Showing 81001 words to 84000 words out of 113443 words

Chapter 28 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7572

Alhaji ka jini da wannan masifaffiyar yarinyar dan Allah, na rasa meyasa gabaki ɗaya halinta ya fita daban dana sauran mutane, kaji kuma wai auren ne take jin haushin dan ance zatayi...?"


Kallon Shatun Abbie yayi kafin yace "Uwata zancen auren ne yanzu baki so yasa kike wannan haƙilo da tada jijiyoyin wuyan..?"


A shagwaɓe Shatu tace "Inaso mana Abbie amma nifa ko saurayi bani dashi ne, kuma shine zata wani dinga yi min zancen aure alhalin tasan cewa ko mai zuwa gurina bani dashi, taya zanyi aure a haka...?" Ta ƙarashe maganar a sanyaye tana hararar Zahran.


Da hanzari Ummi tace "Ai bakiso auren bane, amma ai ko Suhaib ɗin Baffanku Buba yaso ku daidaita kece kika ƙi masa daɗin hannu, ki kai ta botsarewa kina zille zille. Gashi nan har ya samu mata yayi aurensa har da ƴaƴansa biyu abinsa, ke ko kina nan jaɓe in banda son girman tsiya babu abinda kika iya..."


Abbie kuwa murmusawa kawai yayi yana gyaɗa kai, kafin ya dubi Shatu yace "Kina dai son auren ko Mamana...?"


Da sauri ta gyaɗa mai kai tana faɗin "Eh Abbie inaso, Amma sai na samu mijin tukunna ko...?" Ta faɗa a hankali tare kuma da rufe fuskarta da hannuwanta alamar jin kunya.


Idanu Abbien ya ɗan tsura mata, kana kuma cikin nazari yace "Allah ya zaɓa maku abinda yafi zama alkhairi a rayuwarku baki ɗaya..."


Da Ameen duk suka amsa kana kuma daga haka Abbien yasa kai ya fice daga falon, yayinda kuma Ummi ta rufa masa baya domin yi mai rakiya zai wuce kasuwa.




********






*BAYAN SATI BIYU*




Yau ɗin ta kama Asabar ba makaranta, wanda kuma tun ƙarfe 10am. Dai-dai Shatu ta tashi daga baccin data sake komawa tun bayan sallar asuba.


A hankali ta tashi zaune ta zuro ƙafafuwanta ƙasa kafin kuma ta miƙe tsaye lokaci ɗaya ta sauko daga saman gadon kai tsaye ta wuce toilet.


Koda ta fito mai kawai ta ɗan shafa a jikinta, ba tare kuma da ko hoda ta kalla ba ballantana tayi tunanin shafawa fuskarta ba, ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinta ta zaro wata rantsatstsiyar ɓaƙar abaya, mai tsananin kyau da taushi ta zura a jikinta.
Sosai kuwa rigar tai mata mugun kyau a jikinta ta fito das gwanin sha'awa.
Sassanyan turarenta ta fesa a jikinta, kana ta yana gyalen rigar a kanta, ba tare kuma data tsaya komai ba ta ɗauki wayarta tasa kai ta fice daga ɗakin.


Tana sako kai kuwa ƙofar ɗakin suka kusan cinkaro da Zahra data taho da sauri zata shigo cikin ɗakin.


Jada baya da sauri Zahran tayi tana dubanta sama da ƙasa, kafin ta saki murmushi tace "Kai Masha Allah My Aunty kinga yadda kikayi wani masifaffen kyau kuwa..? Gaskiya kin haɗu ba ƙarya wallahi..."


Murmushi Shatu tayi ta kalleta kafin tace "Toh faɗi ba'a tambayeki ba, ni matsa ki bani guri in wuce..."


Ta faɗa tare da raɓawa ta gefenta zata fice daga ɗakin, ajiyar zuciya Zahran ta sauke tana faɗin "Aiko ni fa Abbie yayi yace in kiraki ki samesa a falonsa..." Ta faɗa a hankali tana ɗan turo bakinta, kai kawai Shatun ta jinjina ba tare kuma da tace komai ba ta sauka ta nufi falon Abbien.




Koda ta isa falon kuwa Abbie kaɗai ta samu zaune a saman kujera yana kallon TV, bayan ta durƙusa ta sake gaishesa ne kuma ya nuna mata gurin zama, ɗan nesa kaɗan dashi ta matsa ta zauna a saman kafet ɗin dake falon.


