar kuwa dama jira take baƙin su tafi, ta fashe da kuka ta hau labarta masu Basma irin muguntar da Ya Azeez yay mata daren jiya.
Nan fa Basma ta hau tsokanarta tana ta mata dariya, itako Husna gaba ɗaya tausayin ƙawar tata ne ya lulluɓeta, yayinda kuma lokaci guda taji tsoron auren ya cika mata zuciya, wanda har sai da taji kamar tace ta fasa, dan ma tana ganin Suhail ɗinta mai haƙuri ne bai da matsala, tasan zai ɗaga mata ƙafa idan anyi auren.
Suna gidan tare da ita har bayan sallar magriba, bayan sunyi sallah ne kuma Basma ta ƙara bata shawarwari kan yadda zata kula da mijinta ta tarairayesa sannan ta ƙara da karfafa mata gwiwa kan tattali da jure duk wasu buƙatunsa.
Kafin daga bisani kuma sukayi mata sallama tayo musu rakiya suka tafi kana ta koma cikin gida.
Basu daɗe da tafiya ba kuwa shima ya dawo, tana jin motsin shigowarsa ta miƙe da sauri tana yi masa barka da zuwa.
Ƙarasowa yayi kusa da ita ya zauna a saman kujera ya jawota jikinsa ya ɗorata akan cinyarsa.
"Bari in kawo maka ruwa..."
Ta faɗa kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
Girgiza mata kai yayi alamar a'a, kana ya ƙara kwantar da kanta a jikinsa ya rungumeta.
Sun jima a haka tana rungume a jikinsa, kafin ya ɗagota yana kallon kyakkyawar fuskarta dake fitar da wani annurin kyau na musamman, kana ya miƙe da ita a hannunsa suka haura sama zuwa bedroom ɗinsu.
Wani irin mummunan faɗuwar gaba taji lokacin daya direta a saman lafiyayyen gadonsu da sauri ta tashi zaune tana gyara rigar leshin dake jikinta, kafin ta ɗago ta kallesa ganin kuma yana tuɓe kayan jikinsa ne yasa ta saukowa daga saman gadon, kai tsaye ta nufi ƙofa da sauri zata fice, cikin zafin nama yayi taku ɗaya ana biyu ya riƙota ya ɗagata cak ya nufi toilet da ita.
Duk noƙe noƙenta kuwa haka ta haƙura tana ji tana gani ya cire mata kayan jikinta tas yayi mata wanka da kansa, kana ta ɗauro alwalar sallar isha'i da ta jiyo ana kira ta fito, sannan shima yay nasa wankan ya ɗauro alwalan ya fito.
Duk a tsorace take dashi, shiyasa suna idar da sallar isha'in ta haye gado ta kwanta ta ƙudundune a cikin bargo ta juya masa baya.
Ganin take takenta ne kuma yasa koda ya hau gadon shima bai taɓata ba, ba dan kuma baya buƙata ba, sai dan kawai yana tausayinta.
Itako Shatu a nata ɓangaren gani take wayau kawai yake mata so yake sai tayi bacci sannan ya lallaɓa ya sake maimaitawa, dan haka ko baccin kirki ba tayi ba, sai can cikin dare kafin wani daɗaɗan bacci mai masifar daɗi ya kwasheta.
Haka suka kwana bai mata komai ba har gari ya waye, tun daga nan ta ɗan ji sanyi a ranta, har ta saki jikinta, ta ci abincin da Zahra ta kawo musu washegari da safe.
Sosai ta saki jiki taci ta ƙoshi abinta, suna gamawa ya goge mata baki kana ya riƙe hannunta suka dawo cikin falo ya zauna, kana ya zaunar da ita a kusa dashi.
A hankali ta ɗaga kai ta kallesa ganin shima ita yake kallo yasa ta sunkuyar da kanta da sauri tana murmushi.
Sake ɗago kanta yayi ya matso da ita kusa dashi yana faɗin "Ina matuƙar sonki da ƙaunarki Eishatuna..."
Murmushi tai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Shafa bayanta yayi yana murmushin shima, kafin ya ɗagota yana tsura mata idanu yace "Allah yayi miki albarka, yasa mu rayu tare har ƙarshen rayuwar mu..mai daɗina..."
Ya faɗa a kunnenta cikin raɗa yana ƙara ƙanƙameta.
Ranar wuni sukayi tun safe har dare yana naniƙe da ita kamar wanda akace za'a ƙwace masa ita, wanda kuma ko toilet zata shiga tare suke shiga, bai yarda ta matsa ko nan da nan.