Tsawon mituna goma ta kwashe a zaune shiru, kanta a sunkuye ba tare da Abbie yayi mata magana ba, yayinda kuma falon ya ɗauki shiru babu motsin komai a ciki, dan tun lokacin data shigo ya ɗauki remote ya rage ƙarar volume ɗin Tvn yayi ƙasa dashi sosai, ta yadda ba zai damesu ba.


Jin shirun tayi yawa ne kuma yasa ta ɗago kai a hankali da nufin ta kalli Abbien taga me yake yi, wanda take ganin kamar mantawa yayi da tana zaune ne yasa bai ce komai ba.


Ɗago kan nata kuwa yayi dai-dai ne da ɗagowar da Abbie yayi lokaci ɗaya yana gyara zamansa cikin tsantsar dattako da nuna manyantaka yana faɗin "Gyara zamanki da kyau Mamana, magana nake so zanyi dake mai matuƙar mahimmanci wanda kuma nakeso ki natsu da kyau ki saurareni...."


Da sauri ta ɗaga kai ta kallesa, kafin kuma lokaci ɗaya ta gyara zamanta da kyau tana fuskantarsa.


"Aishatu...." Abbie ya kira sunanta cikin sanyin murya mai cike da son bada umarni.
A hankali ta amsa kana lokaci ɗaya ta ɗago tana kallonsa, sakamakon kiran sunanta da yayi sak ba tare da wani sakaye ba kamar yadda ya saba mata, wanda kuma tun tasowarta bata taɓa jin ya kira koda wata mai irin sunanta bane kai tsaye kasancewar sunan mahaifiyarsa gareta sai dai yace Mamana ko uwata, ballantana ita da tun tana ƙarama ta gama sabawa da kiranta da yake da uwata, amma yau sakamakon kiran sunanta da yayi dangas sai abun yazo mata a wani irin yanayi na daban.


Gyara zamansa yayi a hankali, kana kuma cikin sanyin murya da nuna tsantsar kulawa yace "Inaso ki natsu da kyau kiji abinda zan gaya miki, sannan duk abinda zan gaya miki inaso ki natsu da kyau kuma ki bani gamsashshiyar amsa wadda zata gamsar dani..."


A hankali ta gyaɗa mai kai kafin kuma cikin sanyin jiki tace "Insha Allahu Abbie..."


Jinjina kansa Abbie ɗin yayi, kafin kuma yace "Kin dai san aurene ya haifeki ko..? Kuma duk wata ɗiya mace mai cikar kamala burinta shine aure...? Amma ke meyasa baki so ko maganar auren ayi miki....?"


Rass rasss haka gaban Shatu yayi wani mugun bugawa, runtse idanunta tayi a hankali yayinda take jin yadda gaba ɗaya jikinta yake son ɗaukar rawa.


Abbie kuwa maida hankalinsa yayi gabaki ɗaya kanta ya zuba mata idanu ƙirr yana kallonta cikin nazartar yanayinta.
Sakin murmushi yayi kafin ya ƙara tsura mata idanu yana faɗin "Ina saurarenki..."
Ya faɗa kai tsaye yana kallonta.


Saurin girgiza mai kai Shatu tayi lokaci ɗaya tana ƙoƙarin haɗiye wani kakkauran yawun daya daskare mata akan harshe, kafin kuma a hankali ta tattaro jarumta cikin in ina tace "A'a Abbie...ba..ba haka bane..bani da saurayi ne kuma ma ni kwata kwata ban taɓa..yin wani saurayi ba shiyasa...." Tai maganar a rarrabe tana sunkuyar da kanta.


Ɗan guntun murmushi Abbie yayi tare da gyara zamansa kafin yace "Amma kinsan cewa dole wata rana komin daren daɗewa zakiyi aure tunda ba haka zan ta zuba miki idanu ina kallonki a cikin gida kina jera kafaɗa da kafaɗa da mahaifiyarki kuna kaiwa da kawowa a tare kanku ɗaya ina kallonku ba ko Mamana...?"


A sanyaye Shatu ta sake gyaɗa mai kai tana jin taruwar wasu hawaye a idanunta tace "Zanyi insha Allahu Abbie ku tayani da addu'a Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi..." Ta faɗa lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta da zuciyarta na mata wani irin bugu da take jin zuciyar tata kamar zata fasa ƙirjinta ta fito waje.


Da Ameen ya Allah Abbie ya amsa mata kana ya ɗora da faɗin "Insha Allahu kuwa kyakkyawan zaɓi mafi alkhairi Allah zaiyi muku, tashi kije in kin fita ki turo min Ummin ku..Allah yayi muku albarka yasa a gama lafiya..."