A hankali a hankali yanayin ya fara bin jikinta, kafin sati ya kai idan zata zauna sai dai a kusa dashi ko akan cinyarsa, haka a wajen bacci sai ya ƙanƙameta sannan yake iya runtsawa.
Wanda kuma zuwa lokacin tuni ta gama sabawa da yanayinsa, tun tana ɗan jin zafi sama sama har ta dawo yanzu bata jin komai sai daɗi, dan haka ta ƙara sakewa dashi sosai ta saki jikinta.
Bayan sati ɗaya ya canza mata sabon layi ya canza mata waya, ya saka mata numbern Umma data Imaan.
Aiko tun da ya bata numbern kusan kullum da safe sai ta kira Umman sun gaisa, haka Imaan itama koda yaushe sai sunyi waya da ita.
Satinta biyu a gidan kuma Ya Azeez ya ɗauketa daddare ya kaita gidansu Fahad ta gaishe da Mami da Abba.
Nasiha sosai Mami tai mata, haka Abba shima yayi mata nasiha sosai sannan yace ta bi mijinta sau da ƙafa.
Daga nan kuma direct sashen Fahad kuma suka shiga, inda suka daɗe suna hira da Basma wacce Shatu tai mamaki sosai da ta ganta da ciki wanda har ya fara girma ya fito sosai, dan ya kai kusan wata huɗu zuwa biyar, amma bata taɓa lura ba.
Nan ma sun daɗe, da suka tashi tafiya kuma Basma ta bata turarukan humra masu ƙamshi da sinadari tace ta dinga amfani dasu.
Sai wajen ƙarfe 11pm. Suka baro gidan inda kuma a hanya suna tafiya yake sanar da ita cewa cikin satin da za'a shiga zasu Kaduna su gaishe dasu Umma.
Wanda saboda tsabar murna bata san sanda ta ruƙunƙumesa ta sakar mai zazzafan kiss a laɓɓansa ba.
Washegari kuma gidansu ya kaita da kansa ta wuni inda Ummi tai ta nan nan da ita tana riritata, abinci kuwa an dafa mata ya kai kusan kala biyar idan taci wannan sai taci wannan.
Ganin haka kuma yasa Zahra tace itama zata gayawa Abba ta gaji da karatun a fitar mata da miji tayi aurenta itama ta huta taji abinda ake ji.
Dan tunda taga yadda Aunty Shatun ta tai wani irin fresh ta ƙara kyau sosai tasan ba ƙaramin daɗi take ji a gurin Ya Abdul ɗinta ba, dan haka itama auren nan zatayi hankalinta kwance ta huta abunta.
Shatu da Ummi sukayi ta mata dariya, inda kuma anan Ummi ta dinga yiwa Shatun nasihar kula da miji da irin abubuwan da ya kamata ta dinga yi masa da wanda basu kamata ba.
Sosai Shatu ta ƙaru da abubuwa da dama a gurin Ummi, wanda har ji tayi ta ƙosa Ya Azeez ɗinta yazo ya ɗauketa suje gida ta fara gwada masa abubuwan da Ummin ta koyar da ita a ranar.
Sai dare sannan Ya Azeez ɗin yazo gidan ya ɗauketa suka koma gida.
A ranar kuwa Shatu kusan zautar da Ya Azeez tayi da salonta, domin gaba ɗaya susuce mata yayi ya dinga sambatu da sakin layi yana saka mata albarka.
Itama kuma sosai taji daɗin yanayin duk da tasha wuya sosai a hannunsa, amma haka nan ta daure ta gwada masa jarumtarta, hakan kuwa shima sosai yanayin yayi masa daɗi, ya kuma sa ya ƙara ganin kima da mutuncinta na ƙara hauhawa a idanunsa.
Bayan Sati Biyu
Zaune suke a falo ya kanainayeta a jikinsa tana ta zuba mai shagwaɓa, hannunsa ya zura cikin rigarta yana shafar cikinta a hankali yana faɗin "Ina ne yake zafin..nan ne..ko nan...?" Ya faɗa cikin wani irin yanayi yana shafo ƙasan mararta haɗi da ɗan dannawa kaɗan.
Saurin riƙe hannunsa tayi tana faɗin "Wayyo Habiby akwai zafiiii..."
Ta faɗa cikin sangarta tana janye hannunsa daga gurin.
Kumatunta yaja a