Ya faɗa cikin tsantsar kulawa da dattako.
A hankali Shatu ta miƙe lokaci ɗaya tana ƙara rusunawa tace "Na gode Abbie Allah ya ƙara girma da nisan kwana..." Ta faɗa tare da juyawa tasa kai ta fice daga falon.




Tana fita kuwa ba jimawa Ummi ta turo ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Yanayin yadda taga Abbien nata sakin murmushi ne kuma yasa ta sakin wani lallausan murmushin itama, kafin ta ƙaraso ta zauna a kusa dashi tana kallonsa.


Gyara zama Abbie yayi yana fuskantarta kafin ya soma zayyano bata duk yadda sukayi da Shatu, kamar yadda Ummin da kanta ta bashi shawarar ya titsiyeta ya tambayeta ta fito da miji, sosai mamaki ya kama Ummi dan ita har ga Allah tana burin taga auren babbar ƴar tata, shiyasa duk ta ƙosa taga ta gama makaranta ko taji anyi sallamar neman aurenta saboda ita duk a tunaninta karatun da Shatun ke yi ne yake hanata saurarar samari.


Fatan samun na gari tayi mata, kafin daga haka suka cigaba da tattaunawa akan yanayin karatun Shatun.


































*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
*WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






3️⃣2️⃣






A ɓangaren su Ya Azeez kuwa yau kimanin watansu biyu kenan cif a ƙasar China.
Wanda kuma zuwa lokacin tuni har sun kammala siyan dukkan abinda ya kai su ƙasar, inda kuma wani abokin kasuwancin Abba Mr Yuang da Abban ya haɗasu dashi ne wanda asalinsa ɗan ƙasar Chinan ne, shi ya dinga yi musu jagoranci yana kaisu kamfanonin da suke siyan nagartattun motocin da suke shigowa dasu ƙasar ta Nigeria.


Sai da suka kwashe watanni biyu cif har da kwana goma a ƙasar, wanda zuwa lokacin kuma tuni kayansu sun jima da isa ƙasar Nigeria.
Inda kayan sun isa ne da kwana biyu suma suka fara shirin dawowa gida.


Ƙarfe 5pm. dai-dai na yammacin yau ɗin ne kuma jirginsu ya ɗaya zuwa gida Nigeria.




*BAYAN SATI BIYU*


Yau kimanin sati biyu kenan da dawowarsu, wanda kuma zuwa yanzu komai na tafiya dai-dai musamman ta ɓangaren shagunan Ya Azeez ɗin da gidan motocin su, dan zuwa yanzu kam an gama tsara komai da komai lokaci kaɗan gidan motocin nasu zai fara aiki.


Sai da sukayi sati huɗu cif da dawowa gida sannan suka buɗe gidan motocin wanda kafin kace me har sun fara samun jama'a kota ina.
Bayan sun zuba ma'aikata ne kuma da masu kula da gurin da dukkan wani ciniki dake shiga da fita, wanda tuni dama shi Fahad Abba yasa ya barwa Ya Azeez garamar kula da komai na gurin a matsayin manaja, murna sosai Ya Azeez ɗin yayi ya dinga yiwa Fahad da Abba godiya har da kwallarsa.


Haka Umma da Ya Azeez ɗin ya kirata ya gaya mata sai data zo har Kano tai ma Abban godiya, kafin Ya Azeez ɗin da Fahad suka ɗauketa a danƙareriyar sabuwar motar da Abban ya siyawa Ya Azeez ɗin ƙirar Mazda CX-30 fara sol suka kaita har kamfanin motocin da shagunan Ya Azeez ɗin dake cikin kasuwa ta gani, kafin ta kwana washegari Abba yasa direbansa ya maida ita Kaduna.






Alhamdulillahi Ya Azeez ya fara kasuwancinsa da ƙafar dama, kuma komai yana tafiya dai-dai akan tsari, dan zuwa yanzu hatta da Umma Ya Azeez yanzu ya huttasheta bata zuwa kasuwa, shi ke tura mata da kaya ta mota har Kaduna.


Kafin kace me dan da nan Ya Azeez ya canza lokaci guda yay wani irin kyau na musamman har da ƴar ƙiba ya ƙara, ga kuɗi nata shigo masa kota ina, basu rufe wata uku da fara harkar kasuwancin su ba abubuwan alkhairi suka soma shigo masa kota ko ina, Allah ya sakawa kasuwancinsa albarka dan da nan shagunansa suka yi fice a faɗin kasuwannin, wanda kasancewarsa kuma mutum mai taimako da rangwame akan kayansa yasa dan da nan sunansa yayi fice a garin Kano, wanda bama ga ƴan kasuwa kaɗai ba hatta da kamfaninsu na siyar da motoci komai tuni Allah ya sakawa nemansu nasibi.




Abu na farko kuwa da Ya Azeez ya fara yi da abubuwa suka fara warware masa shine taimakon danginsa, yan uwan Abbansa dana Ummansa tamkar yadda mahaifinsa yayi lokacin da yake raye, wanda a tashin farko Babura ya fara zuwa kai tsaye yaje yay musu sha tara ta arziki, inda daga nan kuma yasa aka neman mai babban shagon saida zannuwa a Chechenia Market dake garin Kaduna, ya zubawa Abban Fadwa kaya kama daga kan less, atamfa, shaddoji da yadikan maza dana mata, sai abayoyin mata, da jallabiyoyin maza.
Sai daya cika masa shagon taf da kaya sannan ya mallaka masa ƙaramar mota ƙirar Camry domin zirga zirgar yau da kullum ta zuwa kasuwa da dawowa.


Lokacin da motar ta isa ga Abban Fadwa kuwa yayi matuƙar murna sosai da farin ciki, dan har ƙwalla sai da ya zubar saboda tsantsar farin ciki da jin daɗi.


Yau kwanan motar biyar kenan da kawota amma koda wasa Abba bai taɓa gayawa Mama ba, sai dai kullum da safe idan zai tafi kasuwa yaje gidan wani Alhaji dake nan ƙasan layinsu ya ɗauki motar ya tafi, haka idan ya dawo da yamma ma sai yaje ya kaita gidan ajiya sannan yake takowa da ƙafa yazo gida, shiyasa har yau Mama da Fadwa basu taɓa sanin wani sauyi da Abban ya samu ba, ballantana har su san halin da yake ciki, wanda su har yau a tunaninsu faci yake.
Dan kullum cefanen da ya saba shigowa dashi gidan har yau haka yake musu babu abinda ya canza, sai dai tun bayan da Fadwa ta dawo gidan har yau basu ƙara cin tuwo ba, dan koda ya kawo garin tuwon da kayan miya basa amfani dashi sai dai su ajiye.


A haka rayuwa tai ta tafiya, yayinda kuma zuwa yanzu ɗan kuɗin da Fadwa ke samu tana kashewa take kuma badawa ayo musu cefane su yi cima mai daɗi sun fara ƙarewa, dan ta kai yanzu tunda taga kuɗin sun fara ƙarewa, kullum da sassafe zata shirya ta caɓa uban kwalliya ta fita abunta kai tsaye babu abinda ya dameta, idan ta fita kuma bata taɓa dawowa gidan sai dare kuma kullum idan zata dawo da manyan ledoji cike da kayan ciye ciye take shigowa gidan.
Amma koda wasa Mama bata taɓa tambayarta a inda take samosu ba, sai dai kullum idan ta kawo jiki na rawa tasa hannu ta karɓe tana washe baki suyi kasafi su raba su ci abunsu suyi hani'an babu abinda ya damesu.


Ana cikin haka wata ranar juma'a da daddare Fadwa ta dawo daga gidan bikin ƙanwar ƙawarta Hajiya Zalika wanda aka yi anan Kaduna.
Tana zaune a tsakar gida ita da Mama dasu Ilham da Amatullah da suka ɓararraje suna ta ciye ciyen abubuwan da aka raba a gurin bikin da tazo musu dashi, lokaci ɗaya kuma tana basu labarin yadda manyan mutane masu ji da kuɗi da kansu suka halarci taron bikin.
Suna cikin haka wani almajiri yayi sallama yace ana sallama da Fadwa a ƙofar gida.


Da sauri Mama ta yafito yaron tana washe baki tace "Kai waye ya aikoka...?"


Yaron yace "Wani Alhaji mai mota ne yana ƙofar gida..." Ko kafin yaron ya ƙarasa Mama ta miƙe da rawar jiki tana kabbara tace "Allahu Akbar! Yaro maza jeka kace tana zuwa yanzun nan..." Ta faɗa cikin zallar farin ciki tana bin bayan yaron har zuwa zauren gidan.


Laɓewa tayi a bayan ƙofa tana leƙa ƙofar gidan, ganin wata tsaleliyar ɓaƙar mota ƙirar Benz da tayi ne fake a ƙofar gidan yasa ta juyowa da sauri jiki na rawa ta koma cikin gidan tana kwalla kiran sunan Fadwa dake cikin ɗakin tana ƙoƙarin canza kaya, da sauri ta fito tana faɗin "Gani nan Mama..."


Cikin rawar jiki da tarin farin ciki Mama tace "Lallai yau kinyi gam da katar ƴar albarka, wallahi ba kiga tsaleliyar motar da yazo a cikinta ba. Yi ki shirya ki fito yana jiranki, kar kuma ya gaji da jira ya tafi..." Ta faɗa da sauri tare da faɗawa cikin ɗakin ta ɗauko turare ta hau feshe mata jiki dashi sama da ƙasa, sai data gama mata ruwan turare a jikinta sannan ta ɗauko wani ɗan siririn gyalen daya shiga da rigar leshin dake jikinta ta sagala mata a gefen kafaɗarta.


Ɗan ja da baya tayi da sauri tana ƙara ƙare mata kallon sama da ƙasa, kafin ta jinjina kai tare da ɗaga mata babban yatsa tace "Komai yayi maza jeki. Adawo lafiya..."
Ta faɗa tare da kama hannunta suka fice daga gidan, suna zuwa zaure ta sakin hannunta tace "Allah ya tsare adawo lafiya..."
Ta faɗa tana komawa bayan ƙofa ta laɓe tana leƙensu.


Cikin wani irin takun yanga Fadwa ta ƙarasa gurin motar ta tsaya, lokaci ɗaya tana ƙarewa motar kallo cike da ɗokin son ganin mamallakin motar.


A hankali ya buɗe motar ya fito cikin isa da ginshira yake ƙare mata kallon tsaf, kafin ya ɗan saki wani malalacin murmushi yace "Ya akayi ne Baby..?Ƙaraso mana..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa.


Ƙarasowa gaban motar tayi ta tsaya tana jin kamar ta daka tsalle dan murna da farin ciki.
Ɗan karkace kai tayi gefe, kafin kuma cikin iyayi tace "Ina yini yallaɓai...?"
Ta faɗa da rawar jiki tana ɗan rusunawa.
Jingina yayi da jikin motar yana kallonta sama da ƙasa kafin yace "Fadwa ko...?"


Ya faɗa a hankali yana ɗan sakin murmushi, kaɗa kai tayi kafin cikin ƙaƙalo wata siririyar murya tace "Eh yallaɓai nice..sunan kenan..."


Murmushi mutumin yayi kafin ya ɗan kalleta yana faɗin "Ok ni kuma sunana Muhammad Al'ameen Zailani kuma nine shugaban majalisa ta Kaduna, kuma na ganki ne a gurin bikin abokina Alhaji Hannafi Mamadi da akayi yau, bari dai in barki haka kar in cika ki da surutu, in ba damuwa inaso ayi min iso zan shiga in gaida Mama..."


Mama kuwa dake laɓe ta kaso kunne, jin abinda yace yasa ta juyawa cikin gidan da gudu ta faɗa ɗaki ta ɗauko wata sabuwar darduma wacce ko Abba bai taɓa ganinta ba ta shimfiɗa a ƙofar ɗakinta, bayan ta kori Ilham da Amatullah tace duk shige ɗaki ta koma ta canjo hijabin jikinta ta dawo ta zauna a gefen darduman tana jiran shigowar su.


Ganin shigowar Fadwan ita kaɗai ne kuma yasa ta ɗaure fuska ta kalleta tana faɗin "Ya haka kuma, ina baƙon yake...?"


Ta faɗa tana kallon bayanta, wani irin faɗowa jikinta Fadwa tayi tana faɗin "Mama kinsan waye kuwa...?"


Girgiza mata kai Mama tayi tana faɗin "Ai da gani ma ba sai an faɗa ba dama wannan mutumin shine irin mijin daya cancanci mallakarki Fadwa, shine irin mutumin da muke ta dakon jiran zuwansa tun tuni, sai gashi yau ɓagatatan Allah ya jefo mana shi, dan haka maza jeki shigo mana dashi ɗan albarkan..."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana katseta daga abinda take shirin gaya mata.


Miƙewa Fadwan tayi da sauri ta juya ta ta fice daga cikin gidan.


Ba jimawa kuwa sai gasu sun shigo cikin gidan, yana biye da ita a baya suka ƙaraso har gaban Mama dake ta faman yage baki tana mai barka da zuwa cike da tsantsar murna da farin ciki.


Matsawa yayi ya zauna ɗan nesa kaɗan da Mama akan darduman, suka gaisa kafin ya gabatar mata da kansa, inda tunda ya fara maganar Mama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login